/>
Gyada masa kai ta yi alamar ta ganta.
Abbie ya sa'ke cewa"daga yau ita ce mahaifiyarki,ki maida ita mamarki,tana son ki zama yarta,yanda zakiyi wa mahaifiyar ki biyayya haka zaki mata,shi kuma wannan shine mahaifin ki"ya sa'ke nuna mata uncle Hameed"sune iyayenki kinji ko?,gyada masa kai ta yi.
Kallon gaba daya wa'yanda suke cikin falon ya ce "daga rana irin ta yau, Sabriyah da Asmita suma ya'ya ne a gidan nan,yanda kuke da yanci a gidan nan suma daga yau haka suke dashi, ya'ya ne a wajena,wajen Isma'il,wajen Abdul Hameed,kuma yaya a wajen iyayenku mata.ku duakesu kamar yanda kuka dauki yan uwanku,ku daukesu kamar yanda kuka dauki ƙannen ku,kar inji kar in gani banason nuna bambanci duk da nasan yarana ba haka suke ba,kuna da ilimin da bazaku taɓa wulakanta dan adam ba,kunde ji abinda na faɗa ina!?",ya tambayesu yana kallon ko wanensu, suka amsa mishi da eh.
Murmushi ya yi"very good yanzu ku,nuna mini me zakuyiwa kannen naku da zasu ji dadi!?",Abbas ne ya fara ajiye ATM dinsa ya ce"ga shi a cire duk adadin kuɗin da akeso ayi musu abinda yakamata "Ahmad ma ya ajiye na shi ATM din"ga shi duk kudin dake ciki a yi musu amfani dashi"haka Hafiz shima ya ajiye nashi, Sudais ya ajiye nasa ya ce"na bawa ƙannena ATM din nan a musu duk abinda suke so da kudin ciki nasu ne hallaka malak",Sahil da Salim ma suka ajiye nasu, Saghar na murmushi ya ajiye nasa ya ce"nima ga nawa nan ayi sister's dina abinda ya dace,sannan duk sanda ake da bukatar a yi musu allura in basu da lafiya,dan Allah a sanar mini"dariya sukayi gaba dayansu,Jawan ma ya ajiye nashi "ya ce tom dama ance yan mata se da ado ga shi a siya wa ƙannena kayan make up da duk abinda ya dace".Abbie ya ji dadin yanda suka nuna soyayyarsu akan su,duk abinda suke so cikin mintuna ƙalilan zesa akawo musu amma dake yanason yaga yanayin yanda suka karbesu ne shisa ya yi haka.
Hannunsa yasa acikin wallet dinsa ya fito da ATM guda biyu ya ajiye ba tare da ya yi magana ba ya mike,da kallo suka bishi suna murmushi dan sun san dama, rashin damuwarsa da damuwar mutane be kai har nan ba yana da tausayi sosai,kawai mutum ne in be san shi ba ze mishi kallon mugu.
Haurawa part din sa LTG ya yi..
Dawood da Ashman suma sun ajiye nasu ATM..
Anty Sameera ce ta matso kusa da ATMs masu yawan dake zube a inda suka ajiye su,ta ce"gaskiya Sabriyah yayyunku suna matuƙar sanku wannan ruwan ATM haka bari mu kirga mugani".kirgawa ta yi tana jinjina kai "inyaaaah!,guda goma sha daya,se san barka"murmushi sukayi.
Tunda take a rayuwarta bata taɓa tunanin wannan ranar yana zuwa a cikin rayuwar su ba,bata taɓa tunanin wasu zasu maida su ya'yan su ba, musamman ma yanda wasu suke kyamarta su suna kiran su da karuwai.wai yau sune aka wayi gari kowa yana yin abinda ze sasu farin ciki,yau jinta tayi duk wani gurbin kadaici da take tare dashi ya cike jinta take yi,kamar yanda masu iyaye suke ji.
Batasan da wani baƙi zata gode musu ba .
Kukan farin ciki ta fashe da shi wanda bata taɓa tunanin zata yi sa ba.
Folding din dukka hannayenta ta yi tana kuka ta soma magana.
