KANDE Zaɓaɓɓiya By SADIKA IBRAHIM

Author :  SADIKA IBRAHIM Category :  Romance

Chapter   9 / 9

24K to 24.8K   out of 24.8K words

dubiya ba da ga fanni ka?"


"Wlh jabir kacika ɗan banzan surutu,haba mutum yana kwance bashida lfy amma ka sanya shi agaba se famar ratattako batu kake babu birki,sekace an buɗe dam din ruwa,haba dan Allaha"


"Kaiko lurwanu daɗi na da kai kenan ka cika saka ido da yanƙwana mutum,haba kalli fa yadda ƴan matan cen suka kakkallo ni, se wani faɗa kake min acikin jama'a dan na tambayi mamuda ƴan uwansa,naga ai gsky na faɗa,tunda muka kwaso shi ranga ranga muka kawosa nan bawani daga nasa da sukazo da sunan duba jikinsa,kuma dan na tambaya shike nan nayi lefi haba du Allah du Annabi lurwanu".


Se cecekuce samarin suke a tsakaninsu,wanda aka kira da mamuda kuwa yana kishingiɗe akan gadon marasa lafiya ya lumshe idonsa,ƙala be ce musu ba amma duk abinda suke fada yana saurare,har suka gama faɗan nasu kuma suka koma fira.



..... Moscow, Russia....

Wani irin gidane cable front acen cikin wani guri wanda ya yi nesa da cikin garin Moscow ɗin,kusada wani madedecin tafki,wasu manyan security ne suke shawagi agurin,duka ƙofofin gidan masu password da thumbprint ne,wasu manyan motocine kusan guda goma sha ɗaya suka parker a waje gidan,biyar agaba biyar abaya,se wata golden lemo a tsakiya,kusan atare ƙofofin motocin suka buɗe banda ta tsakiyan wacce ta kasance lemo.

Kusan mintuna asirin kafin aka buɗe daya daga cikin ƙofofin lemo din,wani ingarman namijine ya fito daga cikin motar,jikinsa sanyeda wasu simple Pakistan wear farare tas,se wani madedecin makawuya daya naɗa akan hular kansa wacce take baƙa, ƙafarsa sanye cikin takalma sau ciki baƙake,hannunsa sanyeda wani danƙareren agogo me matuƙar tsada,fararen yatsunsa sanyeda wani zobe baƙi me fuskar zaki,ya riƙe wata sanda kamar da gold me shegen kyau se walwali take,saurin buɗe masa lema akayi saboda snow ɗin da ke sauka agurin.


Fuskar mutumin kadai idan ka kalla seka kuma kallo,mutum ne majiyi ƙarfi, ingarman namiji ne sosai,fatarsa har wani yello take,fuskarsa cike da beard me ɗaukar idon me kallo,yanada kyau me suna kyau*wild king Rolex*kenan,tafiya ya fara cikeda izza irinta maza majiya ƙarfi,duk inda ya gifta se securityn wurin sun rungume hannunsu ɗaya a ƙirji tare da sunkuyarda kansu.


Yana zuwa gaban main entrance na shiga gida kofar tayi scanning na idonsa,bakinsa ɗauke da fito ya danna kansa cikin falon wanda ya ɗauki ɗumi me daɗi da ƙamshi,wata matace zaune fara me dogon gashi ta juya baya,hannunta ɗauke da wata ƙatuwar mage fara me kyau.


Takawa yake yana nufar inda take zaune,bakinsa yana fito,yana isa inda take gaban wasu duwatsu masu ci da wuta irin room heater ɗin nan na jikin bango amma wannan wasu irin duwatsu ne masu kyau da sheqi kamar normal dutse suna fitar da zafi de ɗumama daki.


Hannu yasa yana shafar dogon gashinta me kala biyu baƙi da roɗi roɗi kamar fari kamar milk,ko gezau bata motsa ba,ya cigaba da shafar sumarta har zuwa dogon wuyanta,hannu yasa ya juyo da kanta da ƙarfi ya juyo da fuskarta...ba zato wayar ɗauko rahoto ta faɗi saboda ganin fuskar matar nan..

Jama'a kande ce faaaaa, a Moscow😱😱😱


End of free pages kuma book 1.
*************************
Shin menene ainahin asalin kande?

Wanene wannan mighty wild king Rolex din?

Wanene chief commander RAYYAN RAHMAN?

Wani lokaci yake jira?

Wanene mamuda me barrow wanda ke kwance a asibiti?

Wanene general Asim?

Wanene mahaukaci kirezi?

Wai ma suwanene mlm habu da inna?

Wani sirri suka sani akan kande,wanda aljanin kanta yake yawan nanatawa?


Meye alaqaar da aljani yace akwai tsakanin kande da kirezi?


Wani mission ne RAYYAN RAHMAN ze tura special force ɗinsa?




*Duka wannan amsoshin suna dunƙule acikin littafin kande kashi na biyu wato book 2.*



# love
# hate
# crime
# black money
# soccery
# betrayal
# illegal trafficking
# smuggling
# comedy
# romance
# momsani✍️

_Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daɗe suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma yakawomu acikin wnn daddaɗan labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_


_shin dake akayi daddaɗar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku da wani daddaɗan labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_


_zazzafar tafiyace me ɗauke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haɗi da ban tausayi,tattareda zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_


*kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin 07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret*



Masoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all😘

9 / 9