Bintu Diyar Bayice Jinin Gado By GARGA'DI

Author :  GARGA'DI Category :  Romance

Chapter   22 / 24

63K to 66K   out of 70.2K words

har su ma su ka gaji su ka yi na su gurin. Da ya gaji da zaman ne ya watsa ruwa yayinda ya sanya jallabiya, kai tsaye in da ya saba zuwa duk sanda ran sa ya ke 6ace ya nufa, wato lumbun da yake k’yatare da 6angaran matan Sarki. Nan bisa dutse ya kusa raba dare, sai da ya ji idanun sa sun masa nauyi sosai sannan ya tashi a hankali ya nufi 6angaran sa. Ko da ya zo giftawa ta 6angaran da ya san babu shakka nan aka sauki amaryar da aka aura ma sa, sai ya tsinci kan sa ya na mai mummunar fad’uwar gaba. Hakan ya sa shi wucewa da sauri ya na mai ambaton ubangiji. Bakin kofar sa ya tadda dogarai da bayin sa sun yi jugum jugum kasancewar ya mu su hani da biyo shi, ganin sa su ka fara masa kiran lafiya su na mai fad’in

‘’takawa sannu Yarima Barde, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’

Ganin ya zo daf da shiga kofar da za ta sada shi da 6angaran sa, su ka taka masa baya, har ila yau fad’i su ke
‘’gicciye dama Yarima, gicciye salamun’’
Tsayawa Yarima Barde ya yi, ya d'aga mu su hannun alamar baya buk’ata su biyo shi kafin ya sa kai ya shige ciki. Ya bar su waje su na kallan kallo, dan kuwa sun san lamarin auren Yarima Barde kan su zai k’are duk da dai ba su suka kar zuman ba, rataya aka ba su.

Washagari da sassafe jama’ar Fabarusa, Samari da ‘Yan mata har da tsuffin cikin adon su na burgewa su ka yi dandazo kofar fada domin kallan hawan angonci bisa al’ada. Amma Yarima Barde ya yi k’yememe ya ki fitowa ko da kuwa kofar 6angaran sa ne bare a sa ran zai hau. Ko da su Khalil su ka je da numin bashi baki, a bakin k’ofa dogarawa ma su tsaran kofar Yarima Barde su ka fad’a mu su buk’atar Barde na kada a bawa kowa damar isa gare shi. Dan haka sai hakura su ka yi, Magatakarda ne yayi shela ga jama’a cewar Yarima Barde be shirya yin hawan angoncin shi a ranar ba, su yi hakuri sai zuwa ran da ya shirya za a sheda mu su. Da kyar kamar ba su hakura ba su ka watse, dan ba k'aramin cin burin hawan angoncin Yarima Barde su ka yi ba, kasancewa akwai k’auna tsakanin sa da Talakawa, musammam ‘yan mata da samari, Yarima Barde na su.

"Bayan hayaniyar kofar fada ta lafa, jama’a sun watse su Gwaggo Munari da sauran tawagar Sa’ayrasa su ka yiwa iyalan Sarkin Fabarusa sallama, an had’a mu su koma ta arziki sannan su ka d’auki hanyar komawar su gida S’ayrasa, in da su ka bar Bintu tare da bayin ta, wato Ladiyo, Hansai, lantana da Maman Cangwai a sabon Masarauta. Gwaggo Munari ce ta shedawa Iyalan Sarkin Sa'ayrasa irin tarbar da aka mu su da tarin dukiyar da Bintu ta samu. Gimbiya K’amariyya kuwa sai da ta had’a da kwanciyar asibiti. D’aya daga cikin bayin da su ka juyo ne ta isar da sak’on Lantana ga Yarima Nuhu. Sakon na cewa ta aikata komai yanda ya umarce ta, kuma komai ya tafi daidai. Tsabagen dad’in sak’on na ta har kyautar zani da kallabi ya bawa baiwar domin kuwa in har maganar hakan ta ke babu shakka hakin sa ya cimma ruwa.


