Sarki Sameer Book 3 By Yaya Azeema

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   56 / 57

165K to 168K   out of 170K words

kuma soyayyar dake tsakanin su, hakan yasa bazasu iya haƙuri ba zuwa koda washe gari ne adaren ranar dukan su aka dawo dasu cikakkun ƴan mata, ko wacce ta karɓi gashi ta gane Allah ɗaya ne a wannan ranar,

 
                 After 3 days.....

Kamar yanda Meer ya ɗauki alƙawari Saida ya cikasa dan duk nacin Ameesha dole ta rabu dashi ta haƙura ta zauna dashi, a kwanakin nan kam har ta fara saba dashi da abubuwan da yake mata, 

Soyayya kam da ƙwarewa wajen iya salo na musamman ba'a magana domin Meer na dabanne duk wani salo da zaiyi amfani dashi wajen ganin ya kashe mace da su shi yake yiwa Ameesha, saida ya sabar mata da komai da wasu salon sa duk saida ya koya mata,  kuma yaci sa'a kam duk tana kwashewa, kunyace wataran kawai take hanata nuna masa,

Suma su Papa kawai zuba musu ido sukayi babu wanda ya ƙara neman su, bare Meer yagayawa mutum wacce zai kwana a zaune yakasa bacci,

A cikin kwana ukunnan itama Hamra ankaita gidan nata mijin, sannan kuma anbawa Hamza sarautar mahaifin sa, an ɗora sa akan karagar mulki tare da tarewar santaleliyar gimbiyar sa Hamra,

A ɓangaren Meer kuwa koda suka fito da Ameesha yana manne da ita duk kunyar da take ta faman ji, shi ko ajikin sa babu wanda yake jin kunya, Abu nema yaso yayi masa faɗa, ya dakatar da shi tunda wuri yace ai dai matar sace ba matar wani ba, dan haka yana da iko da ita inyaga dama ma, zai iya ɗauke ta babu wanda zai ƙara ganin ta,

Daga nan babu wanda ya ƙara yi masa magana akan abun da yayi, dan anga alamun yanzu ba wanda suka sani ba, ya ƙaro rashin mutunci, ga rashin kunya da yakowa da ba'asn daga inda ya koyo taba, idan yana abu kamar bashi ba,

Ameesha tayi matuƙar farin ciki da ganin an haifa mata ƙanwa, sai nan nan take da yarinyar kamar ta cinye ta haka take ta faman nuna farin cikin ta, da son yarinyar, dan koda Meer yasaka ta agaba akan sai sun tafi kamar tayi kuka saida tace abata ƴar ta tafi da ita, Maman ta ta kore ta tace bata son shashanci, ta tafi tabata guri, 

Tunda suka fito take ta faman tutturo baki ita ala dole haushi take ji, akan me zai tursa sata gaba akan sai ta tafi, gashi yaja mata faɗa gurin maman ta, ta koro ta,

Tsokanar ta yai tayi daga ƙarshe yace "indai baby take so tabari zata haifa mata yana nan zuwa, nan da watanni tara masu zuwa,

Nan ma ƙara ƙullar da ita yayi harda sukai masa duka shi kuma yasamu abun da yake so, daga nan aka zarce harka, dan tafi jin rarrashin da kyau.......

          ************************

Yau sati guda da haihuwar Maman Ameesha, duk da ance ba suna amma duk da haka saida mutane da dama suka zo, aka ci aka sha aka sanya wa yarinya sunan Maama (SABREENA) inda zasu ringa kiran ta da Bibi.....,

Ameesha sai aranar suka haɗa da su Azeema, amma ba Hamra acikin su, dan bata samu damar zuwa ba, ɗaki guda suka ware suka shige aka ringa buga hira, suna tsokanar ta wai ita takai kanta ɗakin mijin ta tun kafin a kaita, nan take basu labarin abun da yafaru ranar denner ɗin su,  sunyi mata dariya sosai tare da mamakin yanda akai yayi mata haka,

Tunda suka zo hira kawai suke daga a taɓa wannan sai asaki a ƙara kamo wata hirar haka suka wuni sunayi, dan abinci ma sai nan aka kawo musu,

Da daddare kowacce mijin ta yazo ya ɗauke ta, nadan son ransu ba suka rabu, suka tafi gidajen su.......

