KANWAR MAZA 1&2 BY By Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  Aisha Adam (Ayshercool) Category :  Romance

Chapter   99 / 128

294K to 297K   out of 382K words

saka tsohuwar mutane kuka, saboda ke baki san abun da ya dace ba?" Yayi maganar yana son ta yi magana, dan ya ji meya haWa su da su Fauziyya, dan ya san idan ya tambaye ta, yadda ta ?ule Win nan, ba zata gaya masa ba.

"Wallahi duk wadda ta kuma zuwa ta zageni, sai na rama, kayi zuciya ka mayar da ni gidanmu, sai ka tattaro su su dawo gidan nan su zauna, gida zan tafi dan ni ba banza ba ce, da za su din ga zagina ina jin su ba, me na yi musu? Nima ?anwar wasu ce, kuma suna sona, dan wallahi ko za su kasheni, suka zageni sai na rama, ita kuma baba uwani ta cigaba da yi mini sharri" ta yi maganar tare da shigewa toilet.

Har dare ta?i ko sake fitowa, dan ko abincin dare ba ta nema ba, ta yi kwanciyarta.

Sai da takawa ya nemi, Asiya da barira ya tambayesu abun da ya faru, amma suka ce ba su sani ba, baba Uwani ta hana su hawa saman, amma sun jiyo su Fauziyya suna zagin rumaisa tana ramawa.

Daga nan gidansu ya wuce, bai ko je sashin Ammi ba, ya nufi sashin Mummy.

Ya tarar da su gaba Wayansu, har da Mahmud da Mummy, da ru?ayya da Fauziyya, sai dai babu Samha.

Mummy na ganinsa ta ce "Ahh, takawa barka da wannan lokaci, ?araso mana, ya jikin naka, tun da na shiga ban sake zuwa ba, ashe ka samu sau?i".

Ya ce "Eh"

"Sabuwa, ?aro plates, a zubawa takawa abinci shi ma".

Ya girgiza kai ya ce "Na gode, Fauziyya"

Ta kalleshi ta ce "Na'am yaya"

"Kun je gidana Wazu?".

"Eh yaya mun je, zamu sake dubaka ne kuma baka nan, matarka ta yi mana rashin mutunci, har da zagin baba uwani".

Adam ya ce "Daga yanzu, idan har ba alkhairi ne zai kai ku gidana ba, kar ku sake zuwa, ina baku wannan sa?on ne har Samha, idan ma baku gaya mata ba, ni zan gaya mata. Kar ku sake zuwar mini gida ku ci mutuncin mata ta, ni na ajiyeta ba ita ta ajiye kanta ba, kuma ban aurota, dan ku je ku ci zarafinta ba, ita Aisha dama taku ce, kuma mai ha?uri ce. Wannan kuma tawa ce, sannan ba zata iya jure abun da Aisha ta jure ba, yarinya ce ba zan lamunci a saka mata tension depression ya kamata da ?uruciyarta ba".

Baki a sake Mummy ta ce "Yanzu matarka ka fifita a kan ?annenka, duk da sun gaya maka ta wula?anta su? Bayan kai suka je dubawa?".

"Mummy ko dabba na ajiye na ce nawa ne, bai kamata a je ci mutuncinsa ba, idan har ina da kima a idon su ba, balle Wan adam na ajiye, idan banda rashin girma, me zai saka su biye mata, tun da ba sa'arsu ba ce ba, na san rigimammiya ce, amma ba ta yi haka kurum, ku kiyaye, aje a ci mata mutunci ace mata ?waila, ko ba mace ba ce, ni a idona mace ce kamar kowa.? Dan haka Please allow her to enjoy her marital home. Ko ba ku yi zumunci da ita ba, ni na isheta, na san yadda nake bi da ita mu zauna lafiya"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Hmm, wannan dai kashedin na samha ne, zuwa aka yi a gaya mana ana son ta kenan".

Ya tashi yayi murmushi? ya ce "Ta cancanci hakan Mummy, a rashin Aisha ita ce uwar Wana, idan na bari aka wula?anta ta, ni aka yi wa, dan haka a kiyaye"

Mummy ta yi shiru, tana sa?a wani abu a ranta, lallai akwai ?ura ba ?ar kaWan ba, Samha tana ruwa, dan ba ta tunanin baba uwani na abun aka sakata yadda yakamata.

Mummy ta ce "Gaskiya ne, tayi rawar gani kam, ta cancanci a kula da ita. Duk da ka Soyewa duniya ita, da muhimmancin abun da tayi maka"

"Ni ta yi wa, ba duniya ba, dan haka ni yakamata na girmama abun da tayi mini".

