Sarki Sameer Book 3 By Yaya Azeema

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   12 / 57

33K to 36K   out of 170K words

sannan suka bar wajen,

Tun suna cikin mota Meer yake ta faman waya, har suka ƙarasa wata unguwa da babu wanda yasan inda suka dosa,

Wani gida yakasu da tun zuwan sa yasa ka wani abokin sa da suka haɗu a Abuja kuma ɗan garin kano ne, shiyasa tunda abun yafaru yasa shi ya lalubo masa gidan,

Suna shiga suka ajiye su acikin gidan, sauran kuma Meer yasa ɗayan driver ɗin yakai su Ameesha gida.......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
Suna shiga suka ajiye su acikin gidan, sauran kuma Meer yasa ɗayan driver ɗin yakai su Ameesha  gida.......,

Meer bai baro gidan ba saida yagama duk binciken da zaiyi akansu, sannan ya bar mutum biyun da yataho dasu su kuka dasu, sannan yatafi gida,

Loƙacin da yaje gida kowa yayi bacci yakarasa part ɗin su, da sallama ya shiga saboda yaji dan motsi acikin falon amma da ya shiga sai yaga babu kowa abun yaso yabasa maamaki amma sai kawai yayi saurin kawar da tunanin ya shige ɗakin sa, yana shiga ya cire kayan jikin sa yayi wanka yayi sallah, mai makon ya kwanta sai kawai yaƙara shirya cikin wasu baƙaƙen kaya, ya rufe fuska, ya fito, cikin masarautar ya nufa gidan gaba ɗaya ya ɗauki shiru babu motsin mutane ko ɗaya, sai kukayen tsuntsaye kawai kake ji, zagaye ta ya shigayi ya miƙe wata hanya, dake kama da daji, can bayan masarauta gurin yake, saida yayi tafiya mai nisan gaske dan saida yafara tunanin ma kodai babu wani guri agun, sai ya fara ganin sahun mutane gurin yabi inda sahun yake, can ya hango wani abu mai kama da bukka, gurin ya dosa babu tsoro babu fargaba,

Yana zuwa gurin a rufe yake, sai yazagaya ta wani guri ya ɗan leƙa, gurin amma baya gani sosai, saida yasaka hannu yaƙara buɗa wajen sannan yafara hango cikin gurin, mutane yagani a zazzaune sun ranƙwafa ƙafafun su tare da rufe idanu wansu agaban wata wuta, inda wani ƙaton namiji yake gaban su ko kaya babu ajikin sa sai ɗan ƙaramin wando  sai kansa da ya naɗe da wani ƙaton abu, yana zazzagaya wani abu akan wutar saida yayi wajen sau goma sannan ya miƙe tsaye yafara yayyafa musu akansu, kowa saida yayi masa sau uku sannan ya kwashe da dariya yana zare idanun sa kamar na sheɗan jajawur dasu sunkaɗa kamar jan ƙwai,

Komawa yayi inda ya tashi ya zauna ya ɗauko wani jan ƙyalle ya rufa akan wutar atake ta mutu sai kuma gurin ya ɗau haske gaba ɗaya har wajen bukkan saida yayi haske,

Cikin wata irin murya mai kama da ta ibliss yace "an gama komai ya kusan zuwa ƙarshe zasu mutu indai kunyi abun da yadace kada ku ƙara raba kanku, sannan kutabbatar atare zaku watsa wannan abun acikin fadar adaidai kan kujera kowa zai yayyafa da hannun sa, sannan kuje ɗakin ta ku ɗaga gadon ta, ku cusa, wannan adaidai makwan cinta wannan basai kunyi ku duka ba zaku iya tura mutum ɗaya duk yanda zakuyi kuma kar kubari wani yaganku idan kujayi ido huɗu da ɗaya daga cikin su to zai warware kuma babu abun da zai hana tonuwar asirin ku amma indai kunyi komai daidai aranar za aƙara nemansu arasa kusa da ƙasar ma baza su zauna ba zasuyi nesa daku nesan da bazasu ƙara dawowa ba har abada, 

