Bakar numba biye da shi. Da gudun ta ta dawo d’akin Bintu in da ta zu6e k’asa ta na kuka fad’i ta ke
‘’ki min rai Gimbiya, kwankwatsi ban san shi an Yarima Barde ba, aradu da na san shi na da ban bi bayan shi ba, in k’arya na ka yi aratta kashe ni’’
Cike da mamaki Bintu ta yane lifaya da ta rufe fuskar ta, tambaya ta ke
‘’gide lafiya? Yo to minana? Mi Yariman yay mi ki da har ya sanya ki kuka Ladiyo? Ina Yariman ya ke?’’
Ladiyo wacce duk a zatan ta Yarima Barde ya gano ta ne ran sa ya 6aci har ya juya ya fasa ganin Bintu ta ce
‘’ Yarima Barde ya juya ya koma, ki min rai kar ya sa a tsire ni, ina ni ina lek’en surrun Yarima Barde, ki taimaka ki min rai, wayyo ni Ladiyo sai kuma yanda aka yi da ni d’an daudu a kabari’’
Ganin dai Ladiyo ba ta da niyar bata cikakkiyar amsa ya sanya Bintu tashi ta fita da kan ta, ita ma Ladiyo bayan ta ta biyo wanda kukan ta ya sa sauran bayi fitowa. Maman Cangwai na mai tambayar ko lafiya? Ina Yariman ya ke? shin me ya fito da Bintu daga uwar d’aka ita kuma Ladiyo kukan me ta ke?
Kasa amsa mu su Ladiyo ta yi har sai da Maman Cangwai ta daka mata tsawa sannan ta iya labarta mu su yanda ta bi bayan Yarima Barde zuwa Lambu ba tare da ta fad’i jan Bintu zuwa lambu da ta yi ba, yanzu haka ya gano ita ta ke lek’en asirin sa.
Cikin jimami kowa ya ke duban Ladiyo wacce ta had’a zufa, hawaye da majina. Ita kuwa Bintu waje ta samu ta zauna cikin neman mafita, dan kuwa muddin abun da Ladiyo ta fad’a gaskiya ne, ko shakka babu dole sai an hukun ta ta, lek’en asirin Yarima ba k’aramin laifi ba ne, za a iya amfani da wannan ace so ta ke ta idda wani mugun nufi kan sa ko kuwa dai ta ha’d’a baki da abokan gaba ta na san halaka shi.
Yarima Barde kuwa da fitar sa kai tsaye gun Jakadiya ya nufa. Ya tadda ta bisa sallaya tana lazumi kan ta zo ta shiryawa sarki sauwar dare. Ganin Barde ta san da matsala wanda shi ma be 6oye mata ba ya sheda mata cikin azanci ba tare da ya fayyace mata komai ba.
‘’ya Jakadiya, a had’a fanteka na turaruka, na jiki zuwa na kaya, a aika ga Gimbiyar Sa’ayrasa, a kuma sheda mata Yarima Barde ma’abocin k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta sauya gimshikin kusurwar ta’’
Cewar Yarima Barde, wanda ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya amsa tambayoyin da Jakadiya ke shirin jera masa ba. Abun da kuwa ya fi d'aure mata kai shi ne fantekar turaren da za a kai, ga kuma batun na Barde na Bintu ta gaggauta sauya gimshikin kusuwar ta, ko shakka babu Barde ya ji wari daga wani 6angare na Bintu ko kuwa bayin da ke tattare da ita.
