Author : Aysha Cool Category : Romance
ake baice komai ba akan su,
Tafiya kaɗan ta kawo su, cikin masarautar, bayan sunyi parkin, Abban Ameesha ne ya fara fitowa sannan ya yasa hannu ya fito da Dadda, tare suka jera, Dadda gidan ta ringa kallo sai ta tuna loƙacin da ta fara shigowa neman shalelen ta, tana ta kallon gidan har suka ƙarasa part ɗin su Maama, da sallama suka shiga, ciki, babu kowa a cikin falon dan haka suna shiga, Abban Ameesha yaɗan ɗaga murya yace Maama Papa gamu mun dawo ku fito kugan ta,
Dariya Dadda tayi tace "kai ya zaka fara kira min wasu al'umman daban, to ba wanda zangani, jikalle kawai nake son gani ba wasu tsaffi ba, da bansan dasu ba,
Bossay da ya shigo yanzu yaji abun da take cewa yace "Ke kuma gajen haƙuri to ai jikar taki bata nan kamar kura ta cinye ta, kwanaki da wasu maza suka fita da ita ai basu dawo da ita ba, dan haka sai kalli waɗanda ba kyaso ɗin ko kuma mu mayar da ke inda muka ɗauko ki, in bazaki iyayiwa mutane shiru ba, ke bakin ki kullum haya haya,
"Yo inajin dai ba da bakin Aminatu nake suruntun ba, kuma bakai ka dawo dani kaida a tunanin ka idan takaine zan yarda indawo ai da inbiyo ka mu dawo gwanda inmargaya, dan haka kaja bakin ka kamin shiru kaga nifa karka ƙara yi min magana, ina farin ciki baza ɓatan raiba, kuma bakin ka ya sari ɗanyen kashi na me jego mutuwa saidai kaga anayin ta agidan ku amma ba anan ba, saidai idan gyatumar ka kurar tacinye, kaji mu da ɗan banzan yaro watakon har yanzu baka canja hali ba to wallahi ka fita daga idona tun kan na zubawa idon barkono,
Bossay zaiyi magana, Abban Ameesha yayi saurin cewa Dadda ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya ɓata miki rai rabu dashi, jikar ki ta nan babu abun da yasame ta lafiyar ta ƙalau, wataƙil suna makaranta shiyasa baki gansu anan ba, amma nasan suna kan hanya, yanzu zasu shigo,
"Allah Abba itace da wata magana matar nan fa ba'a iya mata maimakon tayi shiru ta jira anuna mata komai amma sai tayi gaba gaɗi, nifa dama anbarta ta lulu mutum ya tsufa sai ƙin mutuwa,
"Kai kai wallahi ka kiyaye ni kaga zo ka fita daga gurin nan,daman haka kake bantaɓa sani ba, to wallahi akanta zamu ɓata da kai, zo ka fita, cewar Abban A,
Dadda harara ta watsawa Bossay tace "ai indai wannan ne kaɗan ma kagani, wallahi kaf duniyar nan babu yaron da ya raina ni irinsa, duk maganar da yaga dama gayan yake saboda bashi da ta ido wallahi kaide bakayi gadon arziƙi ba irin na ƴan uwanka, wai me yasa ma kake cigaba da bibiyata, ka fita harkata tunkan jikinka yagaya maka, dan zansa wannan basumuden ya karkarya min kai,
"Ah ah Oyo Oyo suka jiyo muryar Maama tana faɗa tana faɗaɗa murmushin ta, ta ƙaraso gurin, sannu ku da zuwa kunsha tafiya, sai yau tun jiya muke zuba idon ganin ku,
Murmushi Abban Ameesha yayi yace wallahi bamu samu damar dawo wa jiya ba, sai yau ta samu lafiya,
Itama Dadda sakin fuskar tata tayi sannan suka gaisa, tare da komawa kan kujeru suka zazzauna,
Dadda de duk a ƙage take ta ga shalelen ta dan haka ta kasa haƙuri tace "wai ni sai yaushe zata dawo ne nifa in ba yanzu zata dawo ba ku kaini inda take ni inje inganta, dan wallahi ita kaɗe nake son gani,
Maama ce tace "ai yanzu hakama suna kusa da gida yanzu zaki gans......., Shiru tayi sakamakon maganar su da tajiyo, sai tace to kinji suma sun dawo,
Da sallama Azeema da Ameesha suka shigo cikin falon,
Dadda ce ta riga kowa amsawa da "wa'alaikissalam shalele na,
Cikin mamakin ganin ta da zaro ido Ameesha tace DADDA..!!!!
