ASHE ZAMUGA JUNA

Author :  MRS ISHAM Category :  Love

Chapter   28 / 33

81K to 84K   out of 97.2K words

san an yi miki aiki ba saboda zata iya tayar da hankalinta amma gobe duk zasu zo dubasu da jiki"gyada masa kai ta yi.

"Kai na!,na mini ciwo sosai kuma ina ganin jiri"zama ya yi a gefen gadon ya ce "ehh wannan normal ne,nan da wasu kwanaki za ki dena jin haka".

Shuru ne ya biyo baya daga ita har shi babu wanda ya sa'ke cewa komai.

"Me kyau ban san sunanka ba"batare da ya kalleta ba,ya amsa mata da "Saghar".

Nan ma shuru ne ya sa'ke ratsawa, miƙewa ya yi ze fice,dan ya rasa meyasa duk lokacin da yake tare da ita se ya ji wani iri.

"Ya Saghar tafiya zakayi ka barni ni ɗaya!?"ya tsinkayi muryarta tana tambayarsa.

juyowa ya yi idonshi ya sauka cikin nata narkakkun idanun ta kafesa dashi tana kallonsa.

Komawa ya yi,ya zauna yana kallonta.

"Asmee dama kema matsoraciya ce!?".

"Ah ah naga zaka tafi ne ai to"

"Ke kuma bakya son in tafi?",sun kuyar da kanta ƙasa ta yi.

"Kina bukatar hutu ne za'a miki allura,za ki yi bacci ba'a son ki dinga magana sosai"gyada masa kai ta yi.

Yanda suke yiwa juna magana duk wanda ya kallesu ze yi tunanin sun daɗe da sanin juna,ko kuma akwai shakuwa sosai.

Se karfe goma ya bar dakin nata se da ya tabbatar da ta yi bacci kafin ya fito.yana kashe mata light.

Tana part din anty amarya idonta biyu ba tayi bacci ba tana jiran dawuwar LTG.

Anty amarya ma idanunta biyu,ita kanta jiran LTG takeyi ya dawo, saboda duk sanda ya fita ya yi dare ita da Ammi in ba sunji dawuwar sa ba tofa basa iya bacci.

Suna zaune tana ta koya mata wasu abubuwa.idanunsu biyu har sha biyu ya gota,nan ma shuru be dawo ba.

Wayarta ta dauka ta kira layinsa sede switch off.hakan yasa anty amarya ta dinga addu'a Allah de yasa lafiya.

Karfe 1:00 na dare motocin suka diro cikin gidan,anty amarya da Ammi da Abbie da suka kasance idon su biyu suna jiran dawuwar su sukayi hamdala.

Dama ya saba duk sanda ya yi dare ita yake kira a kawo masa coffee.

Suna zaune kira ya shigo wayarta ganin shine yasa ta daga.

"Anty amarya coffee please"haka kawai ya ce ya kashe wayar.

Miƙewa ta yi ta shiga kitchen din part dinta,cikin mintuna ƙalilan ta haɗa masa coffee, tunani ta fara zuwa ta tashi fatime ko kaltume,se kuma taga in ta yi haka kamar bata kyauta ba,duba da yanda suke yini suna aiki,dare ne kawai lokacin hutun su.

Kallon Sabriyah dake ɗale akan gado ta yi ta ce"sa hijabi ki zo ki nan"dogon hijab din da ta cire akan gadon ta dauka tasaka har ƙasa yazo mata.

Ba ta tray din coffee din ta yi,"ki kaiwa ya'yan ku Tajuddeen".

"To"har ta kai bakin kofa anty amarya ta ce"karki kuskura ki kirasa da wannan mugun da naji kike kiransa,ya Taj haka su Umaisha suke kiransa"gyada kai ta yi ta fita.

Knocking ta yi,ta ji shuru kusan five minutes tana tsaye can ta yanke shawarar shiga ciki kawai.

Ba kowa a bedroom din da alama yana wanka.

Ajiye coffee din ta yi akan Centre table.ta tsaya tana jiransa dan ta kudurci niyar tambayarsa ganin Asmita.

Idonta ne ya sauka akan wani ƙaramin hotonsa da Asrah a jiye akan bedside locker.

