ZAFIN WUTA

Author :  MARYAM STAR Category :  Love

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 23.3K words

ka kaima?."

Girgizamin kai ya yi alamar a'a.

Cike da mamaki na ce "Ammafa kasan baka ci komi ba du yau."

"lokacin Sallah yayi shi yasa yanzuma ina jiranki ki taimaka min in yi alwala sai idan na yi sallah zan ci, amma kingin na ki nike so."

Ban musaba na rufe food flask ɗin na mayar a cikin basket sannan na ajiye gefe ɗaya na tashi ina gyatsar ƙoshi, sai a sannan na jini na fara dawowa daidai, toilet na numa na haɗo ruwa kamar yanda na saba haɗawa idan zan yi mashi alwala ko wanke mashi jiki, bayan na kawo ne na danna madanin da ake danmawa gadon ya ɗaga, bayan ya ɗago na fara shirin tai maka mashi amma sai ya katse ni da faɗin.

"Dan Allah idan babu damuwa ki taimaka min zan yi bawali, ya matseni sosai." waro ido na yi ina tuno ranar da naga ya yi fitsari da irin wahalar da ya sha, sai naji jikina ya sake yin sanyi kamar marar laka haka na ƙarasa tare da saka ma shi robar da naga Pahpah ya saka ma shi a ranar, duk da hannayena na kyarma, riƙe kafaɗuna yayi ya shiga jujjuya kai gefe da gefe ya na yamutse fuska kamar me shirin yin kuka, sake ƙanƙame damatsan hannuwana yayi da wani ƙarfi kamar zai ɓalla ni, sai ga wani abu me ɗumi na gangarowa jawur kamar ruwan lipton, ashe fitsarin ne ya fito, sassauta riƙon yayi amma bai sake ni ba sai da ya gama sauke numfarfashi sannan ya sake ni na fara tsarkake wajen ina yin yayyafi tare da wanke inda ta fallatsa dan ban iya saka robarba, wajen yi mashi tsarki kasawa na yi saboda kunya, dan haka sai kawai na taimaka mashi ya tashi zaune ni kuma na juya mashi baya har sai da ya gama sannan na juyo na tayashi yai alwala ya gabatar da sallah, bayan ya gama gama ne na haɗa ma shi abinci sannan na fice dan gabatar da tawa sallar nima, sai da na fara da tsarkake jikina sannan na nasake wanka, a gurguje na fito ya tayarda sallah gudun shuɗewar lokacinta, bayan na gama na yi tilawar haddar alƙur'ani da ka, bayan na ida zan yi addu'a kawai sai na ji bakina na furata.

Ya Allah kai ne majiɓancin lamuran bayinka, Allah ka jiɓanci lamurana, ka saka haske imani cikin ayyukana, ka tsareni da sharrin dukan abin ƙi, Yah Allah ga bawanka nan cikin mawuyacin hali, Allah ka sauƙaƙa mashi yanayinda yake ciki, ka haskaka rayuwarshi ka bashi lafiya madawwamiya, wacce za ta amfani musulmai baki ɗaya." haka naita jero mashi addu'o'in samun lafiya, bayan na shafa ne na nufi wajenda Mommy ta saka aka jere min kayan sakawa kala-kala, wasu riga da wando na pakistan irin waɗanɗa indiyawa ke sakawa ne suka ɗauki hankalina, sai na janyo su na shiga ɗaga su, ga mamakina daidai da nine kayan, ban ja da nisa ba na saka su, aiko sukai bala'in yimin kyau sosai kamar dan ni aka yi, gaban tangamemen miron da ke kafe na isa tare da zama akan stool na shiga mulke jikina da tsadadun mayuka da turaruka waɗanɗa Pahpah ya kawo min ranar da yaje Chaina, da yake ya saba duk idan ya yi tafiya koda ta kwana biyu ce to sai yayowa su Mommy tsaraba, haka ya jibgo min su da mayukan gashi masu inganci, ni kuma na zage ina lafta gyara abuna, aiko yanzu laushi da taushin fatata ya daɗu sosai, ga wani walwali da ɗaukar ido da nike kamar irin sababin ƴan gayun amarenan, bayan na gama na rage man fuskata da form, sai na zagaye lips ɗina da wani ɗan ƙaramin res lip stik me dango, wanda ya sake fito da kalar lips ɗina wato pink, na zizira kwallin kajal a idona wanda suke kamar ruwa ya kwanta a ciki saboda tsabar hasken da Allah ya wadata su da shi, tsaf na fito kamar me shirin zuwa gasar kyau, ban tsaya gyaran gashiba na taje shi na ɗaure da ribon na saki doguwar jelar na yawo a bayana, kallon kaina na yi da kyau, ni kaina na bala'in burge kaina ba ƙarya ni kaina nasan ni ɗin kyakkyawar mace ce, a hankali na kai duba zuwa ga ƙirjina, sai naga ana ɗan ganin shatin nipples ɗina alamar ban saka bra ba, nan take maganar Fauzan ta faɗo min, da sauri na buɗe ma'ajiyar ƙananun kayan wanda Sulaima ce ta jere min su dakanta,wata farar bra na gani wacce ta burgeni, sai de tana da ɗan tudun soso, kwale rigar jikina na yi na saka ta ina ganin yanda ta dace da farar fata ta, sai kawai na tsinci kaina da tunanin ko tayaya za'ayi Fauzan yaga wannan shigar tawa, ba ina nufin yaga kayan da nasaka ba a'a ina nufin yaga undis ɗina, sai kawai na zauna jugum a bakin gado ina tunanin, can sai wa ta zuciyar ta ce min.