Ba tare da 6ata lokaci ba Jakadiya ta aikata yanda Barde ya ce. Cikin baitul mali ta shiga, daga cikin daular iyalan Sarki Abdulrahman ta jido turarurruka fanteka guda, cikin bayi ta za6i wacce ta fi tsana sannan ta d'aura mata fanteka ta tere da bata sakon Barde zuwa ga Bintu. Jin sak'on da aka bata sai ga baiwa a k'asa ta na yiwa Jakadiya magiya da kada ta tura ta da wannan mugun aike, amma ina sai ma tafiyar ta yi ta barta ta na share hawaye dan kuwa dai ta ta ce ta same ta kishiya tara rana d’aya.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[9/11, 4:28 PM] Shams Danbaiwa: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣3⃣
Sidiya ce....✍🏼
Hankalin Bintu be kwan ta ba sai da ta tsinci kanta cikin lambu. Lambu ne mai ban sha’awa wanda ya sha ado da bishoyin kayin marmari iri daban daban. Hasken wata da yayi fari kal a wata tare da hasken lantarkin da ke daga cikin kowacce kusurwa na cikin lambun ba k’aramin k’ayata shi yayi ba. In ban da koken tsuntsaye da na kwari babu abun da ke tashi cikin lambun.
Tuni Ladiyo ta shiga raba ido ko Allah ya sa ta ga wannan mutumin da ta ga mutumin nan, ita kuwa Bintu wani dutse ta samu ta yi zaman ta kai ta na fad’in
‘’kai Ladiyo wagga lambu ba dai ni’ima ba, ni dai na yi wajan zama daga nan’’
Ladiyo na mai raba idanu ta ce da Bintu ita dai za ta d’an taka to, yanzu za ta dawo. Nan bisa dutse ta bar Bintu yayinda ta kutsa cikin lambu domin neman wannan mutumin.
Barde kuwa zaman Lambun ne ya ishe shi, gaba d’aya ya kasa samin nutsuwa. A hankali ya ke shawagi cikin lambu, wani irin wari ya ji yana bakuntar hancin sa sannu a hankali, tun ya na iya jurewa har ya kasa ya yanke hukuncin ficewa daga Lambun gaba d’aya dan kuwa warin ya fi k’arfin na mataccen dabba. Ko da ya d’auki hanyar fita daga Lambun nan ya ji wari na k’ara gabato shi. Nan bisa dutse yayi kaci6us da ita kishingide, idanun ta runtse tamakar mai bacci, hakan nan wani irin wari da tun da yazo duniya be ta6a jin irin sa ba ya daki hancin sa har sai da ya ja baya da sauri wanda k’aran sautin motsin na sa ya sa Bintu bud’e idanun ta yayinda ta kai kallan ta ga kyakkawan buzun da ke tsaye gaban ta, hannayen sa biyu bisa hancin sa da alama yana k’ok’arin kare hancin daga jin wari ne.
Kallan sa ta ke baki bude yayinda shi kuma Yarima Barde kenam hanyar ku6uta daga warin da ya tabbatar daga jikin yarinyar da ke gaban sa warin ke fita. Kai tsaye hanyar fita ya nufa. Har ya fice Bintu ba ta motsa daga in da ta ke ba dan kuwa ta yi mutuwar tsaye ganin Barde ta yi zatan gamo ta yi.
Ko da Ladiyo ta dawo cike da takaicin rashin ganin buzu, sai ta tadda Bintu zaune baki bud’e kamar gunki, fad’i ta ke
‘’gide lahiya kuwa Bintu? Wanga fuska ta ki hallo kin yi gamo ne?’’
Bintu na mai duban Ladiyo yayinda ta saki ajiyar zuciya tafurta
‘’ aradu aljanu su ka rikid’a zuwa ga halittar bil adama ba karamin kyauwu gare su ba, Ladiyo ni Bintu yau na ga aljan, kwankwatsi ma kuwa’’
‘’aljan Gimbiya? Ina ki gan sa?’’
Cewar Ladiyo ta na mai dafe k’irji cikin takaicin kar dai buzun nan Bintu ta gani ya fita. Bintu na mai nuna in da ta ga Barde tsaye gaban ta ta furta
‘’nan gaba na Ladiyo, nan gaba na tsaye, hallo ya na mai k’ok’arin rufe kyakkyawan fuskar shi na gan shi, idan karya nai aratta kashe ni’’
‘’yo to yanzun ga ina ya tai? Hallo 6acewa ya yi?’’
