Author : MARYAM STAR Category : Love
Fauzan, wanda nike tunanin yayi barci, ƙafar ya buɗe idonshi jin na tsaya da bashi labarin kuma na janye hannuna daga kanshi wanda gashin ya harmutse kamar anyi sukuwa bisa shi.
"Daga nan mi ya faru, shin Iroro ya amince da auren Umma kokuwa?.
Please kici gaba dan Allah, ina so inji yanda aka kaya."
Lallausan murmushi na saki jin yace inci gaba, nayi zaton barci yake jin yayi shiru ni kuma ina ta zuba, ashe yana jina da alama kuma yana fahimtar labarin, buɗe baki na yi cikin ƙosawa na ce.
"zanci gaba amma gaskiya zan rage tsayin labarin zan baka shi a taƙaice idan ka yarda."
"Na amince." yai saurin furtawa tare da mayarda hannuwana akan sumar wai inci gaba, murmushi na yi tare da fara kitsa kan na shi sannan na ɗora da labarin.
"Bayan ankai ruwa da Baban Umma akan yayi haƙuri amma sai ya tubure tare da fashewa da matsananci kuka, hakan ya saka Iroro fito da duka kuɗaɗen da ke aljihunshi ya amince akan zai auri Umma duda bai shiryama hakan a yanzu ba, ɗaura auren aka yi anan cikin masallacin inda liman ya wakilci ango, Malam kuma yaiwa Umma wakilci, addu'ar zaman lafiya alhazawan sukaiwa Iroro tare da nasiha sannan suka yi ma shi ɗan ihsani.
Ko da Baban Umma ya koma gida da labarin ɗaura igiyoyin aure tsakanin Umma da iroro ya isa, Maman Umma sam bata ji daɗin hakan ba, amma ganin yanda Ummar ke murna da farin cikin mallakar sanyin idaniyarta sai taɗan saki ranta gami da yi musu addu'a.
Bayan kwana biyu Iroro ya turo dangin Lubabatu suka kawo ƴan tsirarun kayan lefe waɗanda suka haɗa mashi a matsayin gudunmuwa, gidan haya Iroro ya kamawa Umma a unguwar Tudun matawalle, suka tare da ƴan tsirarun kayan ɗaki.
Soyayyace ke gudana babu kama hanun yaro tsakanin ango da amarya, babu kunya Umma ta baje take zubawa Iroro zallar ruwan madarar soyayya, shikuma ya biye mata suka samawa kansu farin ciki.
Bayan shekara uku da yin auren Umma ta haifi yarinya mace wacce aka sakawa suna Sumayya, kuma ta na ɗauke da wani cikin har ya tsufa, a ɗan tsukin ne kuma Iroro ya samu aiki a Abuja inda yakewa wata hajiya Fateema jigilar kaya da motarshi, takan aikeshi garuruwa da dama dan ɗauko mata kayan da ta sarah ko zata tura don kasuwanci, sosai Iroro ke samun ƙatuwa da Hajiya Fateema Abbas, yanzu a wadace suke gudanar da rayuwarsu shi da iyalinsa, bayan Umma ta haife cikin jikinta, inda takuma samun ƙaruwar ƴa mace aka saka ma ta suna Habiba, watanni goma da haihuwarta sai ga Iroro kwatsam cikin wani dare ɗauke da kyakkyawar jinjira ya kawo wa Umma akan tahaɗa da Habiba ta shayar, nan tashiga tuhumarsa akan inda ya samo jinjira, sai yace ma ta dama ya na da wata matar kafin ita, shine yanzu ta haihu kuma Allah ya amshi ranta, nan yaga bala'in da bai taɓa ganiba domi tsalle Umma tai ta dire akan bazata ko taɓa jinjirar ba, sannan ta dinga auna ma shi nau'ika iri-iri na rashin mutunci, sosai suka faɗa inda ta zazzageshi akan dama amanarta yake ci yasan yana da aure shine bai taɓa gayamata ba kuma bai taɓa haɗata da matarba, nan ya nuna ma ta halin maza akan shifa ba shi yaganta yace yana so ba, ita ce ta liƙe ma shi har mahaifinta ya liƙa mashi aurenta badan yaso hakanba, sai kuma jikin Umma yai sanyi jin irin kallaman daya yaɓa ma ta, kyaleshi ta yi amma bata ko kalli inda jinjirar ta ke ba, ganin Umma nason ɓata mashi shiri sai ya nuna ma ta baƙar jakar da aka shaƙe tab da kuɗi,yayi ma ta bayani akan zasu bar Katsinan cikin daren zasu kama hanyar Legos, ganin yawan kuɗin yasaka ta amince dan sosai ya kwantar dakai yai ma ta daɗin baki da alƙawurra maras adadi, abinka ga zuciyar mace sai ta amince da shi nan tahau haɗa kayansu ita da yaranta, kasancewar Iroro nada son yara kusan komi ya iya na hidimarsu,sai tari shike yiwa su Sumayya wanka ko wanke fitsari harma da goyo, haka ya ari zanin Umma ya rangaɗa ƴar kyakkyawar jinjirar a bayanshi ya ɗaure tsam, kasancewar ba wani shaƙuwa sukai da mutane ba dan ko ƴan uwansu ba zuwa inda suke yake ba bare kuma Umma wacce sam bata da zumunci, hakan ya saka basuyiwa kowa sallama ba suka garƙame gidansu suka ɗauki hanya da kaya niƙi-niƙi....✍️LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK THREE 3
CHAPTE 33
بسم الله الرحمن الرحيم.