"Mungode! mungode! mungode,ban san da wani baƙi zanyi amfani wajen gode muku ba ,ku din mutanen kwarai ne,ban taba tunanin rana irin na yau zezo a cikin rayuwarmu ba,kowa kyama yake nuna mana,amma yanzu kun zame mana ahali,uwa,uba,yan uwa duk kun bamu,ko da yaushe inuwar kadaici je bibiye dani kullum cikin kadaici nake jina amma yanzu na ji ni kamar kowa,nima yanzu naji rayuwata tana da amfani,a ko da yaushe Asmita tana cewa my Tom duk sanda muka bar gidan boss lady to wajen mamana zamu koma,se inji jikina ya yi sanyi inna tuna Ni banida kowa,banda wanda zan kira nawa a wannan duniya se Asmita kadai.amma yau nasamu a halin da suka amshe mu hannu biyu cike da kauna.ya saka muku,yanda kuka taimakawa rayuwarmu,kuma Allah ya taimaka muku a lamurran ku."ta gama maganar tana fashewa da sabon kuka me taɓa zuciya.
Tashi yan matan sukayi gabaki ɗayansu harda Jaleelah da Iftisan suka zo suka rungume su,suma suna hawaye suna jin kaunar su na shiga zuciyar su musamman Sabriyah.
"Am sorry Sabriyah!,kiyi hakuri ki yafewa yar uwarki"cewar Zoya dake rungume da ita.
"Nima kiyi hakuri"Sabriyah ta faɗa.
Kukan Asmita sukaji,tana kuka sosai itama idanunta ya yi jajir,da sauri Sabriyah ta rikota ta yi tunanin ko akwai abinda take bukata ne yasa take wannan kukan.
Muryar ta sukaji tana cewa"my Tom bana faɗa miki ba,akwai lokacin da ƙaddara ze fitar damu daga wannan gidan!?,mun gode muku sosai ku din mutanen kirki ne"mamaki iya mamaki sun sha shi domin ba suyi tsammanin zata dawo hayyacinta a yanzu ba amma sun yi murna da haka,banda mutane biyu da uncle Hameed da Saghar domin su kadai suka san meye matsalar da hakan ze jawo domin ta dawo hayyacinta ne ta karfin tsiya,kuma mantawa sukayi da baza su bari Sabriyah ta fadi tarihin rayuwarsu a gabanta ba.
Abinda ya faru shine tun sanda Sabriyah ta fara bada labarin su ta fara jin kanta na juyawa,nan take ta fara ganin flash din hotuna a idonta,a haka ta dawo hayyacinta, batare da kowa ya sani ba,taci gaba da sauraran abubuwan da suke faruwa.
Tallafo fuskarta Sabriyah ta yi tana hawaye ta ce"my Jerry na godewa Allah da kika dawo hayyacinki" "nayi kewarki my Tom, wayan'can mutanen sun wahalar dani sosai"ta faɗa ta hawaye.share mata hawayen fuskarta ta yi.
Abbu ya dora daga in da Abbie ya tsaya"to Alhamdulillah, Allah shine abin godiya,da ikon sa ga shi kin samu lafiya kin dawo cikin hankalinki.kamar yanda muka dauke ku kamar ya'yan mu kuma ku sa'ke jiki,kunji!?,kuma nan gidan ku ne,Umaisha yanzu tunda kun kara yawa zaku koma babban part din kusa daku be three bedrooms a ciki da extra room se kunfi sakewa a can".
A tare suka ce"to Abbu".
Wani farin abu ne kamar kunu yanada dan kaurin fari tas ya fara zubowa daga hancin Asmita hannu tasa ta lakuto shi ihu ta yi ganin abun dake fitowa daga hancin ta.
Lura da abinda yake fitowa daga hancin ta yasa suka rufu akanta,dama uncle Hameed da Saghar sun san za'a rina.
Rike kanta ya fara yi,anky chef Saghar yasa yana goge mata hancinta rike hannunsa ta yi kam tana kuka.kallonta ya yi kafin ya ce "shiiii!,ki yi shuru ki sa idonki cikin nawa"hakan ta yi,idonsu na cikin na juna.yasa hanky chef din yafara jawo farin abun dake fitowa din,sosai ya fito dasu, ƙasa jure kallon cikin kwayar idonshi ta yi se kawai ta rufe,se da ya fito da su tas kafin ya sake kanta.kallon Fatime ya yi "please a gyara wajen nan"fita tayi domin kawo abubuwan da zata kwashe su dashi.
