ASHE ZAMUGA JUNA

Author :  MRS ISHAM Category :  Love

Chapter   21 / 33

60K to 63K   out of 97.2K words

nan".kallon su ɗaya bayan ɗaya ya yi sun bashi tausayi,idon sa ne ya sauka akan Sabriyah da ke kneel down din rakube ajikin bangon dakin,ita kam tsabar wahala ko idonta bata iya budewa.

Lamarin LTG ya bashi mamaki yanzu har da wacce yake bincike akanta din ya saka kneel down din bayan su Umaisha ne suka mishi laifi(Ni Ko araina na ce ai kai Sahil kawai kayi shuru ba kasan komai ba,ita Sabriyah ce ya fara kamawa!hhhhhhh).

Shigowa sukayi dakin banda LTG dake zaune abin sa a palour.

Rike kugu Sudais ya yi duk da baya wani wasa da su sosai saboda a cewarsa basa jin magana.kwashewa da dariyar mugunta ya yi yana binsu da kallo musamman da idonsa ya sauka akan Umaisha da ta marairace fuska tana kallonsa, maimakon ta bashi tausayi amma se ma sake basa dariya ta yi.

"Ba kun ce bakwa jin magana ba!ai ko nine na kuskura naji ko da labarine kunje part dina bincike to abinda LTG ya muku kadan ne". hararansa Sahil ya yi "yanzu Sudais dan Allah basu baka tausaya ba?, shine zaka wani tsaya kana dariya jibi yanda suka galabaita"dage kafadunsa ya yi alamar i don't care.

"Ka duba har da Sabriyah fa da ba wani biye musu takeyi ba"Sahil ya sa'ke magana yana musu nuni da Sabriyah dake gefen su.

A tare Salim da Sudais suka kalli inda Sabriyah take,zaro manyan idanunsu waje suka yi cike da mamaki Salim ya ce "yanzu tsabar iskanci irin naku se da kuka jawa yarinyar nan!?,nasan de Wallahi babu ruwanta".

Zoya dake fama da kanta tana kuka ta ce"ya Salim ita ce fa,ya samu tana mishi bincike"mugun kallo ya watsa mata saboda be yarda da abinda ta faɗa ba.

"Karya kikeyi Zoya da bansan rashin jin ku bane!".

Kamar zata yi kuka ta ce "shikenan ai"

Wajenta yaje ya taimaka mata ta zauna. duk zaunar da su sukayi.

Rameesa da Umaisha ko magana basa iyayi sede binsu da kallo da suke yi ,yau LTG yabasu a jikinsu.

"To yanzu ke Umaisha tashi ki wuce part din ku"Sudais ya yi maganar fuska babu alamun wasa.

Marairaicewa ta yi kamar zata yi kuka"ya Sudais Wallahi ƙafata sun yi tsami,bazan iya tafiya ba"kamar zata yi kuka ta ƙarishe maganar.

Hararanta ya yi ya ce"to ina ruwana?,ku de ba rashin ji ba?".

Shigowa dakin ya yi, ya tsaya daga jikin kofar ya harde hannunsa a kirji.

Salim ne ya kallesa "LTG a yi musu afuwa bazasu karaba"

"Su bar mini part kafin in canza ra'ayi"

Dariya sukayi dukkansu mazan banda shi LTG din.

Sahil ne yasa hannu ya daga Parsa,dakyar ta iya mikewa ta rike shi gam tana cize libs dinta saboda azaba.

Taimaka mata ya yi,ya kaita har part dinsu ya ajiye ta akan gado sannan ya koma.

Mikawa Sabriyah hannu Salim ya yi yanaso ya taimaka mata.

"Ban gama da ita ba ku barta anan ita".

Kallonsa sukayi jin abinda ya faɗa.

"Haba LTG wannan fa bakuwarmu ce,dan Allah kabarta haka".Sudais ya yi maganar yana kallon shi.

kamar wanda yake magana da gini haka LTG ya sharesa be kulasa ba,ganin haka da Sudais ya yi yasan baze bar Sabriyah din ba.

Wajen Zoya Salim ya je yana hararanta ya dauketa can kuma ya fashe da dariya"ƙaramar mara kunya,yau kinci Sa'a ba dan tausayin da kika bani ba ko kallon ki bazanyi ba".

Ita de batace komai ba Allah _allah takeyi ya fitar da ita daga part din,suna kokarin fita Sahil ya shigo.

