Author : SADIKA IBRAHIM Category : Romance
wani kallo,sauran yaran mutum biyu suke rirriƙe mata hannuwa suna faɗin ita hukunci ta na daban ne,su zata nunawa shigar maza to sune maza na ainahi, sbd duk da shigar maza da kande keyi hakan be hana agane cewa ita mace bace da kallon farko.
Dauda shine sunan yaron daya fara dukan layuza kuma ya ture kande,wanda suka riƙeta kuma da zakariyya,da Buhari,gefe kuma wani yaro ne kamar wawa hancinsa duk majina,ya sake baki,cikin sakalta se kallonsu yake, ɗauke da tiren dafaffiyar gyaɗarsa,ko inda ake rigimar be matso ba yana gefe yana kallo sake da baki.
Dauda ya ɗaga bulalarsa ze sake dukan layuza wacce harta fara kuka, kamar wata jarumin namiji haka ta fizge hannuwanta da suka rirriƙe,kamar kaji haka suka biyo hannun kamar an januosu suka haɗe,gib goshinsu ya daki na juna,ihu sukayi suna faduwa ƙasa kowa ba laluba kansa dan sun bugu sosai.
Juyowa Dauda ya yi aiko sejin saukar bulala ya yi ajikinsa, dukansa kande take kamar Allah ya aikota, sekace uwarsa gashi ya fita tsayi ta haɗa da su zakariyya da Buhari se jibga take,tuni sukayi buɗu2 da jikinsu agurin, se susar jiki suke suna kuka,seda tayi musu duka sosai kafin ta yarda bulalar wacce duk ta karye ajikinsu.
Bello ko harararsa batayiba amma yamaƙale ajikin bishiya yanata rusa kuka,fuskarsa tayi dameji da hawaye, ga majina yarara tanabin hancinsa har zuwa cikin bakinsa,se kuka yake jikinsa na makyarkyata.
Juyowa kande tayi ta kallesa ai tuni ya ƙara ɓare baki Yana kuka,fadi yake tayi hakuri karta dakesa, dan Allah karta dakesa,wata irin dariya ta kwashe da ita tana kallonsa tace "kai sagalo na dakeka ne kake wannan kukan?" Saurin girgiza Kai yayi kamar ze tsinke wuyansa yace "a'a baki dake niba,amma kar ki dakeni dan innarki fa baffanki yuuu wayyo Allah na" dariya take sosai ganin yadda yake kuka sosai yana suɗe majinarsa,sak dolo.
Daka masa tsawa tayi tace "ya suna ka?"
Seda ya shanye majinarsa yace "Bello",zuwa tayi inda yake tariƙe kunnensa tace "daga yau sunanka Bello sagalo kaji" tafaɗa tana zare masa manyan fararen idonta, dasauri ya jijjiga kai yace "eh naji na yadda dan Allah karki dakeni".
Juyowa tayi kansu Dauda daketa kuka tace "duk kufaɗa min sunanku", da sauri zakariyya yace "sunana Zakaria" , "nikuma sunana Buhari",nide sunana Dauda "
Seda ta sake dingure masa kai tace "daga yau sunanka Dauda duna, kaikuma zakariyya zakarius,kai kuma Buhari boris,kunajina ko" tazare musu ido.
Kamar puppet nata haka suka dinga gyaɗa kai,tace "oya zaa goo,maza2 kutashi kubar nan arnaye kawai"tafaɗa tana cije baki.
Aguje suka bar gurin tare da kayan tallar su, Bello wanda tasaka wa sagalo kuwa ko tiren dafaffiyar gyaɗarsa be dauka ba ya ruga aguje.
Allah ya yiwa kande wani irin kwarjini,ko babban mutum baze iya kallon ƙwayar idonta kai tsaye ba balle yara ƴan uwanta.
