Bintu Diyar Bayice Jinin Gado By GARGA'DI

Author :  GARGA'DI Category :  Romance

Chapter   19 / 24

54K to 57K   out of 70.2K words

Binta ya hau k’yarma tsabagen firgici, kowa sai da ya sha jinin jikin sa, Jakadiya ta durkusa ta na fad’in

‘’tuba mu ke ran Babban biji ya dad’a, Allah huci zuciyar Babban Biji, lafiya salamun’’

Sarki kuwa be gushe b ya cigaba

‘’mun biye mu ku mun bi san zuciya mun aikata ha’inci, hakik’a Sarki Abdulrahman ya kasanse mai zurfin tunani, mu kuma mun kasance daga cikin ma’abota san zuciya, fatan mu shi ne gyara wanga kuskure da mu ka aikata bisa san zuciya ba tare da 6ata dangantakar arziki da mu ka kulla a wanga rana ta yau ba’’

Kallan sa ya mayar ga Bintu, kana ya ce

‘’ina Kilishi?’’

‘’ran Takawa ya jima, gani kusa gaban ka’’

Cewar Hajja Kilishi.

‘’wagga d’iya ta arziki (yayi nuni ga Bintu) ta ma na abun da jinin mu basu ma na ba, sanadiyar ta yunwa ta kau a masarautar mu, idan ba mu maishe ta d’iya ba, ko shakka babu mu na daga cikin wanada ake kira butulu, wagga d’iya d’iyar mu ce, ni Sule na kira wagga d’iya da d’iya a gare mu, maza a shirya d’iyar arziki, idan an wayi gari ta bi tawagar masarautar Fabarusa dan kuwa jinkirin makwannin biyun ka iya zama barazana a gare mu, da zafi zafi akan bugi karfe…mun gama Magana’’

Ya na dasa aya ya tashi cike da Sarauta yayi shigewar shi daga ciki, ya na jiyo koken Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta amma ya mu su kunne uwar shegu duk da kuwa har ran sa ya ke jin abun.

Ita kan ta Bintu jin gobe gobe za a wuce da ita hankalin ta ya dad'a tashi, ta ma kasa motsawa daga in da ta ke, ta nemi kuka ta rasa.

Gimbiya K’amariyya kuwa wacce har shid’ewa ta ke tsabagen kuka da ya ci karfin ta, tuni ta sake fad’uwa sumammiya a karo na biyu. Nan waje ya sake kaurewa da salatin su Hajja Kilishi da Jakadiya. Dan kok’ari har da Bintu cikin kawo d’oki ta hanyar ciro mayafin ta, ta shiga yiwa Gimbiya K’amariyya fifita, yayin da Inna Salti ke yayyafa mata ruwa.

Wani k’akk’arfar ajiyar zuciya ta saki, alamar ta farfad’o, amma idanun ta lumshe ta kasa bud’e su, hawaye ke gudana bisa kuncin ta. Sai fa a sannan Gimbiya Binta ta ankare da Bintu da ke sunkuye bisa kan Didin na ta, sai fifita ta ke ma ta, ai kuwa ta daddage ji kake tas! Ta sauke yatsun ta biyar bisa kuncin Bintu sai da ta ga wuta a idanun ta. Hannun ta biyu bisa kuncin ta ta ke duban Gimbiya Binta, hakan ne ya dad’a k'ular da ita, ta sake d’aga hannu da niyar kai mata wani marin caraf Inna Salti ta ruke hannun ta, ta na mai fad’in

‘’kul kar ki kuskura ki sake! Kin san kuwa matar Yeriman Fabarusa ki ka d’aga hannu ki mara? Ina hankalin ki ya tafi?’’

Jin haka Gimbiya Binta kamar ta yi hauka, fad’i ta ke

‘’d’iyar bayi na mara, d’iyar bayi wacce na saba takawa ita na mara, babu wata matar Yariman Fabarusa da ta wuce Didi, duk makirci da munahunci wanga wulak’antacciyar Baiwa arudu ya k’are bisa kan ta! Ku ma mu zuba ni da ke ina mai tabbatar mi ki alkiyamar ki ta zo dan kuwa da ki tafi zuwa Fabarusa a gurbin Didi gwamma ki je ki kashe kan ki, dan kuwa masifa da balak’I ya na nan an tanadar mi ki, kuma shi za ki riska, sai dai uwar ki ta haifi wani…..’’

