ASHE ZAMUGA JUNA

Author :  MRS ISHAM Category :  Love

Chapter   22 / 33

63K to 66K   out of 97.2K words

yana tsula tsiyar da yake so,to bazaku kasheni ba se lokacin mutuwata ya yi ".magana take yi amma mom Rumanatu tana jiyo hucin da takeyi ta waya.

Dariya ne yaso kufcewa mom Rumanatu jin yanda Hajjatiye ta kira helicopter da anlikonta,ga kuma maganar dawuwarta da takeyi wai anki turawa a ɗaukota.bayan yau da safe aka gama waya da ita ana sanar mata kan cewa gobe jirgi zezo ya dauketa.duk yanda su Ammi suke mata ladabi da biyayya amma yanzu rikicin tsufa yasa tana cewa wai duk sun renata basa ganin girmanta.

Gyaran murya mom Rumanatu ta yi cikin kwantar da murya da ya,lallashi haɗe da girmamawa ta fara bawa Hajjatiye hakuri da kuma rarrashinta har ta samu ta shawo kanta.da kuma yi mata alkawarin gobe za'a zo a dauketa.

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

Page 21&22

*_Story & written_*



By

*MRS🌹ISHAM🌹*

( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*

*NIDA PATIENT DINA*

~And now~

*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

*Kamar yanda kuka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kadan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi dan banason bata lokaci ina gama book one za'a daura da book two*

*Ga duk me son biya, littafin ASHE ZAMUGA JUNA naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 09024503194 Mrs isham.*

_______________________________

Page 21&22

Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 2309617787 Fatima Abbas UBA BANK.duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min.

Ba ta daɗe da gama waya da Hajjatiye ba, su Ashman suka shigo da daddyn su,bata rai mom Rumanatu ta yi.ba tason daren da suke yi a waje.

Ta ce "yau kuma aina kuka tsaya!?"murmushi abu Sufyan ya yi,ya ce "amana afuwa mun tsaya wani meeting shisa mukayi dare".

"Shikenan abincinku na kan dinning"wucewa dinning din Ashman da Dawood sukayi dama a gajiye suke ga kuma yunwan da suke ji, mommyn su ta hana su cin abincin da bana gida ba.

Serving din su ta yi,itama ta zauna suna hira nan take cewa Ashman tana suyiwa Jaleelah da Iftisan dukan tsiya.

Kallonta Abu Sufyan ya yi "yanzu,yaran nan duka nawa suke da zakice wai a dake su!?,ni fa banason lamari da duka da faɗa".

Tabe baki mom Rumanatu ta yi domin ko baya nan se tasa an zanesu, wannan alkawarine,saboda rashin jinsu ya ishe ta.

Ashman deke cin abinci ne ya dakata ya soma faɗin"daddy gaskiyar magana,kai ka sangarta Iftisan da Jaleelah,gaba daya yara a ce ko laifi sukayi baza a musu faɗa ba" "ehh!na ce ba'a dake su din ba,ko kana da ja ne!?"shuru suka yi dan yanzu inde akan Iftisan da Jaleelah ne,se ku kusan yin faɗa da Abu Sufyan.

Canza hira mom Rumanatu ta yi,nan tabasu labarin yanda sukayi da Hajjatiye sun sha dariya kam, Abu Sufyan cikin dariya ya ce "Allah sarki Hajjatiye namu,Allah yakara miki lafiya da nisan kwana!"duk suka amsa da Ameen sannan ya sa'ke cewa"in ta shigo Katsina gobe,mu kuma se mu tafi Maiduguri jibi".haka suka ci ga hirar su suna taɓa abincin gabansu din.

Kammala cin abinci suka yi kowa ya wuce part dinsa,Abu Sufyan bedroom din Iftisan ya shiga ya sameta ta yi bacci,rufa mata blanket ya yi ya kashe wutan dakin ya shiga bedroom din Jaleelah zaune ya sameta rike da teddy tana kuka,da sauri ya karaso kan gadon ya zauna tana ganin shine ta rungume shi tana"daddy!".

Shafa bayan yar autar nashi ya yi yana tambayarta "meyafaru leelah! waya taɓo mini ke!?".

