KANDE Zaɓaɓɓiya By SADIKA IBRAHIM

Author :  SADIKA IBRAHIM Category :  Romance

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 24.8K words

anci dafifi ba wanda ya isa inda suke se kallo ake ana mayarda yacce akayi,gasu tsakiyar titi ga rana,ga motocin nan dole suka dakata saboda basu gama wucewa ba mahaukacin ya ratsa har aka buge shi.


Kallonsa tayi tace "kai kirezi ina zaka je ne bakada farin tuwo ne acikin kanka iye?wai ƙwaƙwalwa ce farin tuwo,kana kallo kowa an saka masa pause saboda lakwaye zasu wuce amma ka wani taho aguje, inama zakaje ne,ba a area na baroka ba meya kawo nan?kar de sake biyo ni kayi?aiko gashinan ka samu riba Dilla miƙe kirezius kawai" se masifa take masa tana turancesa kamar yana fahimtar me take faɗa,kama masa hannu tayi ta miƙar dashi tace "taho na kaika gefe ka huta".


Wani soja ne ya fito cikin baƙaƙen kaya fuskarsa sanyeda face mask ya rike wata bindiga abar tsoro yana zare jajayen idonsa yace "hey u bunch of lunatics,bazaku tashi agurin ba?bakwa gani kun tsare mana hanya ne?"


Juyowa kande tayi tana kallonsa kamar bazata ce komiba sekuma ta tsaya tamasa kallon sama da ƙasa tace "me i no wasa da ragwayen sojoji lyk U,kuma kaine benci ba ni ba ɗan renin hankali kawai, ɗan wulaqanci ku bige mutum ko sannu baku ce masa ba sannan kawani taho ciki agaba kamar tankar miyau dawasu idonka kamar gautar ɗaci kanaso ka karanta min nonsenseus,eh r u mara foka living things kawai, ni bana tsoron ka ehe ,i no tsoronka" daga hannu cikin ɓacin rai ze mareta mutane se kallo akw,wasu ma tafiya suke amma sun tsaya kallon yacce zata kaya tsakanin wannan yarinyar me shigar maza,dan bazasu ce itama mahaukaciyar bace duba da yadda take tsaf tsaf,kawai shigar ta ce ta maza.


Tana tsaye ƙiƙam ko gezau batayiba mahaukacin nan kuwa hana tsaye a bayanta se ɓoye fuskarsa yake alamar tsoro yakeji,ya rirriƙe mata riga ta baya,ganin za'a mareta da sauri ya kama hannunta yana ja alamar ta zo su gudu amma kande da taurin kai ta fizge rigarta tace "Dilla cen cikamin rigata,idan tsoro kakeji koma gefe kayi kallo,ko kuma ka hau legediz Benz dinka ka ja saɓa,wannan kurtin sojan besan ni bane,nima fa banaji Allah wlh, Nima soja ce daka ganni anan kawai wannan kayan ne bana sakawa",ta fada tana juyowa kan wannan sojan,dede sanda ya sauke hannunsa caraf aka cafe hannun,juyowa ya yi yaga wanene wannan me rabon shan wahalar,saurin ƙamewa ya yi yana sarawa wanda ya riƙe hannun nasa,yace "sorry boss,wannan mahaukatan ne suka tsayar damu,sun shiga kan hanya" yafaɗa har lokacin yana ƙame"


Kallon kande da taja daga wanda ya fito yanzu ya yi,yana sanye cikin wasu irin kaki na sojojin ciki wato elite force,ya ɗaure gashinsa da band baƙi,fuskarsa rufe da mask iya idon sa ne abuɗe,kallonta yake yadda take wank hura hanci taja ƙafa ɗaya baya ɗaya agaba ta dunƙule hannu kamar zata kai naushi, irin tana jiran kora kwana,matsowa ya yi kusada ita cikin wata exotic voice yace "sorry ƴan mata,bakuji ciwo ba ko?" "Normal kawai oga,beji ciwoba ai bani aka bigeba wannan kirezin ne" tafaɗa tana wani karkace baki gefe tana hura hanci tare da nuna mahaukacin wanda har lokacin idonsa aƙasa yana ɓoyewa abayan kande, se wani sunkwi da kai yake.


