Author : Aysha Cool Category : Romance
wani irin kallo wanda yakasa tantance wane irin kallo take masa,.
Ji yayi gaban sa yayi wani irin bugawa, tsoran shi ɗaya kar tace masa bata sonsa, marairai ce fuska yayi kamar zaiyi kuka yace "dan Allah ki fahimci irin son da nake miki, naƙi gaya miki tun aloƙacin baya saboda karatunki shiyasa amma yanzu naji bazan iya haƙura ba shiyasa na yanke shawarar sanar dake yanzu, Dan Allah kice min kin amince zaki karɓi soyayya ta sannan kiyi min alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance tare bazaki taɓa bari na, wallahi idan ban aure kiba inajin kamar bazan iya ci gaba da rayuwa ba.......,
Kukan Ameesha ne ya fito fili hakan yasashi dakatawa da maganganun da yake mata, tunda yafara take zubar da hawaye, jin maganganun nasa sunyi yawa yasa kukan nata yaƙara ƙarfi, ita ba komai yafi saka ta kuka ba face yanda yake maganar tasan baida labarin auren da akayi mata, gashi takasa sanar dashi, dan batasan halin da kuma zata ƙara jefasa, shiyasa kawai take kuka, tare da tausayin kanta, itama dan itama ba ƙaramin so take masa ba dan har tanajin tama fi sonsa akan yanda yake cewa yana sonta, ita da sonshi ta taso tun bata kai haka ba, tun loƙacin da ta fara ganin sa take son sa, amma gashi ana ƙoƙarin rabasu, aikwa dole tasan abunyi a warware wannan auren ta auri wanda take so,
Yana tayi mata magana batajin sa harsaida ya riƙo hannun tayi saurin dawowa tare da saurin janye hannun ta daga nasa tana cigaba da kukan ta,
Gaba ɗaya hankalin sa yagama tashi yanzu ma kamar zaiyi kuka yace "Dan Allah kidai na kukan haka indai magana tace take saki zubar da hawaye wallahi nayi shiru bazan ƙara cewa komai ba kuma bazan miki dole ba idan bakyaso na shikenan zan haƙura, amma dan Allah kidai na kukan nan, wallahi har cikin raina nake jin sa bana so dan Allah kidaina, muci gaba da zaman mu kamar yanda muke kar ki sauya min dan Allah saboda nayi miki wannan maganar, najanye magana ta indai hakan zai faran ta miki rai,
maimakon tayi shiru saima ƙara volume da tayi,
Rasa inda zai tsoma ransa yayi, duk wani abu da zaiyi dan yaga tayi shiru amma taƙi yi, kuma taƙi yarda ya taɓata, kuma taƙi tashi, dan har ce mata yayi ta tashi ta tafi to amma sai ta maƙe masa kafaɗa, shide ya rasa yanda zai yi da ita,
Wani tunanine ya faɗo sai yayi saurin zaro wayar sa ya buɗe tare da shiga gallery ɗin sa, hotunan da yasa Ammi ta ɗaukar masa, folder su da ya ware ta musamman, ita ya shiga, hoton su da sukayi su biyu Abban Ameesha da mahaifiyar ta, shi ya shiga wai duk dan ya faranta mata yasan bata taɓa ganin taba,
Yana shiga yace Baby kinga mahaifayar ki, kamar ku ɗaya,
Cak ta tsaya da kukan tare da saurin juyowa tana kallon sa, shi kuma ya nuna mata wayar, yana jinjina mata kai,
Tana ɗora idon ta akai tayi saurin fusge wayar daga hannun sa tana miƙewa tsaye, tama kasa magana kawai ta ƙurawa matar jiki ido ko ƙifatawa batayi,
shima miƙewar yayi yana riƙota ita da wayar yace " zauna mana, tsaya kiga sauran ma, yafaɗa yana riƙo wayar tare da hannun ta,
Kamar wata sakarai haka ta koma tana kallon wayar,
Meer dake tsaye abakin ƙofar shigowa tun loƙacin da Bossay yake zayyana mata yanda yake son ta, yake gun yana kallon su, jira yake kawai yaga iya gudun ruwan su.....,
Bosaya: Wayar na hannun ta yajawo mata hoton gaba, shi kuma dadda wanda Sukayi su su uku da Dadda da mahaifiyar tata da Abban ta,
Gaba ya kuma ja mata sai gashi wanda suke susu dukan su, harda Malam,
Idonta na sauka akan Malam ta zaro ido tare da miƙewa tsaye cikin fitar hayyaci tace "BABA ɗan TSOHO!!!!