Bayan kwana ɗaya da suna, kawai aka ga anhau rushe rushen wasu ɓangarorin na cikin masarauta, daga ɓangarorin kuwa harda ɓangaren inda fada take,

Wasu duk zubawa sarautar Allah ido sukai dan basu san me ake shirin yi ba,

Kan kace me a cikin sati guda har antada gini masu kyaun gaske, fada kam gaba ɗaya a canza mata fasali an ƙwata sosai, tare da zagaye ta da abubuwa masu kyau da ƙayatuwa,

Sati biyu aka ɗauka ana gudanar da gyararrakin da akeyi, zuwa yanzu an kammala komai, ita kanta wajen masarautar sai aka gyara ta, duk wanda yazo ya ganta cewa zaiyi sauya ta akayi gaba ɗaya.........

Daga waje aka rubuta sunan ta da manyan baƙi,

MASARAUTAR SARKI SAMEER.....

              *********************

Lungu da saƙon cikin gari da gidajen rediyo da tv da kafafan yaɗa zumunta kowa ya shaida da sabon sarkin garin Kano da za'a naɗa, aranar Juma'a uku ga watan may,  kuma ana gayyatar kowa da ya hallici wannan taron naɗin sarkin da za'ayi,

Kuma mutane da yawa suna murna da alƙawarin son zuwa gurin taron,

   💃💃💃💃💃💃
Yau naɗin sabon sarki💃💃💃💃

An ƙawata cikin fada sosai da ado kan kujerar kuwa kamar ba mutum ne zai zauna ba saboda kyaun ta, ga gwalwa gwale da akayi ado dasu ta ko ina ajikin kujerar, ita kanta cikin masarautar abun kallo ce bare kuma kan karagar mulkin,

Wajen ƙarfe sha biyu na rana, aka gama naɗa sarki tare da ɗora sa akan kujerar sa, sannan ya amsa wasu tambayoyi da akeyiwa duk wani sarki idan ya hau kan kujerar mulki, tare da rantsuwa da Alqur'ani da yin alƙawari kula da duk wani wanda ke karkashin sa, da gudanar da mulki cikin adalci da tausayawa mabuƙata,

Dagana aka sallami manyan baƙi da suka zo daga nesa, tare da sanar da jama'a zuwa anjima ƙarfe 4:00 pm za'ayi hawan sarki.....,

  Tun kan loƙaci yayi Cikin masarauta da wajen ta kai bama iya nan ba gaba ɗaya garin Kano ya cika da al'umma, domin wannan karin har waɗanda ba'ayi tunanin su ba Saida suka zo,

Daga cikin manyan baƙi harda dangin Ummy da suka haɗo ƙwansu da kwarkwatar su suka taho,

Can na hango wasu zuga ana ta kiɗai kiɗai da ganguna tare hura sarewa,

Idan kazo filin wajen dokuna ne masu kyau da akayi musu ado nagani na faɗa wani gurin ma gold aka saka wajen kwalliyar dokin sarki,

Nan aka ƙara fitowa da sarki cikin sabuwar shigar sa, gefen sa kuma matar sa sai ɗayan gefen mahaifayar sa, daga baya kuma su Maama ne da sauran ƴan uwa duk sun saka shi a tsakiya, sai daga can bayan su kuma masu take musu baya gaba ɗayan su, harda jami'an tsaro, saboda guri irin haka dole sai an haɗa da jami'an tsaron,

Haka suka tun karo wajen da dokuna suke, yana tsakiyar su yana taku ɗaiɗai kamar ba ƙasa yake takawa ba, ga hali kuma ga mulki abun ba acewa komai,

Nan guri ya ƙara rikicewa da ihu da hayaniya aka ƙara volume ɗin kiɗan, wasu na kiɗa maroƙa na kwararo kirari,

Suna ƙaraso wajen, Gaba ɗaya guri kowa ya zube a ƙasa ana gaida sarki, maroƙa kansu a ƙasa suka shiga jerowa sarki kirari,

Waɗan da suke bayan sa suka shiga cewa gyara kintsi da kyau, ga sarkin namu nan ya iso akula da kyau a kiyaye harshe da kuma ido, sarki sarki ne ayi gaisuwa da kyau,