Dariya take itada layuza sunata nishadi suna mayar da yadda abin ya kasance har suka kai ƙofar gidansu kande,dake gidansu ne farkon isa,ta shige layuza tayi gaba tana murna ta siyarda dankalinta,ga yadda kande ta tare musu faɗa.
Wasa2 seda aka jera kwana biyar inde kande taje gurin tallah tofa su zakariyya zakarius sede suyi cimbi,bame kallon sashe da suke balle asiya, sede sunaji suna gani kande tasiyar da tallarta,takoma kan tallar kowa na gurin seta siyar masa bandasu, nan da nan tayi suna agurin kande me Sa'a,kowa kande ɗalibai kande masu tallah kande,malaman makarantar ma harsun san labarin kANDE me Sa'a.
Ana haka yauma kamar kullum sun biyo hanya kawai Sega su zakarius da uban tallarsu akai,Dauda awara yake da yaji, zakarius kuma shinkafa da mai Buhari kuma doya da ƙuli me mai da albasa, Bello sagalo kuma dafaffiyar gyaɗa.
Ja tayi tana kallonsu da niyyar duk wanda ya matso inda take seta zubar masa haƙura.
Amma kawai seganin tayi sun zube aƙasa suna bata haƙuri,dan Allah tayi hakuri tayafe musu ta temaka ta cire ƙofin da tayi musu aka dena siyan Kayan sana'ar su,kuka suke wiwi suna roƙonta,nan danan zuciyarta ta karye tauasayinsu ya kamata,mace koya takaiga taurin zuciya mace ce kuma me rauni,balle yarinya kamar kande.
Amma ta dake tace "dalla arnaye ku tashi kun wani riƙen kafa,oya ku ajiye kayan tallar acen", ta nuna musu gaban itacen durumi kusada wani masallaci, dassauri suka kai kayan sana'ar suka ajiye,ana idar da sallar azahar kamar anyiwa mutane kiranye suka fara tsaya wa suna siyan abinda su Dauda duna suka ajiye,kan awa daya ansiyarda kaf abincin da suka ajiye,aikuwa banda ihu ba abinda suke,suna kiran se kande me Sa'a,bata rai tayi tace ita sede su dinga ce mata zaa kand ko kuma zaa soja da turancin literature kenan.,aikuwa suka dinga fasa mata kai suna kambabata se wani hura hanci take ita adole boss.
Tundaga wannan ranar tare suke tafiya tallar su,duk shiriritar kande basa tafiya se tazo,sedaga baya suka san ashe duk a unguwa ɗaya suke,kawai layine kowa da nasu,kullum seta siyar da awararta sannan take siyar musu da tasu,agidan iyayen kowannen su an san labarin zaa kAND zaa SOJA zaa ƙanwar maza me Sa'a.
Daga baya sauransu suka dena tallar kowa ya koma makaranta,dama ana cikin hutun yajin aikine a makarantun gwaunati,a lokacin kuma aka ɗauki Bello sagalo jikan me unguwa,aka kaishi cen garin bauci gurin ƴan uwan babansa almajiranci.
Kande kuma atafau taki komawa school,har school authority dinsu sunzo dubata,Kuma sun aiko da letter akan ana buƙatar ta a school dan zasuje wani debate na state kuma sunada cikakken yaƙini da hope me yawa akan kande cewa idan akaje debate din nan da ita to ba makawa zasu lashe,sbd turancinta ma is totally different,kamar ba a Nigeria take karatuba.
Amma wat shock dem the most shine zuwan wasu malaman makarantar da aka wakilta domin zuwa duba kanden shine ganin yadda takoma, sam dafarko basu yadda cewa itace takoma total tomboy ba,abin ya basu tsoro matuƙa,sannan yadda sukaga tayi biris dasu kamar batasan inda suka fitoba ya ƙara basu mamaki,dan se wani cijewa take tana shamusu ƙamshi,ga wani kafurin turanci da take suburbuɗo wa kamar bata taɓa sanin hanyar ajin school ba.