Kallo abun suke kafin Abbie ya ce "to shi wannan din meye!?", Saghar ya ce"cocaine din da suka dinga dirka mata ne ya taro a waje daya,kuma ya taɓa mata kwakwalwarta,dawowa hayyacinta da tayi cikin karfi,ze iya jawo mata babban matsalar da yafi na farko,abinda za'a yi cikin gaggawa shine a yi mata brain surgery shine kawai solution in kuma ba haka ba,zata faɗa faint condition,ze zama a ko da yaushe zata dinga suma ne,duk bayan awa daya."be gama rufe bakinsa ba ta sume a jikin Sabriyah da Zoya.
Abbie ya ce "ayi gaggawar yi mata aiki".
Hajjatiye ta ce "yaran nan kuma ganin rayuwa Allah sarki Allah de ya saka muku".
Se mun haɗu Monday in me duka yakaimu da rai da lafiya.
Book one ya kusa karewa remain some few pages,na yi wa mutane 20 na farko discount din 200,zasu biya 300 kenan.idan mutum ashirin na farko suka gama biya ze koma 500 domin wannan shine standard price dinshi.luckiest 20 people ku hanzarta biyan naku.😍😍😍😍😍💝
Comment,share and like.
*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*
Page 25&26
*_Story & written_*
By
*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)
*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️
__________________________________
Page 25&26
"Saghar kai ta part dina,kafin a gama shirin yi mata aikin"dagata ya yi cak i zuwa part Hajiya babba din,bin bayansu Sabriyah take kokarin yi,ta ji muryan Ammi na cewa"karki damu ze dubata"ba don ta so ba haka ta tsaya,murna ya koma ciki,da ta ga Asmita ta farfaɗo ta yi tunanin matsalar su yazo karshe,yanzu ga maganar aikin da za'a mata.
Rike hannunta anty amarya ta yi suka tafi part dinta.
Kiran asibitin ya yi ya sanar dasu da komai ya zama cikin shiri zasu zo dan gabatar da aiki.
Dawuwa falon Saghar ya yi bayan ya kai ta part din Hajiya babba kamar yanda ta umarce shi da ya yi.
"Uncle yau ne za'a mata aikin!?"cewar Dawood,"eh yau ne yanzu ma kuwa,ku fara yin gaba da ita banason Sabriyah ta fito ta samu baku tafi ba,dan zata ce dole se ta bi mu,so you have to hurry"a tausashe Dawood ya sa'ke cewa" Saghar ku tashi muje" "Ammi ba se kunzo ku ba, duk ku zauna a gida daga zaran aiki ya yi kyau an kammala lafiya se mu sanar daku,ku zo ku duba ta,in ba haka ba in Sabriyah ta fito taga bakwa nan zata fara zargin wani abu dan yanzu haka ma jikinta ya yi sanyi"uncle Hameed ya yi maganar yana miƙewa,ya fice a cikin Mansion.
Wannan karon Hajiya babba da Ammi ne suka fito da Asmita a ka sa ta a motar.su kuma suka wuce asibiti.koma wa ciki sukayi suna addu'a Allah yasa aiki ya yi kyau.
Yana part dinsa,system ne a gaban shi yana video call da general cikin turancin da ya zauna a bakin shi kamar yarensa,ya ke sanar da general ya samu memory sede ba ya son kowa ya ji abinda ake ciki har se an kammala operation din da suke yi na kama Italian Mafia,domin ya gano kan cewa akwai munafiki a cikin su yana sanar da shugaban Italian Mafia duk wani motsin su.jinjina masa general ya yi ya kuma dau masa alkawarin baze sanar da kowa abinda ya ke faruwa ba.
Shigowa major Marry ta yi ta zauna a kan kujerar dake facing dinsa hannunta sanye cikin jakan da ake sa hannu in an samu wani rauni, sosai ta samu lafiya hannun ne kawai ya rage ta yi recovery.
"LTG i heard that, you have the memory with you!?" ..
"Yes!how are you feeling now?",ya tambayeta yana rufe system din.
"Am quite well buh I have important information to share with you"kallon ta ya yi alamar go ahead.
