Author : SADIKA IBRAHIM Category : Romance
wuce,tana zuwa tun daga nisa ta cenza tafiya tana "yoo yoo maza,ya ake ciki ne,hi gayis y me news ne" ihu suka ɗauka ganin ta da wata sabuwar shiga kuma basu santa da kayan ba,se wani juyi take tana breakinh dance tana faɗin "yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta kawai se kicibis suka haɗe da wannan mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii birki agaban sa tace ......
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Not edited
Free page:08
Bismillahirrah manirrahim.
"yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta kawai se kicibis suka haɗe da wannan mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii birki agaban sa tace "arna yane? Kai kirezi r u in zaa ur hankali kuwa? Tun dazu na lura da kai se folowin ɗina kake,yane iye hw market ko kaima wankan ya maka ne?" Tafaɗa tana tsaresa da manyan idonta.
Juyawa kawai ya yi yawuce yana tafiya yana waiwayenta, zakarius ne yace "zaa kand wannan ai ya kwana2 a unguwar nan,kusan kullum yana unguwar nan ya daɗe sosai, kawaide baki taɓa ganinsa bane" taɓe baki tayi kafin tace " wai ina sagalo ne yau bezo cika chamber ba Wetin hapin dashi ne eh?"
Duna ne yace "dawa de zaa kand,wai bakisan cewa ƙojensa yana asibiti ba?,ai shekaran jiya tsohon sa yaje yasha tamasa over kawai yazo yasamu babar sagalo ya sauke mata rabin bulo atsakar baya,ai yasin baban sagalo bulkumi ne,shi har yau beyi hankali ba,tun muna yarafa yake kwalɓewa har yau be dena ba,kullum idan yashawo kayarsa seyazo ya tarawa babar sagalo gajiya,arne kawai, ga babar sagalo 50inch shine kawai ta fara nuna masa itama fa arniya ce,yadda yake wani figigi kamar taliya ƴar murji Allah ɗaukar amarya kawai tamasa ta dinga maka arne da ƙasa kan azo akawo masa agaji ya wulla second barzahu arne kawai".
Dariya kawai kande ke ƙyaƙyara,dan ita har ga Allah babar sagalo ta birgeta data sumar da baban,tun suna yara yake shaye2 daga su wiwi abun ya yi yawa har giya sha yake,kuma idan ya dawo gidan ya kwara mata amai haka zata wanke tana kuka,amma bawan Allahn nan ba wacce ya rena irinta,abu kaɗan duka,badama tayi magana seya zare belt ya yita laftar baiwar Allah,gata irin matan nan ne masu jiki da tsawo sosai gata fara dan ita Bello sagalo ya biyo,baban Bello kuwa baƙi ne wuluk,gashi kamar taliya ƴar murji ta bakin duna,sirirne sosai,auren gida aka musu da babar sagalo baya sonta shiyasa yake wulaqanta ta,ansha zugata tadena zama yana dukanta abanza amma setace bakomi wata rana ze dena,haka za ata zugata amma bata ɗauka,ko agaban su Bello da ƙannensa ne seya mata duka ba abinda ya dame shi,ansha kai ƙararsa gurin babansa me sunguwa yasa akamasa aɗaure amma take tayita kuka tana bada haƙuri wai asakesa ita ta yafe masa,haka me unguwa yashe cewa ze raba wnn auren taje ta auri wanda yasan darajar ta amma tayita kuka tace ita abarta da mijinta tanason sa,wannan dalilin yasa me unguwa ya ɗauke Bello yakaishi bauci gurin yayan baban su Bello,dake shi makamin tsangaya ne,se aka kai Bello domin ya yi karatu yadena ganin wannan taladdancin da babansa yakewa uwar amma har kawo yanzu be dena ba.
Shekaranjiya cikin rashin Sa'a yadawo abuge yazo yafara jibgar ta,to dama tafara gajiya kuma tafara ɗaukar shawarar mutane na cewa tadena zama yana dukanta agaban yara,idan ba haka ba zasu ɓatawa yaransu tarbiyya tunda dukansu mazane,haka zasu tashi kamar yadda sukaga ubansu,aiko yana fara lafta mata belt cikin zafin rai ta warto gaban rigarsa tayi sama dashi kamar ta ɗaga ƴar kaza ta haɗe shi da bango ta dinga makawa,tun yana ihu har ya fara bata hkr, amma ina tayi zuciya seta ta fasa masa kai taga yadena motsi sannan ta yasar dashi aƙasa,ko ajikinta tasaka hijabi tafita ta kira me napep tasakashi takaishi asibiti tace musu santsin ya kwashe shi yafaɗi.