Ƙura masa ido general Asim ya yi wanda sunansa yake rubuce agaban rigar kakin jikinsa,har lokacin be cire mask ɗin ba,kallon mahaukacin yake sosai kafin ya juyo kan kande yace "cool down soja girl yi hkr naga beji ciwo sosai ba ma,amshi wannan ki siya masa maganin ko a chemist ne" yafaɗa yana mikawa wannan sojan na ɗazu hannu, kuɗi ya miƙo masa masu yawa ya amsa yana miƙawa kande,amsa tayi tana wani ci cijewa ta ƙirge 5k ta miƙa masa sauran tace "wannnan ma sun isa,zan siya masa harda abinci ma,1k kuma na siyi waken soya na dana zubar nasan yadda ake yunwar nan wasu sun kwashe" kallonta kawai yake be amsaba ta ajiye akan wata mota dake kusa dasu tace "censa yakkaɓai na sara maka,naga kamar kai nagari ne,mazan fama Allah tsare gaba da bayanka, banda wasu masu neman dukan talakawa,censa yakkaɓai" yafaɗa tana sara masa,amma wai yakkaɓai zatace masa.


Shide yana tsaye yana kallon ikon Allah tajanyo hannun mahaukaci wanda g.Asim keta ƙarewa kallo sukayi gaba, mutane se kallon kande ake ana mamakin ƙarfin halin ta,haka ta dinga tsara mutane tana wucewa janye da hannun mahaukaci wanda yake ta rawar jiki kamar yanajin tsoron mutane.

Komawa mota su g.Asim sukayi suka ƙara gaba.


Haka kande ta kai mahaukaci wani chemist aka wanke masa ciwo se yatsina fuska yake,kande na gefe tana yi masa sannu cen tace "Dilla jishi ƙato da kai se wani kwaɓe fuska kake,bawani zafin kirki nasani, kuma ma wai ina ƴan uwanka ne suka barka se galantoyi kake layi2 kwararo2,koda yake ma kaida kake kirezi ina zaka sani" haka ta dinga ɓaɓatu me Chemist nata dariyar yadda take wani buɗe kafaɗa take ita adole najimi ce.



Ana gamawa ta biya kudin taje bakin masallaci ta siya masa shinkafa da wake me mai,ta siya masa kifi soyayya ta saka aciki ta sai nasa fanta ta haɗa ta kawo masa,ko wanke hannu be jiraba ya zurma hannu yafara kai loma hannu baka hannu ƙwarya.


Kallon sa take seya bata tausayi tace "oo kirezi anji gumama, kai wlh yunwa arniya ce baruwanta da hauka ko kai yaro ne,kawai kowa farmaka take,kai yunwa Allah gama mana dake arniya kawai" idan ba gizo idon ta ya yi ba kamar murmushi mahaukacin nan ya yi,amma se taga kamar idonta ne,yana gamawa ta zuba masa ruwa ta ɗau gorar da ya shanye fanta ta watsa maganin da me Chemist ya basu ta zuba ruwa ta jijjiga yana narkewa cikin dabara ta baiwa mahaukacin nan aiko ya amshe ya shanye ba musu ta kalle sa tace "kai kirezi a haka de kamar me hankali, duk yacce akayi da kai ba wata damuwa,kuma dan Allah duk ƴan uwanku aka rasa wanda ze kula dakai,nagade ba ka duka balle suce, yaude nayi aikin lada,dole ma na faɗawa su zakarius".


Seda ta ga ya fara bacci aƙasan bishiyar mangoro da suka zauna sannan ta tashi tace "barin ware nide,gashi bakada suna to korezi se anjima na saɓe".



