Author : SADIKA IBRAHIM Category : Romance
cikin zuga mazansu suke akan sun zauna basuda ƙwaƙƙaran aiki se noma,gashinan habu ya amshe girma da ragamar komi,sugasu su biyu shikuma shikaɗai amma yafisu arziki,akan haka Musa yataɓa sakin matarsa Zabba'u, wacce takasance sumumu kasau, batada hayaniya sam amma muguwa ce,ko alama bazata nuna fushi ko ɓacin rai afuskarta ba amma seta bada mamaki ta hanyar abinda zata aikata,batada mutunci,amma sam ba a ganewa,tunda aka mata saki ɗaya sbd iyalan mlm habu dashi kansa daga nan seta cenza takunta, ganin faɗan zahiri ba riba seta koma yi ta bayan fage.
Seta zuga matar Mudassir Hadiza,dake ita Allah yamata bakin tsiya,batada kunya ko kaɗan,idan faɗa yahado ku duk abinda ya fito abakinta faɗa take yi kanta tsaye,sam bata ganin girman A'isha,ta tsani A'isha ga jan faɗan tsiya duk yadda ka kaiga hkr seta ƙureka ka tanka ta.
Hakan yabaiwa Zabba'u damar aiwatar da yaƙinta ta hanyar Hadiza.
Abangaren Mudassir tun baya ɗaukar zigar matarsa Hadiza hartaci galaba akansa ya fara adawa da ɗan uwansa,sam baya ganin ƙoƙarin mlm habu akansu.
Gashi su har lokacin Allah be basu ƴaƴa ba,seda A'isha ta haifi maza shida ajere, sannan haihuwa ta tsaya mata,Hamza,Hamis, Ibrahim, Musa, Mudassir,dan sefa yayiwa ƴan uwansa takwara sannan Aminu,bayan Hadiza matar Mudassir tasaka an riƙe bakin mahaifar A'isha ta hanyar asiri acewarta dan ita komi nata ba sirri,idan ranta yaɓaci seta furta mugun alkaba'i tare da cewa mutum seya gani,hakance ta kasance tacewa A'isha seta gani akan sunyi faɗa ranar sunan Aminu.
Alokacin ne kuma matar Musa ta haifi mace aka samata sunan Hafsatu,wata shida tsakani Hadiza ta haifi mace itama,Musa yayi2 da Mudassir yasaka sunan Amina amma ƴaki,sbd Hadiza tace muddin ya yarda aka sakawa ƴarta sunan amo to sede ya saketa kuma ba inda zata da ƴar sede ya kaiwa Amo bebiya da akayiwa takwara ta shayar da ita,shikuwa ba wacce yake ƙauna aduniya bayan Hadiza da ƴarsa,haka aka sanya wa yarinyar suna Hulera sunan uwar Hadiza kenan.
Alokacin ne mlm habu yarasu yayi ciwon kwana biyu yarasu.
Kwatsam Sega A'isha da ciki,hakan ya firgita Hadiza matuƙa dan tayi tunanin A'isha tagama haihuwa,a tunaninta A'isha bazata kuma haihuwa ba har ta mutu,hakan yasa ta sakankance kawai sede suka farga da tsohon ciki ajikin A'isha,haka tasake haihuwar ƴan biyu maza, alokacin ne akayi tashin hankali dan kiri kiri su Hadiza suka nuna baƙin cikinsu afili wai da gangan take haihuwar maza sbd ta cinye dukiyar gidan, alokacin ne suka raba gari tadena mu'amala dasu kwata2 bayan ta sauke musu kwandon hauka da shika-shikan rashin mutunci,dan ƴan uwanta masifaffu ne suma haka akayi baram baram,sam malam habu bayajin daɗin wnn rashin jituwar ta matansu,daga lokacin A'isha bata shiga harkar kowa acikin su,sbd akan fuskarta suka fada mata basa ƙaunarta itada mijinta da ƴaƴanta kuma in Allah ya yarda seta gani,hakan yasa ta tayarda bala'i sede mlm habu ya cenza mata gida sbd abinda facalolinta sukace, shikuma yace bame rabashi da ƴan uwansa, duk abinda yasamesa ko ƴaransa daga Allah ne bawanda ya isa ya cutar dasu se abinda Allah ya tsara masa.