Cewar Ladiyo cikin k’aguwar ta ji in da Barde ya yi. Ita kuwa Bintu zuciyar ta d’aya ta amsa mata da
‘’ gide rariya ya tai, yanzu ba da jimawa ba’’
Jin haka Ladiyo ta tabbatar ba wani aljan da Bintu ta gani, wannan buzun nan da ta ke san gani Allah yayi raban ganin Bintu ne. Ji ta ke kamar ta bi bayan Barde da gudu ko Allah ya sa ta gan shi. Dan haka sai ta yi kamar ma ba ta san me Bintu ta ke magana akai ba, ta na mai k’ok’arin boye takaicin ta ta ce da Bintu
‘’yo to ai sai ki tashi mu tai ciki Gimbiya, kar tin ki na ganin aljan mai kyau ki ga wanda zai firgita ki ko?’’
Cikin hanzari Bintu ta tashi, fad’i ta ke
‘’gide kin ko yi gaskiya, gwara mu tai din.....’’
Kafin ma Bintu ta gama magana Ladiyo ta yi gaba, Bintu na biye da ita har su ka fito daga cikin Lambu amma babu Yarima Barde babu alamar sa. Cike da takaici su ke tafe, kowaccer su ba cikin hayyacin ta ta ke ba, yayinda Ladiyo ke fama da takaicin rashin ganin Barde, ita kuwa Bintu mamakin sifar da wannan aljanin ya bayyanar mata ta ke, ashe dai da gaske cikin jinsin aljanu akwai bayin Allh wanda ba sa cutarwa.
Yanayin da su ke ciki ya sa ba su ankara da Yarima Sadauki ba, wanda ya ke tafe tare bayin sa maza guda biyu suna mai take masa baya. Tun da ya hango su Bintu idanun sa ke kan ta, ya na mai kallan yanda zubin jikin ta ya dace da yanda ta ke tafiya tamkar d’awisu, hakan ne ya sa shi ya tsaya cak cikin shagaltuwa da kallan Bintu duk da kuwa kallabin da ta d’aura fuskar da kuma duhun dare ya sa shi kasa ganin fuskar ta, Allah Allah su k’araso kusa da shi dan ya wayi wacece ita, duk da kuwa shigar su ya nuna ko shakka babu bayi ne, amma ba bayin Fabarusa ba.
Har su ka gifta su ba su lura da su ba, ganin haka d’aya daga ciin bayin yayi yunk’urin tsayar da su Yarima Sadauki yayi saurin katse shi ta hanyar d’aga masa hannu domin kuwa tafiyar Bintu ba ta isheshi ba, be so a katse masa jindad’i. Sai da su ka k’ure masa yana murmushi gami da shafa gashin baki ya dubi bayin sa tare da tambayar
‘’ gide wagga bayin wani Masarauta ne? me ya kawo su Masarautar mu?’’
Zu6ewa k’asa su ka yi, sa’annan d’aya daga cikin bayin ya amsa masa da
‘’bayin Masarautar Sa’ayrasa ne ran Yarima ya dad’e, hallo ina da labarin su su ka rako Gimbiya Fatima d’iyar Sarki Inuwa na S’ayrasa a matsayin bayi na ta....’’
Cike da gamsuwa Yarima Sadauki ya ke gyad’a kai, kafin daga bisani ya ce
‘’doguwar mai tafiya uwa d’iyar Saraki, ita na ke da muradin gani, hallo a duk in da ta ke a mata iso zuwa ga turaka ta’’
‘’an gama ran Yarima Sadauki ya dad’e, yo to ko Gimbiya Fatima ka ke da muradin ganin ai dole ta taho gare ka bare kuma baiwar ta, babba gare ka Saudakin Sadaukai, ba hau da wani ba sauke wani, Sadauki maida garin wani kango’’
Ya na mai hura hanci cike da sarauta da tak’ama ya wuce gaba, yayinda bayi su ka tashi su na mai rufa masa baya ba kuma su fasa fasa masa kirari ba.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[9/11, 4:28 PM] Shams Danbaiwa: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣6⃣
Sidiya ce...✍🏼
Ta na tafe ta na hawaye haka ta isa 6angaran Bintu in da ta tadda Ladiyo zaune gaban Bintu ta sha kuka ta k'oshi, daga gefan Bintu kuwa Maman Cangwai ce zaune a k’asa, d'ayan 6angaran Hansai da lantana ne zaune. Bintu ta sallami dukkanin bayin Fabarusa domin samarwa Ladiyo masalaha.
