ZAFIN WUTA

Author :  MARYAM STAR Category :  Love

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 23.3K words

wacce ta ruɗarda Sir Umar harya kasa sukuni sai da ya mallake ki ba hawayeba waɗanda babu abin da suke yi sai ɓata maki fuska sam basa miki kyau." Malam ya faɗi cikin muryarshi me taushi da kamala.

Dariya da kuka ne suka kubcewa Sadiya lokaci ɗaya, nan take farin ciki ya bayyana a kan fuskarta musamman da taji yace.

"Indai kika dinga yin kuka har kika yi muni to fakaina zan shigewa Alhaji Umar gaba muje Saudiya ya zaɓo ƴar lukuta me manyan kumatu mu haɗa shi aure da ita, kinga idan kika yi kuka za ta goyeki a baya tai ta rarrashi."

"Kai Malam wallahi bazan yarda ba, kuma da kake cewa kai zaka rakashi neman aure, ai wallahi idan kuka je kai zasu auramawa ba shi ba, tunda dai kaine matashi akan shi, kasan su basu son auren tsofi kamar me gidana."

Tai maganar ta na wani farfara jajayen idanuwanta waɗanda suka rine daga farare tas zuwa jajah.

Rufe baki Malam da hannu kamar yanda ma ta ke yi idan sunji gulma sannan ya ce.

"Ki tufemin asiri ni ɗansu, ki bari inmutu maza su kaini da mata ba, kar ki kuskura ki bati Mom Ihsan ta ji wannan kalami na ki, idan har baso kike ta daka ni a turmi dakan daudawarta ba."

Dariya sosai Sadiya ta yi dajin kalaman yayanta, haka suka rata ranat da firarraki waɗanda suka mantar da Sadiya damuwar da take ciki.

Wunin ranar wani irin amai marar kyan gani Alhaji Umar ya dinga yi, yayinda Malam ya kwantarwa da Sadiya hankali akan babu komi alamar maganin nakan yin aiki ne, addu'ar samun dawwamamiyar lafiya tabi mijinta me ƙaunarta da ita.

BAƘIN DAJI.

ZUKA👽👹

Zazzaune suke akan wani ɗan daddamali ƙasan bishiyar wa ta tsohuwar babbar kuka, yayinda wa ta iriyat wuta ke ci balbal babu kyan gani, hucin wutar kaɗai ya isa ya markar da Bil Adama bare ace ta taɓa shi, wani ja jazur ɗin hayaƙu ne ki fitoda daga wutar wacce sarki kuma shugaban jajayen mugayen aljannu ne zuba wani abu wanda ke ta fitarda wari marar daɗin shaƙa, direct hayaƙin ke kwaranya jikin Zuka wanda aka zaunar akan wa ta baƙar kujera, wa ta arniyar mummunar dariya marar daɗin sauraro ce ke fitowa daga wawakeken bakinsa, duk idan yai dariyar sai dajin da abin da ke cikinshi sun girgiza, yayinda manyan namun dawa waɗanda ke whalar samu a sauran dajijjika ke tsere wajen ɓoye kawunansu, a gefen Zuka tawagar wasu irin baƙaƙen Jinnu ne su na waƙe cikin wani irin yare tare da watso wani abi jikin Zuka wanda ake yiwa tsumi daga naƙin aljani zuwa jajayen Aljannu mugaye marrasa imani bare tausayi.

Da wani razanin ɗan leƙen asirin Sarauniya Zubudiyya ya juya hankali tashe zuwa, buɗe fukafukanshi yayi ya nausa cikin sararin samaniya, bai sauka ako ina ba sai daidai bakin wani babban tekun dake garin Legos, nan take yai nutso zuwaga fadar da Sarauniya ke zaune ita da mahaifinta daƴan zaman fada su na fira cikin nishaɗi, zagaye da su hallitu ne na cikin tuwa iri-iri suma su na yawata cike da nishaɗi sai kaiwa da komowa suke, sannn hadiman aljannu su ma sai farin ciki suke da labarin da Sarkin ruwa ke basu....✍️

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTE 35

بسم الله الرحمن الرحيم.

Tsulum ɗan leƙen asirinta ya dawo tare da zubewa agabanta ya dinga zubo kirari tare da gaisuwa zuwa ga sarki, nan take ta dubi tsakiyar kanshi inda tai alama idan tasaka shi aiki za ta dinga ganin dukkan abin da ya garu kamar vedio, nan take yanayin fuskarta ya canza, bayan kallon abin da ya faru da tai a cikin abin da bai zaga second ɗaya ba, bata nuna komi akan fuskartaba, duda tashin hankalinda labarin ɗan aikenta ke azalzalarta, amma bata bada damar byyanarshi ba har sai da Sarkin ruwa ya gaji dakanshi yai musu sallama ya koma zuwa can ainahin inda fadarshi ta ke.