Ɗaukan Rameesa ya yi da se" wayyo Allah! Abbie ƙafafuna sundena aiki" "za ki mini shuru ne ko se na sauke ki!?"shuru ta yi dan tasan karamin aikin Sahil ne yabarta agurin.

Kwashe su sukayi a wajen ya yi saura daga Sabriyah se Umaisha, Sudais kam ma waje ya samu ya zauna suna magana da LTG.

Gasu Sahil da Salim tunda suka dauki Rameesa, Iklas, Parsa, Zoya bazasu ƙara dawowa ba.

Tagumi Umaisha ta yi tana hawaye zaman da tayi dinma kwata_kwata be mata dadi ba rabin hips dinta ya gaji,kallon Sabriyah da ta jingina kanta da jikin gini idanunta a rufe kamar me bacci,ta yi sannan ta maida kallonta kan LTG da Sudais da suke magana.

Fashewa ta yi da kukan takaici ganin sauran yan uwanta duk an kwashe su saura ita,tunda Sabriyah LTG kam ya ce be sallame ta ba.

Ta kasan ido Sudais ya kalleta yaga yanda take kuka bil haƙƙi, murmushi ya yi.

"Kukan me kike wa mutane"ya tambaye ta yana tsare ta da ido.

Tsinkayar Muryar sa da tayi yasa ta dago suka haɗa ido,irin kallon da taga yana mata ne yasa ta sunkuyar da kai,ta riga da tasan inde Sudais ne ze dauketa to zatayi shekara a haka.

Ji ta yi an dagata sama a tsorace take kokarin sa ihu ta ji,muryarsa"shiiiiii!be quiet"tunda take bata taɓa kawowa a ranta yau ya Sudais ze taimaka mata ba, saboda yadda yake cin zalinta da kuma mata faɗa, babban abinda ya fara haɗa su shine rashin saka dan kwali.

Zubawa kyakkyawar fuskarsa ido Umaisha ta yi tana kallonsa.

Har ya kaita part din su bata dena kallon da take mai ba,kallon cikin nata idon ya yi kafin yaci gaba da tafiya. bedroom dinsu ya shiga, duk sun baze akan gado suna kwance ko wacce se ya mutsa fuska suke yi masoyiya Parsa kam tana toilet ta yi wanka ta tsaya danna ƙafafunta da ruwan zafi.

Sauketa akan gadon ya yi,shi bayan dariyar da suka bashi har da haushi.

Kallonsu daya bayan daya ya yi,"meyasa kuka ja punishment din ya shafi Sabriyah,ku bakwa martaba bako ne?".

Rameesa mikewa zaune ta yi, ta ce"ya Sudais Wallahi Sabriyah bata da laifi duk mu muka ja mata"nan ta fara bashi labarin abinda ya faru.

Girgiza kai Sudais ya yi"Allah ya shirye ku to, in kuma ba zaku shiryu ba jikin ku ze dinga faɗa muku"ya fice a dakin .

Fitowa daga wanka Parsa ta yi taji dadin jikinta ba kamar dazun ba da komai wahala yake mata.

"Da wannan kwanciyar da kukayi da wanka kuka rufawa kanku asiri ku kayi se kun fi samun salama"

"Shawara me kyau masoyiya bari in yi kawai"Rameesa tana magana ta yi shigewarta toilet.

Daga shi se ita ne a bedroom din nasa tana a yanda take , jingine da bango idanunta har time bata bude su ba.

"Ka sato ni ka kawo ni gidan ku da sunan bincike,na nuna maka bansan akan abinda kuke tuhuma na dashi ba,shin menene kake so wanda zan maka ka mayar dani in da nake in nemo yar uwata!?, Asmita ita ce farin cikin rayuwata bana iya komai seda ita haka itama nice komai dinta,ka faɗamin meyeeeeee..... Kake bukata a wajena nagaji da rayuwa awannan kurkukun"ta gama maganar da karfi Muryarta cike da kunci da damuwa.

"Memory card din wajanki za ki ban daga nan kuma zan kyaleki ki tafi duk inda kika gadama".ya faɗa yana danna wayarsa.

Rarrafowa gabanshi ta yi,da alamar tambaya ta soma cewa"shin in na baka memory card din zaka kyaleni!?,kuma zaka tabbatar da ka cika burin Barrister Lameer kamar yanda ya buƙata!?"ta yi masa tambayoyi biyu a lokaci daya tana kallon cute face dinsa.