Wani ƙarin abin mamakin ma seda sukaga Ikilima ta shigo tanata rusa kuka,fuskarta kamar tumatir sbd jaa dan itama farace,kuka take tana faɗuwa tana tashi,yauma de tsautsayi yasake haɗata fada da kande.
A hanya taga kande da bokitin awarar ta ta dawo tallah,se tafiya take tana buɗa kafaɗa tana shan ƙamshi sak de irin yara marasa ji din nan, buɗar bakin Ikilima se cewa tayi,"a'a ƴar daudu an dawo daga aikin banzan? Allah yasa ba ƙwaƙwuleki akeyi agun tallar ba yasa kika nace kullum se kinje,duk gidanmu bame tallah seke,mtwss aikin banza", tafaɗa tana yin gaba kamar wata babbar mace,Ikilima a lokacin bata wuce shekara 7 ba,amma sbd tsabar rashin kunya da manyance idan tayi magana seta baka tsoro,kuma hakan ya samo asali ne daga yadda umma take,duk nauyin zance bata jin kunyar fadarsa agaban Ikilima,kuma abakin ta Ikilima taji cewa wai kande ƙwaƙwuleta ake agurin tallah.
Cikin wani irin fusata kande ta fizgo Ikilima wacce tayi hanyar gida, jikinta sanye da uniform din sabuwar private school din da mlm yasaka su itada Abdullahi, kamar jaka haka kande ke fizgarta har zuwa gaban wani kanti, ba tsoro tare da ita tacewa me kantin "bani razor blade yanzun nan", miƙo mata ya yi tabashi kuɗi yana cemata tayiwa yarinyar ahankali kartaji mata ciwo,danshi ya dauka rikon wasa ne tayi wa Ikilima bawai rigima suke ba.
Da karfi ta janyo Ikilima har wani ɗan lungu daba mutane sosai,fizge hular kan ta tayi tasanyata atsakanin cinyoyinta da karfin bala'i ta askewa Ikilima kai tas,se kyalli yake kamar silba, kuma ta kwashi gashin ta zuba mata a jaka,Ikilima zuwa lokacin kamar zata shiɗe sbd kuka,se mulmula take akasa tana ihu, fuskarta gwanin ban dariya,kallonta kande tayi tace "now we luk zee same,duka mun koma maza dagani harke, nonsenseus kawai arniya" tasa kai ta wuce tabar Ikilima agurin.
Riƙe haɓa sukayi dukansu daga mlm har teachers din bayan sungama jin jawabin komi abakin Ikilima wacce tasha aski kamar namiji,se kuka take sherɓawa,haƙuri mlm yabata yace tashiga ciki zaizo yasamesu itada kanden yaji meya haɗasu,dan Ikilima bata faɗi gskyr me tacewa kande ba,cewa tayi haka kurum kande ta kamata tamata aski. Gogar kuwa tana gefe tana hura hanci taƙi cewa komi.
Anyi anyi da ita har malam seda yasa baki amma ta turancesa tsaf da haukarta,kuma tace wlh idan aka matsa mata seta koma sede anemeta arasa,gatade yarinya sosai amma kalaman bakinta abin tsoro ne,sanin matsalar ta yasa Malam ya basu haƙuri da cewa suje kawai daga baya ze lallaɓata ta dawo.
Ya faɗa musu haka ne kawai dan su tafi,amma yasan tunda ta kafe to no way out,Kuma ajikinsa yakeji yafara nadamar hukuncin da ya yanke a kanta.