Jan ɗan aiken ta yi suka fice inda babu wanda ke ganinsu, nan suka shiga tattaunawa akan lamarin, dan abin da Zuka ya je yayi na nufi zai koma ɗaukar fansa, haɗa hannu da jajayen Aljannu na nufin kawo zalunci da tashin hankali a cikin mutane harma da ƙananan aljannu, sun tattauna sosai har sai da suka samo mafita sannan tai sallama da shi ta fice ayyukan gabanta.

Babu abin da ke tashi a cikin bakin daji sai iface-ifacen taya Zuka murnan samun nasarar mallakar ƙarfi irin na jinsin jajayen mugayen Aljannu, inda ya tashi ya fara ƙone dajin cike da farin cikin ganin yanda ƙarfinshin ya linka na baya sau goma, wa ta iriyar girgiza ya dinga yi wacce ka harmutse dajin da hallitun da ke cikinshi, suko waɗanda sukai mai aikin sai farin ciki suke yi tare da murna akan yanda Zuka ya samu damar zama ɗaya daga cikin jinsinsu, kwarya-kwaryar liyafa irin tasu ta aljannu suka shirya, inda suka dinga party su na shan jini iri-iri, su na kururuwa tare da feshin wuta kowa nason gwada bajintarshi.

Lagos.

Jigun suka yi, kowa ya rafka uban tagu su na jimami akan labarin da Fauzan ya gama basu wanda yai sanadiyar faɗuwata, nisawa Hajjo ta yi tare da katse shirun da ɗakin yayi ta ce.

"Da dukkan alamu wannan jinjirar daka bamu labari ba kowa ba ce face ita Mubarakar, idan ba ita ba ce to tayaya daga kayi tambaya sai ta maimaita kalmar ta faɗi ta suma, adai bincika lamarinan."

Sake famƙe hannun Pahpah Fauzan ya yi, famuwa ɓaro-ɓaro a fuskarshi ya kalli fuskar Pahpah sannan ya ce.

"Pahpah! laifina ne ko, bai dace inyi ma ta wannan maganarba tunda ba ta gama bani labarin ba, zuciya ta zafi ta ke min sosai Pahpah, pls kayi wani abu kai, ku kira ma ta Doctor bana so wani abu ya same ta, bazan iya jure ganinta cikin wani hali ba."

Tallafar haɓarshi Pahpah ya yi, shima fuskarshi da alamun damuwar halin da nike ciki, amma sai yai ƙoƙarin ɓoye damuwar saboda gwararawa Fauzan zuciya, dan ya tsorata da ganin yanda ya gigice akan halin da nike ciki, ko rantsuwa Pahpah yayi bazai yi kaffaraba akan ya daɗe baiga wanda Fauzan ya nuna zallar damuwa akanshi irina ba, yana matuƙar damuwa da lamarin mahaifiyarshi, saboda akwai shaƙuwa me tsanani a tsakanin uwa da ɗan.

"Kadaina damuwa pls babu abin da zai same ta, kuma sam ba laifinka ba ne, tambaya ce kai ma ta arashin sani, so abin ya bata shock dayawa shiyasa ta faɗi, amma ba wani isue bane, ka kwantar da hankalinka, kasan dai idan ta farka taganka a wannan yanayin sam baza taji daɗi ba, kasandai ta damu da kai ko, wallahi bata son abin da zai taɓaka, kuma tsaye ta ke akanka, akwai ranar da na farka cikin dare sai naji motsi, harna ɗauki gun ɗina na fito, amma abin mamaki sai na taras da ita ta na laɓe kamar marar gaskiya, bin bayanta na yi dan ganin ni takewa sanɗa sai na taras ashe kai tazo dubawa, ka na barci ta zo ta shafa kanka ahankali na tofa maka addu'a fuskarta yalwace da fara'a, ina tsaka da mamakinta naga ta juya ta koma ɗakin Hajjo, daga ranar na ɗauki yarda 100% na damƙa ma ta, ban san mi ƙaddara zata wankar nan gaba a tsakaninku ba, amma nasan muddin ka na tare da ita, komi zai zo maka da sauƙi, nasan ba zata taɓa barin rayuwarka ta shiga cikin garari ba."

Papah na aje maganar Mommy wacce ta ɗaura kaina akan cinyoyinta ta na kuka kashirɓan ta shiga karkaɗa kai alamun maganar Papah nakan hanya.