Dama shine yake taka mata birki take rage wani abun,amma dan ta ita kullum se anyi bala'i agidan,ƙiri ƙiri se a dokar mata yara amma mlm habu yahata magana,ranar da ƴan biyu suka rarrafa sukaje sashin mama suka zubar mata da gasara kashesu ne kawai Hadiza batayiba, dake tana sashen itama, A'isha na sallah sede ta dinga jin ihunsu ga ƙarar duka alamar dukansu ake,tana zuwa mama dake bakin ƙofar shashen tashige toilet da sauri, Hadiza ko bataga zuwan A'isha ba tayi nisa se zabga musu tsintsiyar kwakwa take a hannu,aikuwa kamar walƙiya A'isha tayi wani irin tafiyar yaji da Hadiza, duk kibarta seda A'isha ta kaita kasa tanata jibga, daƙyar aka raba wnn faɗan lokacin Hadiza tayi laushi se kuka take an fasa mata baki da hanci, se bayan anrabasu sannan mama tafito daga toilet tana sallallami, ko kallonta A'isha batayiba ta kwashi yaranta wanda suke ta ajiyar zuciya.
Aikuwa aranar Hadiza bata kwana agidan ba dan wani ƙaton macijine yashige ɗakinta kan gado ya fasa kai se huci yake.
Daga kan twins inna bata kuma haihuwa ba, kullum addu'ar ta Allah ya bata mace,tanason ƴa mace arayuwarta, gashi ba halin ta ɗauki yaran facalolinta yanzu se suce tanason ta kashe musu ƴaƴa.
Ahaka Zabba'u takara haihuwar mace aka sanya mata siddiqa se Maryam, Hadiza kuwa bayan Hulera ta kara haihuwar Asiya, se Ikilima.
Mama kuwa daga baya Allah yabata namiji,kusan tare suka kara haihuwa da A'isha wacce batasan tanada cikiba har seda yayi girma ajikinta,bata faɗawa kowa ba segashi sun haihu tare da Zabba'u wacce yaran gidan suke kira da Mama,aranar Hadiza har suma takusa yi saboda baƙin ciki.
Zabba'u bata wani damuba ganin ta haifi namiji itama,amma sam aƙasan zuciyarta bataso A'isha wacce yara ke kira da inna tasake haihuwa ba,amma bakomi zasu gani,Hadiza de ita nata baƙin cikin afili yake amma bawanda yasan me mama take ciki tunda ita mijin nata yaƙi ɗaukar zuga.
Kasancewar inna a asibiti ta haihu wnn karon daga ita se mijinta, dan ƴan uwanta ma seda aka sallamota sukaji haihuwar, ba wanda yasani har uwar mijinta Amo hakan yasa seda suka dawo snn ƴan gidan sukasan ma haihuwa tayi kuma mace,ƴan uwan A'isha ƴan bala'i ne basuda mutunci haka suka dinga kiɗe kiɗe suna shewa da guɗa an haifi kANDE,ranar suna yarinya taci suna Amina,anyiwa Amo takwara ba zaman lfy lols,seya kasance kamar ba suna biyu akeyi ba,ƴan uwan Aisha sun cika gida an kashe kuɗi anyi ɓarna sosai da kuɗi da abinci da nama, sam bazakace wai ana wani suna a sashen Zabba'u ba,dan da gayya ƴan uwan Aisha suke wani abun dan niyyar su ana tankasu se sun ci uwar mutum.
Wannan yaƙara girmama baƙin cikin Hadiza kuma taci alwashi sosai akan seta lalata rayuwar ahalin A'isha,inda mama Zabba'u ko ajikinta tunda de ta haifi namiji to ai angama komi,yaro yaci suna Abdullahi.