Ta juya fuuuu ta fice gudun kar Bintu ta ga hawayen ta, dan kuwa su ke sauka d’aya bayan d’aya tsabagen bakin ciki da takaici. Hajja Kilishi shi ce ta ja Bintu zuwa turakar ta dan neman yanda za a yi idanun Bintu da ya kumbura da shatin yatsun Gimbiya Binta ya baje, bayan Inna Salti ta bata baki bisa ga lamarin Gimbiya Binta da kuma mata alk’awarin irin haka ba mai sake faruwa ba ne. Nan su ka bar Inna Salti ta na rarrashin Gimbiya K’amariyya, domin kuwa bakin alk’alami ya bushe tuni.


🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[8/16, 4:34 PM] ‪+234 803 583 5431‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


5⃣


Da daddare bayan an idda sallar isha’i, Yarima Jafar da Yarima Barde zaune a falo sun yi jigum kamar wanda aka yiwa mutuwa, Khalil na daga d’aka ya na waya da matar sa.

Babban falo ne mai d'auke da k'ayataccun kujeru na sarauta, masauki ne da dama a ka tanada na musammam domin saukar bak'i na alfarma irin su Barde.

Tun da su ka isa ga masauki Barde ke zaune nan falon, sallah kad'ai ke iya sawa ya motsa. Shigar sa na d'aurin aure ke jikin sa, sai dai ya cire babbar riga da rawani, sumar kan sa kwance lub lub bisa kan sa.

'Daya daga cikin dogarawa da ke ciran kofa ne ya shigo ya zube gaban Yerima Barde, kana ya ce

‘’ran Yarima ya dad’e, Gimbiya K’amariyar d’iyar Mai martaba Sarki Sule na S’ayrasa ce me neman iso gare ka’’

Jin sunan K’amariyya tuni kafad’a Barde ta tasa, yayinda jijiyoyin wuyar sa su ka bayyana. Amma ya kasa furta komai. Yarima Jafar ne ya ce

‘’ka iso da ita gare shi’’

Dogari na mai fad’in

‘’an gama ran Yarima Ja’afar ya dad’e’’

Ya tashi da sauri ya fice. Yarima Ja’afar ma tashi yayi, ya d’an dafa kafad’ar Yarima Barde sa’annan ya shige ciki. Shigar sa ke da wuya Dogari ya shigo biye da shi Gimbiya K’amariyya ce. Sai da ya kawo ta gaban Yarima Barde sannan ya juya ya koma waje in da bayan Gimbiya K’amariyya ke tsumayin ta.

Tin shigowar ta ya kafa mata ido, har ta iso gare shi sanye cikin atamfa koriya wanda ta rufe da farar alkyabba ta alfarma. Duk tashin hankalin da ta ke ciki da kuma wanda Yarima Barde ke ciki be hana shi ganin kyauwun Gimbiya K’amariyya ba. Ga wani k’amshi mai saka kwanciyar hankali da ya kasa gane kan sa ke tashi daga jikin ta sa’in da ta zaune gaban shi. Yayi kok’ak’arin sanya kwayan idanun sa cikin na ta, amma hakan ya gagara kasancewar ta yi k’asa da na ta idanun.

‘’K’mariyya…..’’

Ta ji murya mai d’auke da tarin kwarjini ta daki kunnan ta, wanda tun da aka d’aura masa aure da Bintu, kwakkwarar kalma d’aya be fito daga bakin sa ba sai a yanzu da ya ga K’amariyya zaune gaban sa.

‘’K’amariyya’’

Ya sake kiran sunan ta a karo na biyu, maimakon ta amsa, kawai sai ta sa ma sa kuka, ya rasa yanda zai yi da ita dan kuwa Barde sam be iya rarrashi ba. Ta d’au lokaci mai tsayi ta na rera kuka gaban sa, tin ya na iya ba ta baki, har ya mata shiru dan kuwa shi dama Magana wahala ta ke masa. Sai da ta yi shiru dan kan ta, sannan ya dube ta, kana ya ce

‘’ban san kud’irin mahaifina ba, sai bayan da bakin alk’alami ya bushe, sai da aka d’aura min amre da kauna gun ki Fatima….’’

