Sarki Sameer Book 3 By Yaya Azeema

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   4 / 57

9K to 12K   out of 170K words

muraɗa handle ɗin kai tsaye kuma tajisa a abuɗe ɗan tura ƙofar tayi yanda bata hango ɗakin sannan ta tura Ameesha ta ƙarfin tsiya tana shiga taja ƙofar ta rufeta aciki,

juyawa Ameesha tayi tana niyar buɗe ƙofar amma taji ƙam Azeema ta riƙe ta ta waje,  juyawa tayi ta shiga bin ɗakin da kallo sai taga babu kowama aciki amma taji motsi abanɗaki dan haka sai ta sauke ajiyar zuciya ganin ba yanan sannan ta ƙara juyawa bakin ƙofar tana ja murya ƙasa ƙasa tace "besty baya nan fa yana banɗaki ki buɗe min na miki alƙawari wallahi zan dawo anjima da kaina Allah da gaske nake saboda tana tsoron ko wanka yake kar taje kuma ya fito ba tare da kaya ajikin saba shiyasa ta tsorata take gudun kar ya fito tana cikin ɗakin,

Azeema najinta tayi banza da ita tana mata dariya ƙasa ƙasa tayi ma kamar bata gun,

Sosai Ameesha ta shiga roƙon Azeema akan ta buɗe mata amma taƙi haushi ne da ta ƙaici ya isheta da yasa ta saki handle cike da gajiyawa ta bayanta dan taji ko yana daf da fitowa,

Saidai kuma abun da bata sani ba ya daɗe da fitowa har ya ƙaraso inda take ta bayan ta basan yazo ba, juyowar da zatayi kenan taci karo da mutum agaban ta, wata iriyar mummunar faɗuwar gaba taji, take zufa suka shiga karyo mata ta kowacce mafakar gashin jikin ta, ji tayi kamar ta nutse agun karo da tayi da faffaɗan ƙirjin sa mai kwance da ita wasu siraran gashi ɗaiɗai ku da zama ka iya irgasu saboda rashin yawansu agun dan basu hana bayyanar hasken fatar shi ba,

Saura kaɗan numfashin ta ya ɗauke tayi saurin runtse idon ta jikin ta yafara rawa dan baƙaramin tsorata tayi dashi ba tasan shikenan tafaru ta ƙare yau ranar cin ubanta ta kama yau zai sauke mata duk tara tana da yake,

Baki na karkarwa tace P...lea...se I'm so sorry nashigo maka batare da izinin kaba wa...lla....hi ba......n....., shiru tayi bata ƙarasa ba sakamakon tsinkayo muryar sa da tayi yana cewa "shhhhhhhhit........✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By uu
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_P4,_*
          
Bakin ta na karkarwa tace P...lea...se I'm so sorry nashigo maka batare da izinin kaba wa...lla....hi ba......n....., shiru tayi bata ƙarasa ba sakamakon tsinkayo muryar sa da tayi yana cewa "shhhhhhhhit.......,

Ɗif tayi bata ƙasa maganar, kuma bata buɗe idon taba ta ƙulle sa ba,

cikin daka tsawa yace mata "me kika shigo yimin ɗaki sa'an kine ni da zakishigo min ɗaki kai tsaye ba "eh!

kai ta shiga girgiza masa hawaye na zubowa daga idon ta,

Yace "I'm asking u kina girgiza min kai, baki da baki ne?

Bata daddara ba yanzu ma ta ƙara girgiza masa kai,

Tsaye yayi yana kallon ta yana mamakin yanda akai ta raina sa har yana mata magana amma still ta ƙara girgiza masa kan, ji yayi kamar ya ɗauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hanesa da hakan har yafara tunanin ko muhimmun abune ya kawo ta ganin yanda ta tsora, ga kuma maganar da yaji tanayi, tunanin hakan yasa ya ɗan sassauta murya tare da ɗan matsawa daga kusa da ita,

Ɗan sassauta muryar sa yayi cikin sanyi kamar yanda take yace "open ur  eyes.

