boma_bomai,da Masallatai,da kuma churchs, kasuwanni,makarantu,ko ina za'a dasa bom,bayan nan kuma zamu kwashe samari mu karasu akan dakarun mu,zamu yaƙi sansanin sojaji da yan sanda,babu wa'yanda zamu kyale da rai.yan mata ɗari da daya zamuyi garkuwa dasu duk wanda yazo kawo fansar su a kasheshi,yara matan kuma zamu maida su namu,ta border za'a shigo mana da manyan makamai,da kuma sauran mutanen mu duk ta jirgin ruwa zasu zo".cikin jinjina wa da girmamawa suka fara zuba mishi tafi,hannu ya daga musu ɗan su dakata.cak suka tsaya.
"Ku tabbatar da a cikin ku duk wanda ya bata mana aiki komin muƙaminsa a cikin Italian Mafia dole ze mutu,mutuwa kuma mara dadi".
A tare suka mike tsaye sunawa kansu kirarin ƙungiya su.
"we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union".suna gama anthem dinsu suka fara shan giya ana shagali.
Barrister Lameer ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun,to kunji abinda wa'yannan azzaluman suke shiryawa.sunan location din da suke shine,okir......."buge wani karfen ya yi ya fadi a ƙasa yabada sauti da seda suka ji.
Da karfi" sukace waye a wajen" ku duba ko waye sannan ku kashe shi,nan take Barrister Lameer ya fara salati domin yasan tunda suka ganshi kam na shi yazo karshe.fita a inda ya buya ya yi ya fara gudu yana son barin wajen,yana cikin gudun ya cire memory cikin wayar ya jefasa cikin bakinsa.nan ne video din ya dauke gaba daya.
Ransu ya matukar ɓaci lokaci daya kuma ya tashi,suna son kashe rayuwakan al'umma da basu ji ba ,basu gani ba.
Da Karfi LTG ya daki table din gabanshi da karfi ,idon sa ya yi jajir.
Furzar da iska me zafin gaske ya yi daga bakinsa.
Sudais shafa gashin kansa ya ce"wa'yannan sun riga da sun gama shirin su,babban abin takaici shine bamu san ya kamanin sabon shugaban nasu yake ba, yana da wayo yaƙi yarda a san fuskar sa,ba musan a wani lokaci ne zasu tayar da bom din ba yakamata mu dakatar da su".
"Duk wayon sa baze taɓa kaucewa tarkona ba,koma wanene shi se na kamosa na mishi hukunci dede da Abinda yake aikatawa"LTG ya faɗa yana miƙewa tsaye.yana kallonsu"Sudais dakai zan fara, suna kokarin shigo da mutanen su da mugayen mukamai ta border,you're comptroller General,nauyin dakatar dasu ya rataya a wuyanka kabada umarni duk wani abinda za'a tsallakar dashi border daga yanzu zuwa end of this month, ka sa a rufe border babu abinda za'a shigo dashi har se da sa hannunka,saboda you're comptroller General Sudais"jinjina kai Sudais ya yi.
Maida kallonsa kan Jawan ya yi "kai mataimakin commissioner of police ne,ka zuba jami'o'i ta ko ina bama iya garin nan ba da duk sauran state. communicate with your co assistant commissioner of police".
Gyada masa kai Jawan ya yi.pointing din Saghar da hannu ya yi"Saghar make sure ku ankara a hospital daga zarran kaga wa'yanda baka yarda dasu ba don't hesitate to inform me".
Yaci gaba da magana"bana son kowa yasan da shirin da muke yi so becarefull".
"In sha Allah LTG,zamuyi nasara akan su" "very good,nasanku bakwa wasa da aikin ku, rayuwakan al'umma shine muka shiga wannan aikin akai with any cost we have to save their life's"ya ƙarishe maganar yana rike kansa dake sara mishi.yana jin kan ya fara ciwo,amma bayanin da zeyi yana da matukar muhimmanci hakan yasa yaci gaba da maganar ba tare da ya dakata ba,amma shi kadai yasan yanda yake ji,abun a jininsa yake rashin dogon magana in ba ya zama dole ba,baya dogon magana.
Kallo ɗaya suka mishi suka fahimci kansa ya fara mishi ciwo.hannu Saghar ya sa a aljihunsa ya fito da maganin ciwon kai ya basa karba ya yi ya jefa abaki ya haɗiye.