Hartayi nisa mahaukacin nan be dena kallonta ba,idonsa cike da hawaye.


Bayan inna ta gama kulawa da hafsatyta mata duk wani abinda yakamata tamata sallama ta wuce asibitin mlm Aminu Kano gurin Maryam wacce take nan rai a hannun Allah, ta kasa haihuwar abin dake cikin kula ga haihuwar,duk ta galabaice ta fice a hayyacinta, tana ganin inna ta fashe da kuma tana rike hannun innar tace "kuyafemin inna mutuwa zanyi,dan Allah kice mama da baba su yafe min,momy da Abba kuma ku yafe min dan Allah mommy kicewa Aliyu shima ha yafemin" tana gama faɗa tafara salati,da sauri inna ta ciro ruwan addu'ar da mlm yabata ta kafawa Maryam abaki wani ya shiga wani ya zube haka har tasha kusan rabi,mintinan goma tsakani tafara wata irin jijjiga kamar convulsion ya kamata da sauri mommy sarakuwar Maryam ta fita ta kira nurses suna zuwa sukace kowa yafita abasu guri.


Kafin awa daya Maryam ta haifi abinda ke cikin ta ashe twins ne gasunan kamar ƙadangaru haka aka nannaɗe acikin tsumma aka baiwa daddyn Aliyu dan shi Aliyu mijin Maryam baya gari yana hanyar dawowa.


Tasamu bacci,acen inna ta wuni har dare, koda kande ta koma gida bataga inna ba agurin mlm ta tare se addabar sa take da sheri kala2 tana masa zancen bazawararsa batula,anan unguwar take tana mugun son mlm habu,hakan yasa duk inda taga kande yi take kamar ta mayar da ita cikin ciki.

Se dare kusan taran tare inna ta dawo,koda ta dawo ta samu kande tayi bacci a ɗakin Amo.



Zaune take agaban madubinta na tsafi ta saka doguwar rigarta baƙa wacce take sawa idan zasu gana da bokanya mama,cikin ɓacin rai da murya me firgitarwa mama tace "Zabba'u babu yadda za'ayi aikin ki ya yi kyau bayan kin zauna kina bacci,an toshe mana duk wasu hanyoyi da zamu kuma samun galaba akan ƴaƴanki,daga yanzu bazamu kuma samun damar sadaukar da jininsu wa dodo ba,sannan ƴarki siddiƙa ba abinda zamu iya yi mata,na gargaɗeki akan karki yadda kowa ya ganki alokacin da kike birne mahaifa da kuma jinjirin karyar nan,kin karya mana doka saboda haka dole ki karɓi hukuncinki"



Cikin matsanancin firgicin mama take cewa "kitemakeni yake mama Ajuji yaja da zamaninki yake mama me tukunyar Sheri,wallahi bansan yadda akayi hakan ta kasance ba,bansan wanda ya ganni ba a sanda nake aiwatar da aikin,seda na tabbatar kafa sun kau kafin na aiwatar da aikin,sannan bansan taya aka toshe mana hanyoyin baiwa dodo Ajuji jinin su Hafsatu ba,mama kitemaka min,abani wani aikin komin hatsarinsa inde ƴata siddika zata dawo cikin nutsuwarta to koma meye na amince zanyi".



Ɗago kai mama bokanya tayi baka iya hango fuskarta sam,se wani abu jaa sosai kamar garwashi wanda yake nan kamar idonta,cikin muryarta me rarrabuwa tace" babu wani aiki da zaki aiwatar da ze ceci ƴarki,tun farko mun gargaɗeki amma shashancinki da banzan tunanin ki yabaki cewa ke kaɗai ce me jiran duhun dare domin aiwatar da buƙatarki,saboda haka a yanzu de babu abinda zamu iya miki,karki kuma nemana idan ba abu me muhimmanci kika zo dashi ba"


Jiki a sanyaye mama ta rufe madubin ta na tsafi,kuma ta duƙufa acikin tunanin neman mafita,tabbas ko ya zatayi seta ga bayan A'isha,tunda suka taso a rayuwa itace matsalarta, tunani tafarayi rahuwarta ta baya.