Tsugunnawa sukayi agabansa sukayi masa sujjada sannan suka ɗago tare da haɗa baki sukayi masa godiya, sannan ɗaya daga cikin su yace "to boka Gundur maiyi tuƙwicinka, idan ka abu yayi kyau,

Wata dariyar yasaki sannan yace mungama magana da ɗaya daga cikinku yayi min alƙawarin ko abu yayi kyau ko baiyi ba, kafin ma kufara agobe nake buƙatar ganin ta anan zaku ɗauko min, aljanu suna buƙatar jinin ta, dole ma da jinin ta ragowar aikin ku zai kammala yanda yakamata, bai gaya muku ba,

Kallon juna suka shiga yi a tsakanin su da sauri waziri ya sunkuyar da kai tare da ɗan gyaran murya yace "agafar ce ni ban sanar daku ba, aloƙacin da akace yarannan sun dauki komai shiyasa raina yaɓaci tun kan na sanar daku nazo nafara yi masa magana shine yace zai magana ce mana matsalar mu saboda ina tunanin boka BunGu yace indai asirin nan ya karye shikenan bazai yiyu aƙarayin wani ba shine hankalina ya tashi na lalubo boka  Gundur na sanar dashi abun dake faruwa shine yace zai yimana aikin da muke so amma saidai da sharaɗi sai mun bashi yarinyar jikar Sabreena (Ameesha kenan) saboda jinin ta zai aikin inba hakaba duk asirin da za ayi mata bazai kamata ba saboda tana tare da wani tsari ajikin  kuma ankasa gano meye tsarin nata bare ayi maganin sa dole sai ankawota gurinsa komai zai tafi daidai inbahaka zata iya wargaza mana komai, ta hanyar tsarin dake jikin ta, amma idan aka kawota aka fara kawar da ita shikenan komai zai tafi yanda akeso,  nikuma na amince masa da hakan kunji yanda mukayi dashi kafin mu haɗu anan,

Sauke ajiyar zuciya sukayi gaba ɗayan su saboda atunanin su wani daga cikin su za subayar shiyasa hankalin su yaɗan tashi, amma jin ba ɗaya daga jinin su bane yasa suka sauke ajiyar zuciya akusan tare,

Amma ɗaya daga cikin su sai yace "amma kuna ganin kuma tsarin jikin nata zai bari a ɗauko ta ta cikin sauƙi babu abun da zai faru? Yafaɗa yana kallon boka Gundur,

Haɗe rai bokan yayi yace "bama son tsoro ko wasiwasi a aikin mu babu abun da zai faru kawai kusan yanda zakuyi ku kawota nan,

Jinjina kai suka shiga yi tare da cewa shikenan boka godiya muke Allah dai yabamu sa'a kaima zaka ga sakamako mai kyau ko ya kuka ce,

Duk suka amsa da kwarai kuwa, Waziri  yace "ai ni idan komai yatafi yanda nake so asirina bai tonu ba babu abun da Bazan iya bayar wa ba mutuƙar wannan abun da suka  ɗauka bai fallasu ba zakayi mamakin irin kyautar da zanyi maka, nandai kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa gun nuna jin daɗin su ga sabon bokan da suka haɗu dashi yau yau ɗinnan,

Saida bokan ya dakatar dasu sannan suka yi shiru tare da yi masa godiya ɗaya bayan, sannan suka mimmiƙe tsaye boka yabasu umarnin su fita ɗaya bayan ɗaya, shima idan ɗaya ya fita sai bayan minti biyu wani zai ƙara fita, ahaka suka fara fita daga gurin,

Tunda Meer yaji haka suna shirin fara fitowa yayi saurin barin wajen ya koma bayan wata bishiya dake gurin da haske daga inda yake zuwa inda zasu fito zai iya ganin fuskar kowa,

