ZAFIN WUTA

Author :  MARYAM STAR Category :  Love

Chapter   2 / 8

3K to 6K   out of 23.3K words

Sadiya, cikin dabara Lawan ya janyo wayarshi ya danna number da aka yi save da Babbar giwa ya rubuta "DONE👍." yai sending a daidai lokacin da ya isa bakin get ɗin gidan Alhaji Umar,horn ya buɗe Me gadi ya wangale mashi get ya shiga, jikin Alhaji Umar in banda rawa babu abin da yake yi, a haka Lawan ya taimaka ma shi ya shigarda shi har cikin gidan, sannan ya zauna parlour ya na jiran ya fito.

Kwance male-male ya iske Sadiya, babu abin da ke motsi a jikinta sai idonta da ke tsiyayarda hawaye, da kyar ta miƙa mashi hannunta ya kama ya soma ƙoƙarin tada ita zaune amma abin ya gagara dan shima duk a ruɗe ya ke, sulalewa kawai ya yi ya zauna tare da tallafo ta jikinshi, da raunanniyar murya yai amfani wajen faɗin.

"Sadiyanah! dan Allah ki faɗa min mike damunki, please bazan iya jure ganinki a haka ba, baki da lafiya ne ko wani abu ya faru?." Ya jero ma ta tambayar zuciyarshi na sake tsinkewa, musamman da yakai dubanshi cikin ɗakin yaga yanda ya harmutse sannan babban abin da ya dugunzuma nutsuwarshi bai wuce yanda baiga Babynsu ba akan baby bed ɗinta, da mugun sauri ya tashi tsaye a ɗimauce ya na faɗin.

"Sadiya ina my Baby? karkice min wani abu ne ya taɓa min ita." Yai maganar yana girgiza ma ta kai wani irin dunƙulelen ƙaton tashin hankali da fatgaba na mamaye shi.

" Sai na faɗa maka Umar, kayi wani abu please, wallahi ina son Babynah, bazan iya rayuwa babu ita ba, ka yi wani abu a kai tun kafin mu rasa ta."

Dawowa da baya yai ya wani damƙi hannunta da ƙarfi cikin ficewar hayyaci ya ce.

"Mi kike nufi wai Sadiya? ban fahimce ki ba, ina yarinyata abin ƙaunata, fatan dai kin riƙe amanar da na baki ba ki bari wani abu ya taɓamin ita ba, zan iya jure komi amma bazan iya jure ganin wani abu ya same ta ba, saboda ita nata so me tsanani, da dukkan zuciyata nike son MUBARAKA."

Yai maganar murmushi da kuka na kubce mashi lokaci ɗaya, still yana riƙe da Sadiya wacce zuciyarta ke barazanar tarwatsewa saboda tashin hankali.....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK TREE 3

CHAPTER 21

بسم الله الرحمن الرحيم

"Ka yafemin Umar, wallahi bada son raina hakan ta faru ba, hasalima duk son da kakewa MUBARAKA bai kai kwatar wanda nike mata ba, tun lokacin da take kwance a cikin cikina nike jin tsananin ƙaunarta, nasha tashi cikin dare idan kayi barci in zauna ni kaɗai ina surutu da cikin jikina, a duk lokacin da zata yi juyi a cikina sai ta juya min da tarin ƙaunarta, ita ɗin farin cikina ce, sai de ƙaddarar da take baibaye a rayuwarta ta shiga tsakanin ƙauna uwa da ƴa, da ace mutuwa Mubaraka ta yi da bazan ɗaga hankalina har haka ba, ko babu komi nasan bata raye, amma mi kake tunanin zan ji idan aka ce ƴa ta na raye amma bama tare waje ɗaya, mi kake tunanin zan ji idan akace sacemin ƴarda har yanzu ban gama warkewa daga zafin naƙudarta ba, mi kake tunanin zanji idan aka sacemin ƴata ina tsaka da murnar samunta, Umar ina jin rayuwata ta zo ƙarshe, ina jin zuciyata na gab da tarwatsewa, abin yamin nauyi, bazan ɗauka ba, Umar ka tashi ka je ka nemo min ƴata duk inda ta ke a faɗin duniyarnan, Umar ka je ka nemomin azzaluminda ya raɓa ƙaunar uwa da ƴa tun kafin uwar ta gama warkewa daga zafin ciwon naƙuda me raɗaɗi." tana gama faɗin gaka ta sulale a wajen a sume, yayinda Alhaji Umar ke furta.