Dandanan hawaye suka shiga rige rigen saukowa daga cikin idon ta,
Da sauri shima Bossay ya miƙe yana "cewa Baby kin san shine?
"Eh wallahi shine na sanshi na taɓa ganin sa bai mutuba wallahi bai mutu ba yana raye,
Bossay zaiyi magana kenan Meer ya ƙaraso gurin tare da karɓe wayar da sauri dan ganin wanda tagani take wannan maganar,
Ai Meer yama fi Ameesha shiga ruɗu loƙacin da idon sa yayi masa tozali da mutanen dake cikin hoton baisan loƙacin da yasaki wayar ba ta faɗi ƙasa,
Tsugunnawa Ameesha tayi ta kuma ɗauko wayar da sauri tana ƙara kalla, sannan tace "kaima ka gani ko wallahi shine nima na gane sa ga wannan abun na gefen hancin sa, kaima shi ka gani ko, mutumin da nake gaya makane wanda ya taimake mu, to me yasa ya tafi ya barmu bayan yasan ko mu suwaye,
Ai Meer bai samu damar bata amsa ba, ya fusgo hannun ta, tare da cewa "ka biyo mu, ɗakin sa yajata, shi kuma Bossay ya shiga binsu abaya kamar jeka cike da rashin fahimtar maganganun da suke yi yakasa gane kansa,
Suna shiga Meer ya sakawa ɗakin muƙulli, baice musu komai ba kuma ya shiga zagaye ɗakin, yakai wajen minti biyar yana zagayen batare da yace musu uffan ba,
Da sauri yaje gefen gadon sa, tare da zama yajawo system ɗin sa, tare da ɗauko wayoyin da duk aka bashi dana wajen su Sam, da kuma wayar wajen Dadyn Rasheeda, har ya zauna sai kuma ya ƙara tashi yace ina zuwa, waje ya fita can wajen motar sa ya ɗauko akwatin da ya karbo tare da takaddun da kuma wayoyin sa daman duk bai ɗauko suba yabari sai yafara shigowa idan bai tarar da mutane ba sai ya koma ya ɗauko idan kuma ya tarar dasu, sai yabari sai kowa ya kwanta sannan zaije ya ɗauko, dan baya so kowa yaga shigowar sa da akwatin....
yana shiga ɗakin duka ya baje su yayi akan gadon, sannan ya fara ɗaukan wayoyin ɗaya bayan ɗaya ya fara dubawa, Bossay ya kira yace "duba min wannan wayar ka faɗo duk nombobin da akayi kira dasu ƙarshe guda huɗun ƙarshe da kuma misalin ƙarfe nawa,
ke kuma ungo yafaɗa yana miƙawa Ameesha akwatin yace "ki gwada buɗewa ko zata buɗu, kisaka duk abun da kikaji yayi miki, koda sunan ki ne,
Karɓa tayi bata ce masa komai ba dan ta fahimci kamar wani abun yake mai muhimmanci shiyasa itama ta nutsu bata ƙarayin wani abun ba,
Haka suke aikin wayoyin nan daga ya ajiye wannan sai ya ɗauko waccan tare da taimakon Bossay,