Ɗaya daga cikin maroƙanne ya karɓesa da cewa....
"Taka warka lafiya sabon sarki Allah ja da zamanin ka, Allah ya kare gabanka da bayan ka Allah yasa kafin haka, sarki me adalci Sarkin adale, kai sarki, mahaifin ka sarki, kakan ka sarki, mahaifin ka kanka sarki, kakan mahaifin ka sarki, kakan kakan kakan ka sariki, mulki gaba da baya, babu wanda ya isa yaja dakai, duk wanda yayi hakan kuwa sunan sa asararre kuma dole ya karɓi hukuncin da yadace da shi, Allah ya kawar da idon mahassada daga gare ka, kafi ƙarfin su kafi ƙarfin kowa kafi ƙarfin ma ƙiya.........nan ya zage yana ta zabga kirari kala kala,

kowa ƙasa yayi da kansa babu wanda ya ɗago saboda sarki zai hau doki,

Daga shi sai ƴan uwan sane suke kallon sa, Ameesha na gefen sa da taimakon ta  dafafa ka faɗar ta yayi sannan ya hau kan dokin,

Sai loƙacin kowa ya ɗago suka ci gaba da kirarin,

A can wani ɓangare ma, su Sam sun shirya nasu dawakan tare da tarin abokanen su, duk sun ɗane kan dokunan tafiyar sarki kawai ake jira,

Wasu ma ɓangaren sun shirya domin dokuna da yawa aka siya shiyasa Saida aka tara mutanen da zasu hau kai,

A hankali dokin sarki ya fara tafiya, sannan su Bosaya suka fara mara masa baya, suna tafiya mutane na datsewa suna rabewa su basu hanya.....,

Komai ya tafi yanda aka shirya, harda masu ƴar tsere da dawakai, basu suka gama gudanar da komai ba saida aka kira sallar magriba,

"Dan daman  wasu tundaga wajen hawa wasu suka tafi gida,

Bayan sallar isha'i da mutane duk sun tafi, na ne sane da kuma ƴan uwa na jiki su kaɗai duk suka rage, suma kuma duk da safe zasu wuce, dangin Ummy kam da asuba zasu ɗauki hanya jirgin su ƙarfe bakwai zai ɗaga.....

***********************

Bayan wasu watanni da ɗora Sameer akan mulki, ba laifi yana ƙoƙarin gurin gudanar da mulkin duk da bayaso amma haka yayi haƙuri ya karɓa tunbaya so har abun yazo ya fara shiga ransa ya fara sabawa da sarauta,

Bai wani daɗi ba da hawa amma kowa zancen sa yake duk da idan aka taɓoda ba sauƙi kowa yasan waye shi, ana jin daɗin mulki, idan kaga ya ɓatawa wani rai to kai kajawa kanka ko kuma kayi ƙarya ko ka aikata wani babban laifin sannan kaima zaisa ayi maka hukuncin da yayi daidai da laifin da ka ai kata,

   Ameesha na ɗauke da cikin wata shida dan Meer yayi gaskiya tun a bugun farko ya jefa ƙwallon sa ya shige, har ƴar musu suka ƙulla akan idan anyi gwaji anga yayi daidai da ranar aka sameshi zatayi masa kyuata shima kuma yayi mata alƙawarin idan ba haka bane, zai mata babbar kyau ta,

Ana gwaji kuma aka gano hakane loƙacin da akayi gwajin akace musu wata ɗaya da kwana shida daidai suna irgawa kuwa aka gano ranar ce, Nan ya riƙe Ameesha har saida tayi masa kyautar wani abun sannan ya rabu da ita......yanzu dai cikin ta wata shida yana cikin na bakwai,

Cikin ta na samun kulawa ta musamman ta ko wane ɓangare, sarki Sameer kuwa awaje yake sarki da zarar ya dira ƙafar sa acikin ɗakin sa yake ajiye sarautar sa, gefe dan watar ana rakosa idan fadawan sa suka fita yake sa hannu ya tsige rawannin kansa da samun sa yake, da ƙyar Ameesha ta hanasa cire wa, idan yadawo take zama ta warware masa,

Duk da haka bai manta da soyayya ba yin abarsa yake kamar yanzu hafara shigar ta,