Jin haka Gimbiya K’amariyya ta kai duban ta gare shi, ta ga ya k’ara ma ta kyau da kwarjini na kwaran gaske, wai kuma an d’aura ma sa Bintu! Bintu dai d’iyar bayi! Ji ta yi kamar ta bud’e baki ta fad’a masa gaskiya komai ta fanjama fanjam, tunawa da ta yi da na ta Mahaifin ya sa ta a dole ta na ji ta na gani ta yi shiru, babu mamaki shi ya na da wani shiri ne na daban. Murya na rawa ta ce

‘’ina cikin damuwa Yarima, ina mafita?’’

Kallan ta yake na wasu dak’ikai, kafin daga bisani ya saki ajiyar zuciya mai karfi gami da sauke kafad’a, kana ya ce

‘’Allah shi ne mafita, shi za mu kai kukan mu gare shi, hallo bana yiwa Mahaifina musu, ban ta6a ba K’amariyya shi ya sa ma ki gaya aiwatar da wanga lamari ba tare da ya tuntu6e niba, yanzu ban da tsumi hallo ba dabara, amma ina so ki sani ina son ki, kwaran gaske’’

Cikin hawaye K’amariyya ta ce

"me zai hana ka sanar da Mahaifin ka gaskiya kamar yanda na sanar da nawa Mahaifin?’’

‘’ban da wannan ikon K’amariyya, da ina da shi da tuni na aiwatar da hakan’’

Cewar Yarima Barde ya na amai girgiza kai. Nan Gimbiya K’amariyya ta fusata, ta tashi da sauri za ta fita. Yarima Barde ma tashin ya yi, ya dakatar da ita ta hanyar fad’in

‘’kar ki yi fushi K’amariyya, kunar za ta min yawa, badan wacce aka d’aura min jinin ki ba ce kuma kauna gun ki da na ce duk duniya babu wacce na tsana face ita, sam ba za ta sami kulawa bare wani abu wai soyayya daga gare ni ba saboda soyayyar ki, hallo babu yanda zan yi dole haka zan zauna da ita har Allah ya kawo karshen zaman, dan darajar Mahaifan mu da Masarautun mu’’

Kallan sa ta ke yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta, a hankali ta furta
‘’ina ma ka fatan alkhairi Yarima Badde’’

Sannan ta juya a hankali ta na ficewa. Tsayawa yayi ya na kallan ta yayinda ta ke ficewa daga rayuwar sa, idanun sa sun yi jajur, ji yayi k’afafun sa sun kasa d’aukar gangan jikin sa, a hankali ya zauna zuciyar sa cike da tunanin yanda rayuwar sa ta sauya a wuni d’aya. Shi ba mutum ba ne mai san mata, mata ne ma ke san sa da bibiyan sa. Tin da Allah ya had’a shi da Gimbiya K’amariyya, ita ce mace ta fari da ya ji ya na kauna zai kuma iya aura. Amma yau gashi an ma sa Katanga da ita ta hanyar aura ma sa kanwar ta. Yatsun sa ya tusa cikin sumar kan sa sanadiyar sarawa da ya ji kan sa na yi, ya na fad’in

‘’lahaula walakuwata illa billah!’’




🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.




Khadija Sidi..✍🏼


6⃣

Ko da Gimbiya K’amariyya ta koma d'akin ta, sai ta sallami bayin ta gaba d’aya sannan ta kulle d’akin ta haye tsakiyar gado ta na rusa kuka. Bintu kuwa d’akin Hajja Kilishi bayi ke jera kaya da aka d’inka ma ta na alfarma, yayinda Hajja Kilishi ta sa ta gaba sai bayani iri-iri ta ke mata akan kayan da kuma yanda za ta na amfani da su, da yanda ake son zaman na ta ya kasance a fadar Fabarusa kasancewar Sarki ya janye makwanin biyun da ya kamata a kai Bintu ga Masarautar Fabarusa.

Bintu da ba cikin hayyacin ta ta ke ba, babu abun da ta gane kawai dai amsa ma ta ‘’um’’ ta ke. Da wuri Hajja Kilishi ta bawa Bintu umarnin kwanciya saboda sammakon da za su yi a washagari. Yanda ta ga rana haka ta ga dare, haka ta kwana cikin zulumi sai da asuba wani bacci mai nauyi ya sace ta.

