ZAFIN WUTA

Author :  MARYAM STAR Category :  Love

Chapter   1 / 8

1 to 3K   out of 23.3K words

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTER 18

بسم الله الرحمن الرحيم.

A cikin barcin ne yayi mafarkin ni da shi a wani fili wanda ke ɗauke da mutane mabanbanta, ya na kwance akan ciyata ni kuma ina shafa kanshi ina faɗa ma shi zafaffan kalaman soyayya.

Tun da na shiga ɗakin Hajjo na ɗane kan gadonta na duƙunƙune ina maida numfarfashi, wani irin yanayi me wuyar fassara na tsinci kaina, daga can ƙasan zuciyata ni ke jin wani irin nishaɗi da farin ciki, sannan uwa uba yai dai Fauzan ya yi min doguwar magana da muryarsa wacce ke bala'in burge ni, idan na tuno abin da yai min sai in sake ƙanƙame pillow ina jin wani yanayi na daban na sake lulluɓe ni, Hajjo ce ta shigo ɗakin ta ganni kwance ƙudundune ta yi tunanin ko bani jin daɗi sai ta koma, ashe Yaya Hashim ne Mommy ta saka aka kira dan mu gaisa, hakanan suka bashi haƙuri suka ce ya bari sai zuwa anjima idan na tashi, babu komi ya ce amma a zuciyarshi ya na jinjina lallai na samu duniya, wato yanzu har nakai matakin da idan ina barci babu wanda zai tashe ni sai na tashi da kaina.

ABUJA.

Yau tun da wuri Sadiya ta tashi, sai ta ke jinta wasai tun wayar da tayi da ɗan uwanta Malam jiya, ya tabbatar ma ta da yau zaizo da yardar Allah, hakan ya saka bayan ta tashi tayi wanka gami da shirya yaranta suka fito tsaf da su, sai ta fita zuwa sashen ƴan aiki ta basu umarnin abin da take so a girka, sannan ta saka masu shara suka gyara ma ta BQ, sannan ta dawo ta taimakawa Alhaji Umar ya shirya shima, bayan ta gama break fast ta ba Alhaji Umar sai ta kama hanunshi kamar ƙaramin yaro ta kaishi wajen babys ɗinta, nan ya shiga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya ya na musu wasa ya na hawaye, itama Sadiyar hawayen tausayi kanta da mijinta ne ke gangarowa daga fuskarta, ta na tuno ranar da Malam ke faɗa ma ta wasu maganganu masu muhimmanci amma ta saka ƙafa ta shure ba tare da yi duba da lamarinba, gani ta ke kamar ita ke da alhaki akan ciwon Alhaji Umar, tun da tun kafin faruwar matsalar ɗan uwanta Malam yai ma ta hannunka me sanda amma sai ta share, tunani ta lula me nisan gaske, nan take abin da ya faru a shekaru ashirin da ɗoriya ya shiga dawo ma ta.

FLASH BACK

"Halimatu ina so ki nutsu ki kalli batun da zanyi ma ki da idon basira, abin ya daɗe ya na damuna, da farko ban damu in sanar ma ki ba, amma yanzu naga ya dace ace kinsan da abin, kar kiga inata jan zancen da nisa ba wani abu bane ba face wasu mafarkai da suka addabi rayuwata, ana haskamin mijinki a cikin mawuyacin hali, sannan ina ganin wasu abubuwa na kewaye da shi tako ina su na ƙoƙarin cutar da shi, sai nike ganin kamar mahassada ne suka taso shi gaba, idan kikai duba da yanzu rayuwar ta lalace kowa kanshi ya sa ni, ƴan hassada da ganin ƙyashi su na iya yin komi wajen cimma wani buri ko ƙudirinsu."

Girgiza kai kawai Sadiya ta yi sannan ta ce. "Haba Malam wannan ai duk mafarki ne kawai ba lallai ya zama gaskiya ba, kuma dama ai dolene ko wane mutum ya fuskanci ƙalubale a rayuwa, musamman idan ya kasance maɗaukaki me dukiya, ni a ganina wannan ba wanj serious abu ba ne, kudai taya shi da addu'a dan a kwanannan za'a bayarda wa ta babbar kwangila kuma muna saka rai akan shi za'abawa kasancewarshi mutum me amana."