itama Daddar meƙiwa tsaye tayi tace "shalele na, ina kika tsaya ne tunɗazu na dawo nake jiran ki,
Da gudu Ameesha ta kwasa tare da yin cilli da duk wani abu dake hannu ta, ta tafi gurin Dadda tana zuwa ta faɗa jikin ta, Dadda saboda murna da farin cikin ganin ta, bata san loƙacin da tayi sama da Ameesha ba, ko nauyi bata jiba, harda suyin juyi da ita,
Sannan ta sauke ta, nan suka shiga sauke nufashi, Ameesha tace DADDA nayi missing ɗin ki irin over ɗin nan, gaba ɗaya duniyar bata min daɗi da ba kyanan babu wanda yake kula dani kowa baya sona kamar ke har auren......., Sauri tayi ta rufe bakin ta bata ƙarasa ba, idon ta ta mayar kan Bossay sai taga yana kallon waya wata ɓoyayyir ajiyar zuciya ta sauke da Allah yasa bata ƙarasa ba,
Sadda kam itama zayyano mata yanda tayi kewar ta ta shiga yi, kuma batayi tunanin komai ba akan maganar auren da tace,
Azeema ma ƙarasowa tayi suka gaisa da Dadda cike da farin cikin ganin juna, nan suka rikice da zance wannan yace wannan, wannan yace waccen ko gajiya da surutu basayi, kowa kaga fuskar sa ɗauke take da farin ciki da annuri marar misaltuwa......,
________MEER
Basu sha wahala ba, gurin gano inda tsohon yake domin suna zuwa yayi wa masu shagon nan jan ido akan inbasu faɗi inda yake ba duk sai ta kashe su domin yaga jakar sa ranar dan haka kawai su faɗi inda yake,
Duk da haka ƙin faɗa sukayi, saida sukaga de dagaske yake zai iya kashe sun, dan har yafara kai musu mazga, ɗaya yayi saurin faɗa yace, "yana cikin dajin bayan mu amma yanzu yana cikin garin ƴarsa ce ba lafiya an kwantar da ita a asibiti, sai Meer yace su tafi asibitin.....
Nan ya tisa ƙyeyar su, suka shiga mota suka tafi asibitin dake cikin unguwar,
Sune agaba su Meer na biye dasu baya har suka ƙarasa bakin ƙofar ɗakin da take, turawa sukayi suka shiga da sallama,
Tsohon dake zaune a gefen matar yana bata abu abaki, ya amsa musu sallamar batare da ya ɗago ba, saboda yasan muryar su, shiyasa baiɗago ba ya amsa, sannan yaci gaba da batan da yake,
Har ciki suka ƙaraso, sai bayan sun shigo suma su Meer suka ƙaraso gaban gadon,
Batare da tsohon ya ɗago ba, yace "kunga ai da baku zo bama, dan har sun bamu sallama, yanzu nake shirin dawowa ma,
"Daidai kenan sai muwuce haka muke so daman, da sauri tsohon nan ya ɗago har cokalin hannun sa na faɗuwa, jin muryar da bai taɓa tsammanin jinta ba,
Meer ne yace "sannu da ɓuya, sai ka taso mutafi, iyalen ka na can,
Haɗe rai tsohon yayi yace "kaga ɗan Allah ka fita daga rayuwata me yasa kake bina ne, ko kasanni, ne, daga haɗuwa rana ɗaya amma duk inda ka ganni sai ka biyo ni me kuma ya kawo ka, nan, to ni babu inda zani bani da wasu waɗanda nasani, a rayuwata nikaɗai ne,
Meer yana kallon tsohon da yabawa ƙarfin halin da, "hmmm oh har waɗannan duk baka sansu ba, yafaɗa yana nuna masa hotunan su da ya tura a wayar Bossay,
Cak tsohon yadaka ta, da komai, sai kuma ya fara kalle kalle shikenan yaron yakamasa bashi da wata hanayar da zai ƙara gocewa dole ya amsa,
"Kayi shiru ko baka san suba, suma,
Shiru yayi anama, sai daga bisani idon sa har ya fara canza kala, zaiyi magana, Meer yace ya isa kar kace yanzu dare nayi Please ka shirya mutafi,