Gyada mata kai ya yi "kwarai kuwa".

Da sauri tasa hannu a cikin rigar roba body hood dake jikinta ta ja zip din breziyar ta fito da memory.

Zuba mata ido ya yi ganin tasa hannu acikin kirjinta,be sa'ke mamaki ba se da yaga ta fito da memory a ciki.

Mika mishi ta yi,ya tsina fuska ya yi kamar wanda yaga kashi ya ce"baki da hankali! ki fito da abu a brest dinki sannan kice in karba?,wait!meye ma zesa kisaka shi a cikin nan!?",ya tambayeta yana nuna dede kan tula_tulanta.

Yau badan bata cikin mood din masifa ba,yau da se yasha maganganu masu zafi a wajenta saboda abinda ya yi ya bata mata rai,ita da ko wani na miji yake mararin jikinta,kowa yana mararin taba wa'yannan tsayayyun tula_tular amma shi yanda yake nuni dasu kamar wanda yaga wani abun ƙyamar.

Amma duk da hakan se da tabashi amsa da"nono na ne zan iya ajiye duk wani abinda na gadama akai ga memory din in ka gadama ka karba".

Sosai ya girgiza jin yanda ta kira sunan brest ba tare da kunya ko kuma kawaici ba,hakan ya sa'ke tabbatar mishi da yarinyar nan cikekkiyar yar hau ce.be yi kasa a guiwa ba wajen cewa"ko kadan banyi mamakin jin haka daga gare ki ba domin karuwai basa da kunya da kamun kai".

Ko a jikinta da maganar da ya faɗa,ko mutum ze shekara yana kiranta da karuwa tofa hakan baya damunta tunda tasan eh ita karuwar ce,kuma wacce take da cikakken lasisi.

Hanky chef ya dauka yasa a hannunsa, kafin ya iya karbar memory card din.

"Za ki iya tafiya"

Bata tanka masa ba ta mike tana cizan libs dinta ta fice masa a part.

Kai kanta toilet ta yi,ta gasa jikinta da ruwan zafi nan taji dadi.ko lotion bata shafa ba ta saka wata karamar riga ta kwanta.

Shigowa dakin Rameesa ta yi tazo dubawa ko Sabriyah din ta dawo,ko kuwa LTG har yanzu yana rike da ita.nan ta sameta baje akan gado.

"Sabriyah yana ganki a kwance!?"ta yi mata tambaya tana shigowa dakin,dago kai tayi ta je fa mata uwar harara kafin ta bata amsa "da a tsaye kikeso ki gan ni!?"ta tambaye ta tana maida kanta ta kwanta.

Dama Rameesa dan neman magana ne yasa ta yi mata wannan tambayar,tana sanye da hijabin da ta idar da sallah isha ta zauna a gefenta.

"Tashi muje dakinmu yau a can zamu ci abinci"cewar Rameesa,tabe fuska ta yi kamar zata sa ihu ta ce"Rameesa dan Allah ki barni in huta bana jin yunwa,haba tun shigowar ki kika dameni da magana bana ciki da tambaɗa", "hhhhhhhh! Allah yabaki hakuri sarkin yaƙi"

Tana gama gaya mata haka ta fice.

Suna zaune a dinning kowa anyi saving dinsa abinci mazan sun fara ci Ammi ta ce"wai nikam ina yan mata na ne!?" "Nima abinda nake son na tambaya kenan yau tunda na dawo aiki banji ɗu riyar su ba"Saghar ya faɗa yana ajiye spoon din hannunshi.

Sahil ya ce"yau ɓarna suka je yi wa LTG shikuma ya sa su punishment,yanzu de suna part dinsu ko wacce na jinyar jikinta",anty amarya, Ammi, Hajiya babba,ummah kallon Sahil dake basu labari suke yi dan su da suke cikin gidan ma basu san anyi haka ba.

Mikewa uncle Hameed ya yi yana magana"yanzu shalelen yan matan namu LTG ka galabaitar wayyo,ko wani hali Madam Zoya take cike oho!?"dariya suka kwashe dashi harda shi uncle Hameed din da ya yi maganar sannan ya nufi part dinsa,shide LTG ko ta kansu be bi ba cikin nutsuwa yake cin abincisa.

Sahil ya sake cewa"kuma babban abin tausayin shine harda wannan Sabriyah din da ya kawo gidan nan ya saka punishment din"zaro ido waje Ammi da anty amarya sukayi sannan suka maida kallonsu kan LTG.