Tunda takaishi tabari asibitin takoma gida,shine ta tura Bello da kuɗin magani da komi shine yake jinyar babansa ita taƙi zuwa,dalilin rashin ganin Bello kenan.
Seda tagama dariyar sannan tace "yakamata muyiwa sagalo solidarity muje muga jikin lamison tsohonsa hhhhhh", tasake sheqewa da dariya se dariyar halin gidansu sagalo suke yi.
Washe gari haka fa sake ɗibar wani wankan wanda yafi na jiya ban dariya,ta shafe fuskarta da basilin se shining take kamar takaddar tsire,tayiwa inna da mlm sallama ta tafi asibiti zasuje itada su duna su gaisar da baban sagalo daganan zata wuce kasuwa tasiyo waken soyar awararta.
Itama innar shiri take zata tafi gidan Hafsatu tayi miscarriage,Maryam kuma tana asibiti tana naƙuda cikinta be isa haihuwa ba watanta biyar kenan,amma naƙuda fa taso mata me tsanani,shine inna take shirin tafiya dubasu.
Awaje kande taga su duna suka fada mata an sallamo baban sagalo yana gida,gidan suka tafi suna sake dariyar abinda ya faru,sallama suketa har ita duk sunƙi shiga su adole maza mazansu faɗa gidan mutane haka kawai ba.
Ƙanin Bello ne yafito yace wai yaya yace su shigo kawai dan yanaji muryarsu ya gane su.
Shiga sukayi kande ce agaba se wani ɗage kafada take tana baje baya da burma burman kayanta ga fuska se shining take gwanin ban dariya tasha p cap ga sumarta data yanke tabarta dede kafaɗa ta tattare ta cusa cikin p cap ɗin,bayan su gaisarda babbar su Bello kande tace "dawa inna kina wuta alqur'an, ashe kinyiwa zaa fazaa lamiso dukan dawa?kai inna kin birgeni Allah wlh,yo dama inna yadda kiken nan da arnen kyau a kamata ya yi ace fazaa yana biye dake sau da ƙafa kamar yaron aikin ki Allah kuwa,Kinga inna ta alqur'an dagus tsoron ta yake" tajuyo kan baban su sagalo dake kwance an laulaye masa kai da bandeji tace "ahh cau cau fazaa ka daku alkur'an, innalillahi irin wannan rawani haka kallifa yadda aka mayar dakai kamar sarki kasha rawani amma na bandeji wayyihuhu inna tamu dawa de inna kincikawa fazaa aiki alkur'an Kinga kema kinyi free da duka kamar masara,da seki zauna ya yita miki jibgar dawa,amma yanzu ai kinsamu lafiya kema kai cau cau inna Sa'a de inna Allah bar mana ke alkur'an" dariya kamar ga kashe su zakarius dasu duna tun suna kumshewa har suka fara yin abunsu har Bello dariyar yake kamar ba iyayensa akewa iskanci ba,babarsu Bello itama dariyar take,dama ita tun ainahi kande birgeta take,duk yadda ake tsinewa halin kande ita batayi yarinyar birgeta take sosai gata kyakkawa ga ƙarfi kuma zamanta dasu sagalo besa sun lalace ba daga su har ita,hakan yasa ita se kawai Allah ya ɗora mata son yarinyar,baban sagalo kuwa da kande ta saka masa fazaa lamiso yana kwance se wurga idanuwa yake ga fuska a suntume baya iya magana sbd ya jibgu,ya yi gum da baki.
Kallonta tayi tace "kande ina innarki ne? Yau ba tallar awarar ne?" Keɓe baki gefe kande tayi tace "inna anacen gida nabarota tana shirin zata tafi ashibanci yi ashibanci mana waifa su yaya Hafsatu ne sukayi ɓari shine taketa shirin zuwa gaishesu harda kama agwagwarta ta yanka tayiwa yaya Hafsatu miya wai tamayarda kwaɗayi kijifa inna da iyayi,duk da de yaya Hafsatu da yaya mero basuda damuwa amma ai mama ba godewa inna zatayiba,sede ma azageta ita kuma yaya Maryam tana asibiti tana naƙuda kuma batakai lokacin haihuwar ta ba"
"Assha subhanallahi abu beyi daɗi ba Allah yabasu lfy" "amin" kande ta amsa tana ciro ɗari biyar tabaiwa inna tace asiyawa fazaa lamiso lemu,ta cewa su Bello ita zata ware kasuwa zata tafi,tamusu sallama ta fito,babar sagalo har zaure ta raka kande tana dariyar shigar da yarinyar tayi da yadda take tafiya ita bata yadda ba itama namiji ce.