Ba ta jima ta na bacci ba, Hajja Kilishi ta aiko d’aya daga cikin Bayin da aka bawa Bintu, wato Ladiyo ta tada ita gudun kada su makara. Nan ta ke tseguntawa Bintu cewar Gimbiya Binta har ta wuce Nigeria makaranta bisa ga umarnin Takawa. Kuka Bintu ta saka ta na mai fad’in

‘’Na shiga uku ni Bintu, wallahi ni Bintu na ke ba Binta ba, d’iyar bayi na ke ba d’iyar Sarki ba, ashe dai ba zan kammala makaranta ta ba, wayyo Inna ki zo ki taimake ni na shiga uku na lalace!’’

Da ladiyo ta ga haka, kawai sai ta fice, jim kad’an sai ga ta dawo biye da ita Hajja Kilishi ce rai 6ace. Tuni ta hau Bintu da fad’a, ta na fad’in

‘’Wai ashe ba ki da tawassali Fatima? Ba ki yarda da k’addara ba? Idan ba ki fasa kuka ba ba ba ki nuna mana ba a isa da ke ba’’

Jin wanna kalame na Hajja Kilishi tuni Bintu ta shiga taitayin ta, sai ajiyar zuciya ta ke kawai. Hajja Kilishi ba ta gushe ba ta cigaba da maganar ta kamar haka

‘’Ki d’au kaddara ki yi fata Allah ya sa hakan shi an alhairi gare ki, yoto ai alkhairin ne ma. Ina ke ladiyo ?’’
Ladiyo ta matso kusa tare da fad’in

‘’Ran ki shi dad’e’’

‘’Maza ku shiga bayan gida ku had’o mata ruwan wankan amare’’

Cewar Hajja Kilishi.
‘’An gama ran ki shi dad’e’’

‘’Ke kuma Hansai maza shirya kayan Gimbiyar ta ku, Ina Maman Cangwai ne? maza ku sheda mata ta ta kawo maganin d’ar nan da lalle domin yiwa amarya wankan lalle’’

Hansai na mai duk’ar da kai ta ce

‘’Ranki shi dad’e ai tuni Maman Cangwai na can rariya, fitowar Bintu kawai ake jira......’’

‘’Bintu ki ka ce!!’’

Hajja Kilishi ta daka ma sa tsawa. Hansai ta zube k’asa jiki na 6ari ta ke fad’in

‘’Tuba na ke ranki shi dad’e, na tuba ran ki shi dad’e ki min rai aradu na tuba’’

‘’Kwarankwatsi ki na rasa ran ki muddi ki ka kuskure asirin Masarautar ga tonu sanadiyar kuskure irin wang, shasha kawai, me an sunan Gimbiyar ga?’’

Hajja Kilishi na magana ne a hasala kamar mai shirin bugun Hansai. Ita kuwa Hansai idanun ta ke kawo ruwa.

‘’Gimbiya Bintu.....’’

‘’Gimbiya Fatima, ban yarda kin kira ta Bintu ko Binta ba!’’

‘’An gama ran ki shi dad’e, godiya na ke’’

Cewar Hansai. Allah Allah ta ke Hajja Kilishi ta sallame ta ko ta sami sarari. Jin Hajja Kilishi ta ce ta yi maza ta idda umarnin da aka ba ta, Hansai ta tashi da sauri ta fice. Kan ace me? Tuni aka shiga hidimar shirya Bintu, sai ga ta ta fito tsaf da ita cikin fararan tufa tun daga sama har k’asa. Hajja Kilishi ce ta d’auko wani dank'areriyar sark’a na gwal tare da yari da warwaro ta ce a sanyawa Bintu na ta gudunmawar kenan. Haka ma Inna Salti ta turowa Bintu goma ta arziki, ciki har da farrar god'iya. Sauran matan Sarkin ma suma ba a bar su baya ma, sai da su ka yi tattaki domin
nuna bacintar su dan kuwa abu na kishiyoyi sai da ya so ya zama gasa.

Rana ba ta k’arya, sai ga shi ana fitar da kayan Bintu zuwa motocin da ke jere domin kai amarya ga Masarautar Fabarusa, yayinda dattijiwar da ta zo amsar amarya, me suna Uwalanze ke zaune ta na jira. Wasu dattijai mata guda biyu, wanda su ke tamkar kakanni wajan su Gimbiya K'amariyya ne bisa ga al’ada su ka zo raka Bintu wajan Sarki domin su yi sallama a matsayin Mahaifin ta, sannan su damk’a ta ga mutan Fabarusa.

