Author : SADIKA IBRAHIM Category : Romance
Amo kamar abin tsafi duk abinda ya wakana taji raɗau kamar ba bebiya ba.
Zuciyoyin duka wanda suke cikin ɗakin ɗauke da tambayoyi masu yawa amma kowa ya bari har lokacin daya dace kafin ya furta.
Haka mazan suka fito daga ɗakin jiki a sanyaye,akan idon mlm habu yaga gittawar mutum da gudu ya yi hanyar waje.
Girgiza Kai kawai mlm habu ya yi dan sarai ya gane ko wanene,kawai shiri ya yi,kuma yasawa ransa koma menene da yaddar Allah baza ayi nasara akansu ba.
Haka kande ta share kwana biyu batasan inda kanta yake ba,kullum se malam yamata tofi aruwa ashafe mata jiki.
Yau kamar a mafarki inna tana sallar azahar taga wani abu kamar inuwar mutum ya tsaya adede kan kande.
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:04
Bismillahirrah manirrahim.
Kafin inna ta karasa setaga kamar wannan inuwar ta faɗa ajikin kanden.
Saurin miƙewa tayi bakinta ɗauke da addu'o'i ta nufo inda kanden take akwance,tana zuwa dede lokacin kande ta buɗe idonta wanda sukayi jajir jini ya kwanta acikinsu kamar an zuba mata,baka ganin farin cikin idon ko kaɗan,tana gani tar amma idon yayi mata nauyi.
"Alhamdulillah" shine abinda inna ta furta tana kama hannun kanden datake miƙa mata.
Jikinta yayi mata nauyi sosai bata iya motsa ko ɗan yatsan ta,kuka inna keyi ƙasa ƙasa,ta janyo wayarta keypad tana dannanwa mlm habu kira, alokacin shi kuma ya shigo cikin gidan hannunsa ɗauke da wata gora ta ruwan addu'a, Kasancewar an idar da sallar ya sallami ɗalibansa masu ɗaukar karatu,tare suka shigo da twins wanda suka dawo sbd ciwon kanden.
Dasauri mlm habu yakarasa shiga ɗakin yana tofa mata addu'o'i,ahankali yace "mamana", bakinta yamata nauyi sosai amma ta ɗaga idon ta wanda yake nan gwanin tsoro sbd yadda ya koma ta kallesa,hakan yabashi tabbacin ta dawo cikin hankalinta,
Sake tausasa murya ya yi bayan ya janyota daga kwance ya mayar jikinsa ta jingine dashi ya sake cewa "kingane wacece wnn?" Yafada yana nuna inna dake durƙushe kusada gadon tana hawaye,ganin yadda fuskar ƴar ta ta ya kumbura sosai bakinta abushe idonta babu daɗin kallo.
Jinjina kai tayi a hankali alamar ta ganeta, "waɗannan fa?" Ya nuna su twins wanda suma hawayen suke,dan akwai shaƙuwa me tsanani tsakaninta dasu kamar ba saƙonnin ta ba,duk ma yayyen ta maza suna matuƙar ƙaunarta,sake jinjina kai taji a hankali,amma ba magana.
Hamdala mlm da inna sukayi,gorar ruwan addu'a mlm ya ɗakko ya yi bismillah ya kafa mata gorar abaki,ba musu ta amsa ta fara sha da sauri, sefa tayi rabi kafin ya cire mata ta huta,sannan ya sake miko mata ta amsa seda ta shanye tas,kaɗan ta bari ya zubaa hannu ya shafa mata afuska sannan ya ajiye gorar.
Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fara yinƙurin amai,da sauri inna ta miƙo mata wani ƙaramin baho aikuwa tafara sheqa wani irin amai baƙiƙirin dashi,harda wasu abubuwa kamar kwalba, aman babu kyan gani,ga wasu abubuwa kamar tsutsa se motsi suke,seda takusa yin rabin bahon kafin aman ya tsaya mata,takoma jikin mlm tana sauke wani wahalallen numfashi,ba jimawa wani baccin ya sake kwasheta.
Shimfiɗeta mlm yayi yasake tofeta da addu'a kafin suka sake fita.
Seda takai la'asar tana bacci kafin ta farka,cikin ikon Allah koda ta farka idonta ya fara washewa kuma harta iya tashi da kanta ta zauna, Amo na gefe se zare ido take,dazarar taga kande zata kallo ta setayi maza ta ƙara damƙe carbin ta,murya asama take istigfari,dan wlh tsoron bala'i kanden ke bata,ganin take har yanzu al janun na nan basu tafi ba.