A gaban Bintu baiwa ta aje fanteka ta na mai rawan jiki, tun gaisuwar da ta kai ga Bintu, bakin ta na motsi amma tsoro da kwarjinin Bintu ya sa ta kasa furta komai. Maman Cangwai na me duban ta ta furta
‘’ke mu ke sauraro ya ke d’iyar Fabarusa....’’
Maimakon Baiwa ta fad’i dalilin zuwan ta da kuma sak’on Barde, sai gani su ka yi ta fashe da kuka ta na mai fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e, ki min rai na tuba ki rufa min asiri, tuba na ke’’
Nan fa su Ladiyo da lantana su ka shiga kallan kallo cike da mamaki. Bintu ma mamaki ya ne ya lullu6e ta, cikin ba da umarni ta ce da Maman Cangwai ta bud’e fantekar ta ga abun da baiwar ke tafe da shi. Ko da Maman Cangwai ta bud’e fanteka sai da gaban ta ya fad’i ganin turaruka iri daban daban masu yawa ciki. A hankali ta kai kallan ta ga Bintu wacce ita ma ta hango me ke cikin fantekar kafin ta maida kallan ta ga baiwar, kana ta furta
‘’wannan kuma daga ina?’’
Baiwa ba ta fasa hawaye ba ta furta
‘’gide sak’o ne daga Yarima Barde zuwa ga Gimbiya Fatima, hallo ya na mai sheda mata cewar Yarima Barde ma’abocin k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta sauya gimshikin kusurwar ta.......’’
Ta k’arasa furucin na ta ne cikin rawan murya. Shiru kake ji babu mahalukin da ya furta komai tsabagen bazata da kalamin baiwar ya mu su, babu shakka Barde na me shedawa Bintu wani abu daga 6angaran ta ya na wari duk da dai be fayyace mata ko menene ba, wanda turo fantekar turaren da yayi ba k'aramin cin fuska a gare ta ba ne, ba dan ma an riga an d’aura mu su aure ba da hakan daidai ya ke da ya ce ya fasa auren ta saboda wari da ya ji na daga wani 6angare da ya shafe ta.
Sai a sannan Maman Cangwai ta gane kukan da baiwa ta ke, dan kuwa a k’aida ya zama dole Bintu ta hukunta ta bisa ga sak’on cin fuska da ta iya duban tsabar idanun Bintu ta sheda mata, in kuwa ta yi sake ta rabu da ita salin alin, toh tabbas ta siyawa kan ta raini daga kan jama’ar fada har izuwa sauran bayin na fada babu wanda za ta k’ara yiwa kwarjini bare a ji shakkar ta.
Jin Bintu ba ta furta komai ba Maman Cangwai ta dawo daga gefan ta, in da ta zauna kamar me jiran umarni daga Bintu, a kaikaice yanda baiwar ba za ta fahimta ba ta ce da Bintu
‘’hattara Gimbiya, wanga batu ba na sassauci ba ne, dan haka zan ari bakin ki in ci albasa, ina mai neman alfarma rashin maganar ki bisa hukumcin da zan aiwatar kan wagga baiwa ta fabarusa’’
Ba tare da ta jira amsar Bintu ba ta mayar da kallan ta ga baiwa, sannan ta ce
‘’bisa ga umarnin Gimbiya, ta yaba da kyautar Yarima a gare ta, sa'annan wagga baiwa da ta kawo sak’o gare ta, zaki amshi bulala hamsin na daga tsimagiyan Gimbiya Fatima’’
Da sauri Bintu ta kai kallan ta ga Maman Cangwai cike da 6acin ran jin furucin na ta ta yi k’ok’arin dakatar da ita, wanda hakan ya sa Maman Cangwai saurin fad’in
‘’na yi kuskure Gimbiya, bulala sittin Gimbiya ta ke nufi, maza Lanta tashi ku fitar da ita zuwa d’akin horo, ki kuma sheda ma su umarnin Gimbiya kowa ya ji ya gani ya kuma sheda!’’