Sunkai wajen awa ɗaya suna abu ɗaya, ƙoƙari yake tayi zai shiga gundarin ma'ajiyar Dadyn Rasheeda, anan yake ajiye duk wani muhimman abunsa, da kuma duk wani sirrin sa indai ya shiga zai gano komai,
Amma kuma hakan ya gagara daga yafara yunƙurin ɗebosu zai buɗe sai kuma yaga ya dawo baya, saidaga ƙarshe ma yagano ai datse abun ake daga wani wajen, yana ƙoƙarin ƙara ganowa sai kawai yaga anfara goge abubuwan kan wayar,
Cike da tashin hankali Meer ya miƙe yace "Oh kash, ganin hakan Bossay yace "zan iya duba abun dake faruwa, kallon sa yayi Meer yayi kallon irin ni nakasa taya kai zakayi,
Gane ma'anar kallon yasa Bosaya cewa "zan iya aiki na ne fannin na karanta, tare da ɗaukar first class kar ka damu, dan har na hango inda abun yake,
Abun dake faruwa duk yanda akayi ana amfani da Email ɗinne awayoyi biyo dan haka duk abun da zakayi anan ana gani tacan shiyasa aka hanaka damar shiga, kuma ba goge su ake ba kai kaɗaine zakaga kamar ana goge su, ana turasa wata matattarar sirri na biyu wanda ana gama maidasu can na nan kuma zai sauka kafin kuma mushiga gurin za agama maida sune can gaba ɗaya, yayin da muke nan muna tunanin yanda za'ayi zasu raba mana hankali, su kuma anan zasu datse ma haɗar da ta haɗamu, su canza komai tare da canza password,
Yayin da Bosaya yake wannan bayanin tuni Meer yabasa guri tunkan yayi nisa a bayanin nasa, shikuma ya fara gudanar da aikin sa, dan yana daddanawa yana yiwa Meer wannan bayanin, saboda tsabar ƙwarewar sace tasa ya iya haɗa abu biyu loƙaci ɗaya, yana aiki acikin system ɗin sannan yana yiwa Meer wannan bayanin,
Ai duk ƙwarewar Meer sai gashi yazama ɗan kallo yau, dan daman bawai fannin ya karanta ba kawai dai fasaha ce irin tasa yasa ya iya abubuwa da yawa acikin ta, idan yanayi ma sai ka rantse fannin ya karanta, to nayau ɗinne yaɗan so ya girmewa tunanin sa,
Bossay ya maida hankalin sa sosai akan aikin da yake, shi yanda yayi musu kafin su maida su ɗayar ma'ajiyar, dan suna daf da maida komai saura baifi minti biyu ba, shi kuma sai yayi saurin kutsa kai ya ya lalubo ma'ajiyar ta biyu, yana ganin saƙonnin na shigowa,
Har sun fara murna, tare da fara wasu fiders ga mamakin su sai kawai sukaga duk empty ne ashe babu komai a cikin su, sosai suka tsorata gaba ɗayan su da ganin abun da idon su yagane musu,
Sauri ya kuma yi ya fita cike da tsoron abun da yake tunanin zasu iya yi, ya fita daman saida yayi tunanin hakan, zata faru, gashi kuma sauran minti ɗaya loƙaci ya cika, zasu gama kwashe,
Meer ne yace wait!