"In nemo maki Mubaraka, saceta aka yi kenan! no ba haka ba ne babu wanda keda wannan zarrar da har zai iya sace min kyakkyawae yarinyata abar ƙaunata." sai kuma ya fashe da dariya lokaci ɗaya ga kuka ya na yi, haka ya shiga jijjiga Sadiya yana sambatu cikin ficewar hayyaci, ɗaukar Sadiya yayi cak ya fice da ita cikin mawuyacin yanayi, da sauri Lawan ya tareshi ganin yanda ya fito a birkice yana kuka da dariya lokaci ɗaya, taimaka mashi yayi suka fice tare da saka Sadiya cikin mota, Lawan ya shiga mazaunin driver ya ja motar da mugun gudu, tambayar Alhaji Umar abin da ke faruwa yayi amma ina sam ya fice daga hayyacinsa, sai surutai da sambatu maras ma'ana yake.

Muhammad Dikko da maƙarrabansa ne zaune a cikin wani baƙin ɗaki, wanda ke kewaye da wasu irin tarkace babu kyaun gani.

Wa ni ƙasurgumin zindiƙin arnen boka ne zaune bisa iska, gabanshi idanuwa ne kamar na mutum, sai kuma zuciya wacce ke ta motsi tana harbawa, alama yayi akan wani ya matso, da sauri Mas'ud wanda sukewa laƙani da cinnaka baka san na gida ba, ya matsa, mika mashi wa ta allura wace kanta keci da wuta bokan yayi tare da yi mashi nuni akan ya caccaka bisa wannan zuciyar, cike da rashin imani Cinnaka ya amshi alluwar wacce tai zafi zau ya dinga burmawa a zuciyar har sai da tai rami tsokar ta zuganye, sannan ya dakata yana sharce gumin da ya tsatstsafo mashi saboda zafin allurar, sake miƙo mashi wani abu me kama da guduwa amma ɗan ƙarami bokan yayi, ya kuma yi mashi alama akan ya buga akan idon, nan take Cinnaka ya daddage iya ƙarfinshi ya tallarawa idanuwan mumunan duka da wannan gudumar, nan take suka fashe wani farin ruwa ya shiga fitowa, sake jinjina ma shi boka yayi sannan ya daidaita zamanshi akan iskan ya fara magana cikin amo marar daɗin saurare.

"Anyi aiki cikin nasara, daga yau ranakun taɓewa sun soma a cikin rayuwar wanda akaiwa aikin, kamar yanda wanna idon ya fashe ya zama ruwa haka idanuwanshi zasu dunga zubda ruwan hawaye babu tsaitsayawa, nan gaba kaɗan zai makance gaba ɗaya zai daina gani, sannan kuma wannan zuciyar da kuke gani, zuciyarshi ce data matarshi, dan itama aikin ya shafeta saboda zuciyarsu kusan ɗaya a ɗaiɗaikun abubuwane suka banbanta, muddin kuka kawar da jininsa a doran ƙasa ta tofa babu shakka lokacin ɗaukakarku yazo, zaku shahara aduniya gaba ɗaya, zakuyi farin jini sosai a wajen jama'a, sannan kuma zaku shafe tarihin rayuwar shi Umar ɗin za'a manta da shi kwata-kwata, kudai tabbatar da kun kawar da jininsa kar ku kuskura kubar ƙwanshi ya rayu a doron ƙasa, muddin hakan ta kasance tofa akwai ƙalibale babba anan gaba, ku tashi ku tafi."......✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTER 23

بسم الله الرحمن الرحيم.

Babu ɓata lokaci duk suka fice daga ɗakin su na maida numfarfashi, in banda wari da ƙarni marar daɗi babu abin da ɗakin ke yi, amma dayake hausa sunce ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komi yake ba.

A daidai lokacin da Cinnaka ke caka allura jikin zuciyoyin bayin Allah, su kuma su na asibiti kwance cikin matsanancin hali, haka sukaita aman jini guda-guda, likitoci mai zarya suke a kansu ganin yanda lokaci ɗaya suka sake birkicewa, an ɗauki lokaci kafin a samu a tsaida aman jinin, lokacin da hannun likitan ya sauka akan zuciyar Sadiya, wacce ke bugawa ba daidai ba, da wani irin arnen sauri ya janye hannunshi ya ja da baya ciki da firgici, tsayawa abokan aikinshi sukai su na kallonshi tare da tambayarshi lo lafiya. "Anya kuwa waɗanan mutanen zasu rayu, zafi me kama da ZAFIN WUTA naji a kan zukatansu, wani ya taɓa ya ji ko nine naji ba daidai ba." Likitan ya faɗi ya na girgiza kai.

