Author : Aysha Cool Category : Romance
masa still dai bata ce komai ba,
Hannu yasa ya ɗago ta yana kallon ta, sannan yace "plss ki daina nagaya miki yanzu kishiga cikin gidan kifito ina jiran ki a mota,
"To" tabashi amsa
"Yauwa tawan muje in rakaki,
Hannun su riƙe suka ƙarasa bakin gate ɗin sannan ya ƙwanƙwasa gate ɗin mai gadi ya buɗe musu saida yaga shigar ta da ta shiga ɗin ma saida tayi nisa sannan ya bar bakin gate ɗin, ya koma gurin Sam da yana tsaya yana kallon ikon Allah,
Sam na zuwa, Shettima yace "Allah Sam wai kaine haka Allah mai iko yau naga abun da yafi ƙarfi na, yaushe ka zama haka?
Ɗan murmushi Sam yayi yace "abun da yafi haka ma zaka gani indai akan tane,
Shettima yace "ai naga alama, nima akan hanya nake duk ka tsayar dani, yanzu ya muke ciki zaka koma ɗin ko bazaka koma ba,
"Shettima kai kasan yanda akai na ɗauko yarinyar kuma kasan halina kasan abun da zan iya yi da abun da bazan iya yiba, yanzu kamar ni dan momma ta ganni da mace zata ringa zargina har tayi min irin korar nan ta bari inyi mata baya ni ma amma taƙi saurarata ta koreni akan abun da bata da tabbas akai..,
Shettima yace "Tofa mai yafaru ni wallahi bansan komai ba yama akai ka kaita gidan, kuma ka bari ta ganta,
Sam yace "yarinyar nan tana cikin wani hali tana buƙatar taimako bayan na maida ita a loƙacin ta kirani tana kirana kuma sai tasaka min kuka na tambaye ta mai yake faruwa sai tace min mahaifin ta nace zan dawo mata dashi, bayan nan kuma washe gari ta ƙara kirana muna cikin waya kuma najita shiru to da har zan kashe sai kuma naji ana zaginta har da su duka, daganan na tashi na tafi gidan su ina zuwa naga anturo ta waje an watso mata kayan ta ana zaginta..........daga nan dai yabasa sauran labarin da inda yakaita gidan hajjaju har suka cutar da ita ya ɗaukota da labarin da tabasa na mahaifiyar ta shima saida yabasa har zuwa abun da yafaru tsakanin su momma tazo ta gansu tare ta yi masa wannan karon,
Shettima yayi mamakin yanda duk waɗannan abubuwan suka faru amma baisan komai ba, sai yanzu,
Nan dai ya tausayawa Sam, sannan yace masa yayi hauƙuri idan itama da kaifinta shima da laifin sa da yabari har tayi kwanaki a ɗakin sa batare da yayiwa momma bayani ba ai kamata yayi ma tun loƙacin da ya ɗauko ta yakaita gurin ta yayi mata bayani ai zata riƙeta amma baiyi ba, dan haka duk hukuncin da ta ɗaukama bai kamata shima yayi fushi ba,
Daga nan kuma Shettima ya ɗora masa da labarin abun dake faruwa iya abun da yasani,
Ba ƙaramin tsorata Sam yayi ba da jin abun da yafaru baya nan, cike da mamaki yake kallon Shettima yace "wai Ammah kake nufi yanzu bata cikin gidan, shi abun da yafi ƙara basa mamaki ma shine wai shi ake so a ɗora sarauta shiyasa duk suke wannan makircin wannan wacce irin rayuwa ce ai bashiri Sam da kansa yaje wajen gate ɗin yacewa mai gadi yacewa sumayya ta fito, ba daɗewa ta fito, tana fitowa yajata suka ƙarasa gurin motar ya buɗe mata gaba yasaka ta aciki,