Tare kande da Abdullahi suka taso se suka tashi kamar twins, sam basaji ko kadan tare suke zuwa makaranta Arabic da boko kullum se ankawo kararsu ko sun daki yaran mutane ko sunyi wani abun,gasu da ƙoƙari amma sam basaji,kullum mlm habu na hanyar makarantar su,shekararsu biyar amma sam basaji,a lokacin umma takara haihuwa ta haifi Ikilima,daga lokacin se haihuwa ta tsaya musu duka matan gidan.
Kande irin yaran nan ne da ake kira gifted, duk abinda aka karanta mata sau ɗaya yashige kanta kenan ba maimaici,nan take take ɗauke abu a kanta,tanada zuciya sosai batason reni,gata yarinya amma ƙoƙarin ta har tsoro yake baiwa inna da mlm, shekararta biyar amma tana iya karanta duk ayar da aka janyo acikin Kur'ani,sbd idan mlm habu na koyarwa a zaure itada Abdullahi suna gurinsa,hakan yasa duk yadda wasa ze dauke mata hankali baya hanata ɗauke abinda taji an karanta koda ba ita ake gayawa ba.
Kande ta tashi cikin tsananin soyayyar uwa da uba,ga yayye maza kowa kande, sunan da kakarta tasaka mata kenan Amo,itace take kiranta da kande ko kuma tace takwara,A'isha (inna) kuma tace uwar masu gida,wnn suna yana ƙonawa umma da mama rai,gabaki ɗaya sun tsani yarinyar ganin duka ƴan gidan kowa yana son kande, hatta ƴaƴansu ba wanda ya dakko baƙin halin uwarsa.
A cikin yaran Zabba'u siddiqa ita tafi kowa sanyi,yarinyar batada hayaniya sam,ga ilimin addini, baruwanta.
Yaran umma kuwa kusan dukkan su basu da hayaniya bakamar itaba,Ikilima ce kawai tayo halin uwarta.
Matan kusan duk sunyi aure, Hafsatu, Maryam,yaran Zabba'u duka sunyi aure, siddika ce kawai ta rage se Abdullahi autan mama.
Yaran umma ma Hulera da Asiya duk sunyi aure suma.
Kaf unguwar ansan gidansu kande gidane na ƴan izala masu ruko da addini,dan su Hamza daga malamin islamiyya se alaramma,se wanda ke kasuwa gurin kasuwanci,suka sunada aikin yinsu,bame zaman banza, twins kuwa suna jami'a.
Ko daga waje duk wanda ze shigo gidan to ina kande shine abinda ze furta,duk ta dusashe tauraron sauran yaran gidan,tun mama na damuwa harta gaji ta saki,umma ce kullum cikin wahala, batada aiki se jifan kande da inna da mugayen alkaba'i,inde akan inna ne bata furta alheri.
Haka baba Musa komi ya samu kande,ko yace wnn na uwar masu gidane, Abdullahi ko kamar bashi ta haifeshiba ganin tasa tazo ɗaya da kande hakan yasa yaron ya tattare kayansa ya koma ɗakin inna.
Ankai ruwa rana sosai da mama, dan ta kafe akan ɗanta baze zauna agurin innaba, duk ƴaƴa maza da Allah yabata amma se ɗan gudalenta za a ɗauka awani baiwa inna,hakan yajanyo baba Musa yace idan takara tayarda zancen abakin aurenta,dan shi yana ƙaunar ɗan uwansa mlm habu,kuma sam baya ɗaukar wargi, hakan yasa baya iya hanasa ɗan uwansa duk abinda ya nema,duk da cewa bashi ya nuna yanason ya rike Abdullahi ba amma ganin yaron nason zama agurin inna yasa yake jin nauyin amsarsa,dan gani yake kamar idan Abdullahi yabar gurin inna mlm habu zeji ba daɗi.
Mama tanaji gana gani aka rabaga da ɗanta,bata wani damu sosai ba dan tasan inna ba maƙetaciyar mutum bace,dan kular da ze samu agunta ko ita wacce ta haifeshi se haka.
Kwatsam wata rana aka baiwa kande scholarship daga makarantarsu zuwa babbar makarantar nan ta m.m. Haruna English academy, alokacin shekararta goma,tagama primary zataje secondary,dan jumping aka dinga yimata, ga haddar izu talatin akanta na Kur'ani.
