Author : MARYAM STAR Category : Love
lura da hararar da Mama ke zabga ma shi, shi dariya ma abin nasu ya bashi musamman yanda Abban ya kasa ya tsare yaƙi tafiya, badan yaso ba hakanan ya miƙe sanin cewa Abba bazai barshi ba, sallama yai wa Mama suka fice daga gidan.
To kundai san halin Abba da saurin kai hannu kuma kwana biyu da bana nan yanzu hannunshi har ƙaiƙayi ya ke ma shi idan yaga wani yayi abin duka, wata iriyar talla yakaiwa ƙeyar Yaya Hashim ta baya, babu arziƙi yai gaba taga-taga zai kifa sai kuma Allah ya aimake shi ya tsaya ya na susar ƙeya dan babu ƙarya ya tallu, kafin ya dawo daidai Abba ya kuma bashi wani mangarin akan ƙeyar ya na faɗin.
"Dan abu takazan ubanka wane shegenne yabaka damar zama ka na bada labari haka, na rantse da Allah ka sake zama cikin gida kana zuba surutu irin haka ni da kai ne, ayi mutum baki ba linzami, sai zuba kake kamar suda, shashancin banza da wofi kenan."
Shidai Yaya Hashim bai da tacewa, illa susar ƙeyarshi datasha talla da zazzafan hanun Abba irinna ƴan dambe waɗanda suka sha tsumi.
Haƙuri ya baya Abba ganin mitar ta ƙi ƙarewa, korarshi Abba yayi akan ya koma bakin aikinshi, kuma nan kusa karya kuskura ya sake ganin ko da ƙeyarshi ce a Unguwar bare ma yaganshi a gida ya zo, sai bayan wata uku sannan zai zo.
Da mamakin halin Abba yaya Hashim yai ma shi sallama tare da miƙa ma shi ƴan canji kamar yanda ya saba, sai de a maimakon addu'a daya saba yi mashi sai ya sake rufeshi da faɗa, jiki a sanyaye yaya Hashim yaja sanyayun ƙafafuwanshi gami da maida kuɗinshi aljihu yai tafiyarshi.
Abba na shiga gida ya iske Mama tsaye ƙofar ɗaki hannunta riƙe da jakar kuɗin da yakai ma ta jiya, yanda ya ga ta tsare shi da ido sai yai saurin shiga bayi, yakai aƙalla mintuna hamsin a ciki, Mama ganin zai ɓata ma ta lokaci a banza sai kawai ta shige ɗaki tare da ƙudurce sai ta shuka ma shi tsiya, ajiyar zuciya ya sauke ganin bata nan, sai ya lallaɓa ya shige ɗakin Umma, dan yanzu kusan tsoron Mamar ya ke yanda yaga ta birkice, kamar ba ita ba, yanzu wannan sanyin halin duk babu shi bare kuma kawaici, zai rantse da Allah tun ranar da Mubeena tabar gidan aka daina taƙalar Mama akwana lafiya, tsiya ta ke tsulawa abinta kamar ba itace ƴar Malam Sa'idu ba.
"Wai ni Iro haka za ka zuba ido kana kallon yanda waccan matar taka me zubin mayu ke takamu kamar ledar piru water, marin Sumayya fa ta yi ɗazu akan ta je kai ma ta abin kari bayan bataga damar zuwa nan anyi da ita, kuma ba wani abu Sumayyar tai ma ta ba, kawai dan ta yi sallama ƙasa-ƙasa sai ita Halimar bata ji ba, shine ta ce ta koma ta yi sallama, wau dan mi za ta ce ta yi shine fa wai ta ce tayi ma ta rashin kunya ta daddage ta rantsamawa fuskar yariya zazzafan mari, kalli dan Allah yanda kumatun suka kumbure kamar kwaɓin gurasa." Umma tai maganar ta na nunawa Abba fuskar Sumayya da tai suntun ga shatin yatsunan kwance akan kumatunta.
Kafin Abba yasamu damar cewa wani abu sai ga Mama burum ta afko cikin ɗaki, sai da ta shigo sannan tai sallama a ɗage, sake haɗe fuska Umma ta yi tare da buɗe baki zatai magana sai Mama ta dakatar da ita da faɗin.
"Ke sauraramin ba wajenki na zo ba, wajen wanda ya aje ki na zo, da zarar na gama abin da ya kawo ni sahuna a likafa zan fice dan kisan ɗakinki ba wajen da zan iya zama ba ne." sakin baki kawai Umma ta yi tana kallo Mama.
Dire jakar da Abba ya bata ta yi tare da faɗin.