Nufan wajen ta yi tasa hannu ta dauki hoton kenan ta ji alamar mutum daf da ita.a tsorace ta juya,yana tsaye daf da ita distance din dake tsakanin su be fi taku biyu ba kwakkwaran motsi in ta yi jikinsu ze iya haɗuwa,ja da baya ta yi ta manne a jikin bango.

Dan ta tsorata da ganin yanayinsa na yau fuskarsa kamar wanda aka yiwa mutuwa,hannu na rawa ta ajiye hoton a inda ta dauka.

Yana sanye da rigar towel da ya rufe masa jiki kafafunsa ne kawai a waje.

Kallon hoton da ta ajiye ya yi kafin ya kalleta.

"Meye kike yi da wannan hoton!?"ya tambayeta yana matsowa kusa da ita.

"Ya Taj kawai na ji ina son gani ne"

Banzan kallo ya watsa mata kamar ze daketa.

"Fita ki bani guri".

Da sauri ta ce"to!to,ya Taj dan Allah inje in ga Asmita!?".

"Fita ki bani guri"ya sa'ke maimaita mata.

A maimakon ta fita din kamar yanda ya buƙata se ƙara tambayarsa da ta yi akan Asmita.

"Gobe za ki ganta"

Jiki a sanyaye ta ce "to".

"Kina da tabbacin za ki kai goben ne?"cikin rashin fahimta ta ce "bangane ba".

"Da kika ce to kawai,kina da tabbacin za ki kai gobene!?, Allah yakaimu ya kamata ki faɗa".

"Allah ya kaimu".

Ta juya da niyar fita a dakin hannunta ya rike.

Ya ja ta zuwa gaban mirror wani magani me kama da makilin na kashe raɗaɗi, ya bata,ya sa'ke jawo ta zuwa kan gado.

Umarni ya bata da ta hau ta zauna.

Tana dar_dar ta hau jikinta na ɗan rawa,yana ankare da ita,tsaki taja.

"Ubanme kike tunanin zan yi miki,da jikinki yake rawa haka"..

Ita de bata ce mishi komai ba.

Zama ya yi a gabanta ya juya mata baya.

Ita de ta rasa gane me yake kokarin aikatawa,zame rigar towel din jikinsa ya yi.

Zaro manyan idanunta waje ta yi gani ciwuka a bayan sa har waje biyu da alama da wuka aka ji masa su.

Jin bata fara masa komai bane ya ce"ki shafa min mana".

Hannunta na rawa ta matsa ta fara shafa masa kamar me tafiyan tsutsa,ita tsoro take ji karta fame mishi ciwo.

Tana tunanin to aina ya ji wannan ciwo haka.

Yau sun kama kuma sun kashe yan kungiyar Italian Mafia kusan mutane talatin a daji sun yi garkuwa da mutane rai bakwai se yan matan da suka kama,sun kai ashirin,da niyar yi musu fyade da kisan gilla su aikawa iyayensu.

Nan ne major Marry ta samu information akan inda suke shine ta turawa LTG,shine fitan da sukayi shida sojojin sa.

Sun kubutar da mutanen da yan kungiyar Italian Mafia suka kama gaba daya se yarinya daya da already sun yi mata fyade ta mutu.

Bayan sun kashe na kashewa ne sun kama na kamawa sun sa a mota,wani daga cikinsu batare da sun san dashi ba yazo da wuka ta baya da niyar ya kashe LTG, Allah be basa Sa'a ba,ya yanke sa s waje biyu.

Juyowa LTG ya yi ya damkesa,kamar wuyan kaza haka ya murde wuyan sa.

Hankalinta ya yi gaba wajen tunanin ta yanda ya ji ciwo ta taɓa wajen ciwon.

Sautin "ashhh" ya fitar saboda zafin da ya ji.

"Dan Allah ka yi hakuri Wallahi ba da gangan bane".

"Ki kashe ni kawai ki huta!,common shafa abu ne ba ki iya ba se wani shafe ni kike yi kamar wacce ta samu bayan kuliya".

Ya faɗa a faɗace.

Miƙewa ta yi,seda ta zo dede bakin kofa ta ce"tom sannu dama mutane irin ku ba'a musu gwaninta,gobe ko zakuna ne suka ji maka ciwo bazan taimaka maka ba".yi ya yi kamar ze miƙe ai kuwa ah million ta fice a part din.

Kwafa ya yi yaba bayanta da kallo "matsoraciya kawai".