FLASH BACK..


Zabba'u mama da A'isha Inna,maƙotan juna ne kafin suyi aure,tun suna yara ba wani jituwa suke ba Allah be haɗa jininsu ba sam,haka kawai Zabba'u ta tsani A'isha batareda wani ƙwaƙƙwaran dalili ba,irin tsanar nan ta rashin haɗuwar jini marar tushe.


Islamiyyarsu ɗaya, Zabba'u ta girmi A'isha,amma A'isha na gaba da ita a makarantar islamiyya,saboda ƙoƙarin A'isha itace head girl a lokacin,wata rana tana tsaron latti abakin gate itada ƴan uwanta prefect Sega Zabba'u da tawagar ƙawayenta ƴan salon tsiya kai ba kokari,haka sukazo kansu tsaye zasu wuce amma prefect din nan sukace dole se an musu bulalar latti,nan fa faɗa ya ɓarke harda dambe A'isha na gefe duk masifarta bata fiya dambe ba,dan irin mutanen nan ne masu zuciya da nacin faɗa,kuma inda tasaka maka hannu seta fitar da jini,hakan yasa bata fiya dambe ba.


Tafiya tayi ta sanarda shugaban makarantar alokacin yana meeting da wasu malamai da alarammomi akan musabaƙar da za'ayi yana basu sunayen ɗalibai masu hazaƙa,acikin malamai baƙin fuskar da sukazo makaranta harda mlm habu,acikin ɗaliban kuwa harda A'isha,da sauri shugaban ya tashi ya biyo bayanta, haka ma mlm habu,koda sukaje sun samu Zabba'u tacire hijab ɗinta se tiƙar dambe take da prefects ɗin,yaranda tama girmesu,aikuwa nan da nan shugaban makaranta ya tattara su zuwa Ofishin sa, aka tmby meya faru nan fa kowa ya hayayyaƙo tana bada bayani,kowa nason ace shine me gsky, A'isha na gefe batace komi ba,buga musu tsawa shugaban makaranta ya yi kafin ya juyo kan A'isha yace "head girl Muna sauraron ki meya faru?" Nan ta kwashe yadda akayi ta fada cikin nutsuwarta kanta a sunkuye, nan shugaban makaranta ya baiwa wani malami bulala yace ya zane masa su Zabba'u,aiko agaban baƙin malaman nan aka zanesu se sharɓar kuka suke amma Zabba'u ko gezau batayiba duk da yadda bayanta ke raɗaɗi dan sun daku, kuma shugaban makaranta ya fi ga musu faɗa harda ce musu manyan kawai,da ƙannen bayansu suke faɗa,A'isha na gefe tana murmushi, Zabba'u kamar ta tashi ta shaqe A'isha har lahira,bada ita akayi faɗan ba amma duk t fi jin haushin A'isha akan kowa.



Bayan sati ɗaya aka fara zaban ɗaliban da zasuje musabaƙar state,A'isha ce farko acikin list ɗin,bayan an watse daga assembly Zabba'u tasamu shugaban makaranta tace masa itama tana son shiga,haka ya sanya sunanta aka haɗasu da wasu malamai wanda bana makarantar ba suna musu rehazal da testing ɗin karatunsu don jin wanda ya zama colified aje dashi musabaƙar,A'isha ta haye tare da wasu maza biyu,dama mutum biyar ake buƙata,amma Zabba'u ko zango na farko bata wuce ba,gashi ta nace seta yi abinda A'isha tayi sbd sanya wa rai wahala,duk wannan abin da takeyi ustaz habu farin malami me zazzaƙar murya tare da cikakkiyar ƙwarewa akan iya sarrafa karatun Alkur'ani shine yatafi da imanin Zabba'u.