Aranar ko anyi bala'i sosai agidan dan umma wando ta sanyo tazo sashen inna wai yau ko abata kande tamata aski ko kuma su daku da inna,mama na side dinta tanaji amma ko leqe balle tabada hakuri,haka aka dinga bala'i harda Amo,se daga murya take tana faɗin idn umma ta taɓa mata takwara seta saka itace ta sheme ta🤣da kyar mlm ya kashe wutar nan,dan alokacin baban Ikilima baya gari yayi tafiya
Haka kande ta cigaba da rayuwa ba boko ba islamiyya,tunda ƙananun shekarunta ta sami wannan nakasun, yayyenta wani lokaci har kuka suke wa mlm akan araba ta da duk wani aljani da yake tare da ita ko an samu sauƙin wani abun,dan su acewarsu duk abinda yasameta to haka Allah ya ƙaddara mata,babu tsumi babu dubara,amma be dace abarta da wannan aljanin da yake iƙirarin kare ta yake ba yana lalata mata rayuwa da future nata ba.
Duk wannan sauyin marar daɗi daya samu kande hakan be hana an cigaba da jifan rayuwarta da mummunar nufi ba,ga hassada da ƙeta kala kala,sam rayuwarta ce ba a so yanzu.
Duk da cewa ansan babu hanyar ratsa jikinta da wani sihiri hakan besa an saduda ba,dama jaki de akoda yaushe sunansa jaki, kuma duk yadda akayi dashi seyaci kara.
Haka kande ta cigaba da gudanar da rayuwarta har kawo yanzu data girma tazama cikakkiyar budurwa,babu abinda ya sauya sema gaba da yake kara yi,gashi bata ƙaunar sabon kaya,sede taje gwanjo ta zaɓo abinta,gata da tsafta da ibada,amma kayanta kamar an ƙwato abakin kura,sam bata ƙaunar guga, takalma kuwa idan ta ƙadan masa to in Sha Allahu seya dagargaje yadena ɗinkuwa sbd wahala sannan zata dena sakawa,kuma har yau bata dena tallar awararta ba.
Ga awarar tasu da farin jini,amma duk yadda kuka kai da kwaɗayi idan bata tashi fita tallah ba to sede ka mutu, bata siyarwa acikin gidan,dole sede ajirata har sanda ta fito tallarta,kuma ba kowa take siyarwa ba,taga dama ma idan ta fita tayi gun almajirai ta basu bokitin awarar tace su raba,duk maitar me siya kuwa sede ya hkra.
Idan kuma awarar ta kwana seta faɗawa me siya,tace ta jiyace inzaka siya ka siya in bazaka siyaba ka bari ehe.
Kamar de yau da ta kai chamber su ta samari seda ta faɗa musu ta shekaran jiyace idan zasu siya to idan kuma bazasu siyaba su suka sani,lols.
*_cigaban labari*_
"Mama me kikeso kicemin ne?, kina nufin wai har yanzu taurarinta sunfi na duka ƴaƴana haske? haba mama kefa babbar bokanya ce wacce ba abinda ya gagareki, atemaka asan yadda akayi aka dusasar da hasken nata,dan Allah yasani idan ina ganinta jinake kamar na haɗiyi zuciya,na tsani wannan yarinyar daga ita har uwarta,uwarta ita tamini katanga da auren mlm na ƙare a auren ɗan uwansa,gashi nan har yau banida tsuntsu bare tarko, mama kitemaka min bazan iya ƙara jurar faɗuwa ba,baze yuwu uwarta tayi galaba akaina kuma ƴarta taƴi akan ƴaƴana ba,ko ma jini nawa ne zan bayar,wannan karon a shirye nake mama,Ajuji ya ja kwananki mama me tukunyar sharri,".
Ta cikin madubin wata mata ce zaune da baƙaƙen kaya, ba'a ganin fuskarta sbd doguwar rigace ajikinta baƙa me hula hoodie,ya rufe mata fuska ba'a iya gane ainahin kalarta baƙace ko fara,sbd ba wata gaba ta jikinta dake waje.
Magana tafara kamar haka muryarta na amsawa bibbiyu..........
______________?????
Shin wacece wnn matar ta gaban madubi?,
Akan suwa take magana?
Tauraron wacece ta dusashe nata dana ƴaƴanta?