Komawa part din anty amarya ta yi,ta samu ita take jira.bata tambayeta me ya rike taba.

"Kije ki kwanta dare ya yi".

"Seda safe mommy"ta faɗa tana daukar wayarta ta shiga daki na kusa dana anty amarya.key ta murza ta je kasan katifa da ta boye takardar tafito dashi.

Loda number jikin ta yi a wayarta,cikin uku ya yi aka dauka.

"Hello waye ne".

Muryar mutumin daya fara taimakon rayuwarsu ta ji ya sauka a kunnenta,da alamun kuka yake yi.

"My Sabriyah na yi kewarki sosai"hawaye ne ta ji ya taru a idonta.

Under her breath ta iya furta.

"Fu'ad!, da gaske kaine?".

"Ni ne my Sabriyah,ashe zan sake jin muryarki kafin in mutu na dauka se a lahira zamu haɗu,ina Asmita, na yi matukar kewarku"ya faɗa yana kuka.

Ita ma yanda taji yana kuka ne yasa ta fashe da kuka.

"Fu'ad kana ina ne,meye abinda ya faru dakai bayan rabuwar mu,"sune tambayoyin da ta masa.

Sa'ke fashewa da kuka ya yi "my Sabriyah, rayuwata tana cikin halin ha'ulayi.ina cikin masifa.wannan sojan da ya ɗauke ki ne ya kamani ya daureni kullum se an min azaba daban daban,abinda baki sani ba shine yasa aka dauke Asmita saboda yana son wannan memory nan a wajenta.ni kuma ya kashe min mamana da babana dan kawai ya nemi in faɗa masa in da ze same ku ni kuma naki.wannan dalilin yasa ya kashe min kowa nawa ni kuma ya min azaba wanda se da na rokesa da ya kasheni kawai".

Komai ji ta yi ya tsaya mata cak gumi ya fara yanko mata, al'ajabi ya hanata magana,taya hakan ze faru ashe duk tashin hankalin da ta shiga akan Asmita da Fu'ad dama LTG ne ya sace su?,dama abinda yake kullawa kenan,. wannan tambayoyin ta dinga yiwa kanta.

Nan take taji wani irin zazzafar ƙiyayyar lieutenant general Tajuddeen ya mamaye cikin zuciyarta,inda za'a bata wuka ko bindiga a ce ta kashe mutumin da ta tsana yanzu to shine wanda zata aika lahira.

Ganin ta yi shuru ne yasa ya fahimci cewa,ta faɗa tarkonsa,domin ya yi imani da taimakon Sabriyah ze samu damar kashe LTG, muddin in bega bayansa ba tofa babu yanda za'a yi shirin su ya yu, saboda barnan da ya masa yau bana wasa bane,ya kashe masa mutane sosai.

Cikin sheshekar kuka ya ce "my Sabriyah kina jina kuwa?".

"Ina jinka Fu'ad, kawai na ka sa yardan wai ya Taj ze iya aikata hakan ne".

"Sabriyah karki manta mugu bashi da kama,ze iya canza fuska duk yanda ya gadama".

"Hakane kam, Wallahi natsane shi,ban taɓa kawo ze aikata min haka ba".

Murmushi ya yi"yanzu kinsan taimakon da nakeso kimin".

Kamar yana gabanta ta girgiza mishi kai.

"Da taimakon ki zamu ka re mutane da yawa daga muguntarsa.dole ne mun yi hanyar da za'a kamashi yaje ya girbi abinda ya shuka.duk wani motsinsa ina so ki dinga sanar da ni,ki shiga jikinsa sosai ta yanda zamu dau fansar mu akansa.bincike za ki mana sosai akansa Kinga ke ce kuke gida daya,duk wani shirinsa daga zaran kin gano ki sanar dani".

With full confidence ta ce"na maka alkawarin aiwatar da hakan Fu'ad".ji ta yi kamar motsi yasa ta kashe wayar.ta ajiye agefe.

Jin bata sake jin motsin bane ya sa ta,kwanta tunani fal ranta, gaskiya ne maganar da Fu'ad ya faɗa mata shi mugu bashi da kama.

Se juyi takeyi amma bacci ya gagara daukar ta har karfe hudu na dare idonta biyu.

Yawancin ku baku san two pages nake haɗa muku ba, wanda hakan na nufin in an yi update yau, baza'a yi gobe ba se jibi.