Duk yanda Malam ya so ya fahimtar da Sadiya sam taƙi fahimtar shi, sai kaucewa maganar ta ke, ita a ganinta babu wani abu akan irin mafarkin da ɗan uwanta ya bata labari yayi akan mijinta, kuma itama takanyi makamacin irin mafarki amma sam ba ta bawa abin muhimmanci, cike da damuwa Malam ya tafi amma yaso ko yaya ne ƙanwarshi Sadiya ta bashi dama yayi ma ta gamsashen bayani, bai jima ba ya tafi dan ya na da abubuwanda zai yi masu muhimmanci amma ya baro su ya taho wajenta sai dai kash, ita kuma ta kasa fahimtarshi tamaƙi ba shi damar yi ma ta gamsashen bayani. Bayan komawarshi da kwana biyu ya sake tuntuɓar Sadiya da maganar saboda ya sake yin mafarkan, amma dai jiya i yau, bata saurareshi ba sai ma nuna abar maganar kawai da tayi, Malam be karaya haka ya haɗo ruwan Zamzam wanda akai tofin Ayatushshifah a ciki, tare da ganyanyaki masu haɗe-haɗe na tsarin jiki, cikaken bayani ya yi ma ta akan yanda zatayi amfani da su, amma abin haushi da baƙin ciki Sadiya ta rufe ido ta nunawa Malam itafa bata wani yarda da irin waɗannan magungunanba, harda roƙonshi akan ya daina zuwa ma ta da irin waɗanan maganganun ita ta yarda da Allah, ta na da tabbacin babu abin da zai sameshi.

Ranar ran Malam ya ɓaci sosai harya yi zuciya yayi tafiyarsa daga gidan, daga nan ya daɗe bai sake waiwayarta ba har sai ranar da za ta haihu, shima ranar ya zo ne da niyyar yi ma ta sallama akan zai koma Saudiyya zai ƙaro karatu kan fanin islmic medicine, a ranar ne kuma akan hanyarshi ta zuwa aljana Zubidiyya ta biyo bayanshi, kasancewarta me tsananin son tsafta da ƙamshi, lokacin da ya je gidan ya taras da Alhaji Umar cikin yanayi na tsananin farin ciki, jinjirar da aka haifa mashi rungume a cikin hannunshi sai faman zabga ma ta murmushi da sumbata ya ke, zagayawa Zubudiyya ta yi ahankali na shafa fuskar jinjirar wacce ke barci tasha gayu abinta, a ranar ne Zubudiyya taga ƙullin da su Lawan suka shiryawa Alhaji Umar ta so ta aimaka mashi amma sai Allah bai nufa ba, hakan ya saka ta kasa ta tsare ta zauna kusa da jinjirar ta dan tasan shirin da aka shirya na kasheta, itace ta shiga jikin Fateema Abbas ta canza tsarinta ta hanyar sanya ma ta sanyi daga na jikinta, nan take ta saura mumunan tunaninta akan kashe jinjirar, Malam ya tafi yabarwa ƴar uwarsa sabuwar number wayarsa, wacce ya ce duk ranar da take buƙatar temako to ta nemeshi, tsawon shekaru kenan ba ta nemeshi ba amma shi yakan nemeta su gaisa, bai taɓa yi ma ta magana aka yanda yanzu take nuna halin ko in kula da shi ba, dukda abin na mashi ciwo sosai a rai, musamman yanzu da yaga sam ba ta wani yinshi sosai ba kamar baya ba, shi kuma kullum ƙara ƙaunarta ya ke dan har yanzu bayan mahaifanshi bai da abin da yake matuƙar so irin Sadiya.

...

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTER 19

بسم الله الرحمن الرحيم

Share hawayen da suka zubo ma ta tayi ta na kaico da yanda ta rufe ido taƙi ganin gaskiyar da ɗan uwanta me ƙaunarta ke gaya ma ta, tashi ta yi ta duba Alhaji Umar wanda ke zaune ya tasa photo a gaba ya na kallo ya na zubda hawaye, zaunawa kusa da shi ta yi tare da faɗin.