Sauke ajiyar zuciya ta yi "daddy kaga kullum se Iftisan ta dukeni, and se tasa mommy ta yi mana faɗa" "shikenan kiyi shiru bazata sake ba,nayi miki order favorite teddy din ki ke da Parsa in zakuje Maiduguri se ku tafi mata dashi".

Dariya ta soma yi jin an siya musu teddy .

Be bar bedroom din nataba se da ya tabbatar da ta kwanta sannan ya fita.

Washe gari 8:00am na safe,kowa na bacci su Khalifa suka dawo,da majinyata biyu da major Marry da kuma Asmita.

Khalifa ne ya shiga part din LTG ya sanar masa da sun dawo.

Fitowa daga part suka yi tare ya shiga na Saghar ya tashe shi daga bacci ya ce akwai patient din da ze duba,da ke suna da clinic a cikin gidan.

Kai major Marry da Asmita aka yi,da dukkansu suna sume,cire mata bullet din hannunta ya yi,ya kara mata ruwa,bayan ya gama treating din major Marry ne ya koma kan Asmita dake kwance kamar gawa,sosai ya dubata nan ya gane brain dinta ya ɗan tabu, sanadiyyar cocaine din aka dinga dirka mata ba dare ba rana, namiji ma me karfin ƙwaƙwalwa,in ana masa wannan shaƙar dole yamu matsala ɓalle ita mace me karamar ƙwaƙwalwa.

Duk wani abinda ze mata ta farfaɗo ya mata a haka suka fita daga clinic din suka koma cikin falo,nan Saghar ya ke sake faɗa masa binciken da ya yi game da brain din Asmita.

Gamsuwa da bayanan nashi ya yi,ya ce "is okay dama muna da bukatar sanin duk wani plan dinsu, yarinyar can ta bayar da memory card din, binciken ze zo da sauki,yanzu anjuma ka sanarwar da Jawan da Sudais ina son ganin su".

"Okay LTG, yarinyar nan tana buƙatar brain surgery,in kuma ba surgery ba she needs best medication and caring"cewar Saghar,haka suka dinga magana har suka isa part din LTG,a bedroom din Saghar ya koma bacci.

Kamar yadda suka saba yau ma haka karfe goma kowa ya fito saboda ya yi breakfast,anty amarya dake kusa da uncle Hameed, ƙa sa da murya ta yi mishi magana "daddyn Asrah dama tun jiya akwai abinda nake so in sanar maka to kuma se nayi bacci da wuri"murmushi uncle Hameed ya yi,ya ce "inajinki" "yanzu de ka bari se mun koma part din mu".ya gyada mata kai.

Uncle Hameed ya yi tambayar"ina Sabriyah!?", Rameesa iyayen surutu ta yi saurin faɗin "tana bedroom din ta, uncle ka san ita bata son cin abinci a dinning"girgiza kai uncle Hameed ya yi "wannan ba hujja bane"ya kalli fatime ya ce "je kice mata ina kiranta" "to" ta haura upstairs.

LTG shi ya rasa meye matsalarsu da yarinyar kowa maganar ta,shi ba wani son kallon fuskarta yake son yi ba.amma su daga sun zauna se sunyi maganar ta.

Saukowa dinning fatime ta yi ga Sabriyah dake bayanta sanye da wando jeans da riga ta yi donot da gashinta a tsakiya,

Tsayawa ta yi ta ce "ina kwanan ku"amsawa sukayi.ban da shi da ko ɗago kai be yi ba.

Uncle Hameed ya mata nuni da kujera dake gefen anty amarya "daga yau har sanda za ki tafi ki dinga fitowa Muna yin breakfast tare kin ji ko!?",gyada mishi kai ta yi sannan ta zauna, murmushi anty amarya ta mata.

Hajiya babba ta ce "yanzu ke ce kika zama cikiton yan matan suka zama guda shida,har na tuna da Asrah da tana nan nasan da yanzu ta damu kowa da surutu", murmushi uncle Hameed ya yi yana tuna irin rigimar da Asrah take yi.

"Da yanzu ta na nan nasan da tana gefen LTG ta dameshi da surutu,ko kuma wajen Ammi".