Haka akayi ta murna agidan ana tayata farin ciki,inna kuwa har sadaka seda tayi.
Yayyenta maza kuwa kowa seda yabata kyauta.
Ranar ta ta farko a school.......
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:03
Bismillahirrah manirrahim.
Tun ranarta ta farko a makarantar tayi kawaye yaran masu kuɗi,tasaje da yaran masu kuɗi itama saboda irin kalarsu gareta,farace sosai,tanada tsayi ba lefi,gata da hanci da manyan ido,idan tana magana bakinta kamar bashi ke motsi ba,siraran lips ne da ita,fuskarta oval shape,sumar hanta tana da tsayi sosai,ga saje daya biyo ta gaban kunnen ta,tanda 1 side dimple, kyakkawar gaske ce,yarinyace amma jikinta a murje yake sosai,fatarta tanada matuqar kyau,snn gashin ta ba baƙi bane wuluk,akwai ruwan golden brown aciki hade da baƙi suffarta daban take kamar ba ɗiyar hausawa ba.
Ga ƙoƙari kamar alhuda-huda,komi aka fada mata sau daya ya zauna akanta kenan koda ba a ajinsu bane,hakan yasa satinta uku aka fara shirin yimata promotion zuwa j.s.s. 3,ranarda takoma gida tana murna tare da takaddar gayyata izuwa ha mlm habu,koda su umma sukaji labari nanfa bala'i ya tashi akan sede asaka Ikilima da saddiqa da Abdullahi a m.m. Haruna,duk da cewa siddika tana shekarar ƙarashe ne amma haka umma ta dinga bala'i,mama de uffan bata cewa,tagaji da yiwa inna hassada tunda kullum Sa'a a gefen inna da iyalanta yake.
Kwatsam rana tsaka aka dawo da kande dg school tafaɗi,sunkaita clinic na makaranta an dubata har drip ansaka mata amma sam taƙi ta farfaɗo,hankali tashe inna ta shinfiɗe ta,anata shafa mata ruwa taki farfaɗo wa, Amo kuwa banda ihun kuka ba abinda take,murya a sama irinta bebaye take faɗin,duk wanda yake son ganin bayan jikarta karya bari ta ganosa dan seta yi masa rashin mutunci,haka taketa zabga bala'i tana ihu irin ta kurame.
Haka mlm habu yadawo ya samu autarsa unconscious,addu'a kawai yake tofa mata,haka ya karanta wasu manyan surori aruwa yace inna ta shafe mata jiki,yin hakan ko keda wuya ta farka,kamar robot haka ta miƙe tsaye batareda jikinta ya lanƙwashe ba,a tsorace inna ta matsa tana zare ido cike da faɗuwar gaba,duk yayyenta dake ɗakin ba wanda be tsorata ba ganin yanayin da ta farka aciki.
Fuskarta tayi kore sosai,jikinta ma haka,idonta yakoma ɓaki duka ko ƙwayar fari babu,cikin buɗaɗɗiyar murya kamar ta maza tace "lahuhu irmati gidigam gam,abukanwatur fadurma gim gam" kamar wata bokanya haka take furta wasu irin dalamisai,jikinta banda jijjiga ba abinda yake,bakinta har wani hayaƙi yake fitarwa, nan take dakin ya fara jijjiga kamar ze ruguje,cikin ɗaga murya mlm habu ya fara karatun suratul baƙara,yi yake da karfi, nan take su Hamza suka ɗauka,da karfi suke karatun, Amo na gefe se tsandara ihu take kamar ana yankata, ta tsula fitsari yakai sau biyar,sun rungume itada inna se kuka suke, Amo se ihu take tana gwalanci wai nan addu'a take.