Itama kuma ta saba dashi sosai suke nunawa juna so da ƙauna, daga ita har shi har bansan waya fi son wani ba.....,

Watannin haihuwar Ameesha ya cika Suna kwance cikin dare na ƙuda ta riske ta, nan ta tashe shi cikin tashin hankali baisanr da kowa ba ya kasashe ta suka tafi asibiti, inda Allah ya taimake ta bata da nauyin na ƙuda suna zuwa ba daɗewa ta sintilo santalelan ɗanta masha Allah dashi,

Saida Meer ya koma gida, da kansa ya haɗo mata duk abun da yasan zata buƙata shima kuma ya canza shiga zuwa tasa ya fito a Sarkin sa, sannan ya fito tare da drivern sa, shine ya mayar dashi asibitin, sai yanzu wasu mutanen da dama suka lura dashi ne, danma dare ne babu mutane sosai acikin asibitin,

Baisanar da kowa ba saida gari ya waye sosai ita kanta Ameeshan ta farka daga ɗakin hutun da akayi kaita, tunda asuba ta farka,

Meer na gefen ta tare da yaron a hannun sa, a zaune ya kwana kawai yana kallon ɗan,

Saida tayi masa magana yasan ta farka, da sauri ta tashi zaune yana miƙa mata ƴar kusan sussucewa tayi da murna wai wannan ɗanta ne da cikin ta ta haifesa,  rungume ɗan tayi tana me jin wata muguwar soyayyar sa aranta,

Meer ne ya ƙarasa bakin gadon ya rungume su gaba ɗayan su ita da ɗan,

Yana ƙara shi mata albarka tare da yi musu addu'o'i su su duka,

A gurin ya tambaye ta wane suna take so asaka masa, nan tace ta basa zaɓi, take kwa ya gaya mata ra'ayin sa, shi sunan sa yake so yasawa ɗansa saboda ya ɗauko halayen sa sannan kuma ya gaje sa,

Goya masa baya tayi tare da nuna jin daɗin ta da hakan,

Sai wajen ƙarfe goma labari ya riske masarauta, SARAUNIYA KHADIJAH ta haihu,

Wayyo murna kamar a kan ta aka fara samun ɗa,ai munti talatin yayi yawa asibiti ya cika taf da mutane, ana ta zuwa barka, gani akai asibitin na neman yi musu maɗan hakan yasa suka tattara suka koma gida,

Gida akaci gaba zuwa, aranar kawai sai ga labari yazo musu daga Gombe itama Hamra ta haihu amma ita mace ta haifa, murna sai ta kuma ƙaruwa,

Su Amra duk suna hanya dan Sumayya ko zuwa ma bazata iya yiba saboda nauyin da tayi itama haihuwa Yau ko gobe,

Su Azeema ma ana ta faman kayan ciki haka suka zo ita da Amra, Amra cikin ta watan shi bakwai ita kuma Azeema wata takwas itama ta kusa haihuwa,

Sati na zagayowa akayi suna inda aka sanar da mutane sunan da aka kuma sawa anƙara saka Sameer wajen na shida kenan a masarautar, in ka cire mutum ɗaya Sarkin farko da ya mutu, sai kuma Abban Ameesha, Abuu, Sam, Meer, sai kuma auta da aka haifa yanzu,

Mutane sunyi murna da hakan dan ana ganin hakanne ya kamata tunda masarautar ma gaba ɗaya da Sameer ake amfani kamata yayi ace duk sarkin da ya hau idan ya haifi ɗa yasanya masa sunan saboda hakan sai yafi tafiya daidai ta yanda baza'a taɓa mantawa da sunan ba, koda kuwa Masarautar zatayi shekara sama da ɗari za'a samu sunan.