Duk wannan naci da fafutukar shi take wa,amma kamar ma besan tanayi ba,dan ko kallon fuskarta bayayi.


Haka Zabba'u tazama discolified a cikin masu zuwa musabaƙar nan, antafi kuma makarantar su itace taciyo wa Kano ta ɗaya,har kyautar maka da kuɗaɗe masu yawa A'isha ta samo,haka aka dinga murna aka shirya walima akaci aka sha,A'isha ta baiwa abbanta kyautar kujerar hajjin da aka bata.



Kawayen Zabba'u babu wacce batasan irin mugun son da take wa ustaz habu ba,har kirari mata tare da canza mata suna,ZAHAB shine sunan da tamayar wa kanta,ba wanda ya fahimci abinda ake yi,daga ɗalibai har malamai balle shi kansa uban gayya mlm habu,kwatsam aka kawo cingum da alawa anata raba wa ɗalibai wai anyiwa ustaz habu baiko da A'isha head girl,....


Aranar har wata iskar bala'i Zabba'u ta hau,aguje ta damƙi wuyan A'isha wacce take zaune a aji se tsiya ake mata wai dama soyayya suke da ustaz habu amma ba wanda yasani,ƙawayenta sun sata agaba da zolaya ita kuma se sunne kai take tana dariya,ba zato Zabba'u ta shaqi wuyanta,anyi anyi arabasu amma abu yaci tura,se ihu ɗalibai keyi, wasu kuwa aguje sukeje sukazo da shugaban makaranta,kamar haɗin baki sefa ustaz habu shika yazo makaranta kasancewar ba ana yake koyarwa ba,aikuma wani irin karfi ne yazo wa A'isha tayi wani irin kukan kura ta ɗaga Zabba'u sama duk da girman jikin ta amma A'isha sefa ta kaita ƙasa,haka tasamu sa'ar Zabba'u ta dinga naushin baki da hancinta seda ta zubar mata da jini bana wasa ba,koda shugaban makaranta da ustaz habu suka ƙaraso ai Zabba'u ta dena iskoki ta koma ihun neman agaji,ihu take iya ƙarfinta tana faɗin arabafa da A'isha mahaukaciya ce,dakyar da bala'i ustaz habu ya sanya hannu ya fizgo A'isha daga kan Zabba'u wacce tayi laushi,fuskarta ta haɗe da jini,bakinta hanci,idonta duk sun kumbura suntum.


Se fizge2 A'isha keyi tana sake kaiwa Zabba'u cafka amma mln habu ya riƙe hannunta sosai,har seda ta gaji dan kanta ta tsaya tana mayarda numfashi fuskarta tayi jajur,se huci take,haka aka ƙara tara wani taron a ofishin shugaban makaranta,anyi anyi da Zabba'u wacce keta rusa kuka ta faɗi abinda A'isha ta mata harta sameta da faɗa amma taƙi faɗa se kuka take rafsawa.



Wani mlm ne yaje ajinsu Zabba'u da nasu A'isha ya kira mutum uku2,ƴan ajinsu A'isha aka fara tmby meya haɗa Zabba'u da A'isha fada,sukace sude suna zaune kawai sukaga Zabba'u aguje ta damƙi wuyan A'isha ta shaqe ta,sunyi sunyi su raba amma sun kasa shiyasa sukazo suka kira shugaban makaranta.



Ƴan ajin su Zabba'u aka tmby ko sun san abinda ya faru,nan fa kowa ya fara zare ido,seda shugaban makaranta ya daka musu tsawa kafin suka fara inda inda, shugaban makaranta yace wa malamin ɗazu ya ɗakko bulala ya zane masa su,cikin tsoro sukace zasu faɗa.


Babbar ƙawar Zabba'u Hairatu itace tafara bayani,"um dama wai,am um mlm wallahi tsaya kaji,dama Zabba'u ce take son mlm habu,shine yau kawai se muka ji wai an musu baiko da A'isha".