Wacece wnn matar tacikin madubi?
Muhadu a next pg.
#
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:06
Bismillahirrah manirrahim.
Wacce aka kira da Mama ta cikin madubin ce ta fara magana muryarta na amsawa bibbiyu da sauti me firgitarwa "dolene zaki bada cikin jikin yaranki kamar yadda aka saba,sannan a yau base gobe ba kije ki nemo mahaifar baƙar karya tare da ɗan da karyar ta haifa ki binne su da ransu,ki tabbatar kowa be ganki ba,muddin wani ya ganki to kome yafaru dake ke kika janyo wa kanki,kisani wannan aikin bama buƙatar kowa ya ganki ko da kuskure,in ba haka ba komi ze lalace duka abinda kika yi ze komo kanki".
Batareda ta sake samun damar sake magana ba madubin ya yi duhu cen kuma ya washe yakoma normal mirror,miƙewa tayi ta cire doguwar rigar da ta sanya baƙa me hula,fuska wacce ya bayyana seda wayar ɗakko rahoto ta kusa faɗuwa,guess whoo,mama😱
_*Nigerian elite special force*_
General Asim,"munsamu wani hint gameda wadannan ƴan mata tara da aka sace,majiya me ƙarfi ta sanar mana anfita dasu ne da sunan za'a basu aiki a Saudiyya,amma a zahiri ba haka bane,ƴan mata uku kawai aka kai saudiyya suma da niyyar karuwanci aka kaisu bayan an yaudari iyayensu,sauran kuma Uganda aka kai su,wasu kuma south Africa for prostitutional purpose*
Sannan ba iya ƴan mata suke safara ba,harda yara ƙanana suke safara suna kaisu ƙasashen waje,wasu kasuwancin sassan jikinsu ake, wasu kuma ana training dinsu ne dan su zama high assassin's, hacker's,gays etc".
Numfashi wanda aka kira da G.Asim ya sauke,har yanzu fuskarsa tana kallon wajene be juyo ya kalli me basa jawabin ba,ingarman namijine me ƙirar sadaukan maza,girmansa ma kawai ya isa ya firgita me kallonsa,yanada faɗi jikinsa ko ina amurɗe,ya goya hsnnuwansa abaya,jikinsa sanyeda kakinsu na special elite force,yanada yalwar suma me tsayi baƙi siɗik,dan har ɗaurers ya yi ta baya, hannunsa daya goya wasu irin jijiyoyine kwance akansu muscles ta ko ina,hannun kawai zaka kalla kasan ba baƙin mutum bane haka kuma ba fari bane,fatarsa chocolate color ce,sak Ethiopian.
Wani ne yasake shigowa office din yasara musu kafin lieutenant general Habib yace masa "ya akayine Captain Abdul?" Wata takarda wanda aka kira da Captain Abdul ya miƙa masa yace wannan saƙon general ne"amsar envelope ɗin L.G Habib ya yi yace "tnk u captain" seda yasake Sara musu kafin ya fita,har lokacin G.Asim be juyoba.
Tabbas abinda L.G Habib yake faɗa ya ɗauki hankalinsa amma babban abinda yafi damunsa a yanzu shine be wuce yacce yakama matarsa ta aure tana zuba masa poison a abinci ba,matarda sukayi auren soyayya amatsayinta na ƴar uwarsa,duk da cewa da farko be wani damu da ita ba,amma daga baya haka kurum yaji duk duniya ba wacce yake so da ƙauna irin Meerah.
Shiko wace irin rashin Sa'a ce dashi har haka,ace aure har biyu amma babu matar arziki a cikin,shi yasani ba duka aka taru aka zama ɗaya ba dole acikin dubu akwai ɗaya zakka amma a ina? wani guri? "Hmmmmmm" ya sauke gauron numfashi yana juyowa tare da sanya hannuwansa acikin aljihun wandon kakin jikinsa.