jin baiyi mata komai ba yasa ta ɗan ji daɗi ganin yamatsa daga kusa da ita,  a hankali ta shiga buɗe dara daran idanun ta har ta gama ware su gaba ɗaya tana buɗewa kuma idanun ta suka sauka akan sa ganin sa daga shi sai towel ɗaure a west ɗin sa yasa tayi sauri ta juya masa baya tana kallon ƙofar ƙara gwada buɗeta tayi sai taji ta buɗu cike da murna ta jawo zata bar ɗakin tana ɗaga ƙafar ta, yace "idan kika ɗaga ƙafar ki daga nan sai ranki yayi mummunar ɓaci, come here,

Wani ƙatoton wani abune yazo mata wuya ya tsaya na baƙin ciki, cak ta tsaya tare da juyowa ahankali ta kallesa sai taga bama ita yake kallo ba hankalin sa ma kamar baya kanta yana kan shirin da yake yi, mamaki tayi ya akaima yasan tana niyar fita alhalin kuma ba ita yake kallo ba,

Tana cikin kallon sa ta kuma ji yace, "idan kingama kallon nawa sai kizo kiran da nake miki,

Saurin kawar da kanta tayi tana wasa da hannun ta tana tunanin bayan gata gashi kuma wane irin zuwa zatayi duk maganar da zai mata ai zataji, dan haka aranta tace ita ba inda zata daga inda take,

Har yagama shafe shafen sa yasaka kaya ya bata motsa daga inda take ba,

Yana sane da ita shima bai ƙara yi mata magana ba, yaje ya ɗauko kayan zaƙin sa yadawo kan gado ya zauna yafara ɓare wata choculate me ɗan girma ya ɓare ledar yafara kaiwa baki yana taunawa a hankali kamar wanda akayiwa dolen sha,

Time to Time tana ɗan satar kallon sa, ganin choculate ɗin kuma sai kallon yayi yawa dan har haɗiyar yawu take saboda ba ƙaramin burgeta ba tayi, ji take kamar taje ta ƙwace a hannun sa,

Shikam ko kallon inda take bai kalla ba amma yana sane da ita a ɗakin so yake yaga iya gudun ruwan ta idan ya gama abun da yake batazo ya tashi zai nuna mata asalin kalar sa kafin zata kiyaye sa tafara jin tsoron sa dan yaga alamun  kamar bata tsoron sa, bai gama wannan tunanin ba yaga alamun tafara takawa daga inda take, a ransa yace "kin taimaki kanki da jikin ki yagaya miki,

A hankali Ameesha ta shiga takawa zuwa inda  yake amma fa ita anata gurin bawai tsoran sane yasa zataje ba face choculate ɗin hannun sa da takasa kawar da kai so take kawai taji ta abakin ta kuma ta ga ba ɗaya ce da shiba akwai wasu agefen sa, shiyasa zataje wajen sa ko ta halin ƙaƙa taci koma tace yabata, dan ba kunyar sa take jiba, kawai dai tana jin tsoron sa tsoran ma ba wai canba tunda su Maama na gidan bai isa ya cutar da ita ba tasan za a hanasa,

A ɗan gefen sa ta tsaya sai kuma tayi saurin tsugunnawa saboda tunawa da tayi sai kayi biyayya idan kana son abu tunda kwa abunsa take so dole tayi biyayya badan Allah ba,

Bai kulata ba yaci gaba da shan abarsa, tana zaune tana tunanin tayanda za ayi ta tambaye sa ɗin ko kuma tayi masa wayo yanda bazai gane ba har yabata,

Ɗan dagowa tayi taga baya kallon ta sai ta gyara zama daga tsugunnen da take tayi zama dirshen harda tanƙwashe ƙafafun ta, tana ɗan murza yatsun hannun ta, sannan tace "uhmm ya Sameer ta kira da cikin ƙasa ƙasa da murya me cike da ladabin ƙarya,