Sannan ya kalli Shettima yace "mutafi gidan,
Shettima yace "a'a kadai je ni ba gida nayi ba zanje wajen tawa cikas ɗin,
"Allah ko wacece? cewar Sam,
A'a ba yanzu ba idan tayi tsami kaji, yanzu dai sauri nake gashi ka ɓatan loƙaci sai anjima,
Nan dai sukayi sallama kowa ya kama gaban sa, Sam ya nufi masarauta, shikuma Shettima ya nufi gidan su Azeema....,✍️✍️✍️
_SLM, Pls ina ƙara tuni kar wani yace banda mutunci daga wannan satin zuwa wani satin duk wanda bai biya ba, zai iya jin tsit kar kaga shiru ba update mutum yace baiga update ba zan ringa turawa iya waɗanda suka biya, idan ka biya sai intura maka sauran, saboda bana so littafi yazo ƙarshe wasu suƙi biya_
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️26_*
_______zaune suke acikin falo, Papa da Maama,Dadda da gwaggo, Abu da Ummy sai Meer da Ameesha, gaba ɗayan su sun hallara aciki sakamakon umarnin Papa da ya tara su, guri ɗaga dan yin magana,
Papa ne tayi gyaran murya tare da buɗe tare da buɗe musu taron da addu'a sannan ya ɗora da cewa "Alahamdulillah basai na ƙara maimaita abun da yafaru ba, abun da ya faru ya riga ya faru, Allah ya ƙara kiyaye gaba, yanzu dai angama da wannan matsalar haran mu na gaba kuma shine mu cigaba da addu'a Allah ya bayyana mana wannan yaron babana yanzu shi kaɗai ne tunanin mu, to amma kafin nan ina so muyi shawara a junan mu wa kuka fi ganin ya dace a ɗora akan karagar mulkin nan dan barin ta haka nan ba daidai bane dole asamu wani ya hau yafara gudanar da aiki dan dawo da ita kamar da, zamanin da yadawo tunda komai ya lafa kafin bayan raina ina so inga anayin mulki kamar yanda muka gudanar da mulki ni da mahaifina ada tsawon shekaru masu yawa komai ya canza amma yanzu ina fatan komai yazo ƙarshe daga nan har bayan raina, in Allah ya yarda nasan bazan taɓa kukan rashin magaji ba......,
Ɗan dakatawa yayi kaɗan yana kallon kowannen su, sannan yace "to ina sauraron ku maiye ra'ayoyin ku akai wa yafi da cewa da hawa kan karagar mulkin nan tsakanin kai da ɗanka yayi maganar yana kallon Abu,
Tun kan Abu yayi magana Meer yayi saurin cewa Papa wane ni a sarki gaskiya karma ayi wannan tunanin dan sarauta bata ra'ayina hasalima na tsane ta dan haka bazan taɓa zama sarki ba, gara a bawa Abu dai,
Ɗan murmushi Maama tayi sannan tace "nima dai kai na zaɓa amma naji tun kan aje ko ina ka karaya da wuri, to banda abun ka duk tsanar sa kayiwa sarauta tunda ka zama ɗan cikin ta ai ba kama cewa a bawa Abu to idan ya sauka fa saiwa kaga sai kai tunda yana hawama na daɗewa zai sauka kaga kwa dole kaine next ko kuwa?