Subhanallahi wa bihamdihii,fatabarakallahu ashanil khaliqiin,wani irin halitta ne me wata irin fuska wacce kai tsaye bazakace ga daga jinsin daga yakasance ba, wani irin sassanyan kyau ne dashi me sanyaya zuciyar me kallonsa,kyakkawa ne ainun,shi ba fari ba shiba baƙi ba,haɗaɗɗene wanda ya amsa sunan sa me kyau,kai tsaye zaka iya kiransa da giant rocky hanmson.
Fuskarsa meɗan tsawo da faɗi,laɓɓansa jajaye ne pure red,manyan piercy silver eyes,darked brows,pointed nose,he's just damn hamson,_General Asim Al-Amin Muhammad_ the general commander na elite special force,bangare na musamman wato (ALPHAH).
Kallonsa L.G Habib ya yi yace "abokina kana lfy kuwa?anya kana bacci acikin kwanankin nan?kalli yadda idonka ya sauya,nd u look so pale,tun shekaran jiya kake cikin damuwa amma ka ƙi kafaɗa min,pls tell me my friend ko Meera ce?"
"Hmmm, exactly Habib meerahhhh" sekuma ya yi shiru,ya sunkuyarda kai don wani irin zafi zuciyarsa keyi,jiyake kamar yanzu ne yaganta tana zubawa.
"Ehen tell me ok?" Cikin lallashi Habib yake tmbyr sa, kuma ga dukkan alamu damuwar babba ce tunda har yakasa faɗa kai tsaye, "calm down bro,kasan barin kashi aciki baya maganin yunwa,pls tell me friend,kasan koda yaushe problems told is half solved always umm,so kafaɗa mini menene ya faru da meerah".
Cike da jin ƙwarin gwiwa yace "L.G i caught meerah red handed poisoning my food, she's trying to get rid of me,5 wat bloody reason huh? I loved nd care 5 her,cherish her,na bata full asset to do wat ever she want with her lyf nd my wealth, or giving her freedom is a crime? Habib pls tell me am i not worth to be loved huh?*
Habib nakasa ganewa kaina gaba ɗaya ya kulle, menene atare da ni dayasa mata basa sona? Aure biyu duka ba dan Allah suka aure niba,duka kowa da tashi matsalar da ta sanya suke tarayya dani,kowacce she's after my lyf for wat reason for goodness sake?"
Jikinsa har rawa yake idanunsa nan take suka kaɗa sukayi jajir,dasauri Habib ya tashi ya ɗakko ruwa me sanyi acikin deep freezer din dake office din yazuba a glass cup y miƙowa Asim,ba musu ga amsa ya kafa kai seda ya shanye,kara zuba masa Habib ya yi har sau uku har ruwan ya ƙare kafin Habib ya daga kafaɗar sa yana matsawa a hankali,jan ajiyar zuciya kawai Asim yake kafin Habib ya fara magana cikin taushin murya.
"Haƙiƙa Sameerah ta aikata babban kuskure,kuma dole fa fuskanci hukunci,yanzu abinda nakeson sani shine tasan ka ganta ne a lokacin da take zuba maganin?" Girgiza Kai Asim ya yi idonsa a lumshe, yace "kwana na biyu anan ba koma gida ba,tun ranar da naganta banyi making any sound ba na baro gidan,kuma na kashe wayata,kasan baze yiwu naje gidan hjy kwana ba dole zata gane akwai matsala,das y I decided to stay here at d office,tunda i have everything her just lyk home,hjy ma kiranta kawai nayi nafaɗa mata aiki ya riƙe ni bazan samu zuwa gurinta ba".
"gud,yanzu abinda za muyi shine ka kunna wayarka", ba musu Asim ya ɗakko wayarsa ya kunna,tana gama loading saƙonnin barkatai suka fara tseren shigowa,kafin kiran meerah ya biyo baya,alamar ya ɗauka Habib ya masa ba musu ga ɗauka yasa a