Dumm haka gaban kowa ya buga harda Zabba'u wacce ta dunƙule agefe se gumi take,ga kuka tana kan yi.

🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.






Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*


*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.

Not edited


Free page:10


Bismillahirrah manirrahim.

Tunda aka faɗi abinda ya haɗasu kunya ta kama Zabba'u,duk setaji ta muzanta,ace tana faɗa akan namijin da bemasan tanayi ba, mlm habu kuwa tashi kawai ya yi ya bar makarantar ma gabaki ɗaya,A'isha kuwa wani irin tuƙuƙin baƙin cikin ne ya kamata wato akan masoyinta ma aka mata wannan renin wayon ko,shi kuma harda wani tashi ya fita kamar munafuki ai zezo gida anjima ya sameta.


Haka shugaban makaranta de ganin ba wani abin arziki bane ya janyo faɗan se son rai irin na Zabba'u da kuma Sherin zuciya,hakan yasa ya tilasta Zabba'u ta baiwa A'isha hakuri ko kuma tazo da iyayenta gobe,ai da sauri ta bata haƙuri,don gidansu ba wanda ze goyi bayanta idan sukaji abinda ya faru,wata kila ma asaka wani malamin ya kuma zaneta.


Sallamar kowa shugaban makaranta ya yi,ya rage daga shi se Zabba'u se malamin da aka tura kiran ɗakibai ɗazu,nasiha sosai shugaban makaranta yamata,tarefa ƙara lurar da ita muhimmancin kamewa agurin mace,duk da cewa dan taso wani ba lefi bane amma abinda tayi na jan faɗa lefine,idan kuma ta duba shi wanda take faɗan dan shi bemasan tanayi ba.


Godiya ta masa kamar abin kirki,duk taji ta muzanta,tun daga ranar bata kuma zuwa makaranta ba,har aikawa shugaban makaranta ya yi akace lafiyar ƙalau,kuma tace ace ita ta haƙura da makarantar gaba ɗaya.



Haka akasha bikin A'isha da ustazu habu, watansu biyar da aure,Musa ya yi aure shima,se bayan ankawo amarya ne A'isha taga ashe Zabba'u ce,itama Zabba'u data ga A'isha amma seta nuna kamar batasan inda A'isha ta fito ba,dafarko A'isha tayi binta da lalama tana girmamata matsayinta na matar wan mijinta amma daga baya ta tattara ta dena tunda taga abin na Zabba'u ba hankali aciki.



Baran ma da Mudassir ya yi aure,mama ta janye Hadiza matar Mudassir suka haɗe kai iskanci ba wanda A'isha bata gani,har kawo yanzu bata canza zani ba.


Sauke dogon numfashi tayi afili tace "A'isha kin aikata babban kuskure na shiga rayuwata da zame mini katanga da duk wani cikar burina, kuma zan nuna miki kin aikata babban kuskure, Ni dake shega ka fasa.



*_Bayan wata huɗu_*



Kande ce take tafiya tana ƴan waƙe waƙenta,tasha wata burmemiyar rigar me botira agaba,yau kam Amo harda guga tamata,ta fesa turare se tafiya take tana ɗage kafaɗa,hannunta riƙeda kuɗi da wani ƙaramin bakko zata kasuwar ƴan kaba, yau komai na kayan miya basu dashi,waken soyar ta ma ya ƙare shine aka ɗau na agwagwa za'a tafi kasuwa siyyya.


Gitfa wasu ƴan mata tayi,suka kalleta suka kwashe da dariya, ɗaya tace wa sauran "Allah na tuba,yanzu wannan wai mace ce amma duk ta lalata jikinta da tafiyar maza,ita adole namiji ce", ɗayar ma tace "waifa soja take kiran kanta"hhhhhh suka kuma sheqewa da dariya,ta ukun kuwa tace nide birgeni take wlh,ga kyau,wannan idan zata nutsu wallahi mace ce me zati da diri" ta farkon ta kuma cewa ke dilla cen

7 / 9