Yana gurin kuwa matar waziri tafara fitowa, ɗaga ciki wayar dake hannun sa ya saita tana fitowa ya danna mata hoto,

jin ance sai nan da minti biyu wani zai ƙara fitowa yasa yayi saurin bin bayan ta, tana cikin tafiyar ya shaƙeta ta baya zatayi ihu yayi saurin rufe mata baki da hanki ya shaƙa mata shi a hanci tana shaƙa ta zube awajen ya ɗauke ta ya koma inda ya ɓuya ya ajiye ta a gefe, yaci gaba da tsayawa agun yana jiran next fitowa,

Daga ita sai Waziri shima yayi masa haka suka ringa fitowa, daga ciki ɗaya bayan ɗaya kamar yanda boka yagaya musu sai ɗaya ya daɗe da tafiya wani yake ƙara fitowa,

Haka Meer ya ringa ɗaukan su a hoto wasu yasan fuskokin su wasu kuma baisan su ba kuma ganin wasu kuma abun baƙaramin mamaki yashaba da ganin fuskokin wasun su da yasan su sosai, haka ya dake yaci gaba da ɗaukar su, har saida suka ƙare mutum bakwai ne, cif yana irgasu har suka bar wajen, kowannen su ya nufi inda yabaro, cikin sanɗa, suka koma makwancin su,

Saida ya tabbatar da sunyi masa nisa sannan ya nufo hanyar komawa shima mamaki fal ransa, matar Waziri na saƙale akafaɗar sa ahaka yataho da ita har yaƙaraso part ɗin ya shige ya koma ɗakin sa, yana shiga ya sauketa aƙasa yasamu yasamu slatip ya manne mata baki dashi sannan ya ɗaure mata hannuwanta tare da ƙafafun ta, sannan ya ɗauketa ya buɗe drower ya danna ta aciki sannan ya rufe harda saka muƙulli ajiki......,

Kayan jikin sa ya hau cire wa, sannan ya samu na bacci yasaka, ya koma bakin gadon sa ya zauna tare da jawo system ɗin sa ya kunna ta ya jona wayar sa ajiki ya fara aiki, bashi ya tashi daga gurin ba saida akafara kiraye kirayen sallahr asuba sannan ya tashi ya shiga bathroom yayo wanka ya ɗauro alwala, sannan ya fito ya shinfiɗa salaya yayi raka'atul fijr  saida yajira akayi assalatu sannan ya tashi ya tafi masallaci,

Bayan an idar da sallar ya dawo  saida yaƙara ɗan dube duben a laptop ɗin har gari yafara haske sannan ya samu ya kwanta......,

_____papa da Maama ne zaune a ɗaki suna tattaunawa akan batun fulani,

Maama ta kalli papa tace "to tunda har ta rantse ba ita bace ai ni banga amfanin rufeta ba tana matsayin matar ka, ni aganina kawai afito da ita, idan wani hukuncin za ayi mata kuma na ɗauko salahuddeen sai ayi mata afito da ita inyaso sai a cigaba da binciken ko ya kace,  duk dade har yanzu shiru babu wani labari ko alamar cin nasara sai a fito da ita wataƙil ma ta hanyarta zamu iya gano wani abun, kaga ance mutuwar daga ɓangaren ta aka fara sanar da ita, dole idan aka nutsu aka bi a hankali zata iya tuna wasu abubuwan da suka faru aloƙacin sanar da mutuwar,

Tana yin shiru papa ya ɗora da cewa "nima abun da yake ban mamaki kenan tun ranar nake zuba ido ko zan gano wani abun amma shiru, munyi maganar ma tace zatasa a binciko gidan su Wasila (jakadiyar ta kenan) saboda tun loƙacin mutuwar ba aƙara ganin taba acikin masarautar kuma anrasa inda gidan su yake,

Jinjina kai Maama tayi sannan tace "wai ni wama ya kawota da ba asan asalin taba aka kawo min ita duk dade zaman lafiya mukayi da ita tunda nake zaune da ita bantaɓa ganin wata alamar rashin gaskiya ba a tattare da ita ba bantaɓa tunanin za a haɗa baki da ita a cutar dani dan loƙacin da abun yafaru aka shigo min ɗaki dole tasan da zuwan su tunda tunkan dare yayi sosai a ƙa'ida a irin wannan loƙacin tana tare dani bata barina har sai tagama komai taga nayi bacci wataran ma aɗakin take baccin sai na farka nake tashin ta ta koma ɗakin ta kuma bata da nauyin bacci motsi kaɗan yana iya tashin ta, amma nayi mamaki tun wajen magriba na kwanta amma bata leƙo inda nake ba har akazo aka fita dani tace bata sani ba kaga kwa dole da sanin ko suwaye sukayi wannan abun,