"LTG!,make sure you drink water saboda maganin ya yi melting "hararansa ya yi"ba zan sha din ba,kufa doctor's din nan ko..."ya yi shuru yana zama,dariya sukayi Jawan da Saghar suka tafa.
"Ku de anyi yan air,yanzu de kunji maganar da LTG ya yi so concentrate"
"In sha Allah ".
karfe goma na dare kafin suka bar part din nasa cike da tunanin yanda zasu kawo karshen Italian Mafia.
Se 11:00pm suka baro wajen abbu nan ma seda Hajiya babba ta korasu,kafin suka tafi.
Basu shiga bedrooms din su ba suka
shigo nasu Sabriyah suna kwance suna bacci.
"Ayyah yau nasan sun yi missing din mu"gobe se mu haɗu.
Suka faɗa yana barin dakin, Parsa kashe musu wuta ta yi kafin ta bi bayan yan uwanta.
Washe gari bayan sun karya babu wanda ya fita aiki saboda su mom Rumanatu ana hanya sun kusan sauka.
Duk wani abinda ya dace da za'a karbesu an yi sa.
Karfe sha biyu na rana suka shigo gidan,bayan yan gaisa ne suka wuce masaukinsu, Ashman da Dawood a part din Sudais suka sauka.jaleelah da Iftisan part din su parsa suka sauka.
Sauka sukayi sukayi sallah sannan suka huta,bayan sun gama cin abinci ne aka dawo falo ana hira.
Hajjatiye da a jirgi tazo ba'a motar ba amma se bala'in ta gaji takeyi,su Hajiya babba suna mata sannu,Ammuh dake hakimce akan kujera tunda suka zo sannu da zuwa ta yi musu ba ta sake ce musu komai.
"Bak'ar annamimiya,dama nasan tsinannen bakin halinki be ze bari kice mini sannu,yau da zan faɗi in mutu da kin fi kowa murna,ke kam khareema kin yi asarar rayuwa.babu yanda kika iya dani nan gidan ƴa'ƴa nane se in sa ya sake ki inga tsiyar tsinantakar da ze faru,ni maye ma haka yaganni ya barni,bare kuma ke yar adama,mara mutunci kawai". shuru wajen ya yi babu wanda ya isa yace ta yi hakuri ta hakura, mutum na sa baki zata dawo kansa.
Su Ammi de ido suka zuba musu,tun lokacin da Abbie ya auro Hajiya khareema haka kurum basa shiri saboda girman kan Hajiya khareema.shisa Hajjatiye bata santa.
"Hajjatiye wai Ni kadai kika tsana a gidan nan ne!?,duk lokacin da kika zo se kin kwashemin albarka meye na miki da zafi haka ga su hamdiyya da Badeeya,ga Abida su baƙi tsane su ba se ni!?", Bude baƙi Hajjatiye ta yi alamar mamaki"lahaula wala quwata illabilah!, khareema yanzu zagina kike yi saboda ni ba uwarki bace shine zaki za ge kina zagina ko, tabbas Mubarak yau ni matarka take zagi saboda lalacewa yakai lalacewa"ta fashe da kuka,abinda suke gudu kenan da ace Ammuh ta yi shuru batace mata komai ba da Hajjatiye shuru zatayi in ta gaji dan kanta.
Dawuwa kujerar da take zaune Abbie ya yi ya hau bata hakuri,mom Rumanatu da abbu, uncle Hameed suka sa baƙi suka bata hakuri, dakyar ta yi shuru.
Ta goge fuskarta da gefen gyallenta ta ce "nadawo kanku,yanzu meye abinda kuka ribantu dashi da kuka bar yaran nan zabga_zabga dasu babu aure cikin su babu wanda baze iya yiwa matarsa ciki ba, ɓalle a ce basu kai aure ba,dubi yan matan. duk kun haɗa yara kun barsu a gantale se anyi magana a ce wannan soja ne, wannan likita,wannan kustam,wannan police, wannan yan kasuwa,yara duk sun kosa amma kunki aurar dasu se an kawo muku jarirai daga waje a ce wani ya dirkawa wata ciki ko"duk se da sukaji kamar su nitse kasa tsabar kunya, miƙewa da sauri Hajiya babba da Ammi sukayi.