"i already sent it to you through your email"
Duba wayarsa ya yi kafin ya ɗago ya kalle ta.
"Are you sure this information isn't wrong!?"
"Am hundred percent sure LTG"
Umarnin tafiya ya bata, sannan ya tashi ya yi wanka, ya sa uniform.
yana saka takalmin sa ne Khalifa ya shigo,nan LTG ya sanar dashi da su shirya zasu shiga daji operation,sara mishi ya yi kafin ya fita da sauri nan take ya sanar wa sojojin dake gidan,shiryawa sukayi cikin ka'kin uniform din sojoji,ko wanne ka gani da bindiga a jikinsa,ga motocin da ke fake yana jiransu dan fita daji.
Suna shiga part din, anty amarya tasa ta ta yi wanka a toilet dinta,ta fito mata da riga da skirt na Atamfa super wax ya sha dinki ya yi kyau sosai, tunda telan ta ya kawo mata su ta fahimci kayan baze shigeta ba yasa bata sake bi ta kansu ba se yau din nan.ajiye su ta yi akan gado.
Fitowa ta yi daga wankan sanye da dogon hijab din da anty amarya ta bata ta saka, towel na daure a ta ciki.bakaramin kyau hajab din ya mata ba, kyakyawar fuskarta ya fito ya yi kyau.
"Anty amarya na fito ina mai in shafa"ɓata fuska anty amarya ta yi, daga gani bata ji dadin sunan da Sabriyah ta kira ta dashi ba hakan ya sa ta, cewa "Sabriyah ba ki dauke ni a matsayin uwa bane yasa ba ki kirani da mommy ko mama ba!?"cikin jin kunya ta ce "kiyi hakuri mommy bazan ƙara ba" "yawwa daughter na!,hijab din nan ya Miki kyau sosai"murmushi kawai ta yi,ita saukin kan anty amarya da rahanta yana burgeta har cikin rai takejinta kamar ita ce mahaifiyarta saboda yanda take nuna mata soyayya.
Zaunar da ita ta yi akan kujera gaban mirror ta shafa mai kafin anty amarya ta mata light make up ,ta bata kayan ta ce ta je ta saka a cikin dress room.
Kallon kayan ta yi tana tunanin ta ina zata fara sakawa,ita sam ba ta taɓa saka irin wannan kayan ba,daga riga da wando se riga,sune kadai iya kayan da take sawa,yanke shawara ta yi ta dauki skirt ta fara sawa,kayan tab ya kamata Kamar telan da ya dinka ya gwada ta, ta sa rigar.masha Allah ita kanta seda ta ji sauyi a jikinta,gaban madubin da ke cikin dressing room din taje ta tsaya tana kallon kanta,seda ta ja baya tana mamakin kanta,gani take yi kamar ba ita ba gaba daya kayan sauya mata kamani ya yi, tsananin kyaun da kayan ya mata ya sa ta fara juyawa tana karewa kanta kallo kamar ba ita ba,gashinta dake zube a bayanta ta fara kokarin daure su waje daya,dakyar ta iya daurewa,ta dau dankwalin kayan ta fito,tun da anty amarya ta daura idonta akan Sabriyah ta gagara daukewa kallon fuskar yar karamar ƴarta da ta rabu da ita take yi a fuskarta, fuskar Asrah take gani lokacin da tana karama a fuskarta,ta kasa janye idonta akanta bata ma san ta iso kusa da ita ba tana mata magana amma ina hankalinta ya yi nisa.
"Mommy ki daura mini dankwalin ban iya ba"shiru anty amarya ta yi tana kallonta, taɓa hannunta ta yi tana sa'ke cewa"mommy ki daura min"se sannan ne ta dawo tunaninta,da sauri ta ce"sure kawo in daura miki "miƙa mata ta yi batare da ta yi tunanin komai a ranta ba.
Daurin dankwali me kyau ta mata ta saka mata sarka da ɗan kunnen gold me kyau simple design,ji ta yi kayan yana muskulinta tasa hannu zata dan ja zip kasa kadan,rike hannunta ta yi tana tambayarta "meye zakiyi haka"shagwabe fuska ta yi da iya gaskiyarta ta ce "mommy Wallahi muskulina yakeyi"dama ta yi tunanin za'a yi haka duba da babu irin wannan kayan a rayuwarsu bama su taba sawa ba.