Duk murmushi sukayi hatta shi LTG din jin an fara hirar farin cikin rayuwarsa,hakan yasa shi murmusawa.

Anty amarya ta maida hawayen da taji yana son fitowa daga idonta,ta ce"nasan da Asrah na nan, da ta ce mommy ki goyani,hhhhhh!ko da yake ma nasan inta girma bazata yi ba,sede shagwabar da ya riga da yabi jikinta daga anyi mata faɗa zata fara kuka tana neman Tajuddeen dinta",duk jikin su ne ya yi sanyi sosai jin yanda muryar anty amarya yake fita.

Cikin zolaya dan ya kawar da damuwar kan fuskar anty amarya Saghar ya ce"Abokiyar faɗa ta ba, kullum se munyi faɗa, ga kuma LTG dake shiga mata faɗa, lokacin da LTG ya samu addimission,na yi farin ciki sosai saboda na sa araina in ya tafi zanci zalinta sosai"dariya sukayi gaba dayansu hatta LTG se da ya murmusa.amma babu wanda ya lura da hakan Saboda kansa dake ƙasa yana danna waya.

"Yanzu da zan samu ganin yar kanwar tawa zan jata a jiki sosai bazan taɓa barin muyi faɗa ba, ko da kuwa rashin jinta ya zarce na Umaisha da Rameesa"nan ma murmushi suka yi,yau de gaba daya hirar su akan Asrah ne,babu wanda ya saka abinci a bakin shi se hiran da suke yi,duk suna cikin nishadi da kuma kewarta sosai,a duk sanda aka fara hirar Asrah a gidan tofa se sun dau lokaci me tsayi sunayi domin tunawa da ita.

Murmushi Zoya ta yi, ta ce "bana manta lokacin da muna yara haka zamuje wajenta dan muyi wasa amma haka zataki binmu se munyi dakyar kafin nan zata yarda". "To kin manta lokacin da mukaje painting room muka dauke zanen da take yi muka gudu a hanya muka yagashi!"cewar umaisha.

Ammi ne ta yi dariya"ai yanzu da tana nan kaf dinku da mun aurar da ku "rufe fuska Parsa ta yi tana dariya.

Ummah dake gefe ta ce"wato anyi maganar aure kin rufe fuska"dariya sukayi,ganin tana ta dariya.

Tun lokacin da suka fara hirar su suna ambaton sunan Asrah ta farajin kanta na wani irin juyawa,a duk lokacin da aka ambaci sunan se taji tsigar jikinta ya tashi ta rasa meyasa hakan,kuma ita tunda tazo gidan bata ga Asrah din da suke magana akai ba 'shin tana ina ne to?' ta jefawa kanta tambaya.

Dakyar ta kauda damuwar kan fuskarta ta ce "Ammi to ina Asrah din yanzu take!?".

Anty amarya dake gefenta ne ta bata amsa da "Asrah bata a tare damu,bamu san duniyar da take ba ko tana raye ko tana mace!,amma ni a har kullum ina da yakinin tana raye kuma ina jin kusancinta, ina rokon Allah yasa koda a ranar da zan bar duniya ne inga ƴata". tausayi sosai anty amarya ta basu,sun san tana cikin damuwar da ita kadai tasan zafin da take ji.

Shuru Sabriyah ta yi jikinta a mace.ashe kowa yana shiga irin wannan damuwar idan ya rasa farin cikin sa,ta dauka ita kadai ce takejin zafin rabuwa da Asmita.

Murya a karye ta furta"Nima na shiga irin wannan matsanancin damuwar da tashin hankali a lokacin dana rasa Asmita,kowa yana jin ba daɗi a duk sanda ya rasa wani bari na rayuwarsa".

Duk kallonta suka yi cikin jimami,Ammi ta ce"in sha Allah, Allah ze bayyana mana su".

Murmushi me ciwo anty amarya ta yi bata iya cewa komai ba.

Mikewa LTG ya yi a dinning din ya fice daga Mansion din gaba daya.

Bin bayansa da kallo sukayi sun san an fama mishi inda ke mishi ciwo ne yasa ya tashi ba tare da ya yi breakfast din ba.