AGRA INDIA.
SITHABARAN HOSPITAL.
Dr Joshi shine in charge na duba duk wata mace me ciki,ya iya aiki sosai ya kware sosai akan sanin abinda ya shafi mata musamman masu ciki.
Zaune yake a office ɗinsa yana rubutawa wata mace me ƙaramin ciki magani,wayarsa ce tayi ƙara cikin faduwar gaba ya ɗauki wayar yana miƙa wa matar takaddar taya gama rubuta mata maganin da zata je pharmacy ta amsa, nan da nan jikinsa ya jiƙe da gumi,yana picking call ɗin hoton ƴarsa ya bayyana an saka mata wuƙa awuya cikin tsananin firgita yake baiwa mutumin haƙuri akan karya cutar da yarinyar duk abinda suke so ya amince ze yi,dariya ƴan daban suka kece da ita wanda yasawa yarinyar wuƙa a wuya yacire yana cemasa ya kalli babban screen din dake bayan su, wani mutum ne ya bayyana wanda aƙalla ze iya yin shekaru hamsin da takwas,amma sbd kuɗi da suka zauna masa hakan yasa yake kama da ƴan 30y.
Fuskarsa da kansa dake da farin gashi ne kawai yake nuna ya manyan ta amma jikinsa amurje yake kamar matashi, yanada kyau sosai,jikinsa sanyeda wata irin suit se walwali take kamar an shafa mata gold,yana zaune agaban wani babban teburi aɗakin taro,kallon Dr Joshi ya yi yasaki wani wild smirk yace cikin harshen indianci "idan kana buƙatar ƴarka ta dawo gida safe nd sound dolene ka yarda da deal ɗin da muka kawo maka,dole ne kayi mana gwajin magungunan mu akan mata masu juna biyu,dole kuma duk cikin da yakai wata biyar kasan yadda kayi ya lalace domin wannan jinin miscarriage ɗin muke da buƙata a tara mana,idan kayi hakan ina me tabbatar maka seka zama shararren me kuɗin da duk fadin india babu me irinsa,namaka alkawarin wannan,sannan zan saka asibitin ka yazama lamba ɗaya da duk duniya zata san da zamansa,kaide kawai kabi sharaɗin da zamu gindaya maka,ina binka da lalama ne kawai saboda ƙwarewarka a aiki shine jarinda nakeson amfani dashi a wannan harƙallar,amma ba dan hakaba da kota ƙarfi Sena saka kayi abinda nake da buƙatarka".
Banda gumi ba abinda yake zuba ajikin Dr Joshi,Amma ba yadda ya iya inde yana buƙatar zaman lafiyar iyalansa dole ya aikata abinda suka so.
Yana cikin wannan tunanin wasu manyan manyan mutane suka shigo sanyeda kayan likitoci suka ajiye masa wasu akwatuna suka juya suka fice.
Kallon wayar yayi inda yaji ana masa magana "wannan sune allurorin na baƙin case sune muke buƙatar ka gwada su akan duk wata me tsohon ciki,su kuma na jan case din sune magungunan da zakana basu suna sha,se farin case suma allurai ne,duk macen da ka tabbatar cikinta ya kai wata biyar ko shida to akansu ne zaka yi amfani da wannan allurar,sannan zamu riƙe ƴarka dake gurin mu,har seka aiwatar da aikinmu na tsawon shekaru daya kafin musaketa" kafin ya yi wata magana sukayi saurin disconnect na kiran bisa umurnin na cikin babban screen din wanda ko sunan sa Dr Joshi be sani ba.
Wani irin kuka Dr Joshi keyi,ƴar sa shekararta goma sha huɗu,yarinyace ƙarama kuma ita kaɗai yakeda,tabbas bayason ya rasata, haka kuma bayason aikata wannan mummunar aikin da suka sanya sa akan al'ummar da basu ji ba basu gani ba,sbd yasan allurorin yasan haɗarin su.