Ihu kande tafara yi tana jijjiga kamar ba mutum ba,cen tayi wata irin gigitacciyar ƙara wacce duk maƙotansu seda sukaji,gashi marece ne anata kiraye-kirayen sallar magrib, ihu take tana susar jikinta kafin takara yanka wani ihu me karfin da yafi na baya tazube aƙasa ta zauna kamar ƴar bori, still su mlm habu basu dena karatunba sema wasu manyan ayoyi da suke sake janyo wa,kamar a mafarki tafara rera karatun tare dasu,idan suka cenza aya itama tacenza har suka yi shiru,amma ita seda takai ƙarshen aya.
Zuciyar mlm habu akarye cike da firgicin wannan sabon al'amari daya riskesu yau,amma Cikin dakiya ya buɗa muryarsa babu wasa yace "wanene kai? Me kake yi ajikin ƙanƙanuwar yarinya irin wnn? Ko ta yimaka wani laifin ne da ka zaɓi shiga cikin jikinta,kuma ga dukka alamu sun nuna cewa kai ɗin musulmi ne".
Cikin wata babbar murya marar hayaniya akace "Assalamu alaika ya Imam Abubakar bin Hamza,Tabbas ni muslumi ne kamar yadda kaji,kuma sunana Muhammad Arun ɗan Sarkin aljanun baihak,ni musulmi ne,kuma ni ɗin na kasance ajikinta tun tana cikin cikin mahaifiyarta,sannan ni ne wanda nake bata kariya bisa umarnin kakana muzgar".
Jikin inna da Amo banda rawa ba abinda yake,yayyenta ma dauriya kawai suke,domin abin babu daɗin gani kwata kwata halittar jikinta ya sauya kamar wani ƙaton gardi, ga wasu jijiyoyi sun ratsa mata a damtsen hannunta,gashi daga ita se vest da leggins.
Jinjina kai Malam habu ya yi yace "tabbas nagani kuma naji kai ɗin musulmi ne,amma shin me wannan yarinya ta aika maka,ko ta cutar da kai ne dayasa ka bayyana akanta ko kuwa?".
"Babu ɗaya daga cikin biyun tambayoyin ka,wato zancen gsky naso nayi zamana shiru batareda na nuna wata alamar cewa ina tare da itaba,amma hakan baze taɓa yiyuwa ba,anyiwa goɗiya wani mummunar sihiri wanda akaso bayan tagama wulaqanta tayi mummunar mutuwa.
An sadaukar da jini ga baƙaƙen aljanu an tura su jikinta da mummunar niyya,kuwa hakan yakusa yin tasiri sakamakon bama tare da ita a lokacin ,munyi wata doguwar tafiya zuwa ƙasar misra domin gabatar da wani yaƙi acen tsibirin asgarul mundal, sannan mun nasaka fararen rauhanai a domin bata kariya da kuma gadinta kafin mu dawo,amma se akayi rashin Sa'a baƙaƙen aljanun da aka turawa goɗiya sunfi ƙarfinsu,hakan yasa sukayi nasara akansu har suka raunatasu,duk da cewa mun bar wani kariya ajikinta hakan yasa sukayi kwanaki bakwai suna fama kafin su sami nasarar shiga jikinta ta hanyar wacce tayi mata turensu,tabata ɗan wake taci,acikin ɗanwaken akwai wani magani wanda ya karya garkuwar da muka bari atareda ita,a jiya ne muka sami nasara akan baƙaƙen aljanun da suka addabi tsibirin da mukaje yaƙi,cike da azama muka dawo gareta kwatsam se mukayi arba da shugaban baƙaƙen aljanun da muka nema muka rasa a fagen yaƙi, yana shirin ɗaukar rayuwar goɗiyarmu,wanda da hakan ta kasance to tabbas da sede mu mutu atare da ita, domin rayuwar mu gaba ɗaya sadaukarwa ce ga ahalin goɗiya.
Kakan goɗiya ya taba temakon kakana alokacin da yayi ɓadda kama amatsayin ɗan Adam kuma almajiri, lokacin kakana ba musulmi bane,amma karamcin da kakanta yayi masa yataɓa zuciyarsa,har ya amshi musulunci,a dalilin haka yasa yake bibiyar ahalinsu.
kakanta ya temaki kakanmu, yana saurayi a lokacin batareda ma yasan cewa aljani yatemaka wa ba,a hannun kakanta Abu Rayyan kakana ya amshi musulunci,hakan yasa kakana ya tara iyayenmu yabasu labari kuma ya umurce su da amsar musulunci tare da faɗa musu lalle su kasance masu baiwa ahalin Abu Rayyan kariya har ƙarshen rayuwarsu.