Mahmud kuwa, ya kammala cin abincinsa, danna wayarsa kawai yake yi.
Har Adam ya wuce shi, ya dawo ya zauna a kusa da shi, yayi ?asa da muryarsa yadda shikaWai zai ji me yake cewa ya ce "Am warning you, stay away from my family, da Wana, da kuma matata"

Mahmud ya Wan kalli Adam ya ce "Ban ji zan iya ko Waya ba, ina son Wanka, ina girmama matarka, kasancewar tana girmamani, we are having a deal together, dan haka you should stay away from us"

Wani irin zafi maganganun sa, suka yi wa adam, amma ya shanye ya ce "Shikenan, idan ka ?i ji, ba ka ?i gani ba" ya tashi ya fice.

Mummy kasa zama tayi, ta tashi ta bar falon, Fauziyya kuma suka cigaba da caccakar rumaisa, suna bawa Mahmud labari.

Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu'a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi.

Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan.

Yau ya ji ?warin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa Waki, idak bai tashi ba ma, ta din ga ?wale-?wale kenan sai ya tashi ko baya so.
Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba.

Kai tsaye ya tafi Wakinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa.

"Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?"

"Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori"

"Dalla tashi ki shirya zan makara"

"Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka Wora mini laifi, kai ?annenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida" tayi maganar cikin tsan-tsar takaici.

"Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin zaSi mu rabu, abu ne mai sau?i, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki" saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice.

Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe.

A ransa ya ce "Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?".

Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara.

Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa ?ofar makaranta, ta buWe ?ofar motar ta Wau alawarta ta fice.

Yayi murmushi ya ce "Su mimi ba zuciya in dai a kan kwaWayi ne" tana jin sa a ranta ta ce "So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba".

Ana tashinsu ya je ya Waukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin daWin hakan nan, saboda yana Webe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir.

Ammi ta ce "Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?"

Rumaisa ta ce "Eh Ammi, sun je jiya da yamma"

"Ina fatan dai ba wata matsala"

Rumaisa ta ce "Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan"

Ammi ta yi murmushi tana dafa kafaWar ruma ta ce "Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya Soye abu. Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar. Babarsu ta zo Wazu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba ?an uwansa ba".

Rumaisa ta waro ido ta ce "Papan? Amma ni kuma jiya yayi mini wula?anci, suka Sata Waki wai ni zan gyara".

Ammi ta ce "Ki yi ha?uri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani"

"To Ammi in sha Allah"

Ammi kuwa daWi ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren.

"Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun ?i zuwa gidanmu".

Ammi ta ce "Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba".

Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita.

Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce "Ahh babar sabir, ?ar gidan amminta"

Ruma ta ce "Mama na tabattar kin daina so na gaba Waya, baki taSa zuwa gidana ba".

"Ai na san kina lafiya ne, ya Wan naki ya maigidan?"

"?ana lafiya ?alau, maigidan kuma mun yi faWa bama magana"

Mama ta ce "Kun yi faWa ba kwa magana saboda baki da hankali?"

Cikin sangarta ta ce "Mama faWa yake yi mini a kan abun da ba laifina ba"

"Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki faWa ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci, ?an uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki faWa sai ki daina yi masa magana? Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba? Kin ga ki kiyayeni".

"To mama kawai sai na bashi ha?uri"

"Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai Wa'a, tun da ke ba kya ji"

Rumaisa ta ce "Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai ?ara aure ba, daga ni shikenan".

"Kar ki canza hali, na fasa zuwa gidan naki ma, sai kin yi hankali"

Kan ta yi magana, mama ta katse wayarta, ruma ta ajiye wayar tana tura baki.
Tayi shiru tana nazarin maganar mama, ba ?arya duk abun da take so yana bata, ko bai amsa mata ba, za taga abun ya bata.

Kuma ga ammi ta ce ya je ya yi wa ?annensa faWa.

"Ai shikenan, zan daina fushin, amma ba zan bashi ha?uri ba"

Har yamma tana gidan Ammi, sai magariba, sannan takawa yayi waya, ya ce Sidi ya mayar da ita gida.

Yawan zuwan nan da take yi, ya sanya ba ta damu lallai, sai an bata sabir ba, saboda tana samun sha?uwa sosai da sosai tsakaninta da Sabir Win, da kuma Ammi, gashi akwai fahimta sosai tsakaninta da iman, sannan a hankali take ?ara sanin kan masarautar, dan wataran idan ammi za ta fita, binta take yi.

Tana tsaye tana ?o?arin shiga motar sidi, sai ga mahmud.