Inna ce tashigo ta kamata suka shiga toilet takai mata ruwan zafi wanda mlm ya yi mata tofi aciki,inna tayi mata wanka dan har lokacin jikinta babu ƙarfi.
Tea me kauri inna ta haɗa mata da ruwan addu'a wanda mlm ya yi mata shi dayawa komi nata inde naci ne ko nasha to da wnn ruwan za'ayi mata amfani,har wanka.
Duk wannan abin da ake yi umma bata leƙo sashen ba ko sau ɗaya,mama de ta shigo sau ɗaya ta tsaya daga bakin ƙofa tace Allah y kafa afuwa tayi gaba,ko takalma bata cireba balle tashi ɗakin.
Duk da inna taji zafin abinda suka mata amma taji daɗin yadda mama tazo ta duba jikin ƴarta,koba komi de tazo,tafi umma wacce ko bakin ƙofar sashen bata leƙo ba.
Seda kande ta shafe sati ɗaya kafin ta fara magana, maganar ma me ban mamaki dan kamar wata namiji haka take magana tana wani karkace baki gefe,da farko abin dariya ya baiwa inna hartana cewa "haba uwar masu gida,daga buɗe baki kuma se shegan taka,meye haka kamar namiji?" Tafaɗa tana murmushi.
Cikin cijewa kande tace "yo inna da mecece ni ɗin,ai ni namijice kawai totally,kallifa duka yayyena maza ne" tafaɗa tana nuna su Hamza da su Hamis da twins dasuka kalli juna., saboda haka nima namiji ne kuma soja zan zama in Sha Allah.
Ya Musa yace "haba auta ke mace ce,kuma kyakkawar yarinya,ƴar autar inna da malam,jikar Amo kallifa ji sumarki me kyau da ita ga tsayi".
Kallonsa tayi tace "Allah ko ya Musa,wannan gashin shiya sake saka wa nake kama da mata ko? To yau base gobe ba zan askesa,Sena je an aske mini shi".
Kamar wasa tafara acting kamar namiji,duk kayan da inna ta ɗakko mata ta sanya setace sam bata sonshi, ita sede anemo mata riga da wando su zata saka.
Tun Inna na kallon abun a matsayin wasa har tafara jin haushi,cikin fusata tace "zanci ubanki fa,ki tashi ki saka kayanki,tun ɗazu kin sauna da ɗaurin zani,karki bari raina ya ɓaci", se mafifa inna take.
Nan take idon kande ya cenza tayi tsaye ƙiƙam taki motsi ta sunkuyar da kanta gashinta ya zubo ya rufe mata fuska,inna tayi magana har ta gaji amma shiru babu amsa,ganin hakan yasa ta sakko ta fara lallashi da ban baki,amma shiru kamar tanayi da dutse.
Matsowa inna tayi ta dafa kande tana yimata waƙa kamar yadda take mata idan tayi fushi, amma ko alamar zata motsa babu,janyota inna tayi da niyyar rungumeta amma taƙi janyu wa,sema ji tayi kamar ba mutum take jaba, kamar gini haka ta maƙale agurin, cikin tsoro inna ta saketa taja da baya,aguje ta ruga zuwa zauren gidan tana ƙwalawa mlm kira, jikinta banda rawa ba abinda yake.
Arikice ta fada zauren inda mlm ke tsakiyar karatu da ɗalibansa,da sauri ya tashi yana tarota,cikin sauri kuma ya janye ta sukayi cikin gidan yana tambayar ta meya sameta harya firgita ta haka,inna banda rawa ba abinda jikinta yake se nuna masa hanyar ɗakinta take,ta kasa magana hawaye se zuriya yake akan fuskarta.
Hanyar ɗakin ya nufa da ita,amma ta cije a waje taki shiga,baiwar Allah Inna banda rawa ba abinda jikinta yake.
Sakinta mlm ya yi yashiga ɗakin yaga kande a halin da take,bakinsa ɗauke da addu'a yake nufarta,haka mlm ya shafe tsawon lokaci aɗakin kafin ya fito yana sharce gumi.
Yana fitowa Sega kande abayansa tana faɗin "inna yunwa nake ji wallahi,dan Allah kiyi mana ɗan wake", jikin inna be dena rawa ba ta kalli malam,jinjina mata kai ya yi alamar bamatsala.
Cikin ɗari2 inna tace "to auta in Sha Allah,zoki amso mana fulawar", inna ta fada tana miƙo mata naira dubun da mlm ya bayar,cikin murna ta yi hanyar waje daga ita se ɗaurin zani a ƙirji ko ɗan kwali babu akanta,ga dogon two color hair dinta dakenan har kusada mazaunanta yanata tashi iska na kaɗa mata shi,kamar ba ƴar hausawa ba,da sauri mlm yace "a'a uwata kawo na bayar a amso muku", haka tundaga wannan ranar kande ta koma me siffar maza.