Haɗe rai Meer yayi sannan yace "idan ya sauka ai ba dole sai ni ba nasan kafin loƙacin anga ƙanin sa sai a bashi tunda shima ɗa ne,
Gwaggo tace duk goce gocen kadai ai sai ya dawo wajen ka tunda indai da rai da lafiya su ai duk sun girma a ƙa'idama babu wanda zaiyi mulki acikin su saidai kai kaine saurayi kamar yanda ake ɗora sarki tare da auren sa ake ɗorawa ranar ɗaurin auren sa ranar da za anaɗaka sarki haka mukeyi kuma kaima haka zamuyi maka, sai ka shirya,
Wani mugun kallo Meer ya watsa mata jin abun da tace wai za ayi masa aure shi za ayiwa aure hmmm da basu kuma ba kuwa dan sai kowa yayi da nasani, bayan baya son sarautar kuma hadda yi masa auren dole,
"Kalle ni da kyau sarauta ba fashi haka kuma aure ma ba fashi ko ka kawo mana matar aure ko kuma mu aura maka,
"Uhm Gwaggo aikam saidai a aura masa ɗin dan wanna da kike gani baya kula ko wacce macen hasalima duk wacce ta nuna tana sonsa sai ya kamata da duka kamar Allah ya aiko sa,
Gwaggo tace "to kuwa saidai ya kasheta idan ankai masa ita ɗakin sa, amma ba fashi gwanda ma ya shirya,
Papa yayi ƴar dariya shima yace "a'a ba dole, nifa shawara na nema a yanke shawara, amma kunzo kun saka sa agaba, ina ruwan ku tunda baya so ku rabu dashi, yanzu daga yau zuwa wani satin zamu fara shirye shiryen ɗora Abu akan karagar mulki shikenan dai ko, mun gama magana,
Aure kuma loƙaci ne ku barsa duk loƙacin da yasamu matar aure sai yayi auren sa, kar wanda yaƙara takura masa,
Gwaggo zata yi magana, Papa yace "gwaggo dan Allah abar maganar haka, mayita wani loƙacin yanzu dai angama da wannan maganar zamu ɗora Abun Meer akan kujera tunda Meer baya so ko,
Daga nan Papa ya mayar da duban sa kan ko wannen su, yace akwai mai magana amma banda maganar ɗora Meer akai, dan naga wani ya haɗe rai to bani son jin komai daga garesa, ya faɗa yana saton kallon Abu da ya haɗe rai yana son yin magana amma Papa yayi saurin dakatar da shi,
Maama tace "to duk abun da kace hakan ma yayi nasan dai ƙarahen alawa ƙasa mutum ko yanaso ko baya so dole ya shanye ta,
Nan dai kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa, Papa yana ce akan dole Abu ne zai hau kan mulki, haka suka rabu dashi kowa yayi na'am da hakan,
Taro na shirin tashi har zasu rufe da addu'a Ameesha tayi saurin cewa "Papa ina da magana,
"muna sauraronki, cewar Papa,
Papa daman maganar karatu nane ina son mu koma makaranta,
Papa yace "ina sane da wannan abubuwane sukayi yawa amma yanzu komai alahamdulillah, gobe Friday sai kuje da yayan ku ki zaɓi wacce kike so sai aje ayi magana on Monday sai kinfara zuwa, ba wani ɓata loƙaci, bayan nan kuma sai me kike buƙata,
"Papa ni basai ma antafi nemo wata ba kawai asakamu makarantar su Amra nida ƙawata Azeema,
"Tom shikenan ba damuwa sai ki gaya mata ta shirya zuwa Monday zaku fara zuwa, Amma a wane class kuke,
"S.S 2 muke amma muna so mutafi S.S 3 saboda yanzu ƴan mate ɗin mu ma sunje S.S 3 saboda mu mun daɗe bamu je ba loƙacin da za ayi jarrabawa muka daina zuwa,
"To gaggawar mai kuke yi kuƙara maimaita wa mana, cewar Maama ta faɗa cike da tsokana,
Papa yace "a'a saboda dawowa baya, ai gwanda suyi gaba ko,
Ameesha ta kalli Maama, tace "Maama ni da nake soma mu wuce University amma kike maida mu baya,
Maama tace "nima da wasa nake,