"Karki cire ki daure kidinga sakawa a s haka zaki saɓa,ke bakiga yanda kika yi kyau a cikin kayan bane,kamar wata amarya"tsadadden murmushinta dake ƙara mata kyau ta sakarwa anty amarya"mommy dagaske na yi kyau sosai!?"ta tambayeta with excited face,kai ta gyada mata alamar ta yi kyau sosai,itama da murmushi akan fuskarta nan ne dimples dinta suka bayyana,dan yatsa ta saka a ciki ta taɓa kamar wata karamar yarinya ta langwabar da kanta gefe tana kallon kyakyawar fuskarta anty amarya da za'a iya cewa photo copy dinta ce.
"Laaah mommy kema kina da dimple guda biyu iri daya da nawa,kuma ma a waje daya suke"hararan wasa ta mata"ke dama baki taɓa gani bane se yau".
"Allah ban taba lura ba,se yau.mommy kin san meye!?"girgiza kai ta yi kawai ba ta ce komai ba.
"Mommy ke kyakyawa ce sosai ko fa murmushi kikayi se kin ƙara kyau,kalli idanunki Wallahi kamar akwai wani abu kamar man gyada_man gyada a cikin su"rike haba ta yi tana kallon Sabriyah da mamakin ta,kenan itama surutacciya ce rashin sabo da kuma rashin wanda zaka zauna ka sa'ke dashi har ka ta yi masa surutun ne ta rasa shisa a ke mata kallon bata wani magana sosai.
Yanzu da ta samu anty amarya kuma ta dauketa tamkar uwa shisa take ta mata surutu.kuma ita ta ji dadin hakan sosai yanda ta ji free da ita babu wani shuru_shuru ko kuma wani kunya,ta fito tana ta mata surutu da shagwaba hankalinta kwance.
Tunawa ta yi da Asrah,duk lokacin da ta yi kwalliya se ta shafa fuskarta ta ce "mommy kinyi kyau sosai, you're so beautiful mom".
Ruko hannun Sabriyah ta yi "Tom Nagode babyn mommy, yanzu kije palour,in kije ki gaishesu daya bayan daya bawai yanda kika saba yi ba"gyada kai ta yi ta mike da niyar tafiya.
"Sabriyah zo nan"dawuwa ta yi,ta tsaya,dauko gyalen shantali ta yi ta yafa ma,akai.
Fita ta yi a part din ta nufo main part da tabar su.
A hankali take taka stairs da takalmi me madaidaicin tudu,kamar wata hawainiya take tafiya kai kace tsoron taka kasan takeyi,ita kuma ji takeyi in ta yi tafiya da sauri to skirt dinta ze rabe gida biyu duk da kamatan da ya yi ba sosai bane kawai rashin sabo da irin kayan ne yasa takejin wannan sabon a al'amarin.
Jin ƙaran takun takalmi ne yasa suka maida idon su wajen dan ganin waye haka.
In badan sun santa ba to babu abinda ze hanasu cewa wata shuwa arab mix with Hausa ce,yanda ta atamfar ya yi fitting din jikinta se ya zamana kamar tun asali shine suturanta.
Saukowa downstairs ta yi idanunsu duk a kanta musamman su Umaisha da su Ashman,kallonta suke yi babu ko kyaftawa.
Yanda anty amarya ta sanar ita hakan ta yi wajen Abbie ta fara zuwa ta gaisheshi.
"Abbie ina wuni!?".
"Lafiya klau Sabriyah,ya mommy ki!?".
A hankali ta ce
"Mommy na lafiya"
Ta je wajen Abbu shima ta gaisheshi.
"Abbu in wuni!?".
"Lafiya klau alhmdllh yarinyar kirki"
A marairace Jaleelah ta ce "Abbu mu ba yaran kirki bane!?".
Gwalo Sabriyah ta musu
"Eh din,kun ji haushi ne?"
Hararan wasa Rameesa ta mata ta mike ta dawo wajen abbu ta zauna cikin shagwaba ta ce
"Abbu mu ma ai yaran kirki ne ai ko?".
Dariya abin na su yaba kowa