Cak ya tsaya da shan choculate ɗin da yake, tare da saurin mayar da duban sa gare ta cike da mamakin kiran sunan sa da tayi kai tsaye duk da tasa yaya amma dai Sameer ɗin da tace shi yafi basa mamaki meyasa bazata faɗi yanda kowa yake faɗa masa ba, sai wanda ba kowa yake faɗa ba,

Sarai tasan kallon ta yake dan haka ta taƙi ɗagowa ta kalle sa, a haka kanta a sunkayi ta ci gaba da maganar, tace "uhmm yaya Sameer daman wata magana nakeso muyi dakai shiyasa nazo amma kafin muyi mufara gama shan choculate ɗin sai muyi, maganar,

Ɗan kallon ta yaƙarayi akaro na biyu yana mamakin jin furucin ta wai mufara gama shan choculate ɗin daman tare da ita suke sha ne ko kuma wani abun zatace tace haka, zuciyar sa tayi saurin bashi amsa da cewa may be tana so tace kafara shanyiwa sai muyi ta manta tace mu fara shanyewa, hakanne ma wata zuciyar ta basa amsa, dan haka sai ya kawar da kai daga kallon da yake mata, yace "ina ruwan ki da shan abuna kawai kiyi maganar ki ina kunne keji ba, ba baki ba ko,

Shiru tayi tana ƙara tunanin yanzu kuma me zatace wata zuciyar kawai tace kisa hannu ki ɗauka ba yayan ki bane, abun sa ai naki ne, da sauri ta girgiza kai aranta tace wannan jarababban mutumin ba imani ne dashiba baisan wannan tsaf idan na taɓa zai iya ci min mutunci,

"Malama kina ɓatan loƙaci idan ki bari nagama baki faɗi abun da yakawo ki ba bazan saurare ki ba kuma sai na saɓa miki kamanni rainin hankali da kikai min kafin kifita kinji ni ko, yayi maganar yana ƙara kai choculate ɗin bakin sa caraf akan idon ta jitayi kamar ta fisgota daga hannun sa,

Jin batun nasa tagane bai fahimci abun da tace masa ba kenan kodai baiji ta da kyau ba, wannan tunanin yasa taƙara cewa, "To taya zan iya magana da abu abakin na,

Wannan karon kwa da sauri ya juyo ya kalle ta yana kallon bakin nata dan yaga abun da take ci ɗin dan shidai baiga komai a hannun taba da zata ci dan shi har yanzu bai fahimci inda yaren nata ya dosa ba,

Ganin ba komai yace "meye abakin?


Duk yanda taso ya fahimce ta sa kwana kwanar ta dan har magana take masa tana kallon choculate ɗin dan yafi fahimta amma yanuna mata baisan abun dake nufi ba saboda daga baya ya fahimceta ganin tana takallon abar hakanne yasa ya gane so take ta sha saboda tsabar kwaɗayi irin nata amma sai shima yana nuna mata yafita iyawa ya nuna baisan ma tanayi ba,

Rufe ido Ameesha tana taƙaicin ƙin fahimtar ta da yayi da taga dai da gaske idan ba ofulu ofulu ta fito masa ba tagaya masa kai tsaye bazai taɓa fahimtar taba, dan haka ta rufe ido kawai, tace "Babu yanzu amma yanzu zan saka kaban abar hannun ka ko kaban wata nima ido fa gubane kazo gabana kana tasha to ni kuma fa, ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka tana turo baki saboda ta ƙosa tafara sha, kunsan Ameesha da kwaɗayin zaƙi itama kamar shi take koma ince har ta fishi saboda ita ba iya kwaɗayin bane harda yarinta,

Ƙuri yayi mata yana kallon ta da mamaki daman kwaɗayin nata har yakai haka tayi roƙo ba abata, aikwa zai koya mata hankali akan kwaɗayi kenan ko wani wajen ma taje haka zatayi, saboda bata da hankali, yana sane ya fara sauri ya shanye ta tsaf sauran kuma ya kwashe su daga gefen sa, ya zuba su a aljihu, kuma bai tanka mata ba,