Papa yace "nima da shawarar da nake ƙoƙarin yankewa kenan tunda su Amra ma ai jarrabawa zasuyi wannan watan da sai abiya muku gaba ɗaya kawai kuyi sai anema muku extra lesson kafin jarrabawar ta fito idan kunyi ƙoƙari kunce sai ku wuce tare idan kuma kuntsaya wasa zakuga wasa,
"Eh wallahi Papa hakan ma yayi gaskiya naji daɗi wallahi in sha Allah zamuyi ƙoƙari tana maganar harda su tashi tsaye saboda tsabar murna da jin daɗi...,
Gaba ɗayan su sun goyi bayan yin hakan, tunda daman zuwa yanzu yaci ace tagama secondary amma idan aka tsaya sai tace gaba, zata ɓata loƙaci gwanda kawai indai tana da ƙoƙari tayi gaba,
Papa ya kalli Meer yace to kai kuma fa baka da abun cewa,
"Eh banda shi,
"To masha Allah yanzu a rufe mana taro da addu'a kafin kuma musake zama,
daga nan suka rufe taro da addu'a inda kowa ya tashi yakama gaban sa, Dadda ma ta koma ɗaki daman idan suna abun su bata saka musu baki, saboda ba hurumin tabane......,
Ameesha murna akai tayi harda arar wayar Dadda ta kira Azeema dan ta sanar mata amma kuma tana ta kira bata ɗauka ba, fita tayi ta tafi wajen su Amra dan ta sanar dasu....,
**********************
______Azeema,
"Tunda taji maganganun sa kuma ya kashe wayar ta shiga tunani maganganun sa to mai yake nufi da hakan wata zuciyar tace mata to kodai sonta yake wata zuciyar kuma tace idan sonta yake ai zai gaya mata, banda kyara da mugunta babu abun da yake mata amma kuma maiyasa zaiji haushi dan ta kula wani,
Ji tayi gaba ɗaya zuciyar ta wani iri duk sai taji ta kasa sukuni gashi sai so take ta ƙara kiran sa amma takasa, ta tashi tsaye takasa zaune takasa tsaye abun sai yawo yake mata akai ta rasa ta yanda zata fassara abun,
Koda mama ta kirata da ƙyar ta iya saita nutsuwar ta taje, suna aiki amma gaba ɗaya nutsuwar ta bata jikin ta kuma har saida mama ta fahimci hakan ta tambaye ta, sai tace mata ba komai,
Hakadai maama ta rabu da ita suka ci gaba da aikin su suna gamawa kuwa ta koma ɗaki taci gaba da tunane tunane ta,
Wayar tace tayi ringing da sauri taje hartana tuntuɓe wajen ɗauko wayar saidai tana dubawa taga akasin wanda take so tagani, Hamza ne yake kiran ta amma hakannan taji bazata iya ɗagawa ba, tana kallon kiran har ya katse yana katsewa ta jefar da wayar amma sai wani yaƙara shigowa share shi tayi tana ji har yayi sau uku ana huɗun dai ta daure ta ɗauko wayar da niyar kashewa sai taga akasin number ba number Hamza ba,
Hannun ta ne ya shiga yin karkarwa wayar har saida ta suɓuce ta faɗi ƙasa tayi saurin binta ta ɗauko ta, tare da amsawa ta sakata akunne tana sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tana rufe idanun ta,
jitayi yace "kifito ina ƙofar gidan ku,
Jitayi daram daram gaban ta ya faɗi hakan ya hanata basa amsa har ya kashe wayar, sauke wayar tayi ta ɗauki hijabi ta saka, tare da fitowa waje tana fitowa ta leƙa tagaya mama zata karɓo abu awaje sannan ta fita,
tana fita ta hango motar sa, ƙarasawa tayi wajen tana ƙarasawa ya fito da sauri tare da buɗe gaban motar yace "bissmillah shiga, batayi masa musuba ta buɗe ta shiga,
Shima zagayawa yayi ya shiga tare da rufe ƙofar sannan ya juya ya zuba mata idanu, kawar da kanta tayi batare da tace komai,