" Mubeenah ai dolene kisan ta yanda za'ayi yaga wannan bra ɗin, tunda ɗaukar ki yake a matsayin marar jin magana." sai na ce a'a ba haka bane, kar in zaƙe da yawa, sai kuma zuciyata ta sake cemin.

' Ke Mubeena ki raba kanki da irin wannan tunanin, kar ki zaƙe da yawa, daga zuwa jinya sai ki nemi sauya matsayinki, to tun wuri ki daina tunanin baje koli dan nan ɗin ba gidan Abbanki ba ne, nan da wani ɗan lokaci za'a sallame ki da zarar kin gama aikinki, ke hatta igiyar auren da ke tsakaninku sai sun datse ta, dan sam baki dace da ɗansu ba, yanzuma su na yin komi ne dan samun lafiyar ɗansu.'.✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTE 27

بسم الله الرحمن الرحيم.

Saurin ƙaryata zuciyar data bijiromin da wannan mumunan tunanin wanya ke neman hargitsa zaman lafiya da nutsuwata, tuno irin ɓaƙar azababbiyar rayuwar da nayi a gidanmu kaɗai tadamin da tsigar jiki ya ke, kowa da gidansu yake tinƙaho amma ni tsoron abin da zai dangantani da gidanmu nike, na fara haƙa rami ina binne rayuwata ta baya, yanzu gaba kawai na fuskanta, zan ginawa rayuwata gini me ƙarko wanda ba iya ƴaƴan da zan haifaba, har jikokinsu zasu amfana.

Cikin ƙwarara zuciyata nayi ta hanyar hana kaina tuno rayuwar dana gabatar a baya, sai tunanin irin cigaba da na samu a yanzu.

Sallah la'asar na gabatar sannan nasake gyarawa na gyala mayafin kayan na fice zuwa sashen Mommy dan mu gaisa, ina zuwa na tarar da batanan sai kafatanin masu yin aiki a ɓangare waɗanda keta faman aikace-aikace suna kaiwa da komowa, har zan fice sai kuma na hangi Babaa Habiba na ɗago min hannu, tsayawa na yi ina jiran isowarta tare da yalwata fuskata da murmushi.



"Ranki ya daɗe hajiya Ƙarama, ashe rai kanga rai." Babbah Habiba ta faɗi bayan ta ƙaraso, murmushi na sake sakar ma ta sannan na ce.

"Allah sarki Babaah, yanzu dai haɗuwa ta yi wahala, fatan kina lafiya ya kuma ayyuka."

"Ke dai bari ƴarnan, to ayyuka sai dai muce alhmdllh, dan yau kam akwaisu ba laifi, gida nata haramar ɗaukar baƙin turai." sai da na maimaita maganar baƙin turai a zuciyata, amma a fili sai na sake yi mata murmushi sannan mukai sallama kowace ta kama gabanta.