Mun kasance tare da mahaifin goɗiya kafin faruwar wani babban al'amari, daga baya kuma muka koma gareta tun acikin cikin mahaifiyarta,.
Tabbas makashinku na tare daku, tabbas anaso a salwantar da rayuwar goɗiyarmu hakan yasa muka riƙe baƙin aljani Gandamul arzu bawai dan bazamu iya galaba akansa ba, a'a sedan munaso ya bayyana ajikinta akan idon ku,yaso tserewa tun da sa'ar da mukayi arba da juna aɗazu,amma na riƙesa sakamakon munaso kufara hukunta sa da kanku da ayoyin Allah,ya yi iya yinsa dan ganin be iso nan ba,sbd yasan karonsa da mlm ba zeyi masa kyau ba amma sam bamu basa damar yin hakan ba.
Niyyarsa ya aiwatar da abinda aka aikosa yakama gabansa batareda ya iso gidan nan ba amma bamu basa damar guduwa ba.
Shine wanda ya fara bayyana ajikinta sakamakon ruwan addu'a da aka shafa mata, seda muka tabbatar kun ƙonasa da ayoyin Allah ta yadda baze ƙara moruwa ba kafin muka barsa ya fita,fita ta har abada bakuma ze ƙara gigin shafarta ba".
Se yanzu ta sauke numfashi idanunta arufe,cikin sanyin jiki malam yace in Sha Allah babu abinda wani mahaluki ya isa ya yi agaremu face abinda Allah ya tsara mana.
Tabbas munji daɗi kuma muna gdy bisa kariyar da ka kasance kana baiwa ƴarmu,amma kasani mudin bil adama ne babu wani haɗi tsakanin mu daku, muna godiya matuqa amma dole zaka bar jikin wnn yarinya,idan kayi duba da ƙarancin shekarunta sbd haka ina gamaka da Allah akan kayi haƙuri ka barta".
Ido rufe kuma cikin wata murya wacce ta fi ta farko ƙarfi da firgitarwa tace "wannan ne kuma bazamu iya yi muku alqawarin aikatawa ba,zamu tafi yanzu,bazamu kuma bayyana ba,kuma zamu ɗauki mataki dede gwargwadon abinda aka aikata wa goɗiyar mu,sannan zamu aikata wani al'amari atareda goɗiya wanda muka tabbatar shine kariya agareta kuma zaman lafiyar kowa aciki harda ku,duk abinda zata aikata kar wanda ya ƙalubalanceta akai,tabbas komi yanada lokacinsa, kuma idan lokacin da muka dibarwa hukuncin da zamu yanke ya kai to tabbas komi ze bayyana.
Mlm Abubakar bin Hamza tabbas kaiɗin mutumin kirki ne,ka kasance me aikata alheri akoda yaushe,kuma me saka sharri da alheri,saboda haka karka ce zaka ɗauki wani mataki akan hukuncin mu,zamu tafiiii amma kusani muna tare da goɗiya akoda yaushe,domin nauyin kare ta yana rataye a wuyan ahalinmu,wannan alƙawarine.
NATAFIIIIIIII...., KUMA ZAN DAWOOO...."
Wata babbar hamma kande tayi kafin ta tafi yaraf ta kwanta kamar ta mutu, wani nannauyan bacci ne ya yi awon gaba da ita.
A lokacin sallar isha'i ake kira,jikin malam habu amatuqar sanyaye yatashi tasake tofe kande ta addu'o'i,wacce banda gumi ba abinda take,dukama wanda yake ɗakin ya haɗa uwar zufa.
Se a sannan inna da Amo wanda idonsu yajiƙe sharkaf da hawaye ya kumbura suka saki junansu,kaka