"Haƙiƙa sun yi nasarar cutar min da kai, sunyi nasarar kassaramin rayuwarka ta hanyar azabtar da kai da ƙaddarar da tunota ke zama kamar hura wuta me tsananin zafi a zukatanmu, bazan yafewa duk wanda ke da hannu wajen cutar min da kai ba, da sannu duk za su girbi abin da suka shuka, sai sun ɗanɗani ZAFIN WUTA me tsananin ƙuna, in sha Allah duk wanda ya cutar da mu da sannu zaiga sakayyar Allah, bazan taɓa yafewa ba." ta faɗi ta na ɗora kanta a jikin Alhaji Umar wanda ke tsiyayar hawaye kamar an buɗe fanfo, bai ce ma ta komi ba harta gaji ta daina kukan, izuwa yanzu haƙurinta ya ƙare sam batada juriyar shanye kukan da tunkuɗo kanshi ta ƙarfin tsiya, ƙarfin zuciyar da take da shi a da yanzu ya ɓace, ƙunci da damuwa sun bai baye rayuwarta, rabonta da samun farin ciki tun ranar da ta wayi gari babu ƴaƴanta a gabanta, rabonta da murmushi tun ranar da ƙaddarori mabanbanta suka doso rayuwar mijinta, sam ta manta da yanda ake murmushi sai de yaƙe, rabonta dayin murmushin farin ciki yau shekara ashirin da ɗoriya.

A hankali ta fara tariyo ranar da tai ƙaura da farin cikin duniya.

FLASH BACK.

"Sadiyata, ki tabbatar da kin kulamin da mu sweet doughter, idan so samu ne ki rufe gidan kibawa me gadi umurnin kar ya kuskura yabar kowa ya shigo ya takuramin Muby nah, yawan ɗauka da daƙunar da mutane ke mata ya saka yanzu harta fara duhu, ki shafa min kanta sannan ki yiwa ɗan ƴaramin bakinta kiss, ki ce da ita daga Daddynta, zan je shopping ni da Lawan zan yo ma ta babbar tsaraba wacce zata ji daɗinta sosai."

Daga can ɓangaren ta amsa da "Oh my god! haba Daddyn Babys wannan surutu haka, ni kasa na mance mi kace ca farko, Babynka dai gatanan kwance akan cinyata ta na barci, kuma ta ji duk abin da ka faɗi, ni yanzu wanka zan shiga dan yanzu Fateema Abbas tabar gidanan, idan na fito baka dawo ba zan kiraka inyi ma ka albishir da wani abu me daɗi."

Ƙittt ta datse kiran ta na kallon Babynsu wacce ke barci gwanin sha'awa ita kanta kyawun yarinyar na bata sha'awa, tana jin matsananciyar soyayyar yarinyarta wacce bata ji makamanciyarta ba lokacin da ta haifi Miemie, kiss ta mannawa ɗan mitsinin bakin jinjirar sannan ta tashi ta rage kayan jikinta ta ɗaura towel, sai da ta haɗa zazzafan ruwan wanka sannan ta sake fitowa ta ɗauki jinjirar ta na kallonta ta ɗaga ta sama fuskarta ƙunshe da murmushi ta ke faɗin. "Mubarakar mommahnta, Mommah ta na tsananin son ki, kece farin cikin mahaifanki, ni da Daddynki mu na tsananin ƙaunarku ke da ƴar uwarki Miemie." Tana gama faɗin hakan ta sake manna ma ta ƙis sannan ta shige toilet, amma bata rufo ƙofa ba.

Da tasan ƙaddarar da ke jiran gusawarta daga wajen da bata yarda tabar ƴarta a wajen ta shiga toilet ba, da wannan damar Fateema Abbas ta yi amfani wanda ta jima tana kallon uwa da ƴar ta ƙofar labulen window, cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ta shigo tare da saɓar jinjirar ta fice ta ƙofar baya wacce Lawan ya jima da samo key ɗinta wajen Alhaji Umar, cikin sa'a bata samu wa ta matsala ba wajen ficewa da jinjirar daga layin harta shiga mota, Zubudiyya na tare da jinjirar har lokacin ta na shafa kanta lokaci zuwa lokaci, dan sosai yarinyar ta shiga zuciyarta, kuma ta yi ƙudurin taimaka ma ta bakin gwargwado.