"To malam Iroro ga kuɗaɗenka nan na dawo maka da su bana buƙata, ka haɗa ka riƙe a wajenka, shi wanda ya baka kuɗin ka bani yasan nafi ƙarfin million ɗaya, shiyasa yace ka bani million biyar, amma karka damu gasunan na dawo maka da su ka haɗa duka ka riƙe bana da buƙata Alhamdulillah tun da har akwai wanda zai iya ƙirgo manyan kuɗaɗe har haka yace a bani, koda ba'abaninba naji daɗi sosai, sai anjima." Tana gama faɗin hakan ta saka ƙafa tai ficewarta.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK THREE 3
CHAPTE 37
بسم الله الرحمن الرحيم.
Wuf Umma ta matso tare da wartar jakar da Mama ta aje, hannayenta na kyarma ta shiga buɗe jakar, baya tai da sauri tare da buɗe mitsi-mitsin idanuwanta, laɓɓanta sai kyarma suke, zabura ta yi ta sake surar jakar ta matse a hammata, sannan tai miƙe tsaye ta fuskanci Abba wanda keta faman haɗiyar yawo alamun rashin gaskiya ƙarar a fuskarshi.
Ahankali na shiga buɗe idanuwa da sukaimin nauyi, dishi-dishi na fara ganin ɗaki, sai na sake kulle idon, na sake buɗewa nanma dai bangani ba kyau, sai da na maimata kullewa ina buɗewa kusan sau biyar, sannan na samu damar ganin ɗakin dakyau, juyar da kaina nai zuwa gefe sai naga Papah zaune ya na sakarmin murmushi, yunƙurawa nai da niyar tashi zaune sai naji hannun Mommy a kaina ta taimaka ta miƙar da ni, sai de a jikinta ta jinginar da ni tare da riƙe kafaɗuna ta na jeromin sannu, duba nakai kan ƙafafuwanta waɗanda babu tantama akansu na kwanta, ganin yanda daga cinya zuwa gwuiwar tsadadiyar atamfarta ya yamutse harda ƴar zufa, kafin in gama dawowa daidai muryoyin su Hajjo sun cike kunnuwa da sannu.
"Mommy!." na kirata araunane.
"Na'am my yarinyar kirki." ta amsani tana sakar min lallausan murmushi fuskarta fak tausayin halin dana tsinci kaina a ciki.
"Mommy miya same ni?."
Na watsa ma ta tambayar tare da karkatar da kaina ina kallon fuskarta dan jin amsar da za ta ba ni.
Ganin yanda na kafeta da ido sai ta fara inda inda.
"Amm kina ji ko, dama ba...."
Faɗowa kikayi daga kan gado shine kanki yaɗan daku amma basosai, ankira doctor ya duba ki shine yai miki allurar barci shiyasa kikai barci me nauyi."Hajjo tai saurin faɗa dan ta lura da yanda Mommy ta rikice ganin na tsareta da ido.
Mai da akalar kallona nai ga Hajjo sai naga ta kauda kai gefe itana fuskarta da alamun damuwa.
"Anty Sulaima!!!."
Na kirata a raunane dan sam ban gamsu da amsar da suka bani ba, kuma bazan iya ƙaryata hakan ba, dan zai iya zama gaskiya, amma ƙasan raina ke sanar da ni akwai abin da ya faru wanda ake ɓoyemin duba da yanayin fuskokinsu sam babu walwala bare nishaɗi.
"Na'am my Anty ƙanwa."
Sulaima ta amsa ni zuciyarta fal tsoron irin tambayar da zanyi ma ta.
"Kin san wani abu, jina nike kamar na haukace, saboda ina ganin wasu abubuwa, ku kuma naga kamar bakwa ganinsu, na haukace ko?".
Nai ma ta tambayar kamar wa ta geliya.
Ta shi kawai tai ta fice da gudu ta na toshe baki kar kukan da ke barazar ɓalle ma ta ya ɓalle a gabana.
Wata iriyar damƙa Fauzan yaiwa hannun Papah yana jin zuviyarshi na suya, wani abu ne me ƙarfi ke zanshi zuwa gare ni, yai takaicin akan yanda bazai iya taka ƙafafuwanshi zuwa inda nike ba, da abu na farko da fara bani shine kyakkywar runguma wacce zata mantar da ni dukanin wa ta damuwa, labarin da Papah ya bashi ya matuƙar taka rawar gani wajen sake kusanta ni da zuciyarshi, ya jima bai ji ya damu da wani ko wa ta ba kamar yanda ya damu da ni da lamurrana.