"To Ku kuma ina zakuje,anyi maganar ku aurar da yara kun wani miƙe zaku gudu,wato kun fi so ku gansu jere da ku a rasa waye uwar waye yar,to dawo ku zauna "simi_simi suka dawo suka zauna,babu yanda suka iya amma kunya kam sun sha shi.
Masifar Hajjatiye kam sun sha,ta yi hatta gaji ta yi shiru,se kuma aka dawo hirar Sudan da ita kamar ba ita ce ta gama Masifa ba.
Saghar ya ce"Hajjatiye ni fa da kince zaki samo mini mata a Sudan yanzu ya ake ciki"washe baki ta yi "yaron kirki ai matan aure kam akwai su zan sa akawo maka guda uku se dirje ka zaɓi daya a cikinsu musha biki"dariya ya yi"to ai kuwa hakan za'a yi".
Bude baki Hafiz ya yi ze yi magana abbu ya galla masa harara yasan be wuce tsokana bace zeyi.
Ba shiri ya yi shuru.
"Nikam ina katon Gwauron gidan nan ne ko be da wo ba ne haryanzu!?",Ammi ta ce"ya dawo bari a kirasa"tafa hannu Hajjatiye ta yi,ta ce"lallai hamdiyya wuyarki ya yi kauri,yanzu jikan nawa in banda baƙin hali irin naki se na tambayi ina yake kafin za ki sa a kirawo sa,tabb dijam"cikin girmamawa Ammi ta bata hakuri.
Dawood ne yaje ya kira LTG da be ma san da zuwansu ba.
Shigowa falon ya yi yana taku na kasaita jikinsa na sanye da dogon wando da rigar me doguwar hannu.
Hajjatiye na ganinsa ta fara sakin murmushi.
"Kun ga na miji sojan yaƙi,me firgita abokan hamayya,daya tamkar da dubu, Allah de ya biya na mijin duniya". murmushin da beyi niyya bane ya subuce masa duk da se wanda ya kula sosai ze gani.zama ya yi a kusa da ita yana rike hannunta.
Farin cikin Hajjatiye yakasa boyuwa, LTG yana daya daga jikin wanda ta fi kauna acikin jikokinta daga shi kuma se Asrah,kwata_kwata bata ganin laifin sa duk abinda ze yi bata masa faɗa,bazaka tabajin Hajjatiye tana yiwa LTG Masifa ba.
Kunnesa ta kama ta yi masa magana wai batasan munafukai su ji me ta faɗa mishi,shima da ya tashi bata amsa a kunne ya sanar mata.
Kallon su kawai sukeyi,ga shi suna son yin dariya amma wanda ya kuskura ya yi ma yasan ya jawo wa kansa hakan yasa duk suka zuba musu ido kawai.
Hajiya babba ta ce "Abbie dama akwai maganar da nakeso muyi dangane da yarinyar da Tajuddeen yakawo,amma zan so mu fara jin tarihin su tukun,saboda Abida ta nuna tana ra'ayin adopting din dayar yarinyar" "to tana ina ne yarinyar!?",Abbie ya tambayeta.
Kallon Zoya Hajiya babba ta yi ta ce "je ki kira mini Sabriyah"ranta be so ba haka ta mike ta nufi part din su.
kallon anty amarya da aka ce zata zatayi adopting din Sabriyah LTG ya yi,be iya cewa komai ba se kwantar da kansa akan kujerar da yake zaune ya lumshe idanunsa.
Dawuwa falon Zoya ta yi Sabriyah na biye da ita a bayanta,tana riƙe da hannun Asmita.
Ganin yanda suke da yawa a falon, suna shigowa ciki ido ya dawo kansu nan tajita a takure saboda idonsu.
Zama Zoya ta yi ta barsu a tsaye, Abbie ya ce mata "zo ku zauna"in da su Parsa suke zaune a kan lallausan carpet su ka zauna.zaman su beda wuya Asmita ga Saghar.
Da sauri ta tashi taje wajensa ta riko hannayensa biyu"me kyau ka zo muje mu hau lilo"da mamaki suke bin Saghar da Asmita da kallo musamman wa'yanda basu san condition din da take ciki ba,dan in ba tayi magana ba babu wanda ze ce tana da Matsala,kallon su Abbu ya yi yaga yanda idanunsu yake akanshi.