Gaf da asubahi suka isa cikin garin Legos, inda kai tsaye Iroro ya nufi wajen abokinshi driver wanda ke zaune a Legos shi da iyalanshi, sun samu tarba me kyau a wajen matarshi, kasancewar sun san da zuwanshi kuma ya faɗa mashi yana son gidan haya ko yaya yake idan akwai, a cikin daren aka sama mashi matsakaicin gida daidai rayuwar me mata ɗaya da yara, bayan sun yi sallar asuba suka je ganin gidan, sai kawai Iroro ya yanke shawarar siyen gidan kawai tunda ba wani tsada yayi ba, babu ɓata lokaci cinikin gidan ya faɗa aka siyar mushi, a gaggauce suka koma gidan dan har lokacin Umma bata yarda ta karɓi ji jirarba, sai ita matar abokinshi Suwaiba itace ta amshi jinjirar wacce har lokacin ke barcin wahala, wanka taiwa jinjirar tare da bata madarar jajirarai, sai ta sake kwantar da jinjirar, ba ta farka ba sai da gari yai haske sosai, lokacin kuma Iroro ya gama kwashe kayansu tsab ya tsauna a mota yakai sabon gidan dakanshi ya jire komi tsab, godiyar yaiwa matar abokinshi sannan ya bata kuɗi masu ɗan kauri ladar reno, aifa nan Umma ta sake ƙuluwa tare da ƙara jin tsanar jinjirar, musamman yanda ta ƙare ma ta kallo tsaf ta ga irin baiwar kyau da jinjirar ke da shi, sai ta ce aranta anya kuwa ba ɗiyar shegiya Iroro ya haifa ba da matan banza a wajen, nan take ta amince da hakan musamman da kyawun yarinyar yai yawa, sai ta ce ai ƴaƴan shegu dama kyaune da su, kwanan iroro biyu a Legos, zuwa lokacin ya sake sabawa da jinjirarshi shike ma ta komi, dayake baida matsalar kuɗi hakan ya saka baya futa ko nan da can sai idan ta kama, fushi me tsanani Umma ta ɗauka da Iroro, ko magana tabar yarda ta haɗasu bare yaga fuskar da zai saka ta aiki akan jinjirar.
A na cikin haka ne Allah ya haɗa shi da wacce tazama sanyin idaniyarshi wato Halima matar marigayi Usman, sun haɗu ne a kan hanya wasu ɓata gari suka biyota zasu kwace ma ta mota, anan ne dabancin Iroro ya motsa ya shiga fatattakarsu dan dama da wuƙarshi ya ke yawo soke a bayan wando, ganin irin taimakon da yai ma ta yasaka ta ji daɗi har ta gayyace shi gidansu ta haɗa shi da mahaifinta malam Sa'idu, nan shima ya yaba da ƙoƙarin da Iroron ya yi wajen ceton ran ƴarshi, bayan kwana biyu da fatuwar hakan ƴan dabannan da yake sun bi bayan Halima suka far musu cikin dare suka hau sararsu har saida suka kashe rai biyu bayan sun jigata malam Sa'idu da sara shi da Halima, ƴarta da mamanta suka kashe, sannan suka haɗa kan motar Halima da sauran ƴan canjin da ke akwai gidan suka ƙara gaba abinsu, sosai Halima tai kuka da ƙaddarar data sameta ta rasa ƴarta da mahaifiyarta, inda tana cikin jimami wa ta rana Iroro ya zo giftawa ta wajen unguwar sai ya biya gidan dan su gaisa, nan ne ya taradda labari marar daɗi, nan ya jajanta lamarin tare da yi musu gaisuwa, tun da Halima ta ɗaura idonta a kan jinjirar Iroro ta kamu da matsananciyar ƙaunar ƴar, inda batai nauyin baki ba wajen faɗawa Iroro yabarmata ita dan Allah za ta ɗebe ma ta kewar rashin ƴarta, nan ya sanar da ita labarin jinjirar tare da yi ma ta tayin aurenshi dan shidai tunda ya ɗaura idonshi akanta ya ji ya kamu da ƙaunarta, lokacin son yarinya ya rufe ma ta ido bata ja da nisa ba ta amince, dayake a gaban babanta akai komi nan take ya tara mutane suka shaida ɗaurin auren ya bawa Iroro amanarta, nan take iroro yabarwa Halima jinjirar ya koma gida da tsananin murna, ɗakin da ya aje kayanshi ya tattare ya saka aka gyarawa Halima harda yi ma ta sabon fenti, yanda yake rawar ƙafa sai wani shige da fice ya ke ya sanya Umma ɗaura alamar tambaya akanshi, amma dayake haushinshi take ji sai ta watsar da shi ta nuna kamar bata san yana yi ba ta cigaba da harkokinta.