Su wadanda akace ya yiwa masu tsohon ciki illarta shine zata sakarwa jaririn cikin cutar kansa me hadari,wanda zata iya illata har uwar ba wai yaron kadai ba,idan akayi babbar Sa'a shine za a haifi cikin amma baze zo da lfy ba, daganan se su kawo wani magani wanda shine maganin cutar wannan shine kasuwancin da suka kulla da asibitoci da dama a faɗin duniya,wani kuwa tun aciki yake mutuwa kokuma daga uwar har yaron su mutu,kuma se sun zaƙulo babban likita me cikakkiyar ƙwarewa da sanin kan aikinsa sannan suke kai masa wannan farmakin,duk kuma wanda ya bijire ko masa barazanar za akasheshi ko kuma akashe wani nasa da haka wasu suke yadda wasu kuma tayin farko idan sukaji maƙudan kudade kai tsaye suke amincewa.
Ita kuma ta masu cikin wata biyar itace wacce zata lalata cikin har se an kwashe musu,to jini ɓarin ake siyarwa wasu kamfanoni masu yin mayukan fata dana bleaching,ba iya nan ba har matsafa suna siyarwa.
Haka Dr Joshi ya yanke shawarar kawai ya kashe kansa akan ya aikata wannan mummunar aikin da ɗaukar alhakin al'umma Gara kawai yakashe kansa,dan yasan ƴarsa dake gunsu ma ba zasu barta lfy ba,bama ze kuma ganinta ba,gara kawai yakashe kansa,wayarsa ya ɗauka ya yi video akan duk abinda ya faru da duk wani details akan harƙallar ya turawa wani abokinsa dake aiki a Dubai,ko minti biyar beyiba saƙo ya shigo wayarsa da sauri ya duba atunanin sa abokin nasa ne,amma se ganin wani vedio ya yi daya jijjiga duniyarsa.
<><><><><><><>
Kande tana tafiya amma jitake kamar ana binta idan ta waiwaya kuma bata ganin kowa,tun tana shiru harta ci birki tana faɗin "ko wane arne ne yake bin bayana kawai yayo waje na gansa,in ba hakaba zan ci me ɗumama masa tuwo Allah wlh" se mafita take ita kaɗai amma ba wanda ko gittawa ya yi a hanyar,cigaba tayi da tafiyarta ta nigogi tana masifa,amma still tanajin takun mutum alamar ana biye da ita,kamar bazata juyo ba tayi kamar bata damuba kawai ta juyo da sauri aikuwa idonta ya faɗa akan wannan mahaukacin yana dab da ita.
Cikin ɗan firgita da yadda ya ke dab da ita tace "kai kirezi dan fazaan ka kasha Omo ne iye, y are u follow me,are u mad?" Sekuma tace jini kuma ina tambayarasa bayan mahaukacin ne.
Daukar wata sanda tayi tace "ware kabar nan dan me dafa muku tuwo agidanku,bar nan kona maka ɗaukar amarya na jibga a ƙas" bawan Allah ganin ga ɗakko bulala ai aguje ya ruga ya barta se Bala'i take ita kaɗai
Acen gida kuwa mama ce tazugo umma wai an hana ƴaƴanta su Hafsah haihuwa se cinye musu ciki ake tanata kuka,aikuwa umma dake ba hankali ne da itaba ta dinga yada magana acikin gida amma inna bata kulata ba sema ɗauko kwanon silbarta data zuba miyar da tayiwa Hafsatu tayi ta ajiye aƙasa tana kullo kofar sashen ta.
Umma ganin inna tamata banza cikin jin haushi tace "Allah wadaran maye me cinyewa mutane ƴaƴa" cikin zafin rai inna ta waiwayo ta kwashe fuskar umma da mari dede lokacin da Mudassir ya sanyo kai cikin gidan.
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Not edited
Free page:09
Bismillahirrah manirrahim.
Salati Mudassir yasaki yana fizgo umma daga riƙon da inna ta mata se fyalla mata mari take,cikin ɓacin rai yace "yau base gobe ba zamu bar gidan nan,Ni dama na daɗe da sanin ba'a son zamana da iyalina acikin gidan nan,kullum se kande ta kama Ikilima ta daka,yau kuma abin yakoma kan matata to ni bazan ɗauka ba,maza Hadiza tafi ki fara harhaɗe mana kayan mu".