"Asmee je ki zauna wajan Sabriyah anjuma kadan zamu je lilo"sa'ke sa ta yi tafara kirge da hannunta,kamar me lissafi can kuma ta sa'ke cewa"tom shikenan ai jiya da yanzu zamu tafi ko"gyada mata kai ya yi saboda ya samu yaje ta zauna.
Komawa wajen Sabriyah ta yi,cikin rada ta ce"my Jerry in kika sake tashi a wajen nan to zanyi kuka"kwabe fuska ta yi "tom ba zan kara ba".
Gyaran murya Abbie ya yi,ya soma magana"Sabriyah wannan din meye din ki ce!?",a hankali ta ce"yar uwata' ce kuma ƙawata".
Jinjina kai ya yi ya sa'ke furta"ina son ki bamu tarihin rayuwar ku". har lokacin LTG yana a yanda yake be bude idonsa ba duk abinda ake faɗa yana jinsu.
Dogon numfashi ta ja,ta soma magana"sunana Sabriyah wannan kuma sunanta Asmita,mun taso a gidan karuwai ne wanda ni da ita anan muka taso tun muna yara kananu,bata san kowa ba haka nima babu wanda nasani, wannan dalilin yasa muka yiwa kanmu,alkawarin zamawa junanmu uwa,uba,yar uwa,kawa, magajiyar da ta siye mu ta gana mana azaba wanda se da mukaji dama bamu zo duniya,tun muna yara take aka koya mana abubuwan da zamu dinga kawo mata kudi, karuwanci,sata,damfara,rawa.dukka babu abinda bama aikatawa.tun ban kai haka ba nafara rawa a cikin gidan wasa,ban wani saba ba,in mun kayi ranar haka zamu kwana da ciwon jiki babu me bamu maganin ciwon kai,kudin da aka samu da mu a wajen rawa ko ruwa ba'a siya mana dashi,abinci ma sau daya ake turo mana dashi arana, se de wacce ta rene mu ita ce in ta fita nata wajen take samo mana abinda zamu ci,har yakai ga karfinta ya ƙare takamu da ciwo,ya zamana babu me taimakonmu wannan dalilin yasa na busar da zuciyata,na fara yin rawa,domin in samo mana abinda zamu dinga ciyar damu,domin tunda muka kai shekaru goma sha uku boss lady ta cire hannunta akan mu abinci sau daya da ake turo mana ma tadena haka zamu sha wahala muyi rawa amma kudin gaba daya zatasa a kwashe mata,ko biyar bama ci aciki.
Samarin da na fara yi ne suka fara bani kudi,nan na samu nafara biya mana buƙatar mu,nice nake ciyar damu,suturarmu duk yana kaina, in wani babu lafiya a cikinmu nice nake siya mana magani,maganin antynmu da ta rene mu nice nan nake samowa.daga zaran muyi mata laifi ko min kankantar laifi,zata haɗa mu ta mana muguwar duka,duk abinda ze same mu ita be dame ta ba,inde zamu kawo mata kuɗi to magana ya ƙare.bamu da yanci a wannan gidan,in kanason ka samu yanci shine se an maka lasisi,kafin ayi mana lasisi munsha bakar wahala, tasan sarai inada ciwo amma daga zaran na mata laifi haka zata barni a cikin ruwan sama ya mini dukkan da se ciwo na ya tashi ko kuma ta sa in yi kneel down haka zata sa a dinga diban ruwa ana shekamin.
Tunda nayi baki har na fara iya mayar mata da martani,sun riga da sun bude mini ido bana shakkan kowa,duk wanda yace ze takani to Ni se na ta kashi.daga ni har Asmita se da ta tabbatar da ta mayar damu karuwan suka fi kawo mata kudi kafin nan hankalinta ya kwanta daga nan ne ta yi mana lasisin karuwancin.
A da banijin dadin rayuwar can amma nazo na saba da komai in su naji banida in da yafi mini can,domin duk inda naje jina nakeyi kamar akan kaya nake bana samun nutsuwa se in na koma can, kullum maganar Asmita shine yaushe zamu bar wannan gida,ta tsani gidan fiye da mutuwarta.