Ameesha ƙwalla har ta fara cika mata ido tana shirin zubowa tayi saurin mayar da ita tana mamakin rowar da yayi mata daman marowaci ne bata sani ba(daman ance 🎶🎶mai ƙwaɗayi shi yasan gidan me rowa inji adamu ɗan gidan su gwanja hakane wallahi🎶) zancen haƙƙun gwanja)

Wata dabarar ce ta faɗo mata dan haka sai tayi saurin miƙewa tsaye ta koma gefen sa ta zauna cike da rashin tsoro sai kawai ta kamo hannun sa, ta ɗora akan cinyar ta,

Shikuma cike da mamaki da taƙaici da jin haushin hakan da tayi masa ya janye hannun da sauri ta ƙara riƙewa tace wai meye haka ka tsaya mana kaga abun da zanmaka ko zan cutar dakai ne to bana cin hannun mutane ni ba mayya bace,

"Sai ƙafa" taji yafaɗa ɗan murmushi tayi tace a'a itama ƙafar ba ci nayi ba tunda ga abarka nan ajikin ka kuma loƙacin ma kai kajawa kanka, da ka ɗaga ni da hakan bata faruba yanzu kuma babu abun da kayi min dan haka ba abun da zan maka nima, dade kayi min wani abun to da sai na rama danni bana yafiya idan aka min sai na rama,

Jinjina kai yayi cike da gajiya wa da surutun da take masa dan har fa Allah ya gaji so yake tafita ta bar masa ɗaki amma tunda yaji tace magana suke so suyi shiyasa ya rabu da ita kuma daman shima yana so tabashi labarin yanda akai ya koma cikin falo jiya da ana ruwa da kuma warke wasa da wuri, warke tasa da wuri ita tafi komai ma tsaya masa arai dan ba ƙaramin mamaki yayi ba da faruwar hakan,

Akaro na biyu yaƙara ƙoƙarin janye hannu nasa batare da ya ce mata ƙala ba, amma still sai ta ƙara riƙewa itama, mai makon tayi abun da zatayi sai ta tsaya tana kallon hannun nasa, da ta riƙe da nata sai kuma ta shiga haɗa sa da nata wai zatayi comparing da nata,

Ɗagowa tayi tana kallon sa tana taɓe baki tace "ashe ma baka fini haske ba, kamar ma na fika Allah kuwa kalli kaga hasken mu ɗaya, kai da kataso ma acan cikin larabawa kana hutawa, nikwa da na tashi cikin wahala amma hasken mu ɗaya, nasan ma idan nasamu hutu na zama ƴan mata sai na fika haske daman na fika kyau nima kuma zanyi karatu inyi aiki inzama me kuɗi shima infika daga nan bazan ƙara jin tsoron kaba tunda nafika da komai idan kace zaka min wani abun insaka bodyguard ɗin su lallasa min kai kuma daman ina nan banmanta ba sai nasa an ramamin muguntar da kayi min loƙacin da naje gidan saboda baka da tausayi ka taka min ƙafa bayan kasan tanayi min ciwo sannan kasa na shafa aboniki a fuska ta saboda ka riƙa a mugun ta, shiru tayi tana ci gaba da kallon hannun nasa,

Sannan ta ɗago ta kalle sa ganin har yanzu bai tanka mata ba, sai gyara zama tana ƙara damƙe hannun nasa sannan tace "wai dan Allah ina tambaye ka, me yasa baka da tausayi idan kana mugun ta daɗi kaji eh? tayi maganar tana kafe sa da dara daran idanun ta,