Bintu na ji ta na gani su ka sa ta tsakiya, gud’a ke tashi su kuwa tsofi fad’i su ke

‘’Allah Ya ba da sa’ar tafiya Gimbiya Binta, Allah ya sa a dace d’iyar arziki’’

Ba su zame ko ina ba sai turakar Sarki, in da su ka tadda Jakadiya tsaye bakin k’ofa ta na jira. Da isar su ta mu su iso zuwa gaban Sarki da ke daman abun da ta ke jira kenan. Gaban Sarki su ka aje Bintu dan idan aka d'auke dattijiya mai suna Gwaggo Munari cikin su, duk a na su zatan Gimbiya Binta ce. Sai da su ka kai gaisuwar su ga Sarki sannan su ka juya su ka bawa Sarki waje domin su gana da d’iyar sa.

Murya na rawa Bintu ta furta

‘’Barka da safiya ran ka shi dad’e’’

Shiru be iya amsawa ba, tsabagen tausayin Bintu da ya ji ya lullu6e shi, gami da nadamar hukuncin da ya aikata bisa ga san zuciya. Daga bisani ya nisa tare da fad’in

‘’Da wata murya za mu amsa mi ki Fatima? Da wata murya za mu amsa mi ki d’iyar arziki? Da wani baki za mu amsa mi ki wanga d’iya da ke gaban mu? Yau mun yi kad’an mu amsa gaisuwar wagga d’iya, wacca jama’a su ka ku6uta da ga yunwa saboda ita. Sanadiyyar wagga d’iya, mutan Sa’ayrasa na godiya gare mu, mu kuma godiyar mu gare ki ya ke, Allah ya saka mi ki da alkhairi sa’’

Shiru ya yi na d’an wani lokaci sannan ya cigaba

‘’Mungode kwarai hak’ik’a mun yi dana sanin abin da ya wakana a Masarautar mu, hallo mu na fatan hakan ya zama alkhairi a gare ki. Ki tsaya tsayin daka domin tabbatar da rufin asirin mu, shakka babu kin mana abin da ‘ya’yan mu ba su ma na ba. Tashi ki tafi d’iyar arziki, mu na addu’a albarkar Allah ya bi ki duk in da za ki kasance’’

Jiki na rawa, amma Bintu ta kasa tashi ta kuma kasa magana. Jakadiya ce ta lek’o, ganin yanayin da Bintu ta ke ya sa ta yiwa Dattijan nan magana su shigo su tafi da Bintu Sarki ya gama ganawa da ita.


A 6angaran Hajja Kilishi su ka tadda Dattijiwar Fabarusa wato Uwalanze. Nan aka damk'a hannun Bintu gare ta bisa alada da amana. Bintu fuska k’udundune cikin alkyabba kuka har da majina, Uwalanze ta ja hannun ta, biye da su d’aya daga cikin wannan dattijan ne da su ka kai ta ga Sarki, dama kuma ita d’in ce cikin su ta san gaskiyar lamarin wato Gwaggo Munari. Kai tsaye motocin Fabarusa su ka numfa.

Motoci ne na gani na fad’a wanda ke tashe wannan k’arnin. Mota ta farki cike fal da dogaran Fabarusa, sai ta biyu wacce ke rufe ruf da bakin gilashi, ita ce motar da su Yarima Barde ke ciki. A ta ukun Bintu ke zaune tsakiyar Uwalanze da Gwaggo Munari. Sai ta hud'in kuma bayin da aka bawa Bintu ne, wanda idan ka d'auke Maman Cangwi ko wacce daga cikin su tafe ta ke da na ta kullalliyar akan Bintu. Mota ta biyar ma dogaran Fabarusa ne ciki. Nan su ka d'auki hanyar Fabarusa.

A hankali Bintu ta ji ana ta6a kafad'ar ta, maimakon ta tashi sai ma dad'a lumshe idanu ta yi ta na mai murmushi, kasancewar mafarkin da ta ke mai dad'i, wai ga ta a makarantar su, tare da Aisar su na zantawa ya sa ta ji sam ba ta so

19 / 24