Hakanan Sadiya ta kashe shower tare da fitowa a hargitse, wa ta iriyar mummunar dokawa gabanta ya yi, yayinda zuciyarta ta doka da tsananin ƙarfi wanda ya zarta misali, cike da kyarmar jiki ta fara takowa tare da ware duka girman idanuwanta ta na neman inda zata hango jinjirarta, amma sai sake tabbatar ma ta majiyar ganinnta ke yi babu jinjira anan, yaraf ta zube akan dandamalin sassanyan tiyels, idanuwanta na ƙanƙancewa zuciyarta na matsewa waje ɗaya a cikin ƙirjinta, da ƙyar addu'a ta kuɓuto daga bakinta saboda shiga tashin hankali da ta yi, sake fita parlou ta yi ta dudduba ko wani ne ya shigo amma babu alamar mutum a wajen, komawa ta yi ta ziro hijabi sannan ta fito compound ta na ƙwallawa me gadi kira cike da tashin hankali.

"Baaaa,,,,,bab,,,,Baba dan Allah kaga wani ko wata ya shigo gidannan ko ya fita bayan fitar Hajiya Fateema matar Lawan." Tai tambayar cike da fatan ya ce ma ta ih Alhaji Umar ne ya shigo, sai de amsar da ya bata ta taka muhimmuyar rawa wajen tarwatse farin cikinta.

"Gaskiya Hajiya babu wanda ya shigo bayan fitar Hajiya Fateema, kuma babu wanda ya fita, dan hatta wannan yaron me ban ruwa ya jima da tafiya kusan sa'anni uku kenan da yake yace Babanshi ne babu lafiya shiyasa ya tafi da wuri."

Bata bari ya ƙarasa maganarba ta juya cikin tsananin tashin hankali, bed room ɗinta ta koma ta ta shiga hargitsashi ta na ɗage-ɗagen kayan wai tana neman jinjirarta, sai da ta hargitse ɗakin tas amma babu alamar mutum sam, sulalewa ƙasa ta yi wani irin bahagon kuka na kubce ma ta, da iya ƙarfin jiki da na zuciya ta ke kukan, ta ɗauki tsawon mintuna masu dama sannan ta tsahirta, kamar wacce aka mintsina haka na tashi du ta firgice, idanuwa sunyi jazur, fuskartama ta yi jawur musamman saman tsinin hancinta, sau bakwai ta na wuce number da take so ta kira amma idanuwanta sun ƙi bata damar ganin number, harta haƙura ta aje sai kuma ta sake shiga call long ɗin ta dannawa number da aka kurata last calling.

"Momman Babys, kin kasa haƙuri indawo shine kika kira ni ko, to ina gab da gida yanzu haka sannan kuma karki manta sa al....."

Maganarshi ta yanke lokacinda ya jiyo gunsheƙar kukan da Sadiya ta saki.

"Subahallahi!!!! Sadiya lafiyarki ƙalau kuwa, mi yake faruwa ne, waye babu lafiya, ko rasuwa aka yi...." Maganarshi ta yanke jin sautin muryarta cikin kuka tana faɗin.

"Shikenan Umar rayuwata tazo ƙarshe, na tabbatar da mutuwa zanyi bazan iya jurewa ba, dan Allah ko bayan na mutu ka taimaka ka nemo min ƴata kuma ka hukunta duk me hannu a cikin ɓatanta, nasan ba lallai in sake mintuna biyar cikakku da rai ba, ƙarshe rayuwata ya zo, ka yafe min mijina."

Ƙit ta yanke kiran tare da yanke jiki ta faɗi ƙasa dafe da saitin zuciyarta....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA



BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭

KUNCIN CUZIYA,💔

SADAUKARWA,💌

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY

MARYAM STAR ⭐⭐

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚







PAID BOOK 500 ONLY👌

BOOK THREE 3

CHAPTER 20.

بسم الله الرحمن الرحيم.

Da wani irin tashin hankali Alhaji Umar ya saki sitiyarin motar, a maimakon ya taka burki sai kawai ya shiga kiciniyar fita alhalin bai tsaida motar ba, da wani irin sauri Lawan yai wani mugun tsalle ya hankaɗa Alhaji Umar baya ya amshi tuƙin gabanshi na faɗuwa, saura kaɗan Alhaji Umar ya saka suyi accident, wani irin farin ciki ne ya baibaiye Lawan ganin yanda plan ɗinsu ya tafi daidai, ga Umar se kuka ya ke ya na sallati zuciyarshi na dokawa da tsananin sauri tashin hankali da ruɗun halin da ya ji muryar

1 / 8