Kwanci tashi. Bintu ta cika sati guda Masarautar Fabarusa, amma ko da wasa Yarima Barde be ta6a takowa in da ta ke ba bare ma ta san kalar fuskar sa. Gata kuwa ta na sha gurin matan Sarki, musammam Goggon dole da Uwarsoro ,domin kuwannan su burin su ace amaryar Barde daga ta ta ce, Maman Cangwai ce ke saka Bintu a hanya kasancewar ita ta gane manufar su ba lalle alk’airi ba ne. Ita dai ta bi kowa sannu a hankali. Goggon nan kuwa mulki da jin kan ta kad’ai ya fi k’arfin ta, shi Yarima Barde ba gaban ta ya ke ba, bare uwa uba matar sa.




🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


1⃣1⃣


Sidiya ce.....✍🏼

Da hantsi Sarki Abdulrahman zaune bisa kujerar mulkin sa, ana zaman fadanci sai ga Yarima Barde. Ganin sa Sarki be san sanda ya murmusa ba, dan kuwa ya lura wasan 6uya Yarima Barde ya ke da shi, idan har ba zaman fadanci ba ba ya ta6a yarda su had’u da Sarki duk dan gudun duk wate magana da ya shafi Bintu wanda tun da aka d’aura auren ba su sami kye6ewa da Sarki ba bare su tattauna batun.
Sanye ya ke cikin fararan kaya an masa d’inkin hannu irin na sarauta. Ya sha rawani irin na buzaye kai da ka gan shi ka ce daga sahara ya ke. da shigowar sa dogarai su shiga yiwa Sarki kiran lafiya su na mai sanar ma sa da isowar Barde
‘’ kimtsi gyara daidai alher, gyara kimtsi ga kyau’’

Gaban Sarki Yarima ya zube, hannun sa na dama dunk’ule ya kai jinjina ga Sarki, dogarai fad’i su ke
‘’jinjine dama lafiya alher, an gaishe ka Yarima Barde’’

Da ga gefe kusa da Yarima Sadauki ya ja ya zauna. Nan fa aka ci gaba da fadanci ana tattaunawa akan abin da ya shafi cigaban al’umma da ma kuma matsalolin al’umma da yanda za a magance su. Har aka yi aka k'are idanun Sarki na kan Yarima Barde. Ko da Sarki zai tashi sai cewa yayi da Barde su na san ya riske su a turakan su. Yayinda Sarki zai tashi dogarai su ka rufe sarki ta hanyar baza babban rigunan su yanda ba wanda zai iya ganin motsin sa bare tashin sa. Fad’i su ke

‘’ rangwame Tafsawa, sannu rangwame alher, lafiya Adali, lafiya Mataimakin Musulunci, gyara kyamtsi ga kyau’’

Haka su na masa kiran lafiya har ya kai ga ficewa daga fada. Bayan fitar sa ne Yarima ya kai gaisuwar sa ga sauran Hakiman, ciki har da wanda ke masa Allah ya sanya alkhairi. Ya zo fita kenan Yarima Sadauki ya shagaban sa, ganin sa Yarima Barde ya Murmusa ya na mai dunkule hannun sa na dama ya jinjinawa Sadauki sa’annan ya furta

‘’Sadauki ne kai’’

Cike da tak’ama, shi lalle Yarima mai jiran gado, Sadauki ya maida masa da martani yanda ya saba ta hanyar fad’in
‘’kai ma Barde ne, musammam sa’in da na hau kujerar mulki’’

Barde be fasa murmushin da ya ke ga d’an uwan na sa ba duk da kuwa ya san magana ya ke fad’a ma sa. Kana ya ce

‘’barka da hantsi, da fatan mu na lahiya’’
‘’lahiya lumi fa, ya kwanan amaryar dole? Ko da shike har yau ba mu ji labarin budurcin ta ba bare mu ce ango ya sha k’amshi, d’iyar abokan gaba ce duk da kuwa abun ba dambe ba ne ba, kada Barde ya ba mu kunya!’’