Baga sim ɗin ba anan me zai hana muyi amfani dashi muyi saurin katse su ko mu mufara canza password ɗin kafin su su saka,
Girgiza masa kai Bossay yayi tare da cewa babu loƙacin wannan, bari kawai inyi musu wani abu komai zai tsaya musu, nasan inda suka mayar dasu copying ɗin su akeyi,
Nan Bossay ya kuma yin danne dannen sa sai gashi yagano inda suke mayar war, sai shima yashiga, da sauri sai ya fara kwasar su ta ƙasa, sannan ya ƙara musu sauri, dandanan abubuwan suka shiga dawo musu tasu laptop ɗin, tun kan sugama shigowa shi kuma yayi sauri ya ɗauki wayar ya shiga Email ɗin ya danna changing password, yana kawowa yana kallon su, suna saka new password ɗin yayin kuma da idan sun sakama dole sai anturo code kuma layin yana hannun su,
Number suka saka ajikin password ɗin, Bossay har zai goge ta, Meer yayi saurin dakatar dashi tare da cewa "tsaya kamar na taɓa ganin number nan, yana faɗa yazaro wayar sa ya ɗauki number yana saka ta a waya yayi dialling ɗin ta, take ta kawo masa sunna alamar yana da ita ga sunan da ya taɓa saving da ita,
BOSSAY ya tsaya kallon Meer har suka canza password ɗin bai kulaba, ashe da sunan email ɗin sukayi amfani,
cike da tashin hankali Bossay yace "ya Allah akwai matsala sun canza wallahi, yayi maganar cike da damuwa yana kallon Meer, ga mamakin sa, sai yaga Meer hankalin sa kwance kamar ma murmushi yake son yi, alamun da yanayin fuskar sa suka canza,
Meer ne yace "karkadamu bassu sungama bamu komai, sauran bayanan da muke nema da kansu zasuyi bayani da bakin su, basai mun ɗauka anan ba,
Cike da rashin fahimtar sa, Bossay yace "kamar yafa ka gano wani abunne,
"Ɗage girar sa yayi guda ɗaya tare da cewa"yesssss,
Sai kuma yayi shiru yana ƙara mayar da fuskar sa yanda take da,
juya wa yayi ya ɗan yi taku ɗaya biyu sai kuma ya dakata,
Iya kansa ya juya yana kallon Bossay tare da rufe idon sa ya kuma buɗe su duk aloƙaci, sannan yace.....
"CASE IS CLOSED...
"THE GAME IS OVER........!!!!!!!!!
[17/11, 11:06 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️44_*
__Iya kansa ya juya yana kallon Bossay tare da rufe idon sa ya kuma buɗe su duk aloƙaci, sannan yace.....
"CASE IS CLOSED...
"THE GAME IS OVER........!!!!!!!!!
..........A hankali Bossay ya shiga miƙewa yayin da idon sa suke kan Meer, yana binsa da kallon neman ƙarin bayani akan maganar da yaji yayi,
shima Bossay yake kallo tare da jinjina masa yace "of course the case is closed, kagane me nake nufi,
Girgiza masa kai Bossay yayi alamun bai gane ba,
dawowa Meer yayi da baya sannan yace, yi tracking ɗin wannan number yanzu nan ka gano mana inda take,
Karɓa Bossay yayi yana juyawa kan system ɗin tare da saka numaber yafara nemo inda location ɗin number yake,
Shikuma Meer kowa yayi gurin Ameesha da har yanzu tana kan akwatin tana gwadawa, amma takasa buɗewa,
Karɓarta Meer yayi ya zauna agun sannan yace miƙo min wayata, da sauri ta tashi taje ta ɗauko masa,
Yana karɓa ya buɗe ta sai ya ɗauki hoton akwatin, sannan ya kunna data ya turawa shi ta WhatsApp sannan ya kuma fita ya shiga contact ɗin sa, number Abuu ya lalabu tare da danna masa kira, ringing biyu tayi aka ɗaga, amma sai yaji ba muryar Abuu, muryar Ummy ce,
Tana ɗagawa tace "ya akai lafiya dai ko ya, baya nan, na baro sa acikin fada, nima yanzu na shigo,
"Eh lfy Ummy daman inaso a haɗani da Uncle ne zan tambaye sa wani abu Allah yasa yana kusa?
"Eh, yana nan amma shima kamar bai dawo ba, bari dai in duba maka ko ya shigo sai in kai masa, ta faɗa tana fita daga ɗakin,
"Ok Allah yasa ya shigo,,
Tana fitowa falo ma tayi karo dasu gaba ɗayan su, suna shigowa,
"Yauwa kaga kuwa gashi sun shigo bari, gashi, tafaɗa tana miƙawa Abban Ameesha, wayar tana cewa gashi Meer ne yake son magana dakai,
Da sauri ya karɓa yana faɗaɗa murmushin sa, tare da kai wayar kan kunnen sa, sannan yayi masa sallama,
daga can Meer ya amsa sannan yace "yauwa Uncle wata tambaya nake son yi maka da Allah, zaka iya tuna password ɗinka da kake amfani dashi akoman ka, in kuma bada password ɗaya kake amfani ba, kace Abu ya hau WhatsApp ɗin sa na turo masa wani abu ka duba kagani idan takace,
Yana gama maganar Abba yace "a'a nama sani duk wani abuna da zan buɗe indai za'asa Password to sunan ta nake sawa, tunda nataso nake amfani da sunan ta akomai nawa,
"Ok, tom ina sauraron ka, faɗo min, cewar Meer,
"Ok. Kasaka, MY DEAR....,
Nan Meer ya shiga sakawa da sauri amma sai yasaka masa incorrect,
Nan Meer yaƙara cewa Uncle baiyi ba, kade ƙara tunawa,
Da mamaki Abban Ameesha yace "beyi bafa kace?