Bawai jikinta bane ya koma siffar mazan, a'a,tana nan a yadda take,kawai de gabaki ɗaya yadda take gudanar da al'amaran rayuwarta ne ya koma na maza,inna batasan ya akayi ba se ganin kan kande tayi an aske mata rabin sumarta, normally sumarta ta kai har ɗuwawu amma kawai se wayar gari akayi an yanke Mata fiye da rabi yakoma kamar na namijin ba indiye.
Shigarta da komi nata sak namiji, school ma ta dena zuwa,ɗan karatun ta da ake taƙama dashi aka nemeshi aka rasa,bayan fatiha babu abinda kande ke karanta wa daidai,a fannin boko kuwa ɗum,kai ya koma kamar na kifi bata gane komi,tunrancin da yazamewa bakinta kamar yaren ta na usuli shima aka nemesa aka rasa,komi nata kamar an juya mata shi,tamkar yadda ake juya riga daga Dede takoma baibai.
Ada ta kasance me yawan son turanci,har bayan samun matsalar ma bata dena son yin turanci ba,amma fa kafurin broken english take kwaɓawa,baƙaramin ciwa turanci zarafi take ba,idan ta kwaɓa wani turancin se dariya ta kusa kashe mutum,amma ita ko ajikinta,ta fuske,ita adole turancin gaske take.
Ga baki daya rayuwarta tayi juyin waina acikin tanda,yayyenta maza abun ya yi musu ciwo sosai,gashi sun kasa samun wata gamsashshiyar amsa daga iyayen nasu,sude sun san tun sa'adda tasamu matsalar jinnu din nan bata kuma samun kanta ba,kullum da abinda zata fitar sabo arayuwarta.
Tun ranarda sukayi ƙungiya sukayiwa inna ƴar tsure tare da jefa mata wata nannauyar tmby wanda yakusa zautar da jin ta,har girgizar da tayi sanadiyar tambayar su ya bayyana afili,nan take ta fatattakesu sbd rashin gamsashshiyar amsar da zata baiwa ƴaƴan nata.
Hakan yasa suka juya tmbyr izuwa kan mlm,tabbas shima ba ƙaramin jijjigashi tambayar tayi ba,amma dayake namijin gaske ne shi be nuna ya firgita da tmbyr ba.
Cikin dakiya mlm yace "Hamza me kace?,me kuke son sani gameda lalurar ƴar uwarku ne?bayan komi akan idon ku ya faru,kuma duk abinda aljanin yafada kunji da kunnenku".
Maimaita tambayar Hamis ya yi cikin kwantar da murya yace "am mlm dama cewa mukayi,menene gaskiya akan abinda muka ji aljanin kan auta ya faɗi?shin wanene Abu Rayyan,menene dalilin da ya sanya gabaki ɗaya rayuwar auta ya cenza,kuma munga baka ɗauki kowanne mataki ba,kamar ma abinda take yi yanzu baya damunka,gashi mutanen unguwa harsun fara gutsira zantuttuka akan sabon tsarin rayuwar da ta ɗakko a yanzu,sam sekace ba ƴarka ba,komi nata ya sauya,mlm dubi yadda takoma sak namiji,kuma ma dakanka ne kabata kuɗi tasai irin tufafin da maza suke sakawa,wanda kaine ka koyar damu cewa duk namijin da yake kamanceceniya da mata to yanada babban zunubi agurin Allah (s.w.a),haka ma ga macen ta take kamanceceniya da maza,harfa yanke gashin kanta tayi,wanda yin hakan a addini shima haram ne,gashi yanzu bata tsoron kowa,shekaran jiya nan naga ta kama Ikilima tamata shegen duka seda ta yimata targaɗe a hannu,mlm dan Allah kafaɗa mana menene asalin abinda yake faruwa wanda mu bamu sanshi ba,kuma wanene ABU RAYYAN* a iya sanin mu kune iyayenmu,kuma aduk cikin kakanni mu bamusan wani me suna abu Rayyan ba,mlm kai masani ne wanda Allah yabashi baiwar ilimummuka me tarin yawa,kuma abinda take yi Sam ko a addini be dace ba,idan ma sbd aljanun kanta ne ai Allah ya baka sani ta yadda zaka magance komi batareda an bar wani aljani ya sauya mata rayuwarta hakaba,ka gafarcemi mlm idan na faɗi abinda ya sosa maka rai,bada nufi bane ".