"Tsakanina da Allah labarin baiwar Allarnan ya girgiza ni, duk da banji tsakiya da ƙarshe ba, na tausaya ma ta, da alama za ta shiga cikin garari duba da yanda matar mahaifinta ta tuburu taƙi ɗaukarta tun ta na tsumman jarintaka, ga yarinyar da shiga rai, ga nutsuwa da addini, uwa uba sanin yakama, na daɗe banga yarinya me wayo da daɗin zama irinta.....

Bata ƙarasa faɗar hakan ba nai wani irin juyi gami da miƙa, ina gurnani kamar bijimar zakanya, wuyana ya jure kefe, bakina ya karkace ya dinga zubar da yawo, yatsuna suka dangane da tafukan hannunawana kakam, ƙafafuwana suka bandare kamar me cutar sikila, a hankali wani irin sanyi ya fara mamaye ɗakin, nan da nan bakunan su Hajjo suka hau maƙyarƙyata kamar waɗanda ke ciki freezar, a hankali Mommy ta fara jin wani irin sanyi na mamaye ƙasan ƙafafuwanta, dubawar da zatai sai ta ga ruwa fari tas na ɓullowa daga ƙasa, kamin ta yi wani abu, tuni ruwan ya fara gangara ko ina yana mamaye ɗakin, firfito da idanuwa su Hajjo suka yi, cike da kiɗima suka hau miƙewa su na ja da baya a fitgice, cikin abin da bai haure minti ɗaya jal ba, ruwa ya mamaye ɗakin baki ɗaya, haka su Papah suka tsaya kasa idanuwa cike da tsoro da mamaki wanda ya daskarar da su, kam Mommy ta hiƙe rumtsatsun idanuwana amma sai da na kubce daga gare ta, haka na dinga yawo asaman ruwan kamar me mirgina bisa ruwa, bakuna a buɗe suka shiga kallona kwance mala-male, amma babu me ƙatfin gwuiwar tashi daga inda ya ke, dan tuwan sun kai wajen kafaɗunsu, wani ƙarin abin mamakin bai wuce yanda ruwan ya kewaye har Papah ba amma sam bai taɓa Fauzan da ke kwance idanu a waje ba, iya Mommy, Sulaima, Hajjo da Papah kawai ruwan suka mamaye.

A duniyar suman da na yi kuma, Zubydiyyace ta bayyana agare ni ta na shafa gashin kaina cike da kulawa, yayin da ta ke fesomin ruwa daga bakinta irinna Jinnu ta na wankemin damuwar da ni ke ciki, ba ta daina ba sai da ta gamsu dan kanta, sannan ta kwantar da ni tare da juya baya, nan take ta ɓace ɓat.

A daidai lokacin ne kuma ruwan ya fara macewa ɓat kamar bai taɓa wanzuwa ba, nan take na dinga saukowa zuwa inda na tashi wato kan cinyar Mommy, lokacin da jikina na dangane da kan ƙasa nan take ruwan ya idasa ɓacewa, wajen ya bushe yakoma yanda ya ke a farko, kamar wani abu wai shi ruwa bai taɓa wanzuwa a wajenba.

A bin mamaki, a maimakon Mommy ta tsorata da ni, sai ta dake gyara zaman kaina a jikinta ta na tofamin addu'a, idonta fal da hawaye.

FATEEMA ABBAS.....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTE 36

بسم الله الرحمن الرحيم.

Ba tare da ta share hawayen fuskarta ba, haka ta sake jan motar ta na kuka kashirɓan,hawaye sun yi face-face akan kumatunta, ba komi ya sakata juyawa ta koma gidan Lawan ba, sai dan ta nutsu ta sake tunani akan hanyoyin da za ta bi wajen gyara ɓarnar da ta tabka ga aminiya kuma ƙawarta wacce sukai shaƙuwa taban mamaki, za ta koma ne dan nunawa Lawan yanzu wannan jinjirin Zaki wanda ya horar ya girma, kuma zai fara farauta takan wanda ya reneshi ya koyar da shi farautar, za ta nuna ma shi tuntuɗon da yai ma ta tahaye katangar mugunta har takai can ƙoli, yanzu ko yayi shi ba lallai ya iya haye koda rabin katangar ba bare har yakamota, zuciyarta ta bushe kamar ƙodagon goruba wanda aka jima da jefarwa a tsakar fili yai kwana da kwanaki harya bushe ƙayau, yanzu ne take jin dolene ta tashi tsaye wajen nunawa Lawan ya yi kaɗan ya juyata kp saka ta aikin son zuciya da mugunta, dana sanin aurenshi fal ranta, ta yi Allah wadai da sakaryar zuciyarya wacce ta kasance me rauni wajen ɗaukar ƙaddar, tabbas danasani ƙeyace, kuma ta na bayan kai, da tunani iri-iri taiwa ƙayatacciyar unguwarsu tsinke, kai tsaye ta nufi tsalelen gidan Lawan me kamada aljannar duniya, sai de yanzu a idanuwanta kallon baƙin gida ta ke mashi, wanda aka sabauta rayuwar bayin Allah waɗanda basu ji ba basu gani ba, dan kawai a mallake shi, rufe idonta ta yi tare da danna horn me ƙara da cika kunne, a gigice megadinsu ya fito ya wangale get ɗin, da wani irin gudu Fateema Abbas ta shiga gidan, ko parking ba daidai ta yi shi ba dan sai da ta daki flowers, fuska babu annuri haka ta fito ta tunkari shiga ciki.