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

Page 27

*_Story & written_*



By

*MRS🌹ISHAM🌹*

( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*

*NIDA PATIENT DINA*

~And now~

*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

____________________________

Page 27

Se da aka fara kiraye _kirayen sallah asuba ne bacci ya ɗauke ta.tasha kukanta san ranta hatta gaji.

Anty amarya ta tasheta ta hanyar kwankwasa kofar dakin da take kwance,tashi ta yi ta bude mata.

"Sabriyah lokacin ya yi" to "ta ce ta dauko hijab tabi anty amarya zuwa bedroom nata.

Bayan sun idar da Sallah nan ne anty amarya take sanar da ita yau malamin islamiyya ze zo yake koyar da su, boko ma gobe zasu fara zuwa.

Godiya ta yi mata Sannan ta hau kan gado ta kwanta dan kuwa ba ta gaji da yin bacci ba.ita ma kwanciya ta yi kusa da ita tana kallon yanda take bacci.

Karfe tara suka farka bacci,wanka sukayi suka shirya zuwa dinning ita de Sabriyah hijab ta saka dan yanzu dadinsa takeji.

Bedroom din uncle Hameed anty amarya ta nuna mata kafin su fita.

Shiga ta yi ta sameshi yana zaune akan sallaya da alamu tunda suka dawo daga masallaci be koma bacci ba.

Zama ta yi a kasan carpet tana gaisheshi.

"Ina kwana daddy"

Sunan da ta kirasa dashi, ya ji dadi sosai,tun bayan ɓatar Asrah ba'a sake kiransa da daddy ba.

"Lafiya klau sab,ya mommy ki!?"

"Tana Lfy lau, lokacin karyawa ya yi"murmushi ya yi, ya ce "to muje ko!?"

Ya mike suka fito a tare suka samu anty amarya tana tsaye inda ta barta.

Dinning suka shigo suka samu an gama serving din breakfast,kowa na wajen da murmushi suke kallonsu sun yi kyau gwanin sha'awa family.

Zama suka yi,ana cikin cin abinci Hajjatiye ta soma magana.

"Nikam meye ya hana, khareema da Huraira zuwa cin abinci cikin mutane sun maƙale a part din su kamar wasu munafukai,ko har yanzu khareema na nan da ba ƙin halinta nakin zuwa a ci abinci da ita"ta yi maganar tana tsare Abbie da ido.

Abbie bawan Allah gaba daya ya ma rasa ta ina ze fara sanarwar Hajjatiye da Ammuh bata cin abinci kwata_kwata da kowa,ba dan ya so ba ya mata karya ta hanyar faɗin.

"Hajjatiye!, khareema yau da ciwon kai ta tashi"

Dogon tsaki Hajjatiye taja ta ce.

"To waye ya damu da tsiyar tsinantakar ciwon kanta,mu din aka ce mata,wani lafiyar ne garemu ai sede kawai a ce Alhamdulillah,to Wallahi kar ta kuskura a sa'ke zuwa cin abinci ba ta nan ran kowa ze ɓaci".

"In sha Allahu, hakan baze sa'ke faruwa ba".cewar Abbie,dan ya lura Ammuh na son ja mishi magana ne a wajen Hajjatiye.dole ya taka wa rashin fitowarta burki.

Ta maida kallonta kan Abbu,kafin ma ta yi magana ya ce.

"Hurairah bansan me ya hana ta zuwa cin abinci ba".

Tabe baki ta yi,

"To ai dama iyayin su daya,ita da khareemar".

Su de sauran cin abincinsu suke yi suna saurarar abinda ke faruwa.

"Kuna gama cin abinci duk za mu tafi asibiti,bana son African time"Hajiya babba ta faɗa tana rufe plate din gabanta, alamar ta kammala cin nata.

Shurun da taga kowa ya yi basu tambayi waye a asibiti ba,yasa ta fara tunanin to waye ba lafiya.

Se kuma ta yi tunanin ko LTG aka kai asibiti tunda jiya bashi da lafiya.

Tabe bakinta ta yi, acikin zuciyarta ta yi maganar amma bata san cewa ya fito fili ba.

"Allah yasa ma shine"kallonta aka yi nan ta fahimci an ji abinda ta faɗa sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana wasa da spoon.