"Yanzu Tajuddeen har da bakuwar mun ma baka bari ba!?,ni Wallahi har kunyarta ya kamani,ka sato ta sannan kazo kana haɗa ta da kannnenka kana musu Punishment!?"ta tambayesa tana riƙe habarta.

Ɗaukar wayarsa ya yi, ya bar musu dinning table din,ya nufi part din Abbie da baya nan.

Anty amarya da Ammi ne suka shiga part din dubasu.ga kuma fatime da ta shirya musu nasu abincin ta kai musu.

Sosai Ammi ta musu faɗa akan shiga masa part binciken da sukayi domin koda basu ɗauki komai ba ze ce sun mishi ɓarna,ga shi yanzu a banza ya sa su punishment.

Haka suka je wajen Sabriyah ma nan kam sannu sukayi mata sannan anty amarya ta zauna da ita tana bata abinci abaki tun bata karba hatta soma karba,bata barta ba se da ta tabbatar da ta koshi.lokacin har karfe 9:00 saura nan ta yi mata se da safe ta fita.kwanciya Sabriyah ta yi dan bacci takeji sosai sannan ta kwanta da ya ƙinin gobe LTG ze mayar da ita Lagos.

Sergent Khalifa ne da suke cikin dajin Kano sun yi ɗauki ba da ɗi da yan ta'addan da LTG ya tura su wajensu kuma sunyi nasara,nan ya samu ya kira LTG din a waya.

Yana dakin bincike da layin wayarsu yake bibiyar yan ta'addan da kuma su major Marry,shi yake basu direction akan inda zasu je da kuma yanda zasu yi yana daga zaune akan kujera ga hot black tea a kusa dashi.

"Hello LTG, Alhamdulillah mun gama dasu sede an harbi major Marry a hannunta na dama, sannan munyi losing din sojan mu daya!".

"Na sani na turo muku helicopter,ku dawo yanzu.and what about the girl fatan basu kasheta ba!?".

LTG ya jefawa Khalifa tambaya.

"Mun samota sede bata cikin hankalinta ina tunanin ma zeye wuya in bata haukace ba sakamakon bakar fodar ibilis din da suka dinga shaƙa mata"

Jinjina kai kawai ya yi,ya kashe wayarsa.

Bari mu leka bangaren magajiya boss lady.

Tun ranar da aka sace Sabriyah da Asmita boss lady ta tayar da hankalinta,ko ina a cikin Lagos tasa a nemo mata su tunda har ita zasu iya yaudara su gudu daga gidan ba tare da ta yanta su ba amma ba'a samesu ba, domin ita gani take yi Sabriyah da Asmita guduwa sukayi daga gidan, wa'yanda akayi abun a gabansu sun yi mata bayani dallah_dallah kan cewa sace su akayi ,amma fir boss lady ta ƙi yarda da hakan, ta kudiri niyar duk sanda ta yi tozali dasu ko kuma tasa aka kamo mata su seta sa sun dandana guɗarsu.

Cele kullum se ya shigo afafa da sa ran ko ze ga Sabriyah da Asmita sun dawo,amma haka ze jisu shuru,ga anty Teema da ciwonta yanzu ya fara tashi gadan_gadan babu wanda yake zuwa dubata da taimaka mata se Nabiha da Cele,su suke kawo mata abinci da kuma magani.

Katsina state

Gidan mom Rumanatu Bishara yau zamu leka.

Babban gida ne kerarren gida wanda ya gaji da haɗuwa wato gidan minister Abu Sufyan Ubaid. Abu Sufyan ministan harkokin jiga da ficen kuɗaɗe ne,suna rayuwar farin ciki shida matarsa ɗaya se ya'yan su hudu biyu maza biyu mata.

Babban dan su shine Ashman da ya kasance babban manager a company babanshi Abu Sufyan,se Dawood shi kuma engineer ne.

Se ƙannen su mata,wanda suke saƙo da saƙo, Iftisan ce babba se yar autar su Jaleelah me shekara sha shida.

Tunda na shigo gidan na soma jin hayaniya kamar ana dambe a falo,leka kaina ciki nayi na hango wasu kyawawan yan mata guda biyu wanda kan su ɗaya kayan jikinsu kuwa dayar na sanye da jeans din wando baƙi da riga,dayar kuma doguwar riga take sanye dashi.