Serving din kowa abinci Fatime ta yi.suks fara breakfast.

Tashi ta yi ta zauna a tsakiyar gadon da aka kwantar da ita. ƙarewa wajen kallo ta yi sannan tasa hannu ta fincike ruwan hannunta,tsoro ne yakamata ganin ita daya ce a dakin yasa ta fashe da kuka,kamar karamar yarinya.

Fitowa ta yi acikin dakin tana tafiya tana kuka harta iso cikin main part falo,bata dena kukan ba.

Cikin yarinta ta soma kiran sunan Sabriyah,tana tura baki .

Tana kokarin kai bread bakinta taji kamar murya Asmita ce ke kiranta hakan yasa ta kasa kunne ko zata sake ji, amma shuru hakan yasa tayi tunanin ko imagination da ta saba yi ne,dan haka kullum se ta ji kamar Asmita na kiranta.

Ci gaba da breakfast dinta ta yi,da ɗan karfi taji an sa'ke cewa "Sab.....ri....yah".

A zabure ta mike tsaye wanda yasa duk seda suka kalleta, tambayar ta Sudais ya yi "Sabriyah lafiya!?".

Cikin rawar murya kamar me shirin yin kuka ta ce, "ba kuji kamar ana kirar sunana ba!?,muryar Asmita nakeji"da mamaki suke kallonta amma ɗan son tabbatarwa se suka kasa kunnesu suma,nan sukaji "Sab..ri....yah" tabbas su ma sun ji an kira sunanta,da gudu ta bar dinning din suma miƙewa sukayi suka rufa mata baya.

Tana shigowa tsakiyar falon taga Asmita a tsaye se waige_waige take yi da alamar ita take nema,farar fatarta ya yi duhu ga gashin kanta daya hargitse kayan jikinta kansa ya yi datti.

Kamar a mafarki take kallon Asmita murya na rawa ta ce"My Jerry"da sauri ta juyo jin muryar Sabriyah,da gudu suka rungume junansu suka fashe da kuka me ban tausayi,sunkuyawa ƙasa sukayi har lokacin suna rungume da juna,shafa bayan Asmita Sabriyah takeyi tana kuka dan tayi matukar kewarta kukan farin ciki, da kuma na kewarta takeyi ga kuma ganin yanda duk ta lalace kamar ba Asmita ba.

Dakyar ta dakata da kukan ta ce "my Jerry su waye suka sace ki,ya akayi kika zo nan"a maimakon ta bata amsa se turo baki ta yi "my Tom ba kece kika gudu kika barni ba!,tom muje mu hau lilo kinji"zaro duk idanunta waje ta yi kamar zasu fadi ka sa domin tunda Asmita ta bude baki ta fara magana ta fahimci ba a hankalinta take ba ga yanda take magana kamar wata karamar yarinya me kananun shekaru.

Tallafo fuskarta ta yi da duka hannunta biyu ,"my Jerry meyasa kike magana kamar yarinya karama Meye abinda wayan'can mugayen suka Miki!?"oho ita de bata fahimci inda zancen ta ya dosa ba.hakan yasa ta zuba mata ido kafin kuma lokaci daya idanunta ya rufe ta kwanta ajikinta, jijigata Sabriyah ta yi taga bata motsi.

Suna tsaye a falon suna kallon su tausayinsu ya cika su,ganin irin shakuwar da ke tsakanin su,dole ne in babu ɗaya,dayan su ya shiga damuwa,ga kuma mamakin abinda ya faru da Asmita suke yi.

Kusa dasu Saghar yazo ya tsaya yaga yanda ta daga hankalinta.

"Sabriyah ki kwantar da hankalinki!jiya LTG Taj yasa aka kwato ta daga wajen yan ta'adda,ta samu matsalar ƙwaƙwalwa ne ta sanadiyyar shaƙa mata fodar ibilis din da suka dinga yi hakan ne yasa ta samu matsala ,in sha Allah zata warke".

"

Wani shock Sabriyah taji tunda ga tafin ƙafanta har zuwa tsakiyar kanta,wai Asmita ta samu matsala a kwakwalwarta.