Hajjatiye ta ce "sanariya ke da waye haka". innalillahi ga dariya ga kuma basu isa su yi shi ba yanzu se ran kowa ya kusan ɓaci a wajen,wai sanariya, Sabriyah din ne bata iya faɗa ba take cewa sanariya.

Salim duk yanda ya so rike dariyar sa,abin ya gagara se fa da ya kwashe da wani dan banzan dariya kai kace wani zararre ne.

Cikin basaja ya soma faɗin.

"Haba Fatime taya za ki sakamin ruwan tea da yawa duba kiga duk na shanye,ashe zan iya" maganar yake yi amma dariya ya ci karfinsa.

Kowa na wajen ya gano sa.banda Hajjatiye.

Watsa mishi harara Abbie ya yi,irin zamu haɗu din nan.

Dakyar ya tsagaita da dariyar.

Hajjatiye ta ce"amma yaron nan an yi ja'iri, saboda kawai ruwan shayi ya yi yawa ka shanye ne yasa ka wannan dariyar,to zakaci kwal ubanka dakai da tsiyar tsinantakar ruwan shayin".

Tashi kawai ya yi yabar wajen dan ya lura inde Hajjatiye tana magana tofa baze fasa dariyar ba,har ta gano ita yake yi wa dariya,ga kuma kallon da yaga Abbie na yi masa.

Kammala breakfast din aka yi suka dawo falo suka zauna,anty Sameera na rike da baby a hannunta.

Ta cewa su Zoya.

"Ku din kun shirya ne" "eh a shirye muke"duk suna sanye da hijabs.

Sabriyah de yau ba wani son yin magana take yi ba domin abinda ta ji, jiya dashi ta kwana a ranta,duk tunaninta yanzu ya koma ne ta kan ta ya zata fara sanin menene abinda LTG yake shiryawa.shin taya zata shiga jikinsa yanda zata dinga sanin duk wani abinda yake shirin yi.

"Sanariya!,zo ki kira LTG kice mishi,zamu je asibiti"Sudais ya faɗa,yana tsokanar ta.murmushi ta yi dan ta gane tsokanar ce,wato Hajjatiye de ta sa mata wani suna daban.

Ba dan ranta yaso ba ta mike tana tambayar kanta "dama ba ya Taj bane a asibitin ba!?,to waye ba lafiya haka!?",da wannan tunanin ta shiga part din nashi ,ko sallama ba tayi ba ta kutsa cikin bedroom dinsa.

Baccinsa yakeyi gently,his innocent face looks so cute.

Yana cikin bargo ya rufe ko ina a jikinsa, fuskarsa ne kawai a waje.

"Mtsssw!a kwai kyaun fuska kam,amma babu na zuci.mugu kawai".ta faɗa a ranta.

Karasawa jikin gadon ta yi da niyar tashinsa a bacci da yake yi.wani tunani ta yi.

"Uhmm,yanzu ina tashinsa ze hau ni da faɗa kamar wani ubana,gwara in je in samu ya Sudais in ce masa,ya ce bazeje ba kawai "ta faɗa a hankali.

Tana gama faɗar maganar,ta ji an ja hijab din ta,a tsorace ta kai idonta kan fuskarsa domin ita ta ɗauka ya farka ne ya rike mata hijab,ashe cikin bacci ne ya juya ya daura kansa akan hijab dinta,da bata san ya aka yi ta daurasa kan gado ba.

A hankali ta sa hannuta ta fara kokarin jan hijab din nata yanda baze tashi ba.tana kallon kyakyawar fuskarsa,a lokaci daya kuma tana jan hijab din ta.

A cikin bacci yasa hannu ya riƙo hijab din nata gam a hannunsa ya cigaba da bacci.

Zaro ido ta yi ta bude baki ta ce"na shiga ukuna,yau in ya Taj tashi se ya kasheni"ta yi maganar idonta ya fara raina fata.

Wani irin juyi ya yi da,wanda kafin ta ankara taji ta gaba daya ta faɗo jikinsa.

Ji ta yi kamar zata yi fitsari a wando.ta rasa wata kalma zata yi amfani dashi wajen ceton kanta in LTG ya farka ya gansu a haka.

Jin mutum ya faɗo kansa ne,yasa ya bude manyan rikitattun idanunsa da sukayi ɗan yi ja saboda baccin da be samu a

28 / 33