Dogon numfashi mlm yaja kafin yace "duk naji abubuwan da ka faɗa kuma tabbas maganganun ka gaskiya ne,amma abunda nakeson ka sani,duk wata cuta Allah be halicce ta ba har seda ya fara saukar da maganinta, sannan idan ka lura gaba ɗaya rayuwar auta maƙiya ne a kewaye da ita wanda nasani kuma kun sani,tun kafin bayyanar wannan aljanin atare da ita ansha neman nakasta rayuwarta wanda ku ƙila a yau kuka san wannan,akwai aljanun da zaman su atareda mu bil adama babu alheri wanda hakan kesa muke yin duk yadda zamuyi araba wanda suka shafa dasu,akwai kuma nau'in aljanun da zaman su atareda mu wata kariya ce daga Ubangiji*
Tabbas rayuwar auta ta sauya kuma babu wani wanda hakan kewa daɗi daga Ni har mahaifiyarku,kuma duk yadda zakuji ciwon sauyawarta baku kai mu ba tunda mune muka kawota duniya,kuyi hakuri kubata lokaci,idan kun lura harda kuruciya a lamarin uwata,in Sha Allah komi ze dedeta da izinin Allah*
Ni nasan abunda baku saniba,wanda in Sha Allah idan lokacin kusani ya yi tabbas ba makawa se kun sanshi,rayuwar auta akwai wasu manyan sirrika wanda lokaci ze bayyana su,kuyi hakuri ku bata lokaci,kuma ina roƙon ku kar wanda ya hanata abinda take ko ta nema,inde befi ƙarfin ku ba ina neman alfarma abata,sannan Abu Rayyan bakowa bane kawai zancen aljanin ne,nagama magana kutashi kuje Allah ya yi muku albarka".
Sam mlm be basu damar yin wata magana ba,kuma tabbas sunajin cewa akwai abinda mlm be faɗa musu ba,amma kamar yadda yace komi lokacine suna fatar lokacin nan ba anesa yake ba,dan duk wanda yasan auta ada yarinya me hankali ga ƙoƙari ga son karatu,to ba ze yadda itace ta koma yadda take a yanzu ba,yarinya ƙarama me shekaru goma zuwa sha ɗaya,sam kamanninta ya sauya,babu wata cikakkiyar nutsuwa atare da ita,ga rashin kunya,duk wani ilimi da take dashi yanzu babu ya gudu,takoma kamar jaka, bata da mutunci sam,ga ƙarfi kamar ba mutum ba,ba wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa ko ya ɗagawa innarta,duk mutanen gidan yanzu shakkar ta ake, ƙaramar yarinya amma ta addabi kowa,musamman umma da ƴarta Ikilima wanda suke nuna sam basuda alaƙa da ita,mama de dama ba shiga shirgin kande take ba,tun bayan da ɗanta Abdullahi yakoma sashen ta shikenan burinta ya cika,dama ba dan Allah ya barshi a gurin inna ba, barazanar da mlm Musa mijinta yamata ne yasanya ta kyaleshi acen,amma yanzu tunda ya dawo gurinta ba abinda ya shalleta dasu.
Abdullahi ya gudu shashen uwarsa mama ne tun ranar da kande ta tayarda aljanu, yaji tsoro sosai ya kwashi kayansa yakoma sashen uwarsa wanda har yau wata na biyu da faruwar abin be dawo ba,tun Inna na magana da mlm har suka hakura,mlm Musa ma be ce ya koma ba hakan ya yi wa Mama daɗi kuwa, ɗan ta ya dawo gare ta.
Tun daga lokacin kuma Abdullahi ya fita harkar kande ya dena kulata,itama bata damu ba ta fita iskar sa.
Dama acikin unguwar mace ɗaya ce ƙawarta layuza maƙota ne dasu inna,layuza tanada haƙuri sosai bata cika yin fushi ba,duk masifa da bala'in kande tana shanye wa, Allah ya ɗora mata ƙaunar kande,hakan yasa suke ƙawance,.
Tunda ɗabi'un kande suka sauya iyayen layuza suka hanata hulɗa da kande anna ta kafe ta ƙiji,kusan kullum tana hanyar zuwa gidansu kande,.
Layuza tana tallar dafaffen dankali, kasancewar basu kai su kande hali ba,hakan ke burge kande sosai,ita tallah mugun birgeta yake,a ƙa'idar gidansu mlm habu yaro baya tallah,saboda sunada rufin asirin su,amma rana tsaka kande ta tayarda bala'i ita tallah zata fara,tun mlm da inna suna ganin abu wasa har ta fara kuka tana tirje tirje ita se an yimata sana'a ta fita tallah.