Baiwa na kuka ta na fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e’’
yayinda Lantana ta tasa ta gaba, ta na mai fad’in
‘’godiya ta ke Allah shi taimaki Gimbiya’’
Su na fita hawayen da ya ciki idanun Bintu tuni ya gangaro bisa kuncin ta tsabagen tausayin baiwa da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba an k'ak’aba mata horo tsabagen rashin adalci. Cike da 6acin ran da ita kan ta Maman Cangwai ba ta san Bintu na da irin wannan fushin ba, ta furta
‘’akan wani dalili za a yiwa baiwa horo? Gide ita na ta ba sak’o ba ne? idan adalci ne na lalle sai kin nuna an min ba daidai ba ki hukunta shi Barde wanda ya aiko ta mana? Saboda ita baiwa ce? Su bayi ba su ‘yanci? Bayi su an bola?’’
Jiki a sanyaye Maman Cangwau ta furta
‘’hakan da na yi kad’ai zai nuna matsayin ki na d’iyar sarki, dan kuwa babu d’iyar sarakin da za a yiwa wanga cin fuska ta kasa aikata yanda na aikata, in ba dai so ki ke asiri ya tonu ba. Na san yanda ki ke ji, amma fa kada ki manta ko nima baiwar ce, ina fatan za ki fahimce ni.....’’
A fusace Bintu ta tashi tsaye, ta na mai girgiza kai ta ce da Maman Cangwai
‘’ba zan ta6a fahimtar ki ba in dai bisa zalinci ne, ba da yawuna ki ka aiwatar da hukuncin ga ba, umarni na anan shi ne ki gaggauta dagatar da shi!’’
A fusace ta wuce d’akin ta, wanda kan ta kai ga shiga sallamar wata baiwa ya tsaida ita. Ta na ji baiwar na gaishe ta amma 6acin ya sa ta kasa amsawa ta d’aga k’afa za ta shige kenan amma jin furucin na baiwar ne ya tsada ta. Jin ta na fad’in
‘’Yarima Sadauki ya na da murad’in ganin dukkanin bayin Sa’ayrasa!’’
A hankali Bintu ta juyo, wato 6acin ran da take ciki ya sanya ta rikidewa hatta Maman Cangwai, bare kuma su Ladiyo, tashi guda ta tashi daga Bintun da su ka sani ta zame mu su wata daban mai wuyan fasaltuwa. Ta na mai duban baiwar ta furta
‘’wa an Sadauki? A matsayin sa nawa ya ke da muradin ganin bayin Sa’ayrasa gide? Akan wani dalili?
Baiwa ta yi jim dan kuwa ta tsorata da yanayin da ta ga fuskar Bintu, cike da 6acin rai da kwarjini ga kuma tambayoyi na gadara da ta mata akan Yarima Sadauki. Nisawa ta yi kafin ta amsa mata da
‘’Allah huci zuciyar Gimbiya, Yarima Sadauki shi an Yaya ga Yarima Barde wanda ya ke maigida a gare ki, dalilin sa na murad’in ganin bayin Sa'ayrasa shi kad’ai ya barwa kan sa sani’’
Bintu na mai jinjina kai ta ce da baiwa
‘’ki koma ki shedawa Sadauki ni Fatima na ce bayin Sa’ayrasa ba za su isa gare shi ba muddin be zo mana da gamshashshiyar dalilin sa na murad’in hakan ba!’’
🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣7⃣
Sidiya ce...✍🏼
Bintu na k’arasa magana ta shige uwar d’aka. Baiwa kuwa tashi ta yi cikin jinjina maganar ta na mai gyad’a kai ta fice ta bar Manman Cangwai da su Ladiyo cikie da mamakin sauyin Bintu lokaci guda duk akan kishin bayi. Minti kad’an sai ga ta ta fito sanye da lifayar nan da ta cire kafafun ta sanye da cikin farin takalmin fata ta