Lawan wanda ke cikin matsanancin tashin hankali jin dirar mota ya saka shi saurin hankaɗe labule, aiko yai kyakkyawan gani dama bai daɗe da ɗaukar mota ya yawata ba ko zai ga Fateemar sai kuma ga ta ta dawo da ƙafafuwanta, lokacin da ta dazo gibtawa ta gabanshi ɗaure fuska ta yi tare da galla ma shi wa ta iriyar baƙar harara, sannan ta ja tsaki tai hanyar bed room ɗinta.

"Dakata Fateema, daga ina kike?."

Lawan ya daka ma ta tsaya me rikitarwa, amma ga mamakinshi sai yaga ta sake ɗauke kai ta wuce abinta, ranshi ne ya linku a ɓaci, inda yabi bayanta ya na ƙissima yanda zai yi laga-laga da ita, tunda ita tsagera ce, da shigarshi ɗakin ya nufeta gadan-gadan, sai de abin da yaso ya sumar da shi bai wuce yanda yaga ko ajikinta ta nuna jin tsoron wanzuwarshi a wajenba, sakamakon baya idan tasan tayi laifi ya zo hukunta ta take kuka gami da roƙonshi harma da bada haƙuri, wa ta iriyar hankaɗawa yai ma ta sai kanta ya daku da kan bed, amma baiwar Allarnan ko ƙara ba ta yi ba bare razana, ɓacin rai ne ya ƙule Lawan nan take ya kwance belt ɗin da ke jikinshi yabita saman gadon ya dinga labta ma ta shi kamar ya na dambe da ƙato kamar shi, wani azababen taurin kai Fateema ta aro ta yafa, dan kuwa in banda kaucewa dukan babu abin da take, ko hawaye ba ta nabu damar fitowa daga idonta ba, wani ƙarin ɓacin rai ne ya baibaye Lawan, ginin yanda ya naɗe hannu ya na jibkarta kamar Allah ya aiko shi amma ta wani dake kamar ba dukanta yake ba, yadda belt ɗin yayi tare da ficewa azafafe, sai da Fateema ta tabbatar da ya fice sannan ta rarrafa ta rufe ƙofa ta dawo kan gado ta dinga birgima tare da soshe-soshe ta na kuka marar sauti, ba ƙarya da daku yanda ya kamata dan ga shatin belt nan ya fito ruɗu-ruɗu a jikinta.

AGEGE

Sheƙeƙe Abba ke kallon Hashim wanda ya saki baki ya na bawa Mama labari akan kuɗin da Alhaji Abdallah ya bayar Million biyar abawa yace abawa Maman Mubeena.

A kaikace Mama ta rinƙa aunawa Abba muguwar harara, wacce ta saka yasha jinin jikinshi, amma ya ƙudiri aniyar sai yaci ƙaniyar Hashimu idan ya fito.

"Wai ni wannan surutun na banza da wofi da kake yi na uwar minene, haba ayi mutum ba katsari ya zauna yai ta faɗin abin da ba'a tambayeshi ba, bana hanaka irin wannan surutun da ba." Abba ya faɗi ya na zarewa Yaya Hashim jajayen ƙananun idanuwanshi.

"Abba labarin ɗiyarta fa nike ba ta, kuma ai ita ta tambaye ni ya ya Mubeenar ta ke, shine nike bata labari ko Mama." Yaya Hashim ya ƙare da tambayar Mamar dan yasan halin Abba tsaf zai korashi.

"Kai rabu da wannan Abban naku, cigaba da bani labarin ƴa ta." Mama ta faɗi ta na jefawa Abba hararar da ke hautsina ƴan cikinshi.

"Kai Hashimu taso rabu da Halima da hirarta akan Mubeena wacce ba ta ƙarewa, taso in aikeka kasuwa ka sayomin abu."

Abba ya faɗi ya na ɗaure fuska cike da bada umurni.

Dariya Yaya Hashim ke dannewa, dan ya na

7 / 8