Kamar wata wawiya ta ce "matsala a kwakwalwa kuma ya Saghar!?",gyada mata kai ya yi,kuka tasaka tana kallon kyakkyawar fuskar Asmita da ya yi fayau.

"Kiyi hakuri Sabriyah wannan kukan bashi da amfani ki mata addu'a kawai tunda Allah yasa Tajuddeen ya sa an kwato ta,ku taimaka mata,a kai Asmita daki"cewar Ammi.

Su Umaisha ne suka taimaka mata wajen ɗaukan daukan Asmita suka tafi part dinsu.

Zama sukayi a falon uncle Hameed ya ce "gaskiya na tausayawa rayuwar yaran nan duk da bamu san labarin su ba" "ni kaina rayuwar su tausayi yake bani,musamman da Sabriyah ta faɗa mini daga garin da suke".

"Tun jiya nakeson sanar da ku abinda ke zuciyata kuma nasan zaku bani goyon baya akan hakan".cewar Anty amarya,maida hankalinsu kanta sukayi domin jin menene take son sanar dasu.iya kan su ne a falon se su Sudais,su Umaisha kuma basa nan.

Ci gaba da magana anty amarya ta yi "na yanke shawarar zan yi adopting din Sabriyah in mayar da ita ƴata banason tabar wannan gidan,nayi rashin ƴata Asrah wacce ita ce farin cikina banida damar iya haihuwar wata yar,tunda banida mahaifan daukan wani cikin,tun ranar dana fara ganin Sabriyah naji ta shiga raina, Allah ya daura mini son yarinyar,jinta nakeyi kamar jinina!,kamar ni na tsuguna na haife ta haka nake ji.zan maye gurbinta da Asrah kafin Allah ya bayyana mini ita in rikesu su biyun.zan zame mata uwa da ba ta dashi,zan zame mata duk wani gatan da ta rasa,zan mata komai, makaranta boko da islamiyya".

Shuru ne ya biyo bayan,duk sun yi shuru suna nazari akan maganar da ta faɗa,sun san inde ta ɗauki Sabriyah din hakan ze rage mata raɗaɗin da takeji na batan Asrah,kuma inta yi haka zata samu lada.

"Mun ji bayanin ki kuma ni kaina,na gamsu da hakan sede ki bari su Abbie su dawo,se mu ji ta bakinsu tunda Kinga sune manya"cewar Hajiya babba,sun gamsu da zancen ta,tunda yaran nan in an barsu sun tafi ruwa zasu sake komawa.

"Ohhhhh!wato Abida ta nan ta bullo kenan,dole in samu Hajiya khareema in bata wannan sabon labarin"duk wannan zancen da Ummah take yi a zuciyarta take yinsa.

Suna a falon ne nurses guda biyu suka shiga sanye da uniform, Saghar ne ya kira su domin kula da Asmita shi bayi da wani isheshen lokaci.

Kallon kaltume Saghar ya yi ya ce"please kaltume dan rakasu dakin Sabriyah mana".

Bismillah ta musu ta yi gaba su kuma suka biyo ta abaya.dakin suka shiga nan suka samu Asmita dake a sume,ga Sabriyah a gefenta ta zuba mata idanu tana kallon ta ga tausayinta fal ranta,tama rasa ya zatayi,ji takeyi dama matsalar ƙwaƙwalwar ya dawo kanta.

Gabatar mata da kansu sukayi ,su ka sheda mata sune masu bawa Asmita kulawa,ta yi murna sosai duk dama ita dayanta za ta iya kulawa da Jerry dinta.a zuciyarta kam mamaki ya kasa dena mata,a ce LTG ne ya ceto Asmita,batasan da wani irin baki zatayi amfani wajen gode masa ba.

Dan Allah ki dan bamu waje zamu dubata ba dan ranta yaso ba haka ta fita ta basu guri.

Ruwan Allura dayar nurse din ta ja a syringe,ta je gaban Asmita ta tsaya tana jan hannun rigarta kasa zata mata,kamar wacce tasan allura za'a mata ta mike da sauri ta ɓige hannunta,ta koma can kuriyar gado

22 / 33