Papa yace "maganar ki gaskiya ce ai ta inda ma takama kanta barin masarautar da tayi shine babban abun da yasa aka zargeta, daman kuma Waziri ne ya kawo ta kuma Saida ya tabbatar min da cewa yasan ko wacece ita har iyayen tama yasani amma bayan faruwar abun sai ya nemi kowa nata ya rasa ashe ba alkhairi bane ya kawota, tun loƙacin akaita nemanta amma ba asamesu ba,

Tunda yace Waziri amma take binsa da wani irin kallo mai cike da tarin tambayoyi, amma dai bata nunawa papa ba saikawai tace "Allah sarki Waziri nawa, to Allah ya bayyana su duk inda ta shiga zamu sameta da yardar Allah mudai dage da addu'a kawai itace mafita,

"Hakane Allah dai ya ƙara karemu ya toni asirin duk wani me hannu acikin" cewar papa

Maama ta amsa masa " da Ameen"

suna ɗakin sukaji ana nocking Maama tace "waye shigo saboda tasan dai ba wani baren bane shiaysa tace a shigo kawai,

daga can wajen Ameesha tace bani shigowa tsofaffi ku fito kawai abinci yana jiranku in kuma kuka tsaya zakuga wayam muncinye kuyi sauri dan yunwa nake ji nikaɗai ma zan iya cinyewa, tayi maganar cike da tsokanar su tana faɗa musu haka kuma ta juya ta bar wajen tana dariya...,

Suma ga baɗayan su saida suka dara suna maijin daɗin tsokanar da tayi musu, papa na mayar mata da martani amma sukaji shiru tabbacin tabar gurin kenan,

Fuskar kowannen su ɗauke da murmushi suka tashi atare suka fito daga ɗakin, suna fitowa suka ga kowa agun su dadda duk sun hallara a tsakiyar falon inda aka baje musu kayayyakin breakfast kala kala, kuma daman tunda suka dawo idan zasuci abinci gaba ɗayan su suke ci a ƙasan falon kan capet basa hawa dinning,

Maama ce ta kalli Ameesha loƙacin da suka ƙarasa zama agun, tace "to acici munzo da fatan dai kin rage mana baki cinye ba,

Ɗan murmushi Ameesha tayi tace "ai kunji tsoro naga kun fito da wuri amma da tuni kunga babu,

Papa yace yanzun ma da muka fito ai ke zaki cinye shi tunda kika faɗa kam sai kin ciye ko cikin ki zai fashe inkinƙi kuma indanne ki intura miki,

Hhhh Ameesha ta saki dariya "tace lalle ma tsohon nan kai da wannan tsufan nakama me taya zaka iya danne ne ai tuni zan ƙarasaka daman kazama guntu,

"Au haka kikace zakwa kigani bari innuna miki tsohon ƙashi da sabon ƙashi da bambanci, yana faɗa ya tashi ya koma kusa da ita yana kallon kwani kan gaban ta da kansa ya buɗe wani ɗan kwano mai kama flaks ya cika mata shi da doya da dankali ya buɗe wani yaƙara mata yamballs,

Kowa na gurin ya tsaya yana kallon su babu wanda ya tanka musu kowa nason ganin yanda zasu ƙare waye zaiyi nasara tsakanin Papa da Ameesha,

Yana gama zuba mata, ya tura mata gaban ta yace maza fara ci sai kinye duka in kuma ƙaro miki da haka sai kincinye shi duka, kallon sa ya mayar kan sauran yace karfa wanda ya fara cin komai naga wasu sai haɗiyar yawu suke kuma bamai ci duk natane duk wanda ya matsu ya tashi yaje abasa wani amma bazai ci komai nagun nan ba,