Ana gobe Halima za ta tare ya sanar da Umma aure ya ƙara, kuma matar ta amince zata raini jinjirarshi yanzu haka ma har ta amshi yarinyar, aifa nan yaga yanda ake asalin hauka da bori dan tsalle tai ta dire akan bai isa yayi ma ta kishiyaba, ranar sai de barci ɓarawone ya saci Umma dan hauka tuburan taiwa Iroro akan sai de ya saki matar amma ba zata zauna da ita ba, nan yai ma ta jan ido ya fito ma ta a Iroronshi na baya tantagaryin ɗan taba me sara da suka, ganin yanda ya bauɗe zai shirka ma ta tsiya ya saka ta shafa ma shi lafiya amma da alwashi kala-kala a zuciyarta.
Washe gari aka kawo Halima da kayan ɗakinta, amma ɗakin yai kaɗan wasu abubuwan dayawa basu samu waje ba, hakan yasaka aka koma da su aka bar amarya da sabuwar jinjirarta."
Wani irin yunƙurawa Fauzan ya yi lokaci ɗaya, cikin ikon Allah sai gashi zaune da kanshi ba tare da taimakon komi ba, kafin in farfaɗo daga suman mamakin da nashiga ganin abin da yayi, tuni ya watsomin tambayoyin da suka sakana na kafe shi idanuwa ina kallo kamar na samu tv.
"Wai tsaya abin da ban gane ba, shin sagaske hasashen Umma daidai ne akan jinjirar koko, naji, idan dagaske ba ɗiyar shege ba ce to ina mahaifiyarta, duda na ji kince Iroro yacewa Umma yana da wa ta matar, amma miyasa bai nunawa kowa ita ba, koko itama auren bagatatan yazo ma shi kamar yanda na Halima da ita Ummar ya kasance, lallai Iroro ya tabbata me sa'a indai hakan ta kasance wannan irin aure-aure da yake yi babu shiri, gaskiya ya more."
Fauzan yai maganar ya na sakarmin tattausan murmushi.
Domin jin waɗanan amsoshi ku kasance da MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK THREE 3
CHAPTE 34
بسم الله الرحمن الرحيم.
Muƙut na haɗiye kakkauran yawu, yayinda wani ƙulluto ya tokare maƙogarona ya hana busashen yawun da nasamu da tattaroshi da kyar.
'Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un na".
Nashiga maimatawa fuskata ɗauke da tashin hankali, kallon Fauzan nike hawaye namin zirya akana fuska cikin shaƙewar murya na ce.
"Ƴar shege! ƴar shegefa kace, Yah Allahu ya Rahamanu, yah Fauzan kar kaimin haka, kana nufin ni ɗiyar shege ce, innalillahi." kafin in ƙarashe na zube yaraf sai gani na faɗo kasan tayis kaina ya gwaru da ƙasa, ji kake "timm, kwal". haka kaina ya daku sa bed side sannan dum light ya faɗo bisa ni, gaba ɗaya ji da gani na suka ɗauke lokaci ɗaya duniyar taimin shiru.
ABUJA.