"Hmm ayi haƙuri da duk wani abu da yafaru ina mai baki haƙuri duk abun da nayi miki iya haɗuwar mu da baki ji daɗi ba kiyi haƙuri dama maganganun da na faɗa miki ɗazu wallahi duk bana cikin hayyaci nane duk ke kika jawo wannan abun da tun farko kinji magana ta da duk haka bata faru ba,
Sai yanzu ta juyo ta kalle sa cike da alamun neman ƙarin bayani,
Jinjina mata kai yayi yace "tabbas Azeema kece kika jawo haka duk abun da nayi ba komai bane yasani hakan illa kishin ki duk kishin kine yajawo hakan ni kaina sai aloƙacin nasan ina kishin ki Azeema ni kaina bansan haka sonki yayi min mugun kamu ba, har yake shirin yi min barazanar tarwatsa min zuciya ba......,
Hannu ya miƙa zai riƙo hannun ta tayi saurin janyewa tana galla masa harara dan ɗaukar maganganun sa take kamar ta tsuniya,
Ɗan murmushi yayi yace afuwa bazan ƙarba amma dan Allah Azeema ina son ki fahimce ni wallahi da gaske nake sonki ki taimaka ki amshi soyayya ta dan wallahi rasaki daidai take da rasa rayuwa ta, ki taimaka min kinji,
Wani abu taji yana tayi mata yawo akai takasa tantace abubuwan da kunnuwan ta suke jiyo mata,
Ƙara katse mata tunanin ta yayi yaci gaba da roƙonta amma taƙi ta tanka masa, daga ƙarshe dai da ya takura mata sai tace yabata loƙaci zatayi tunanin akai,
Babu yanda yaso dole ya rabu da ita sukayi sallama a haka ta fita ta tafi gida shima ya juya ya tafi batare da yaso hakan ba, shi a yanda yaso yafi so su gama komai yanzu ta amince masa daga nan hankalin sa zai fi kwanciya.......,
************************
_______SAM
Yana shigowa cikin masarautar ya nufi parking space yatsaya yayi parking sannan ya fito waje yazagayo ya buɗe mata tare da miƙa mata hannu, sai ta maƙe masa kafaɗa tare da fitowa da kanta, tace muje ahaka Allah bazaka riƙe min hannu ba, kamanta abun da ya faru ko,
Harara ya watsa mata tare da kama hannun nata ya fara janta batare da ya tanka mata ba, tana ta tirtirjewa amma saida yajata da haka suka nufi part ɗin momma,
Suna ƙarasawa ya tura ƙofar falon ya shiga, momma suna zaune a falo ita da su Amra da Ameesha suna ta hirar makaranta amma ita momma tayi jigum guri ɗaya,
Da sallama ya shigo ciki, ai babu wanda ya amsa ma sai miƙewa da sukayi da sauri cike da mamakin ganin sa,
Da sauri momma ta fara takowa kusa dashi tana cewa Sameer kar kuce min mafarkin da na saba yine ko kuma gizo ɗin da yasaba yi minne yanzu ko Hamra gizo ne ko?
Danni nasan bazai dawo ba ya tafi ya bar ni bansan inda zangan saba,
Sam baisan loƙacin sa ya saki sumy ba ya tafi da saurin sa ya rungume momma kamar zai zubar da hawaye haka yake ji, ganin duk yanda ta canza bai taɓa tunanin abun ya taɓa ta haka ba,
"Momma kiyi haƙuri ki yafe min momma bazan ƙara tafiya nayi kuskuren ƙin dawowa da wuri duk da nasan kina nemana amma dan Allah kiyi haƙuri,
sakin ta yayi yana ƙara bata haƙuri,
Ita kuma sai ta fashe da kuka ta shiga girgiza masa kai tana cewa itace da laifi da bata saurare saba data saurare sa da duk haka bata faru ba, daga nan cikin kuka ta ɗora da cewa Sam Ammah ta tafi Waziri ya tafi ga Abban ku na ya tafi duk sun kasan ce masu son zuciya, Sam yanzu ba......, Hannu ya sa ya rufe mata baki,
Sannan yace "momma kiyi shiru nasan komai kar ki ƙara cewa komai, ki daina tuna abun da ya riga ya wuce,
kamota yaƙarayi yace "momma yanzu ki kwantar da hankalin ki mubar komai mu miƙa lamarin mu ga