"Haba Mubaraka, ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala, kallon me hankali nike ma ki, ga nutsuwa da sanin ya kamata, miyasa za ki dinga faɗar maganganun da sam basu dace daki faɗe su ba, ki kasance me godiya ga Ubangijinki tunda har kika tashi lafiya ba tare da wani abu ya same ki ba, halin da kika shiga ya saka mu a zullumi, ga Abdallah nan zaune ya kasa motsawa ko nan da can, alhalin yana da meeting akan harkar kasuwanci, amma saboda girmama lamarinki da yayi ya saka ya kasa fita ko nan da can, duba fuskar Fatima kiga yanda yai kace-kace da hawaye, duk na tausayin halin da kika riski kanki ne a ciki, Fatima sam bata da cikakkiyar lafiya amma ahaka ta miƙe ƙafafuwanta ta kwantar da ke, bakinta bai hutaba wajen tofa maki addu'a, ga Mijinki can Fauzan a kwance cikin damuwa ya tashi hankalinshi sosai ganin yanayin da kika shiga, bai dace ace kin ƙara mashi wata damuwar ba, maza ki kwarara jikinki ki zo muje kiyi sallah ki ƙara godiya ga Ubangiji da ya farfaɗo da ke cikin hankalinki." Hajjo ta ƙarashe maganar gami da miƙewa tsaye ta kama hannuna, bin bayanta na yi ina jin wani sanyi na huda zuciyata, kalaman da ta faɗa min sun yi tasiri sosai wajen daƙile yanayin da nike, wani irin ƙarfi ya zo ya dabaibaye raunananiyar zuciyata.
LONDON
"Mom bai kamata ace har yanzu ki na biyewa Moon ba, amma duba da plan ɗin da kika tsara babu laifin dan munbita Nigeria, amma ni ina duba irin ɗibar albarkar da muka yi lokacin da muka taho da Moon."
"In banda abinki Jaleela ai Fatima da iyalanta sam basa da riƙo, kuma ai dolene ta tarbemu duk lokacin da muka je gidan dan muma muna da haƙi, in bacin mutuwa me ton asiri ai da yanzu ba wannan zaman ake ba, kai a wannan garon ko ni ko wannan baturiyar tsohuwar banza, babu inda zan je sai an fidda kasonmu na dukiyar Mahamman anbani tawa da taku." mom tai maganar tana ɗaukar wayarta ta lilibo number tai kira, tambaya tai ko akwai fly da zai je nigeria a ranar, nan aka sanar ma ta da akwai amma na marice ne, sallama tayi tare da bucking ɗin ticket na mutum uku, nan tabawa Jaleela umarnin kirar Hajiya Fatima da Hajjo ta sanar musu da zuwansu, babu kunya ha ɗaga waya ta kira ta faɗi saƙon mahaifiyarta idonta shaye da toka, ta mance yanda a zuwansu na ƙarshe ta rufe ido ta zabgawa Hajiya Fatimar rashin kirki, albishir Mom taiwa Moon wacce tuni ta haɗa kayanta dan ta rantse akan babu abinda zai hanata zuwa Nigeria, sosai ta ji daɗi yanda Mom ɗin ta amince ta ce zasu tafi gaba ɗaya, sai de jin cewa da Jaleela za'a tafi sai nishaɗinta ya ragu, harta cewa Mom ɗin.
"Dan Allah Mom muyi tafiyarmu mubarta, wallahi itake sake zuga ki akan wani abu, kin mance rashin kunyar da taiwa Mommy, nidai gaskiya bana son tafiya da ita."
Mom bata kulata ba sai sake haɗa mata wasu kayan da tayi dan tace idan suka je zasu ɗan jima, Moon saurarenta kawai ta ke amma ta riga data yanke hukunci idan har ta tafi tofa ba zata yarda ta dawo ba.
A ranar suka kama hanyar Nigeria suka bi jirgin yamma, bayan sun sauka sai Mom ta sauya shawara akan su fara zama Abuja na kwana biyu, akwai muhiman abubuwan da take so ta haɗa daga nan sai su wuce, dama Moon ce keda damuwa to kuma ganin anzo sai ta share da Mom ɗin kawai ta barsu su gama abubuwanda za suyi, ita angama mata me wuyar tunda ta sadu da Nigeria, zuwa Legos ba abu bane wanda zai mata wahala.
Waya suka kira Mommy akan sun iso amma wanu uzuri ya tsaidasu a Abuja sai nan da kwana biyu sannan zasu ƙaraso, duda Hajiya Fatima bataji daɗin hakan ba duba da yanda akai shirin taryarsu sai suka ce sun fasa, bata nuna musu komi ba saima sannu da zuwan da tai musu sukai sallama amutunce....✍️
WAI WACECE MOON, MOM, DA JALEELA???.
ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFI NA UKU SAI MUN HAƊU A LITTAFI NA HUƊU, WANDA ZAIZO NAN BADA JIMAWA BA.
KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.