Ƙin amincewa yayi da farko har saida matar tace Baba wai akan me kuke magana saboda ita bataga hoton da yake nunawa ba, indai kasan shi mutafi mana, kaifa kace min adaji muke rayuwa, to me yasa zamu koma daji bayan wannan ɗan uwan naka yace mutafi, dan Allah mutafi, danni fa daman bazan iya komawa inzauna a daji ba, da ɗinma dan bana cikin hayyaci na ne,
Babu yanda tsohon nan ya iya dole ya amince dan yasan halin ƴar tasa kodan samun farin cikin ta dole ya amince, nan yace musu ya amince su tafi,
Haka yace su jirasa yaje gurin doctor ya dawo, bayan ya fita,
Meer yayi ta kallon matar, ya ƙura mata ido ko ƙiftawa bayayi, harsai da ta fahimci kallon da yake mata, da tayi shiru amma taga abun nasa ba na ƙarewa bane, hakan yasa ta haɗe ranta tana mishi wani irin kallo, tace Malam kallon fa, bansan kallo Please, tana faɗar haka ta juyar da kanta gefe,
Saurin janyewa yayi cike da kunyar kama san da tayi yana kallon ta, baisan loƙacin da yace "I'm sorry ba"
ko kallon sa batayi ba, tunda ta juyar da kanta, bata kuma kallon inda suke ba,
Shi kansa yayi mamakin jin yabata haƙuri kuma yanda tayi burus da su hakan bai ɓata masa rai ba, sai jima yayi matar ta burge sa....
Jinjina kan sa yayi kawai aransa yana ayyana yanda ya fahimci ɗabi'unta, ita bakamar mahaifiyar ta take, kamar tana da miskilan ci kuma mafaɗaci ce daga ganin ta, yanda tayi da bakin ta tana yatsina fuska sai yaga kamar Ameesha, anan kamar su ta fito sosai, amma normal kallo idan kayi mata in ba kamar jini ba basa kama,
Suna cikin haka tsohon ya shigo tare da Doctor nan yayi musu bayanin duk abun da zasuyi da kulawar da take buƙata da abun da bata so da abun da take so, duk saida yayi musu bayani sannan yayi musu rubuce rubuce ya sallame su,
Daman ba wani kayan arziƙi gare suba, ita de loƙacin da yakawo ta asibitin ya siyo mata wata sabuwar doguwar riga ita kaɗai ce dan wanɗanda yazo dasu an jefar dasu, sai ɗan kayayyakin abincin su duk de suka farka ta komai, sannan ta sauko daga kan gadon da ƙafar ta take takawa jikin ras kamar ba wacce ta tashi daga kan gadon asibiti ba,
Haka suka fito waje har suka karaso inda motar su take, a bun mamaki da sauri Meer yaje ya buɗe mata mota, yana cewa bismillah, ɗan kallon sa tayi kaɗan badai tace masa komai ba kawai ta shiga,
Sai tsohon shima ya shiga, har yanzu hakan yake jin baya son binsu, dan har yanzu da sauran tabon abun aransa, baiga hucewa ba, amma de dolen sa yayi haƙuri ya danne zuciyar sa suje dan daman shi kansa ya fara tunanin idan ta farfaɗo yaga lafiyar ta ƙalau, zaije can ɗin dan yasan daman ba lalle taci gaba da zaman cikin dajin ba, tunda yanzu da hankalin ta ba kamar da ba, gwanda suje kawai ayi ta ta ƙare, komai yazo ƙarshe,
Gaba suka shiga suma Meer ne ya zauna a mazaunin driver sannan yaja motar suka bar asibitin tare da ɗaukar hanayar gida,
Sunyi tafiya me tsawo sannan suka ƙaraso cikin masarautar, tunda suka shiga take faman bin gidan da ido, tunda suka taho take jin faɗuwar gaba, shigowar su ma kuma tasa taƙara jin bugawar zuciyar tata na ƙaruwa fiye da da, hannu tasa adaidai saitin zuciyar ta, tare da rufe idon ta tana sauraron wasu abubuwan dake mata yawo acikin zuciya,
Meer na tsaye da murfin mota yana jiran fitowar ta amma har yanzu bata fito, tsohon ne yace "Deeya.!