"Eh, Meer ya kuma basa amsa,
Sai kuma Meer yayi saurin cewa ka kashe wayar kace Abuu ya yabuɗe wayar sa sai kaga abun da naturo maka, ina tunanin idan ka gani zakafi tuna me masaka,
"Ok, Abban Ameesha yace tare da kashe wayar yagayawa Abuu abun da ake buƙata nan Abuu ya karɓi wayar tare da buɗe datar ya shiga WhatsApp ɗin, yana shiga saƙon Meer ɗin ya shigo, buɗewa yayi tare da yin downloading hoton yana buɗewa ya nunawa Abba yace "kaga abun da yaturo,
Karɓara wayar yayi da mamaki yace "ai wannan akwatin Noori ce aciki muke ajiye koman mu, duk wasu kuɗaɗe da takaddun duk abun da na mallaka suna cikin ta,
Yana cikin wannan maganar Meer ya kuma kiran wayar tare da cewa "Hello uncle kagani takace ko?
"Eh, amma ya akai kasame ta kuma a ina kasamo ta?
Uncle nama bayani daga baya yanzu dai kagaya min password ɗin kawai inaso in tabbatar da wani abune, ka daina wani mamakin ina aka samota gurin da aka samo ta ai me sauƙi ne.
Abban Ameesha hakan nan ya tsinci kansa cikin farin ciki, sai yace "ai dole nayi mamaki takwara saboda loƙacin da nake hannun su kusan kullum sai anzo ance in buɗe ta naƙi buɗewa, daga ƙarshe kuma sai naga sun fara fito min da wasu takaddun daga ciki, wai sai na yi musu signing, bansan ya akai suka iya buɗe taba, dalilin da yasa suka ƙi kashe ni kenan saboda suna so sai nayi musu signing sannan su kashe ni, shiyasa nikuma naƙi yi, sai dana ga azabar tayi yawa sannan nayi musu signing ɗin wasu, sannan suka rabu dani amma duk da haka dai akwai abun da ya basu matsala duk da nayi signing basu samu yanda suke so ba shiyasa suka barni da raina har nakawo wannan loƙacin....., Shiyasa kaga ina mamakin inda ka ganta,
Meer yace "sun kwashe takaddun gaba ɗaya kenan?
"A'a bansana ba saidai ka buɗe ka gani, kana ina da sai inzo in gwada buɗe maka,
Meer yace "no uncle basai kazo ba, kawai ka faɗo min ni zan buɗe ta,
kabari kawai zamu haɗu gobe...,
Abban Ameesha yace "to ai ni sunan dai da nagaya maka shine kuma ni wallahi akomai haka nake sakawa bantaɓa canzawa ba, dan ƴan gidan ma duk saida suka san abun da nake amfani dashi, dan ko securityn wayata haka nasa, sai yazama babu wanda besani ba acikin mu, saboda bana ɓoye musu komai,
Meer yace "to ko an canza shine danni na kuma sakawa baiyi ba, baka ganni acikin su kafin abun yafaru ko wani ya canza maka, ko ita auntyn ta canza maka loƙacin da ta fahimci anaso aka karɓe dukiyar, ka tuna last buɗewar ka, tazarar kwanaki nawace kafin abun ya faru,
Abban Ameesha jim yayi yana tunani har zaice ya kwan biyu rabon da ya buɗeta sai kuma ya tuna ai baza'a iya canzawa ba, da haka sai yacewa Meer "Gaskiya baza'a iya canzawa ba dole sai da finger ɗina