Haka mlm badan yaso ba ya goya mata baya,seda ta zaɓi abinda zata dinga tallar ma,awara ita kadai take so,haka mlm yabata kuɗi taje tasiyo rabin mudu,inna tayi mata awara,ranar da ta fara ɗauka taci wankanta jikinta sanye da wasu riga da wando ƴan dai dai na maza tasha cover shoe dinta babban size wanda yafi ƙarfin ƙafarta,ta ɗauki bokitin ta fito tana ƙwambo tana buɗa kafaɗa dede umma na baiwa Ikilima sako a ƙofar shashensu da alama aikene ake bata,wata irin dariya suka kece da ita kamar zararru,yi suke sosai suna nuna kande wacce ta tsaya sororo tana kallonsu fuskarta a murtuƙe,dake sashen umma dana inna suna kallon juna,sashen mama ne ke cen kusada na Amo suma suna kallon juna.
Cikin hura hanci kande ta dubesu tace "da uwar uban wa kuke ne?"
Dariyace ta sake kama su ganin yadda ta karkace baki kamar wata ƴar daba,umma wnn sauyi na kande ba ƙaramin daɗi yake mata ba,tana rokon Allah ya dawwamar da ita haka har ƙarshen rayuwarta,ko dama yadda ake ji da kande agidan ba ƙaramin ci mata tuwo a kwarya yake ba,kowa agidan idan ka cire umma da mama son kande yake,har ƴaƴansu mata da sukayi aure sunason kande, har mijin umma Mudassir idan ana zancen Ikilima batada ƙoƙari a makaranta seyace tadinga zuwa gurin kande tana koya mata,hakan na baiwa umma haushi,amma yanzu a kalli kanden ita kanta batasan komi ba balle ta koyawa wani.
Cikin fusata ta ajiye awararta agefe ta fisgo Ikilima ta buga kanta da ƙofar shiga sashen nasu,ihu umma ta ƙwallah ganin take kan Ikilima ya fashe jini ya fara fita,juyowa kan umma tayi bayan ta sake Ikilima ta faɗi kasa dafe da kanta tana ihun itama,ai umma na ganin yadda idon kande ya juye tana mata wani kallo kamar zaki yaga nama ai aguje ta koma cikin shashen nata ta afka ɗaki ta rufo ƙofar se zagi take aunawa kande amma ta rufe kofar.
Daukar bokitin awarar ta tayi takara gaba,awaje ta haɗu da layuza ɗauke da tiren dankalinta, murmushi tasakarwa kande cikin murna ta matso tana faɗin "laa ashe dagaske kike,kai aikuwa ji yadda awarar tayi kyau dagani zatayi daɗi" fuska amurtuke kande tayi gaba se banka sauri take,ko saurarar layuza batayi,itako baiwar Allah se sauri take tanaso ta cimma kande amma takasa.
Haka sukaje gurin da layuza take zama da tallar ta bakin wata secondary school suka zauna,adede lokacin ne aka tayar dasu break,haka ɗalibai suka fito kamar kiranye sukayo kan bokitin awarar kande suka yanyane kowa nason ya siya,duk da kuwa ba ita kaɗai bace me awarar.
Seda tagama shan kanshinta sannan ta taso tabuɗe bokitin awarar ta ta tafara basu suna bata kuɗi,tun daga ranar aka dena siyan awarar kowa seta ta,seta siyar sannan seta koma kan tiren dankalin layuza ta zauna,nan ma a yanyame ayita siya,tas suke siyarda komi,har inna ta kara hannun yimata awarar.
Daga gurin tallar yau gungun wasu yara maza wanda suma tallar suke kaiwa amma ba'a taba kallonsu har se idan ta kande ta ƙare,kullum abun na basu haushi,yau suka haɗa plan akan su tare su kande su musu shegen duka ta yadda gobe bazasu kara kai tallah gurin ba.
Tofa suwaye waɗannan masu rabon shan wahalar???
Muhadu a next pg.
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:05
Bismillahirrah manirrahim.
Sun ɗanyi nisa da tafiya kawai Sega matasan yara maza kusan su biyar,ko wanne da ƙatuwar bulalar darbejiya a hannunsa,sun tari gabansu kande gadan gadan,aƙalla yaran zasuyi shekaru sha biyar biyar,ba wata wata wanda yafi Kowane tsayi acikin su ya laftawa layuza bulalar hannun sa,yana zare mata ido.
Hannu yasa ya ture kande wacce ke tsaye ƙiƙam tana masa