Ya na gama fad’in haka ya yi gaba. D'if Yarima Barde ya d’auke wuta, Khalil da ke tsaye daga bayan su, ya kuma ji dukkannin maganan da Sadauki ya fad’a ne yayi saurin ta6a kafad’ar Yarima Barde, kana ya ce

‘’ba kai an babba ba, amma babba gare ka Barden mahadi maida garin wani kongo’’

Jin haka ya san hakuri Khalil ya ke ba shi. Ya ko yi na’am da Khalil ta hanyar murmusawa ya na mai fad’in

‘’ina da muradin zuwa wucan gadi mutumi na, ko za mu sami dama tafiya kafin na sami saduwa da Sukuku Bakaka(Sarki)’’

Cikin jin dad’i Yarima Barde ya fara sakewa Khalil ya nemo Yarima Jafar domin su tafi wucan gadi.

Da yamma likis bayan Yarima Barde ya dawo daga wucan gadi ya isa ga Sarki. Turakar Sarki su ka d’an ta6a hira sama sama, kafin Sarki ya kawo batun Bintu ta hanyar tambayar

‘’ya amanar da mu ka ba ka? Shin an duba kuwa?’’

Barde na mai durk’usar da kai k’asa ya kasa magana. Ganin haka Sarki ya fahimci in da ya dosa, kana ya ce

‘’kar ka damu d’an mu, ka bi sannu a hankali ba laifi ba ne, amma dai mu na ruk’on ka da kar da mu zamo daga cikin azzalumai ta hanyar d'auka lokaci mai tsayi, wannan gona ta ka ce, kada ka manta akwai idanu dayawa bisa kan ta, da fatan za ka kula a wadata ta, san samu ma a ziyarce ta ko da kuwa daga yau zuwa kwana uku ne’’

Maganar Sarki ba k’aramin nauyi ta yiwa Barde ba, dan kuwa ji ya ke ina ma zai iya masa musu ko da kuwa na sakan d’aya ne, amma ina tsaintar kan sa yayi ya na mai fad’in

‘’an gama Sarkin yakin musulmi, bango madafan bayi’’

Sarki kuwa ba k’aramin jin dad’in yanda Barde ke masa biyayya ya ke ba, cikin ran sa ya na mai jin ina ma shi ne babban d’an sa ba Sadauki ba. Sai bayan da su ka idda salar isha’i sannan Barde ya baro wajan Sarki. Kai tsaye lambun nan da ya saba zama duk dare ya nufa, zuciyar sa na sak’a masa yanda zai yi ya gujewa had’uwa da amaryar da aka d’aura masa, wato kanwar budurwar sa.


🐫🐪🐫🐪🐫🐪[9/11, 4:28 PM] Shams Danbaiwa: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

1⃣4⃣


Sidiya ce...✍🏼



Barde kuwa a nasa 6angaran komawar sa turakar sa har da amai. Hankanlin sa be kwanta ba sai da ya amayar da dukkanin abun da ke cikin sa. Abun da ya ke bashi mamaki be wuce yanda yaji dan adam ya na wari kamar na mushe ko kuwa ja6a ba, daga ganin shigar ta ya san baiwa ce sai dai ba irin kalar shigar bayin Fabarusa ba ne, ko koma baiwar wata masarauta ce dole ya sa a nemo masa ita a sallame ta daga cikin fada ta je ta nemi magani gyambon da ke jikin ta idan dai ba so ake kar shi har lahira ba. Da wannan ya sami mafakar rashin zuwa ya ga amaryar sa, yayi kwanciyar sa abun sa.



Washagari da sassafe Jakadiya ta je masa da karin kumallo na musammam bisa ga umarnin Sarki Abdulrahman. Wanda Yarima Barde ya san ba komai ba ne illa tambayar
‘’shin ka je wa matar ka?’’
Saboda haka ko da Jakadiya ta tashi tafiya sai Yarima Barde ya bata sak’o zuwa ga Gimbiya Fatima, ya na mai fad’in
‘’a shedawa Gimbiya Fatima, bayan gaisuwa da fatan ta na lafiya, ta saurari zuwan mu bayan fad’uwar rana, kada ta tsawaita buri ba ma buk’atar komai daga gare ta’’