Dambe suke yi kamar zasu kashe junansu kuma badan komai ba se akan remote,da gudu na hango mom Rumanatu ta sauka daga downstairs tana ihun.

"Iftisan da Jaleelah bazaku bar wannan faɗan ba ko!?"karasowa cikin falon ta yi ta samu ta shiga tsakanin su ta raba faɗan, dukkansu biyu se haki suke yi suna hararan junansu.

"Mommy kin ga yanda Jaleelah take hararata ko!?, gaba-daya ta gama rena ni"Iftisan ta yi maganar tana nuna Jaleelah da yar yatsa.

"Yanzu wannan damben da ku ka za ge Kunayi kamar wasu makiyan juna duk akan menene!?"mom Rumanatu ta tambayesu tana bin ko wacce da kallo.

Cikin shagwaba Jaleelah ta ce "mommy ina zaune ne fa ina kallon cartoon shine Iftisan tazo wai sede in bata remote ta kamo mbc Bollywood shine na ƙi bata remote din,shine fa...shine fa ta fara dukana".

Kallon Iftisan din mom Rumanatu ta yi"yanzu akan wannan abin kuka tsaya faɗa,ina ce ta kan hakane ko waccen ku aka sa mata Tv a bedroom dinta!?,amma hakan be muku ba se kunzo falon downstairs kun yi mini faɗa ko!?,to bari yayanku ya dawo sena saka ya muku dan banzan duka.kuma daga yau kar wacce na sa'ke kallo a falo, da sunan tazo kallo tunda ku kamar wasu mayu kullum kuna cikin faɗa,jini daya uwarku daya ubanku ɗaya amma ko da yaushe kuna cikin faɗa kamar wasu ka ji".

"Mommy kiyi hakuri bazamu sa'ke ba!,and kiyiwa wannan fitsararriya magana ta dena mini rashin kunya na girmeta da shekara daya so am not her mate". Iftisan ta yi magana tana zazzagawa Jaleelah buhun harara kai kace idanunta zasu faɗo kasa.

Girgiza kai mom Rumanatu ta yi dan ita rikicin Iftisan da Jaleelah ya fara isarta,jira take yi Ashman ko Dawood wani ya dawo tasa su zane mata su.

Ta ce"ku bani guri ko in gwara kanku da kujerar nan"turo baki Jaleelah ta yi ido cike da hawaye ta ce"sorry mom! please karki faɗawa su ya Ashman". hararanta mom Rumanatu ta yi, sannan ta sake daka musu tsawa da gudu ko wacce ta nufi bedroom dinta.

Zama ta yi a palour tana girgiza kanta,kallon agogon dake manne a falon ta yi taga 9:50pm na dare ga shi basu dawo ba,jiransu takeyi dan tasan daga su har daddyn nasu suna tare.

Da sauri me aikinta ta shigo falon riƙe da wayar mom Rumanatu da ta barshi a bedroom dinta.

"Anty! Hajjatiye ce ke kiranki"ta faɗa tana me miƙa mata wayar,da sauri mom Rumanatu ta karba jin an ce mahaifiyar su ce kiranta.

Tana sa wayar a kunne ta ji Hajjatiye ta fashe da kuka.

Gabanta ne ya faɗi aranta ta ce "yau kuma laifin me nayiwa Hajjatiye ni Rumanatu".

Murya a sanyaye ta yi magana"assalamualaikum! Hajjatiye na Barka da wannan lokacin".

A bangaren Hajjatiye kuwa jan majina ta yi,ta ce "munafukar banza da wofi babu tsiyar tsinantakar da gaisuwar ki zata mini!ku kasheni kawai ku huta,nagaji da tsiyar tsinantakar ku bazan iya ba,baze yu ba".

Daura hannu aka mom Rumanatu ta yi jin yanda Hajjatiye ke surfa mata ruwan masifa.

Ta ce"haba Hajjatiye na, faɗamin laifin me mukayi nida su ya Mubarak din!?".

Cikin masifa Hajjatiye ta sa'ke hayayyaƙowa mom Rumanatu"bansaniba!, ni zaku mayar tsohuwar banza ko,ku ce zaku turo anlikonta ya ɗauke ni inzo Nijeriya shine zaku watsa mini ƙasa a ido ko!to duk sena yi maganin tsinantakar dake damunku!su kam ma da suka saka yaransu da matan su suka rena ni ina zasu ga girmana kowa

21 / 33