"Daughter, ina ta so mu haWu da ke"

"Ai ban san kana nan ba, da sai na nemeka".

"Kin san bana zuwa ko ina. Jiya mijinki ya zo sashinmu, yayi wa Mamana rashin kunya, saboda su Fauziyya sun je muku gida"

Rumaisa ta ce "Ai gara shi, kishiyar mamansa ya yi wa, wanda yayi wa maman sa fa"

"Ba wannan maganar muke yi ba, idan muna irin wannan maganar, raina zai iya Saci. Yanzu dai ina zaki?".

"Sidi ne zai kai ni gida".

"Duk an yi mini kashedin na fita harkarku, amma ba zan iya ba, Waukko mini Sabir sai na kai ki gidan, na dawo ni da shi"

Rumaisa ta ce "Babu lallai ammi ta bani shi, sai da ka zo mu je tare"

"Ina son yaron nan sosai daughter, mu je"

Tare suka koma Ammi ta din ga kallon Mahmud, Ruma ta gaya mata abun da ya ce, ammi ta ce "Banda abun sa ai shi ma Wan sa ne, Allah ya tsare"

Ruma ta yi ta murna, ta Wauke shi suka fita, Mahmud ya karSe shi, suka shiga motarsa suka tafi.

Nusaiba ta ce "Ammi, kina ganin babu wata, ko takawa ya zo yayi faWa?".

Ammi ta Wan yi shiru sannan ta ce "Yarinyar nan ta zarce duk yadda nake zato, ko da ba ta gaya mini ba, na san ?o?ari take ta sasanta tsakanin Adam da Mahmud, tun da ni na gagara yi, ban sani ba ko ita Allah ya sa ta iya, dan haka ba abun da zan iya, yi mata Addu'a, tare da goyon baya Wari bisa Wari"

Nusaiba ta ce "Ikon Allah, ammi kuma fa haka ne"

"Ku tayani addu'a, a dalilinta sau biyu Mahmud yana zuwa in da nake, in sha Allah ko bai dawo wurina gaba Waya ba, sai an samu daidaito tsakanin iyalina".

Nusaiba ta ce "Allah ya sa".

Har ?ofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy sa?o, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy.
Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir.

Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida.

Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba.

Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta taSa cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su karSa.

Cikin basarwa, ta tashi ta mi?a hannu za ta karSa, ya kalleta ya ce "Kin ci abinci ne?"

"Na ci a gida".

Ya ce "Dafo shayi cup biyu, ki sameni a Waki"

Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen.

Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya.

Ta ajiye cup da flaks Win, za ta fita ya ce "Zauna ki haWa mana"

Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta haWa tea cup biyu.
Gasashshen nama ne, da ?aton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba.

Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce "Can't you smile, or say thank you? Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki"

Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita.

"Zauna zamu yi magana".

Ta zauna tana lashe hannu. Ya Waukko tissue, ya goge mata hannun.

Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ?aro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar Win in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure".

"Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaWai?"

Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta"

"To sai in daina ganinka?".

"Kina son ki d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?inga gani na ne?"

Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka"

Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?"

Tayi dariya ta ce "Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi ha?uri.

Wani irin murmushi yayi, yana jin daWin jirar ta su.

Ya Wora hannunsa a kafaWarta, kamar ?awarsa ya ce "Ban ha?ura ba, fitsararki ta yi yawa, ha?urina ya kusa ?arewa"

Ita ma ta Wora hannu a kafaWarsa ta ce "Allah ya sa kar ha?urinka ya ?are, ai da ban taSa sanin kana da ha?uri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi"

"Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so"

Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce "Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka".

"Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ?ani ko ?anwa"

Ta ce "Eh wallahi, nima ina so"

Yayi dariya ya ce "Are you sure?"

Ta ce "Yes" cikin murna.

Yayi dariya ya ce "zamu gani ai".

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al'amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane"

"Idan bani da laifin sai ka bani ha?uri?"

Ya ce "Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi ha?uri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma ala?arki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya".

Rumaisa ta ce "Gaskiya papa, ni ba kullum nake ?arya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi ha?uri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu ha?uri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son ala?armu?" .

"Ban ji na yadda da ala?ar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving Winki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Amma ka yadda ka yi mu'amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma".

"Ala?ata da su daban...."

"Amma duk wata ala?a barin jini ce da ciki Waya, wai ba Jamil Win ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wata?ila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana"

Gaban Adam ya yanke ya faWi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba Waya jikinsa yayi sanyi, take ya ?aryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taSa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce "Papa sai da safe" ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani.

Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ?aryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami?

Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office Win Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska.

Adam

99 / 128