Kalaman da Barde ya k’arasa da su be hana Jakadiya rangwad’a gud’a ba, dan kuwa ta san tabbas idan aka juri kai zuga gabas wata ran ta zo da ruwa. Ai kuwa ko da sak’on ziyarar Barde ya riski su Bintu, nan fa Bintu ta ga ta kan ta dan kuwa tun da safiyar Manman Cangwai ta shiga gyara ta da su turarukan wuta, tsimi ne da cukwid’i kai har da wanda ma ba a sa ta ba, domin fa Maman Cangwai ita ta na da nata manufar na musammam cikin ran ta na game da Bintu, sai dai sa6anin sauran ita kad’ai ke san Bintu da alkhairi.

In dan ban da fad’uwar gaba babu abin da Bintu ta ke, bini bini ta ke duba lokaci ta na mai fargabar fad’uwar rana da abun da za ta zo mata da shi na daga ziyarar Yariman Fabarusa. Haka kuma kaman nin wannan da ta gani cikin lambu be dena mata gizo ba, da za ta sami dama ko shakka babu ta na komawa cikin lambu ko Allah ya sa ya k’ara bayyana a gare ta.
Yarima Barde ma cikin zulumin had'u da k’anwar Gimbiya K’amariyya a matsayin matar shi ya wuni. Rana na fad’uwa ya shirya cikin shigar sa na saraki, biye da shi amintaccan bawan sa ne wanda ake kira Bakar namba, su ka nufi 6angaran su Bintu.

Lifaya fara kyal Bintu ta d’aura bayan ta sha turaruka na hayaki da humra. Ta na daga zaune bisa gado gaban ta na fad’uwa tsabagen fargaba ji ta ke kamar ta zura a guje. Maman Cangwai ce ta sa ta a gaba ta na ta jera mata bayanai tare da kashedi, fad’i ta ke

‘’kin san dai ke d’iyar Sarki ce ba d'iyar bayi ba, ki kasance mai rowar muryar ki a gare shi, ban da yawan surutu in dai ba ya zama dole ba, ki kasance gwanar iya kalamai duk san da zaki bud’i baki ki yi furuci, ki tabbatar kin tauna kin juya kan ta hito daga leban ki.........’’

Daga waje tun isowar Yarima 6angaran na Bintu warin nan da ya ji a lambu ya fara bakuntar hancin sa, hankalin sa ne ya fara tashi yayinda ya ji bugun zuciyar sa na dad’a k'aruwa. Cikin wannan hali ya yi tsaye bakin k’ofar falon Bintu, yayinda bak’ar namba ya shiga kwad'a sallama.
Ladiyo na mai amsa sallamar ta fito, ganin wanda ke gaban ta tsaye ta yi ta na duban sa. Sanye ya ke cikin fara Jabba wanda aka mata ado da koran zare, bisa babban rigar sa ce na dokakkiyar shadda fara kyal sai d'aukan ido ya ke. Haka rawanin da ke bisa kan sa irin na buzaye zuwa huffin da ke sanye cikin k’afafun sa farare ne kyal kai ka ce shirya shi aka yi.
Ganin ta saki la66a da su ga66a ta na duban Barde, ba ta da niyar motsawa bare ta kai gaisuwar ta gare shi, ya sanya Bakar numba fad'in
‘’hattara d’iyar talakawa! Yarima Barden Mahadi shi an gaban ki’’

Tuni Ladiyo ta zu6e k’asa jin buzun nan dai ba kowa ba ne illa mijin Bintu, fad’i ta ke
‘’tuba na ke Yarima, Allah ya huci ran Yarima, babban Barde babban bako’’

Shi kuwa Barde ganin tufar jikin ta ne ya dad’a d’aga masa hankali ba wai yanda ta masa ba, dan kuwa tabbasa wannan baiwar mai wari da yayi arba da ita cikin lambu a daran jiya irin shigar ta kenan. Idan kuwa haka ne to lalle d’aya daga cikin bayin matar da aka aura masa ne ke wannan mugun warin da ke neman halaka shi.
Bakar numba ne ya amsa da
‘’an gaishe ki d’iyar talakawa, ki shedawa Gimbiya Fatima Yarima Barde na neman iso gare ta’’