Sai yanzu ta buɗe idon ta ta ɗago a hankali ta kalle sa,
Hannu ya miƙa mata yace munzo ki fito mana, tun dazu muntsaya me kike tunanine haka,
Kamar bazata basa amsa ba, dan har ta ɗauke idon ta daga gare sa sannan ta ƙara maidawa, idon ta ya canza launi kamar me shirin yin kuka tace "Baba har yanzu Noory na raye Allah bai mutu ba, kuma inajin sa a kusa, duk inda yake yana kusa dani, Please Baba ka nemomin shi, idanuwana shi kaɗai suke son gani please Baba jikina yana bani yana kusa dani, abun mamaki tana faɗar haka sai kawai hawaye suka shiga sauko mata kamar famfo.....,
Baba jikin sa ne yayi sanyi shi baisan ya zaiyi ya nemomata shi ba, mutumin da ya daɗe da mutuwa meyasa take faɗar haka, da bata da hankali yana yi mata ƙaryar zai kaita gurin sa, to yanzu baisan yanda zai yi da ita ba,
Meer kam kusan ƙamewa yayi agun yana me mamakin wace irin shaƙuwa ce haka ko soyayya sukeyiwa junan su, lalle wannan ba ƙaramar shaƙuwa bace, tunda har take jin yana kusa da ita kuma batayi ƙarya ba yana kusa da itan, aikwa zaiso ganin yanda zasuyi idan sun haɗu wane irin farin ciki zasuyi.........,
[26/11, 12:30 am] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
5️⃣0️⃣
........Har yanzu bata motsa ba, ita kaɗai tasan abun da take ji a cikin zuciyar ta,
"Please dan Allah ko taso muje kina ƙara ɓata mana loƙaci kiyi haƙuri zanne mo miki shi in sha Allah, cewar tsoho,
Saida ta ƙara kai wasu ƴan mintina sannan ta yunƙura da ƙyar, cikin sanyin jiki ta fito, tare da zuro ƙafafun ta, sannan ta ƙarasa fitowa daga cikin motar Meer ne ya rufe kofar, sannan ta shiga gaba yace muje, yayi musu jagora, Sam daman yayi gaba dan yaje ta tabbatar da kowa ya hallara a falo,
wata irin tafiya take kamar wahainiya, ko kuma wacce bata son taka ƙasa haka take tafiya, suma kuma dole suka biye mata suke irin Tata tafiyar, tunda suka fito ake ta kallon su, ƴan kusa su gaidasu, ƴan nesa kuma sai kallo da gulma,
A haka har suka ƙarasa part ɗin, itade matar inbanda salati da take babu abun da take dan jin zuciyar tata take kamar zata fito,
Meer ne ya fara tura ƙofar ya shiga bakin sa ɗauke da sallama, amma sai ya tsaya a bakain ƙofa, yana kallon su kowanne fuskar sa cike da annashuwa,
maida duban sa yayi ga Abban Ameesha sai yaga shi ba kamar su ba, hankalin sa kamar yana wani wajen, baya tare da su, hasashen sane yabasa, wataƙil ko shima ya tsinci kansa cikin halin da take ciki ita ko jikin sa yabasa shima,
"Uncle Meer ya kirasa, mai makon ya amsa sai kawai ya ɗago a hankali yana kallon sa,
Sai Meer ya kuma cewa yade na ganka haka me yake faruwa ne?