Turo baki gaba umma tayi tace "nide gsky wnn gidan ko wutafa baka ja mana ba,Allah ya gani ba zan iya kwana acikin zafi ba,Ikilima ma jikinta baya son sauro kasani"
Mama dake laɓe abayan ƙofar sashen ta tayi tsuki ganin faɗan beyi nisa ba takoma ɗaki.
Umma tuni tayi gaba tabarsu nan suna kayan haushinsu, itade ko gobe idan Hadiza zata dinga shiga hanyarta to baza ta gaji da gyara mata zama ba itama,a zaure ta haɗu da mlm habu wanda duk abinda ake yana jinsu,har abinda Hadiza tace yana ji, murmushi kawai ya yi don yasan ko sama da ƙasa zasu haɗe Hadiza bazata iya barin gidan nan ba,sallama inna ta masa yace mata adawo lfy yabata wani ruwa acikin gora guda biyu yace idan taje ta baiwa ko waccensu, in Sha Allah inde matsalarsu ba daga Allah bace shafar jinnu ce ko wani al'amari na Ubangiji to in Allah yaso bazasu kuma ɓarin ciki ba,dan idan be manta ba Hafsatu ɓari na biyar kenan tayi,ita kuma Maryam ɓarinta biyu wnn ne aketa murna harya kai wata biyar se kuma gashi naƙuda ta taso mata da alama shima ɓarinsa za'a yi.
Amsa inna tayi ta fice,a waje taga baba Musa tayi masa sallama ya tsare mata napep tana ya barshi amma seda ya biya me napep ɗin,yanata yi mata gdy da sa albarka itada mlm habu,dan duk sanda irin haka ta samu yaran nasa itace take ƙoƙari dasu,duk shirin umma da mama,mama bata bari umma taje gidan su Hafsatu ba wanda yasan dalilinta,ita ma umman bata sani ba,ko a kwalar rigarta ma abin baya damunta dan ita ba mutum bace me son zuwa unguwa dama,mama ta fake da cewa tunda uwar asugwui na zuwa wai inna take nufi su suyi zaman su base sunje ba,da wnn mama ta hana umma zuwa gurin su Hafsatu.
Amma ita idan fitar ta ta kamata tana zuwa gidajen ƴaƴan umma batareda ta sani ba.
Kande a hanyarta ta dawowa daga kasuwa tana shirin tsallaka titi amma an tsayar da kowa daga masu ababen hawa har masu tafiya aƙafa,wasu irin maka makan motoci ne na sojoji baƙaƙe suketa wucewa aguje, tana tsaye agefe tana kallo,se masifa take wai an hana su wucewa saboda wasu banzaye masu baƙaƙen kaya,wai su sojoji,wanda tasan yanzu idan zasu ga bomb ba wanda ze tsaya guduwa za suyi "mtswwww*,taja wani dogon tsuki tana cewa "ai wlh idan jarumin soja na gaske akeson gani abari nazama soja za aga jarumta, duk wani bomb ko wata AK47,dasu igwa,dasu gurnet,dasu tiyagas da waye bazasu bani tsoro ba,kai woo ni woo ni,zaa kand zaa ƙanwar mazaje su ustazu Hamis dasu ya Musa,zaa 1 nd only soja of gidan ustazu habu me kayan koli yihuuuu cau cau" ta fada tana wani jijjiga ita bata yadda ba itama namiji ce kuma soja ce, kallonta na kusa ta ita sukayi suka kwashe da dariya.
Ihun mutane suke yi ganin wani mahaukaci ya karto aguje ta cikin jerin motocin nan yanaso ya tsallaka,cikin rashin Sa'a motar ta bigeshi,ai aguje kande ga saki kayan hannunta aƙasa ta ratso cikin mutane tana "kai ku kauce" har ta iso gaban mahaukacin nan wanda yake ta juya kansa daya ɗan fashe ga gwiwar hannunsa ma ta ƙuƙƙuje,saurin tsallaka wa tayi inda mahaukacin yake zaune se yamutsa fuska yake alamar yanaji zafin ciwon nasa,tsugunnawa tayi ta kama kan nasa ta ɗago tayi saurin yago gefen burmemiyar rigar jikinta ta ɗaure masa kan nasa,mutane