Ɗaya daga cikin masu taimaka mashi ne ta matsa cike da iya yi ta kai hannunta akan zuciyar Umar nan take ta kwalla ƙara gami da ja baya tana yarfe hannu, cike da jimami sukai musu iya taimakon da zasu iya yi mashi, bayan sun fito ne likita ya nemi wanda ya kawosu wato Lawan wanda ya kasa ya tsare yaƙi tafiya saboda kar ya tafi a samu matsala wani yazo ya rusa musu aiki, bayan ya gama jin bayanan likita ya wani marairace kamar dagaske abin ya taɓa shi, ya nemi idan babu damuwa a sallamesu kawai zasu koma gida su nemi na islamic tun da likitan da kanshi ya bada shawar a nemi na gida dan sudai sunyi iyakar ƙoƙarinsu amma basu gano komi ba, haka Lawan ya tarkatosu cikin mawuyacin hali yayi gida da su, masu aiki ne suka taimaka mashi wajen shiga da su, ananne ya lalibo number Alhaji Abbas ya sanar da shi halin da Sadiya da Alhaji Umar ke ciki, cike da tashin hankali Alhaji Abbas ya nufo garin Abuja afu jajan, isowarshi yayi daidai da zuwan iyayen Umar wanda suma Lawan yaki ya sanar da su, nan suka duba yanayin jikin ƴaƴannasu, sai de hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin irin halin da yaran nasu ke ciki, musamman Alhaji Abbas wanda yake matsanancin ƙaunar Sadiya, su na zaune jigum kowanensu na addu'a a cikin ranshi.

Bayan Alhaji Umar ya farka Sadiya ma ta farka, ganin mahaifinta ya sanya ta rushe da matsanancin kuka ta na bashi labarin an sace ma ta yara, dan bayan an sace jinjira Mubaraka babu jimawa driver ya je ɗauko Miemie a school nanne aka tabbatar mashi ai anje an ɗauketa, bai gusa daga wajen ba gudun zargi ko samun matsala, ya nemi lambar Sir Umar amma bata shiga, hakan ya saka ya nemi ta Lawan ya sanar da shi halin da ake ciki, lokacin kuma su Alhaji Umar na asibiti cikin mawuyacin hali, da wannan damar yai amfani wajen ɓatar da duk wata shaida da zata bayyana wanda ya saci ƴaƴan Alhaji Umar, a ranshi yana jinjina ƙoƙarin Fateema Abbas da har ta iya sace yaran cikin ƙanƙanin lokaci, ba tare da samun wa ta matsala ba.

Alhaji Abbas da Alhaji Ibrahim ne sukai tsayin daka tare da saka jami'ai binciko wanda ya sace yara, bayan farkowar Sadiya ta basu labarin halin da ake ciki, ita kuma Fateema Abbas tana can kan hanya ta na zullumi kar a ganota ta shiga uku, musamman Lawan wan da ta sanar da shi ta aikata aikin da ya saka ta, alhalin ba gaskiya ba ne.

Sai da marice sosai ta isa cikin garin Abuja babu ɓata lokaci ta nufi gidanta amma sai ta shiga ta ƙofar can baya wacce Lawan ya yi saboda zuwan ubayen gidanshi dan kawar da idon jama'a.

Sai bayan ta yi wanka ta huta ne ta fito tare da nufar wajen me gadi ta kai ma shi abincin dare, yai mamaki ganinta ta fito daga gida dan shi dai yasan ta fita, amma sanin akwai wata ƙogar ya saka shi saurin kawar da tunanin ya amshi abincinshi.