Shiru yayi masa bai basa amsa ba, Dadda ce ta maida dubansa gare sa sai tace nima tun ɗazu nake kulle dakai ana cikin hira kaja bakin ka kayi shiru me yake faruwa, kasan bansan ganin ka cikin damuwa,
Juyawa ya kalle ta ya kuma juyawa ya kalli Meer, da ƙyar ya iya buɗar bakin sa yace "Babu komai kawaide....sai kuma yayi shiru,
Ameesha ce ta tashi daga kusa da Dadda ta koma kusa dashi tare da kamo hannun sa tace "Abba na kana tare da damuwa gata nan a idon ka, ɗazu ba haka kake ba, dan Allah koma me yake damun ka kayi haƙuri kaji,
kallon ta kawai yake maganar da tayi sai duk gaba ɗaya ta ƙara karyar masa da zuciya, rungume ta kawai yayi yana me jin zuciyar sa gaba ɗaya a cunkushe, cike da sanyin murya, yace "Dole in shiga damuwa baby ina cikin kewar mahaifayar kine shiyasa kika ganni cikin damuwa, duk sanda na tuna haka nake kasancewa, naso naƙara ganin ta araye akaro na biyu, amma gashi ta tafi ta barni, ya ƙarasa maganar tare da jin ƙwalla ta cika masa ido,
Hannu yasa yayi saurin share ta, itama kukan take kawai fili ne bai fito ba, amma fuskar ta har ta gama jiƙewa da hawaye, Saida ya ɗagota ya gani da sauri ya shiga goge mata yana so ya rarrashe ta amma yana jin idan ya buɗi baki da niyar yin magana shima zai iya sakin kukan dan yanda yake jin zuciyar sa tana daf da tsinkewa,
A hankali ta shiga takawa ta zuro ƙafar ta cikin falon tare da ƙara zuro ɗayar halin da take ciki yasa ko sallama bata, yi ba baba ne ya shigo shima amma shi da sallamar sa, ya shigo hakan yasa sauran ɗagowa suna kallon inda suka ji sallamar,
Dadda ce ta miƙe tsaye da sauri har ta neman faɗuwa, halin da ta tsinci kanta ya hanata, magana kawai hannu ta ɗaga ta fara nuna su, sai motsi take da baki tanaso tayi magana, al'ajabi da bazata sun hanata furta komai,
Abban Ameesha kuma da Ameesha ya rungume ta hakan yasa basu ji sallamar da a kayi ba, hankalin su yana kan na juna.
Ita kam tunda ta shigo idon ta ya sauka akan su bata ganin fuskar sa da kyau shiyasa ta tsayar da idon dan gano abun da idanuwana ta suka gane mata, idan idanunwan ta basu yi mata ƙarya ba kamar Noory ɗin ta take gani agun, shiyasa bata ma kalli inda Dadda take ba,
Jitayi kamar anajan ta hakan yasa ta shiga takawa zuwa gare shi, bata tsaya ba saida taje gaban sa, cikin wata irin murya me sanyi da nutsuwa tayi ta a hankali, tace...
NOORY....!
Jin muryar yayi kamar saukar aradu a cikin zuciyar sa saura kaɗan ya zauce jin muryar, a sukwane ya ɗago kansa tundaga kan ƙafar ta yafara kalla har ya kawo kallon ga kan fuskar ta, wata iriyar zabura yayi yana ja da baya, cike da zaro ido da tsoro, baisan loƙacin da ya janye Ameesha gefe ba, ya miƙe tsaye,
Bakin sane ya shiga rawa wajen son ya kira sunan ta, amma sai mamar mamar da baki yake yakasa faɗa, ai tunkan yace wani abuma, ta faɗa kansa ta rungume sa, tana fashewa da wani irin kuka wanda ita kanta batasan dalilin saba,
shikam mamaki da shiga ɗimuwa