SADIYA
Da wani irin gudu take taka ƙafafuwanta, bata ko kallon abin da ke gabanta, babban burinta bai wuce ta sada kanta da ɗan uwanta mafi soyuwa a gareta ba, wata iriyar runguma takaiwa Malam tana fashe mashi da kuka me ƙarfi, murmushi ƙawace akan fuskar Malam shima yarungumi ƴar Uwarsa cike dajin daɗin yanda ta taryeshi, sunkai minti biyar a haka, kamin cikin rarrashi ya janye jikinshi daga nata yana sakar mata murmushi gami da goge ma ta hawayen da take kamar ƙaramar yarinya, shidakanshi yaja hannunta zuwa ciki, tarbar bangirma da karammawa ƴan aikinta sukai ma shi, inda suka cikashi da abubuwanda zai buƙata da kuma haɗaɗɗen girkin da Hajiya Sadiya ta basu oder yi, har yagama cin abinci bata daina kuka ba, tana neman yafiya a wajenshi, shikuma ba ƙaramin daɗi yajiba ganin yanda ta sauko tagane gaskiya sannan tai nadamar abin da tai ma shi,sake gaisawa sukai, sai yai ma ta nasiha me ratsa jiki sannan ya faɗa ma ta shi dama bai riƙe araiba duda ya ji babu daɗi akan abin da tai masa, babu ɓata lokaci yai ma ta izinin kaishi wajen Alhaji Umar dan ya duba jikinshi, bayan ya duba shi nan yaga alamun sauƙi sosai, da alama maganin da yabada a ɓoye ana ma shi amfani da shi, zagewa yai wajen yi ma shi hayaƙin itatuwa ingatattu, sannan ya umurci Sadiya akan ta yi mashi wanka da wani ruwan Addu'a, sannan ya bada wani ruwan haɗi da magunguna akan a dinga bashi yana sha, ko kuma adinga yi mashi girki da shi, baya gama yi ma ta bayani akan magungunan nan ne suka shiga hirarsu ta ƴan uwantaka, basu suka tashi ba sai da akai kiran sallar azahar, shima bayan gama sallar sukayi lunch nan suka dasa da firar, cikin dabara Malam ke tambayarta akan yanda kasuwancin Alhaji Umar ke gudana, nan ta faɗa ma shi irin matsalolin da suke fuskanta, ga ƙarancin ma'aikata da masu saka hannun jari, jinjina kai kawai Malam yayi ba tare da yace komi ba yabar zancen sai kuma ya kamo na Lawan, nan ma Sadiya ta labarta mashi abin da ya faru tsakaninta da shi, da yanda yanzu sukai baram-baram, ta na tinanin fitar da hannu da Lawan yayi a fannin kasuwancin Mijinta shine ke barazanar tarwatse kasywancin, tunda gashinan sai manya asarori ake tabkawa, ga ƙaranci ma'aikata, ahankali sao saɓewa suke gudun kar a zargesu. nan Malam ya zauna yabawa ƴar uwarshi shawarar yanda za ta yi ta farfaɗo da kasuwar mijinta, a yanda ya tsara ma ta, zata zabtare kusan rabin ma'aikata ta canza mudu aiki ko muƙami, sannan akawo wasu sabbi masu amana da sanin aiki, idan aka farfaɗo da ma'aikatan daganan sai ta fara neman masu saka hannun jari, fuska faɗaɗe da murmushi Sadiya ta ce.
"Kumafa haka ne, gaskiya naso in cuci kaina dana nesanta kaina daga garaka ɗan uwa mafi kusanci da soyuwa a gareni, ina sake neman afuwarka, kayi yafiya ga wannan mararjin ƙanwar taka, ba zata sake mai maita kwatankwacin kuskure da son zuciyar danayi a baya ba, ina matuƙar jinkunya da danasanin aikata hakan, haƙiƙa ban kyautata agareka ba, ban nemeka ba sai da naga matsaloli sunyi min dabaibayi, haƙiƙa na ji daɗi da baka riƙeni ba, a zuciyarka, kuma ka amsa kirana cikin kulawa tare da barin dukkan abubuwan da kake ka zo ka sadu da ni kuma ka shige gaba wajen fara warware matsalolin da suka dabaibaye ni." sai kuka ya sake kubce ma ta.
"Idan akwai babban abin da na tsana a rayuwata, bai wuce ganin hawaye na zuba a fuskar ƴar uwata wacce nake bala'in ƙauna a duniyarnan, ganin hawaye a idonki na sanar da ni na gaza wajen baki kulawa, bana son kukanki Halimatu please ki daina, na yafe miki dukan abin da kikai min dama wanda za ki yimin nan gaba, niɗin ɗan uwanki ne me tsananin ƙaunarki, farin ciki nike da burin gani a kan kyakkyawar fuskarki