Alhaji Umar tun da ya farko idanuwanshi ke faman zubarda ruwan hawaye babu tsaitsayawa, sannan lokaci zuwa lokaci yakan yi aman jini, abin gwanin ban tausayi, tun manya na yi ma shi nahisa akan yayi haƙuri ya fawwalama Allah komi, har dai suka gane bayin kanshi bane, dan ko barci ya ke hawaye ke tsiyayowa daga idanuwanshi, wannan ya saka Alhaji Ibrahim kaishi asibitoci mabanbanta, amma duk inda aka je maganar ɗaya ce, ciwonshi ba na asibiti bane, hakan ya saka aka koma amso ma shi taimako wajen malaman islamic, amma da yake Lawan munafuki na tare da shi sai yasan yanda yayi ya sace maganinshi ya aje ma shi na wajen boka, ko kuma ya ciyar da shi da kanshi, Lawan bai kyale Alhaji Umar ba sai da ya tabbatar da ya gama lalata rayuwarshi ta hanyar bashi maganin bokansu harda na disashe farin jini, sannan kuma sai da ya durƙusar da kasuwancin shi sosai ya tafka ma shi manyan asarori sannan ya rabu da shi, bayan ya sanar da duniya a ɓoye cewa wai Alhaji Umar ya koma ɗan shan jini, shine ya sadaukar da ƴaƴanshi wajen dodon tsafi dan yayi arziki, aifa nan jama'a aka dinga aibata shi tare da yi mashi tofin Allah tsine, sosai hankalin Sadiya ya dugunzuma wajen tashi, ba ita kaɗai ba, duk wanda yasan Alhaji Umar kuma yake zaune da shi tsakani da Allah sai hankalinshi ya tashi da jin wannan maganar.

Ana haka ne wa ta rana Lawan ya samu Sadiya akan yana so ta taimaka ta biya ma shi buƙatarsa tun da mijinta yanzu shi da babu duk ɗaya, tun da ba cikakkiyar lafiyace da shi ba, sannan bugu da ƙari yanzu babu wani abin da za ta mora a wajenshi ya zama kingi, a ranar kuma Malam ya zo gidan a ɓoye ya bawa Alhaji Umar wani magani bada sanin Sadiya ba, hakan ya saka jikinshi yai sauƙi sosai, har ya iya tashi ya yawata cikin gidan, bayan ya dawo ne ya ji abinda Lawan ke faɗawa Sadiya, bai san akwai sauran ƙarfi a jikinshi ba sai lokacin, dan zuwa yayi ya rufe shi da duka Sadiyama ta taya shi, sukai mai lillis sannan Alhaji Umar ya janyeshi sai huci da zubar hawaye ya ke, da kyar cikon in ina yaiwa Lawan kashedin kar ya sake ganinshi a gidanshi, sosai Sadiya tai farin ciki ganin yayi magana, dan ya ɗauki wattani masu tsawo baiyi magana ba.

CI GABAN LABARI

Share hawayen da suka ɓata ma ta fuska ta yi, sannan ta tashi ta ɗauki ƴaƴanta da keta faman kuka tun ɗazu, amma bata ji su ba saboda tayi nisa cikin tunani, bayan ta shayar da su abincinsu ta kwantar da su akan gado tare da tashi ta kirawo me kula da ƙofar ɗakin yaran sannan ta fice ta dubo masu aiki ko sungama, ta iske su na jere kayan abinci da alama sun gama, masu shara ma sun gama ko ina yai fes gwanin birgewa, sai ta koma ɗaki ta sake gyara fuskarta sannan ta koma ɗakin Alhaji Umar, zaune ta same shi a kan bed kanshi a ƙasa ya na kallon yatsun hannuwanshi, cikin sanyim jiki ta matsa kusa da shi ta zauna tare da kwantowa akan jikinshi, ajiyar zuciya me ƙarfi ya saki sannan ya ɗaga kanshi ya kalleta da jajayen ƙananun idanuwanshi, itama shi take kallo cike da tausayi, kulawa da tsantsar ƙaunar, sassanyan murmushi ta sakar ma shi, a mamakinta sai shima ya mayar ma ta, ɗag hannunta ta yi ta ɗaura shi akan fuskarshi tasharce ruwan hawayen da ke saukowa kamar an buɗe fanfo, idonta gai raurau kamar zata yi kuka, sai kuma ta saki murmushi tare da ƙara sharce hawayen da ke tsatsafo mashi ba tare da ta janye idonta a cikin nashi ba ta ce.

My ɗan Aljanna, yau insha Allah komi zai zo ƙarshe yanzu haka Malam ɗina nakan hanya, zai zo ya taimaka manah."

Still sai ya sake sakar ma ta murmushi, tare da shafa ɗan mitsilin bakinta da hannunshi, sannan ya zamo da kanta ya kwantar akan ciyyarshi sai ya juyar da kanshi gefe dan kar ya zuba ma ta ruwan hawayenshi a fuskarta....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

2 / 8