Da sauri Ladiyo ta tashi har tana hard’ewa, yayinda ta ke fad’in
‘’an gama ran Yarima ya dad’e’’
Ciki ta shige jiki na rawa, ta tadda bayin da ke hidima cikin falo wanda k'atuwar muryar Bakar numba ya sanar mu su da isowar Barde, kowannan su ya nutsu jere cikin sahu, musammam bayin Fabarusa wanda dama sun fi na Sa’ayrsa sanin darajar Barde. Kai tsaye cikin d’akin Bintu Ladiyo ta shige ta na mai zubewa k’asa gaban Bintu dan kuwa ganin Barde ya sa ta tsorata da sa’a tare da nasarar da ke tattare da d’iyar bayi
‘’ran Gimbiya ya dad’e, Yarima Barde ya iso ya na mai neman iso gare ki Gimbiya’’

🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[9/11, 4:28 PM] Shams Danbaiwa: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

1⃣5⃣


Sidiya ce...✍🏼



Jin haka hankalin Bintu ya tashi, cike da fargaba ta kai duban ta ga Maman Cangwai, wacce ta gane halin da Bintu ta ke ciki kana ta ce

‘’ki nuna masa hanya ya iso gare ta, ni da sauran bayi za mu tsaya daga wancan d’aki, ke kuma Ladiyo da ke ku tsaya daga wajen kofa kafin Gimbiya ta sallame ki’’

Cikin rawan jiki Ladiyo ta tashi ta na mai fad’in
‘’an gama ran gimbiya shi dad’e’’
Ko da ta koma gun su Yarima Barde, Maman Cangwai ce ta fito da kan ta ta sallami sauran bayi zuwa ga d'ayan d’akin, duk da kuwa bayin Sa'ayrasa ba haka su ka so ba, su ma dai so suke su ga Yarima Barden nan da jama’a ke yawan ambaton sa wajan kyawu. Ladiyo a gaba, biye da Ita Yarima Barde ne in da shi kuma Bakar numb ya tsaya daga waje, su ka shigo falon Bintu.
Warin nan da ke d’aga masa hankali shi ya ke bunk’asa ya na dad’a bakuntar hancin shi duk sanda ya d'aga k’afa ya sauke a falon. Isar su tsakiyar falon Yarima Barde ya tsaya cak, ga mamakin Ladiyo ji ta ya furta

‘’gide bayi masu shiga irin ta ki nawa ne cikin wanga turaka?’’
Ladiyo na mai susa k’yeya yayinda ta shiga kame kame ta cikin fargabar kar dai ya gane ita ce mai bin bayan sa cikin lambu ta yi saurin fad’in
‘’iye na’am? Mu na da d’an dama ran Yarima Barde ya dad’e, wagga shiga ita an shigar bayin Sa’ayrasa, dukkanin mu wagga shiga mu ka yi Allah shi da ran Yarima’’
Yarima Barde na mai duban ta ya ke d’an tuntuntuni, dan kuwa ko shakka babu ya san wagga baiwa ta gaban sa ba ita ce mai warin da ya gani a lambu jiya ba, duk da dai be ga fuskar waccan da kyau ba amma ya san a jiki waccan tafi domin kuwa Ladiyo irin k’ananan matan nan ne. Shi kuma a yanzu be da buri da ya wuce ya gano baiwar nan da ke wari ko ya sami lafiya domin kuwa muddun ta na nan ba zai iya zama ko da na minti hud’u a turakar amaryar ta sa ba, abun mamaki shi ne ta yaya bayin Gimbiya kamar Fatima za su na zama da wari har haka ba tare da ta d'auki mataki ba? Hakan ke tabbatar masa da k'azantar da ke tattare da ita.
Juyawa yayi ba tare da ya sake tankawa Ladiyo ba, wacce ta yi kasake ta na duban sa ta rasa yanda za ta yi da ran ta, ganin dai da gaske ficewar ya ke ta bi bayan sa da sauri, amma ina kan ta cima su tuni ya d’au hanya,

22 / 24