London

Kwance take akan makeken bed wanda aka shimfiɗe da lafiyayen bed shit me laushin gaske, danƙareriyar tsadaddiyar, scrollyn ta ke na satatus wanda mutanen da take chart da su ke ɗorawa, ita kuma take ɓata lokacinta wajen tsayawa kalla, har ta wuce, sai kuma ta dawo da baya tare, a jikin sunan aka rubuta S S Sulaima, tsayawa ta yi tare da dangwala hannunta kan wayar, nan take gogagen photon ya ɗauku da kyau yai clear tartar, Sulaima, Mommy, Hajja sai ni zaune a ƙasan gadon Fauzan naɗan duƙar da kaina kaɗan, hakan ya bawa gefe kyakkywar fuskata bayyana, Sukaima ce ta yi photon ranar friday muna zaune da marice bayan mun kammala azkar, ware matsakaitan idanuwanta ta yi tare da sake zuƙo fuskar Fauzan da ta fito tar, dayake cemarar normal ce hakan ya bayyanar da tabunan da ke jikinshi wanda suke gaf da warkewa, bai fito sosaiba iya ɓarin hagunshi ne ya futo a photo.

Da tsananin sauri kamar zata hantsilo ta yaye jibgegen lallausan bargon da ta lulluɓa da shi, cikin rawar jiki ta fita daga tsararen bedroom ɗin ta na kwalla kiran.

"Mom! mom!! mom!!! Bloody!!!!!."

Ta fito ta na kwala musu kira a rikice, har lokacin hannunta nakan screen ɗin wayar tana kallon pic ɗin farar fuskarta cike da mamaki.

"Moon!, lafiya kike me irin wannan kiran haka kamar tsohuwar makauni?."

Wace aka kira da Moon ta sake takawa zuwa gaban Mom ɗin tare da faɗin.

"Mom wallahi Allah Sweetie ya warke, kallafa kigani, kalli wannan picture ɗin Sweet sister Sulaima ce ta ɗaura."

"Mtswwwww aikin banza, to se me idan ya warke, wai Maimoon ba za ki fita harkar wannan yaronba, inace nayi miki tsakani da shi, ina ruwanki da warkewarsa." Mom ta faɗa bayan ta kalli picture ɗin, wani malolon baƙin ciki ne ya baibaye zuciyarta ganin yanda fuskar Mommy da ahalinta ke fitar da annurin farin ciki, ta tsani Mommy da dukkan wani abu wanda ze raɓe ta.

"Mom Sweetie na nefa, ba za kiyi farin ciki da samun lafiyarshi ba, sanin kanki ne babu wani ɗa namiji da nike tsananin so kamar Sweeti, wallahi a wannan karon bazan biyewa son zuciyarki ba, tunda kanki kaɗai kika sa ni nima zan bawa kaima abin da zuciyata ke so, yanzu zanje inyi shirin komawa Nigeria, a wannan karon bazan biye muku ke da Sis Meema ba, zan bawa zuciyata abin da take so, ba zan sake saka kaina cikin wani hali ba." tai maganar cike da rashin kunya har ta na yin kamar za ta kaiwa Mom ɗin mangari tsabar jin haushin abin da tai mata.

Ji suka yi anyi magana daga bayansu.

"Kin daɗe baki tartare kafatanin kayan da suke naki in koma can dindidin gidan Fatima da zama ba, bakisan wani abu ba Moon, tuni na sallamawa Fatima ke, saboda nasan baki da zuciya akan wancan banzan guy ɗin wanda in banda wahalar da zuciyarki babu abin da ya ke miki, wallahi ko kin tafi sai kin dawo da ƙafafuwanki, kije ki shirya ni nan na ɗauki nauyin yankar miki ticket na komawa nigeria yanzunan, ba za ki sake ƙara kwana ɗaya a Lomdon ba, kuma idan kika tafi kin tafi kenan dan mun sallama ki, muma mu huta da baƙin naci da jaraba irin ta ki."

Tunda Jaleela ta fara magana, Moon ta haɗe fuska tare da aika ma ta da muguwar baƙar harara kamar idanuwanta zasu zazzago, ƙasa, cike da ƙufula ta ce.