Ita babanta ne ya siyar da ita a wajen boss lady saboda son abin duniya.da wannan abun Asmita ta taso shine a mafarkinta ta kasance cikin kunci da raɗaɗin abinda mahaifin da ya haifeta ya aikata a gare ta, kullum in tayi bacci se ta yi mafarkin lokacin da babanta ya siyar da ita,ta wannan dalilin ne yasa ta fara shaye_shaye ko zata ji saukin raɗaɗin da takeji, kullum cikin yi mata faɗa nakeyi akan shan kayan mayen da takeyi, amma ko a boye se ta sha.
A haka na haɗu da wannan a kasuwa daga nan ne rayuwar mu ya shiga cikin babban matsala,mun haɗu da wani ya bawa Asmita memory card, daga nan ita kuma ta bani shi na boye,a washe garin suka saceta sun yi zaton memory yana wajenta nikuma wancan ya sato ni, wannan shine kadan daga cikin tarihin rayuwarmu".
Sunyi matukar tausayawa yara batare da sun san komai ba aka jefa rayuwar su cikin garari,aka yi musu muguwar illa,sun yi rayuwa batare da sun san dadin ta ba,babu boko ba bu arabic,ba sallah ɓalle salati.
Babu abinda yakai wannan cutarwa ce babu wani kyakyawar alaƙa tsakanin ka da mahaliccinka,baka ma san meye dede maye ba dede ba,hakkin su yana rataye ne akan wuyan wa'yanda sukayi sanadiyyar shigar su cikin wannan muguwar rayuwa.
Ammi,Hajiya babba,Anty amarya,mom Rumanatu hawaye ne kawai yake zuba daga idanunsu suma iyayene yau ya zasu ji idan ace ya'yansu akayi wa haka.ya zasu ji idan a ce yau ƴaƴansu aka mayar karuwai amma ance ko wani bawa da kalar tasa ƙaddara,su tasu kaddarar a haka yazo.
Yan matan kansu kuka suke yi da sukaji labarin Asmita da Sabriyah hatta Zoya se da tayi kuka ta yi danasanin abinda ta aikatawa Sabriyah.
Hajjatiye tsabar tausayinsu seda ta yi kuka itama tana tsinewa wa'yanda suka musu haka.
Su Saghar idanunsu ya yi ja sosai ran maza ya ɓaci sun dau alwashi yanda boss lady take wargaza rayuwar yara mata ita ma se sun wargaza nata rayuwar.
Me gayya me aiki kuwa yanda yake zaune kuwa ji yake yi kamar ya je gidan karuwan ya kashe boss lady y kuma kona gidan,ya tausaya musu da halin da suka tsinci kansu,be taɓa kawo tunanin cewa wannan ne dalilin da yasa suka tsinci rayuwarsu a haka ba,domin akwai ballagazazzu matan da suka watsar da kansu babu wanda ya musu dole,su suke mayar da kansu karuwai.wasu su gudu su shiga duniya suna sheka ayarsu,ga wa'yanda kwadayin abin duniya yake jawo su bariki.wasu kuma matsalolin rayuwa ce.amma koma wani matsala ne be kamata bawa ya jefa kansa cikin saɓon Allah ba.
Hakan ne yasa ya mata kallon ɗaya daga cikinsu ashe ba haka bane.ya kudurta a ransa ze dau mummunan mataki akan boss lady.
Ammuh da Ummah ko kadan basu,basu tausayi ba tabe baki sukayi suna watsa musu harara.
Su Abbie sun jinjina lamarin kuma sun tausaya musu sosai,ganin da cewa su din yara ne da kansu daya da ya'yansu.
Jikin abbie ya yi sanyi sosai da dakyar ya iya cewa"munji labarin ku Sabriyah, tabbas labarin ku akwai darasi a ciki,an cuce ku an cuci rayuwarku,ko kadan baku da hakki wa'yanda suka aikata hakan sune alhaki yake wuyansu, Allah zeyi muku sakayya,in sha Allah daga yanzu duk wani wahalar ku yazo karshe,babu wani wanda ze iya cutar da rayuwarku.kun zama ya'ya a wajen mu.ki saki jikinki da kowa, Asmita kuma Allah ze bata lafiya". Kowa ya masa da 'in sha Allah".
"kin ga wannan"ya faɗa yana,nuna mata anty amarya da har lokacin hawaye takeyi tana tuna to ita yanzu wani hali nata yar take ciki,a wani duniya take.