Maama tace "ai daman babu wanda yace zaici ai gaku ga abincin nan kallo muka tsaya yi, indai zata cinye mukam munyafe ma, koya kukace,

Su Azeema da Ummy suna dariya sukace maganar ki gaskiya ce Maama danni har baji nama ƙoshi cewar ummy,

Abu ma yakasa jurewa saida ya kalli papa yace nidai gaskiya bangoyi bayan hakan ba dan tun asuba nake jin yunwa kuma ga abinci ina kallo awani ce bazan ciba alhalin kuma ba iya zatayi ba, kawai salon ɓata mana loƙaci nidai azuba min bazan iya jira ba idan kuma baza a zuba min ba, inzubawa kaina, yafaɗa yana jawo flate yana shirin zubawa Maama tayi saurin ƙwace kwanon tace "Allah kuwa sai ka jira ko nan da shabiyun rana ne sai kajira ko kuma katashi daga nan,

Haɗe rai yayi yana kallon ta yama kasa cewa komai,

Papa da yaga haka sai yasaka dariya yace "kinga wannan wasan angama sa dan baza a ɓatawa masa raiba agabana abun da yake so shi za ayi azuba masa abinci yaci ke kuma Allah ya taimakeki da kinga yanda ake ɗurawa mutum abinci dan ko ta hanicine sai na ɗura miki amma yanzu dai kin tsallake sauran kuma nan gaba,

Ameesha "tace kadai ji tsoro bawani, dungure mata kai yayi yace "kaf family ɗin mu ba matsoraci, kawaidai kinci da rajar mai daraja,

Duk dariya suka ƙara yi ƴan gurin kowa na tofa iyakacin albarkacin bakinsa cike da raha da tsokana, Saida sukayi mai isarsu sannan suka fara cin abincin,

Suna cikin ci Maama tace wai ni ina mutumi nane bangan saba ko motsin sa banjiba, duk wannan hayaniyar, tayi maganar tana kallon kowannen,

Abu yace "to Maama mu da kikatsatstsare mu da ido ina zamu san inda yake baki san ɗakin saba, ganin damar fitowa ne baiyi ba,kinsandai halinsa,

Hararar sa Maama tayi tace "to ina ruwanka idan kuma bacci yake bari ni inje in nemoshi tunda nan duk tarin maƙita yatara bamai tunawa dashi kowa kansa yasani, wallahi idan baku gyara halinku ba akansa sai mun fara saka ƙafara wando ɗaya daku tana faɗa ta ƙarasa bakin ƙofar sa nocking tayi tana juyowa tana harar su ganin ko ajikin su kowannen su ma abincin sa yake ciki hankalin sa kwance,

Meer dake kwance can cikin bacci yafara jin kamar kuka kukan mutum a hankali yafara buɗe idon saida ya tashi zaune yaji ashe matar da ya ƙulle ce ta farka, shi yama manta da ita so yayi tun asuba ya fita da ita daga gidan amma ya manta ya kwanta tashi yayi ya ƙarasa bakin drower ɗin ya buɗe yana buɗe ta faɗo ƙasa tana ta faman juyi tana son kunce hannun ta, ganin sa agaban ta ba ƙaramin tsorata tayi ba, cike da tsoro tafara uhmm uhmm tana karkaɗa hannun ta da ƙafafun ta,

Tana cikin haka sukaji bugun ƙofar sauri yayi ya maida ita ciki ya rufe sannan ya nufi ƙofar yana gudun Allah yasadai kar ajiyo motsinta dan anaji idan kana cikin ɗakin, cike da magagin bacci ya ƙarasa bakin ƙofar ya buɗe yana leƙawa, ganin Maama atsaye yasa shi ɗan buɗe ƙofar yana kallon ta itama kallon sa take yi,

Murmushi ta sakar masa tana shafa fuskar sa tace "ɗan gidan gwaggo mai ya hanaka fitowa, tayi maganar tana tura kai cikin ɗakin, dafe kansa yayi gashi ba damar yace mata ta fita, yarasa dabarar dazai mata tafita........
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
 

12 / 57