Ranar suna anci ansha ba ƙaraya dan ba ƙaramin taro akai ba acikin harabawar masarautar, kowa teburin sa daban abin ci za'akawo kayi sarving ɗin kanka da kanka,

Can na hango teburin ƴan group ɗin sarki Sameer an gyara zama ana ta kwasar waku, Aunty me jidda na hango da cinyar kaza ankai baki ana yagar ta da hannun biyu, bakin ta duk ya ɓaci da mai saboda ci,

Mrs me martaba naji tana kallon Bajatu tace ke me kuma meye hakan kikeyi sai wani yagan mu, da sauri Bajatu ta ɗago tana mata alama tayi shiru a hankali tace ke ƴaƴana zankaiwa tana faɗa taci gaba da kwasar abincin tana zubawa a cikin jaka,

Mrs me martaba ta ɗan yi shiru can kuma tace kai kuma fa kinyi gaskiya wallahi nima ɗiba, zanyi yo Allah na tuba abun da baka saba ci ba, yau banza ta samu ai kinga fa sauran ma duk ba aciba, wallahi badan kar aganni ba da sai naje na kwaso waɗancan lemukan,

Mr Saif tace "ku wallahi kuyi a hankali kar wani ya ganku, ku ta abinci kuke ni  kun san me na shirya duk ɗagowa sukayi suka haɗa baki wajen cewa a'a, itama tace kunga wancen kuɗin da ake liƙawa ƴan dubu dubu, su zanje in kwasa kallar su fa da yawa su kansa masu kwasar basa kwasa, Maman Faruk dake gefe tayi musu shiru tace da camara dai duk wanda yayi ana ganin sa,

Ƴar baba tace ƙyalesu dai, ni wallahi ma duk sun ban haushi, sai sunsa anyi mana kallon ƴan can garin,

Gaskiya dai nima sun ban amma dai dan Allah idan kun kwaso, su Bajatu  nima ku kawo min in ɗanɗana abincin gidan sarki Sameer kar abarni a baya,

               After 10 yeare ago......

Bayan haihuwar kowannen su na kowa aka nema masa aiki ɓangaren da ya karan ta,

Su Ameesha an zama lauyoyi, inda ta cika burin mahaifin ta, su suka ɗau case ɗin gidan su inda aka fito da su daga wajen sojoji aka gurfanar da su gaban koto tare da bada ƙwararran shedu, 

Ba awani ja case ɗin ba aka yanke wa kowanne su hukunci, Ammah da ƙanwar Dadda da kuma Dadyn Rasheeda life in prison, sauran kuma gaba ɗayan su tunda basuyi kisan kai ba aka yanke musu zaman shekaru ashirin ashirin wanda wasun su ma balalle bane sukai ashirin ɗin basu mutu ba....,

A ɓangaren su Rasheeda kam abun sai gaba da yayi dan ba Sa'a, suna can ƙauye mom wataran sai tayi bara take samun abun da zataci,

Rasheeda kam da taga ba hazi bare hazihi tuni ta koma ƙauyen daga baya kuma wanda de batason ko gani shi ta aura dan har barazana yayi mata idan bata yarda ba sai ya lalata mata rayuwa daga nan kuma ya kashe ta,

Jin tsoro hasa ta amince tun tana ƙyanƙyamin sa har ta dena amma sai ta fara sana'ar kayan ƙulle ƙulle da kuɗin da yake bata taja jari, shima kuma loƙacin ya ɗan ƙara kuɗi, da wayo da wayo ta ringa sakashi yana gyara jikin sa da wanke bakin sa, Allah ya taimake ta kam duk ya gyara, saidai ƙauyan ci kawai da shirme,

Da ƙyar mom itama Allah ya rufa mata asiri ta samu wani tsoho ya aure ta amma irin mazannanne masu ɗaukar mata ba abakin komai kuma shi ba'a haihuwar masa agida, duk wacce ma ta aure sa tasan da hakan, kuma laifi kaɗan zakiyi masa ya kamaki ya jibga son ransa,

Duk wannan rayuwar da suke Khalid bai sani ba babu irin neman da baimusu ba amma ya rasa inda suka shiga saboda baisan sunan ƙauyen da suka koma ba,

Ranar wata laraba, yaje wata kasuwa kawai ya haɗu da Rasheeda duk ta lalace ta fita hayyacin ta kamar ba ita ba ya tausaya mata sosai, nan ta kwashe duk abun dake faruwa da rayuwar da suka tsinci kansu ciki, har kusan kuma yayi musu, dan duk wannan abun ba kowa bane yaja musu illah mahaifin ta alhakin abun da mahaifin ta ya aikata ne yake ta bibbiyar rayuwar su, nan yabita har inda suke ya taimaka musu da kuɗaɗe sannan yace zai ringa zuwa yana duba su, sannan yabata shawara yace ta kira mahaifiyar

56 / 57