Tabbb babbar magana yama tafi duniyar tunani wai yaushe yayi sabo da yarinyar nan da har zata na gaya masa magana son ranta kuma wai zata dena jin tsoron sa nan gaba duk wanda zai iya gaya maka maganganu irin haka ai bawani tsoron ka da yake ji, gaskiya yayi sake yarinyar wallahi tagama rainasa, tagama kaishi ƙarshe kuma dan haka baisan ma me zaiyi mata ba ya huce,

yana cikin tunanin ta katseshi tare da ƙara nanata masa tambayar da tayi masa,

Haɗe rai yayi yanda zata tsorata da shi yace ke dalla mahaukaciya sakar min hannu ki fice daga ɗaki kafin in ɓaɓɓalaki agunan kinzo kin isheni da surutun banza ko ni sa'an wasan kine, daman maganar da ta kawo ki kenan kizo kicika min kunne da da surutun hauka,

Maƙe kafaɗa tayi tana turo baki tace "Allah kwa ko me zakamin bazan sake ka ba sai nayi abun da nayi niya kuma sai kaban amsa ta indai kana so intafi to ka amsa min tambaya ta sai mu rabu lafiya idan kuma masifar zakayi sai kai tayi kuma ka dake ni inje inyi maka sharri wajen Abu yazo yayi maka faɗa tunda naga baka son faɗa saboda gaka ɗan mai kai baza ayi maka faɗa ba,

Zaro ido yayi waje yana duban ta da kyau yana tunanin anya kuwa yarinyar nan lafiyar ta ƙalau kodai tasamu taɓin ƙwaƙwalwa ne basu sani ba ko kuma tana da mental problem, loƙaci loƙaci yana tasar mata yanzu kuma loƙacin tashin nashi ne yazo shiyasa take masa haka a tunanin sa to inba hakaba me zaisa tana gaga masa haka bayan yarinyar tsoran sa take yasani duba da shigowar tama yanda ta tsorata tana kuka amma ace loƙaci ɗaya ta burkice ta ringayi masa waɗannan surutan har yana mata magana tana cewa bazata yiba,

Tunanin hakan dan har ga Allah yagama tunanin tana da taɓin ƙwaƙwalwa dan yasan da a hankalin ta take bazata taɓa yi masa kwatankwacin abun da take masa ba yanzu, dan haka ya yanke shawara gwanda ya bata amsar su rabu lafiya kar haukan ya ƙaru tasaka masa ciwon kai yana zaman zaman sa,

Ɗan sassauta fuskar sa yayi daga haɗe tana da yayi sannan yace "ni ba mugu bane duk wanda nayiwa abu shi yakawowa kansa sa bai shiga harkata ba ko inda yake bazan kalla ba, idan kuma yayi min dole nima inyi masa abun da zai ƙoma masa rai bawai danjin daɗin raina ba dan ya kiyaye gaba kar ya ƙarayi min abun da yayi min, kin gane?

Ɗaga masa kai tayi tace nagane amma kuma ni me nayi maka kada keni kuma kataka min ciwo inda ba mugun ta nace,

"Oh my God, ya faɗa aransa yana dafe kansa, sannan yace ke kikajawowa kanki tunkan in kwanta nace miki kije wajen su ummy su baki abun da kike so sannan kibar gidan kar nafito naganki aciki, amma kika ƙi ji daga ƙarshema kuma ki haumin kangado kika kwanta a inda nake harda rufa saboda kin rainani shiyasa na zane ki saboda banason ko wacce mace ta taɓani, nace kifita kiƙi fita saboda bakya jin magana,

To meyasa yanzu na taɓaka kace bakason mace ta taɓaka,

"Saboda a loƙacin banda alaƙa dake ba kamar yanzu ba, da kike ƙanwa agurina,

Wani daɗi taji jin yace mata ƙanwar sa daman yasan da haka ashe ko shiyasa har yanzu bai dake taba dan itama aƙasan ranta duk abun da take masa tana sane kuma cikin tsoro takeyi tayi mamakin ganin ba abun da yayi mata, duk wannan abun da take masa, amma duk da haka sai ta ƙada dakewa bata nuna jin daɗin hakan ba a fili,

Sai kawai ta karkaɗa kai tace "To ai loƙacin daka faɗa nayi bacci bansan ka faɗa ba kuma abun da yasa naƙi tafiya idan na tafi bansan inda zani ba, shiyasa na maƙale maka da naga ka taimake

4 / 57