"Ke asuwa da za ki dinga saka min baki cikin lamurrana, ba nace kar ki sake sakamin baki cikin hukuncin da zannyankewa kaina ba, ke da Mom sam baku da adalci, kanku kaɗai kuka sa ni, bai shafekuba idan na shiga cikin wani hali, gaskiya wannan karon sai dai kuyi duk abin da zakuyi amma wallahi bazan yarda inbi son zuciyarku ni kuma in ƙuntata tawa zuciyarba, Nigeria kamar na tafi ne, zan koma can in rayu cikin farin ciki da walwal, nasan zan samu ninkin kulawarda kuke bani a can." ta na gama faɗar hakan ta juya ta koma ɗakinta, yayin da tabar Yayara Jaleela nata surfa masifa Mom na tausarta, dan sam bata son yanda Jaleelar ke kyara da tsangwamar ƴar auta kuma sanyin idaniyarta wacce take kallo kamar babyn goye....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTE 28

بسم الله الرحمن الرحيم

Mom ki barni in koyawa waccan shashashar ƴar ta ki hankali, wace bata san inda duniya ta dosaba, ina shi Fauzan ɗin sam bai damu da ƙurar da ta kwaso ta ba, idan aka ce ya manta da ita a shafin rayuwarshi kar kiyi mamaki, musamman idan akai duba da irin ɗibar albarkar da mukayi musu lokacinda muka je tahowa da ita, shikenan zancen wannan banza ƴar iyayin Sulaima ya tabbata da tace indai Moon ce da ƙafarta za ta dawo saboda ta na tsananin ƙaunar yayarta, shikenan yanzu wannan banziyar marar kunyar Sukailar maganarta ta tabbata, tunda gashi daga ganin photo har ta fara zancen komawa Nigeria, Mom kiyi wani abu akai idan ba haka ba waccan marar hankali da hangen nesar zata jiƙa manah aiki ne, ban san wace iriyar kwanya ce da ita ba, sam bata da tunani bare lissafi."

Jaleela ta faɗa tare da juyawa ta koma inda ta fito tana zagin Moon, yayinda haushi da takaicin yanda Jaleelar ke kausasa harshe akan ƴar uwarta Moon Mom ta juya zuwa ɗakin sanyin idaniyarta dan ta rarrasheta gudun karta maida musu aiki baya, dan bata mance irin dambarwar da aka yi ba kafin su samu su ɓallota daga Nigeria gidan Fauzan.

⭐⭐⭐.

Duk juyinda zanyi da wani baƙon yanayi wanda na gaza gane miya assasaminshi nike, a gefe ɗaya kuma ga fargabar zuwan baƙinda na ji mutanen gidan na magana, haka kawai sai nike jin babu daɗi, dan ni sam bana son jama'a daurewa kawai nike yi, lumshe idanuwa na yi ina hasaso yanayin da muka riski kanmu a ciki ɗazu ni da Fauzan, haƙiƙa yakaini wa ta duniya wacce ban san da zamanta ba, na ɗanɗanamin zaƙin zuma a harshe, sai naji ina kewar kasantuwa atare da shi, sai hancina ke jiyomin kamar ƙamshin maganin da nike saka mashi wanda ya kama mashi jiki, wani sanyi na ji yana ratsa sassan jikina, a hankali nike sauke numfashi me fitowa da ɗumi, ganin hakan ba zai kaini ba ya saka na tashi na zura takalmana masu taushi da laushi na fito daga ɗakina cikin bin umarnin zuciyata, bani ke sarrafa kaina ba, zuciyata ce ke sarrafani ta hanyar jan ƙafafuwana zuwaga abinda take muradi, ban samu salama ba sai da na dangana gangar jikina da bangon haɗaɗen ɗakin da Fauzan ke ciki, sannan na ji wani irin ɗumi na ratsani gami da sauke ajiyoyin zuciya a jere a jere, ban tsaya mata lokaciba na shige kaina tsaye tare da sake siranta muryata nai sallama wacce amonta ya fito a sanyaye.

Wani irin sanyi ne ya baibaye duniyar Fauzan yayinda nutsuwa ta safkar ma shi jin sautin muryata ya ratsa dodon kunnenshi a bazata, amsa sallamar yayi tare da yalwata fara'a akan fuskarshi tare da yin wellcoming ɗina a zuciyarshi, kaina tsaye na nufi wajen kagon tare da zama kusa da shi nai shiru dan ban san abin da zance ya kawo ni ba a lokacin, shima shiru yai baice komi ba sai aikin ƙureni da mayataccen kallo da yake, zuciyarshi na matsewa acikin ƙirjinshi tare da harbawa da tsananin ƙarfi wanda yaso zarce kima.

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR

4 / 8