KANWAR MAZA 1&2 BY By Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  Aisha Adam (Ayshercool) Category :  Romance

Chapter   67 / 128

198K to 201K   out of 382K words

albarka, sauran magana duk yadda ake ciki zan yi magana in Allah ya yarda.

Suka fito tsakar gida, takawa ya kalli rumaisa wani takaici ya ?ule shi, wannan fitsararriyar abar ce zai aura.

Yaya Abubakar ne ya shigo, ammi ta kalleshi ta ce "Malam faruku kai ne ka razana mini ?a ko? Kuma ka ce baka son in haWa auren ?a?ana haba mai sunan baba laifin me muka yi haka ne"
Abubakar ya yi murmushi ya ce "Ina wuni"

"Lafiya ?alau ya gida ya ?o?ari?"

"Alhamdilillah"
Iman ta Wan ?ura masa ido, kamar ba wannan ne mai muryar nan ba.

Mama ta ce "?an uwan mai sunan baba ne, shi gashi can a bayanki yana jinki, wannan dattijon arziki kenan malam habu"

Ammi ta ce "Au, ashe fa ?an biyu ne ai ni duk kama suke yi mini" ta waiwaya ta kalli mai sunan baba ta ce "Mun zo neman aure gidanku ka hana, a sassauta adawar nan ba a san in da rana za ta faWi ba, ina da tarin ?an mata a gidana kar ka zo neman aure nima na rama".

Suka yi dariya gaba Waya, mai sunan baba ya Wan sunkuyar da kai be ce komai ba.

Ammi ta Wora da "Dan Allah ayi mana addu'a, na samu duk sun amince in sha Allah lamarin nan alkhairi zai zama, tun da Allah a ka nufa da lamarin, ba za aji kunya ba, karatun rumaisa da komai zamu kula da shi, kuma adam zai ri?eta cikin mutunci da kulawa, mu sanya a ranmu wannan haWin Allah ne, a tayamu da Addu'a".

Mai sunan baba ya ce "Allah ya tabattar da alkhairi "

Ammi ta ce "Amin ya haiyyu ya ?aiyyum, yauwwa mai sunan baba ko kai fa, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku, ya baku mataye nagari sanyin idaniya, ya tsare mana ku daga sharrin zamani". Ya amsa da amin.

Abubakar ya ce "Hajiya babu wata damuwa, har kullum alkhairi muke fata, kuma dama babban burinmu bai wuce rumaisa ta yi ilimi, sannan ta samu abokin rayuwa nagari ba, Allah ya sanya haWin nan ya zama alkhairi".

"Amin ya Allah, na ji daWi sosai na gode da karamcinku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya yayi muku jagora".

Adam har ya fara ?ulewa, gaba Waya ya gaji so yake su tafi, har ya je ya kunna mota, amma ammi tana ciki tana ta faman hira.

Iman tuni ta bi bayan Adam ta shige cikin motar, sai sauke numfashi take, saboda ba ?aramin razanata mai sunan baba yake yi ba.

Aka yi sa'a mama ta yi musu sallama ta fito, ma?wabtan su rumaisa har sun fara surutun, yawan zuwan da mota daban-daban take yi ?ofar gidan su rumaisan.

Suna tafe a hanya ammi tana faWin "Alhamdilillah, na ji daWi an gama da wannan babin, gobe in Allah ya yarda zan je na samu turaki, sai dai dole mu yi shiru da bakinmu, babu wanda zai ji wa za ka aura, sai Allah ya kaimu lokacin".

Adam a ransa ya ce "Sai ka ce wata matar arziki, ni dan ta ni ba wanda zai san ma an yi auren, wannan har wani aure ne"

Ammi ita kaWai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana sa?e-sa?ensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ?arasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.

Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba Waya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a Wakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ?alubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ?arata".

A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faWuwa.

"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ?addarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wata?ila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wata?ila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"

Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.


***
Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.

Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na Wan bashi lokaci tukuna"

"Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"

"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"

Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"

"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ?addara sai ya fara aurenta ne"

"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman Win, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".

"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"

"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"

Ta ?a?alo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".

"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"

"To Allah ya sauwwa?e"

Ya amsa da amin ya fita.

***
Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba Waya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ?yar take ci.

Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"

Ruma ta Wago ta kalli mama.

"Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana"

Rumaisa duk ?aunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ?oshi tafiya zan yi"

Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ?arasa ta zauna a gaban mama.

"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.

"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da ?an unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"

Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"

Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".

"Dan Allah mama ki gaya mini"

"Ba zan faWa ba tashi ki tafi, karki makara"

Ganin mama ba ta da niyyar faWa mata, ya sanya ta Wau jakarta ta fice, ta ?udurce a ranta sai ta san ko menene.

Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ?wala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ?araso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"

Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"

"Amma meyasa, kin ha?ura da karSar Wan?"

"A'a, zan karSe shi"

"Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi ma?ociyarku munafuka ce"

Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?"

Habiba ta ce "Au baki sani ba?"

"Ban sani ba"

"TaS, to da suka je asibiti dubaki, suka ga Wa, suke cewa wai Wanki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wata?ila kasheshi ku ka yi"

Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma? Kamar yaya, to ai ko a gurin ?an bindiga, bana yarda su taSani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan, Wan anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi"

Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to ?ar iska ce"

Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta"

Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi ma?wabciyar nan ta ku munafuka ce"

Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka.

Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta.

A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya.
Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna.

Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata Waliba, duk ?an ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu.

Ta yi ?asa da muryarta ta ce "Yayata, duk wanda aka ce yayi cikin shege wai da gaske Wan iska ne?"

?alibar ta ri?e haSa ta ce "Ke rumaisa, meye haWinki da wannan maganar? Duk wanda yayi cikin shege Wan iska ne, kuma wasan banza yake da maza, yana bari suna ta Sa shi ko taSa al'aurarsa.

A rikice rumaisa ta ri?e mararta ta ce "Wurin fitsari kenan?"

"?warai kuwa" ta bata amsa.

"Mama ta ce mini ba a wasa da al'aura, kuma ba a bari wani ya taSa maka".

"Sosai haka ne, dan haka kar ki kuskura wani yayi miki wasan banza, duk wanda ki ka bari ya taSaki, to cikin shege zaki yi, a gidanku ma korarki za ayi kowa ya tsaneki, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza ?ar iska, Allah ya yi fushi da ke, idan wani ne yake miki ki je ki faWa a gidanku"

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a tambayarki kawai na yi na gode".

Tun da aka yi wa rumaisa wannan bayanin hankalinta ya tashi, wato kallon ?ar iska ake yi mata, mai wasan banza da maza, da aka ce ta yi cikin shege. Ita banda ?addara da tsautsayi da ya sanya takawa ya taSa ?irjinta, ita babu wani namiji, da ko da wasa yayi mata maganar banza balle ya kai hannunsa jikinta, iyaka dai ta san tana dambe da maza, amma ba wasan banza ba.

Duk jarumtar rumaisa sai da ta yi kuka, tare da ganin an cuceta, yanzu duk in da ta wuce kallon da ake yi mata kenan.

Malami ya shigo ajin, yayi musu ?arin al?ur'ani, ana tsaka da ?ari rumaisa ta ce "Malam dan Allah ina da tambaya" yayi shiru sannan ya ce "Ina jinki rumaisa".

"Lokacin da ka bamu addu'a, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, ita na yi ta biyawa, lokacin da aka yi garkuwa da ni, har na kuSuta. Dan Allah ka bani addu'a da zan yi mutum ya zama kurma, da bebe"

Ya ce "Ashsha subhanallah, me yayi zafi haka rumaisa?"

"Wata mata zan yi wa, da wasu mutane" ta yi maganar har zuciyarta.

Ya ce "A'a, ki yafe musu ko ki bar su da Allah, ki yafe musun ma shi ya fi, sai ke ma Allah ya yafe miki laifukanki"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba zan taSa yafewa ba, sai na yi addu'a Allah ya tattaro masifa ya jibga musu"

Malam ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan ba halin mumini bane"

Rumaisa ta tashi tsam tana kuka ta ce "Ni dai wallahi ba zan yafe musu ba, dama ka ce Allah ba ya juya addu'a wanda aka zalunta, in sha Allah sai matar nan ta zama kuturwa ma wallahi, dan ba zan yafe ba"
Statement Win ta ?arshe sai da ya bawa wasu dariya, Yasir yana kallonta ya shareta ta fice daga ajin tana kuka, zuciyarta na wani irin tafasa.

Ba a tashi ba ta tafi gida, dama mai gadi ya daina tareta idan ta zo fecewa muddin an kusa tashi, tun da ta taSa yi masa rashin hankali, ta fita da gudu garin bin ta ya faWi yayi targaWe, a hanya ta tsaya ta sai leda viva ta naira goma, ta cikota da manyan duwatsu, ta cika jakar makarantar ta da duwatsu, ta Wora a ka, ta nufi gida.

**"

Takawa yana gidansa, yana duba wasu takardu da ya taho da su daga wurin aiki, saura sati biyu zai je lagos wani aiki, Jamil yana gefensa suna shan tea, takawa yana duba takardun.

Jamil ya Wan ajiye kofin, ya kalli adam ya ce "Takawa ya batun aure ne? Yaushe zaka yi wani auren?".

Adam ya Wan yi jimm sannan ya ce "Maiyasa ka ke tambaya?"

"Saboda abu ne da yakamata ka fara zancensa, ka san very soon za a fara yi maka magana a kai"

Adam ya Wan numfasa ya ce "Ba shi ne a gabana yanzu ba, cigaba da ayyukana na binciken da nake yi su suka fi damuna".

"Amma kana ganin zaka iya cigaba a haka, duk yadda aka sakoka a gaba, gashi ka ?i cewa komai"

"To Jamil ya zan yi, duk mutanen da suka fito suka wankeni, ba su isa ba ba a fasa yi mini sharri ba, nima idan na yi maganar ba zai canza komai ba, kowa yayi abun da ya ga dama kawai, iyaka duk wanda ya ga ba zai iya ha?ura ba ya nemi hujja ya kai ?arata shikenan"

Jamil ya ce "Lamarin ?asar nan ai sai Addu'a, Allah ya kyauta ya bada nasara, nima akwai special assignment da zan tafi jigawa, na ji kana cikin wanda za su je Lagos ko?"

Adam ya ce "Eh, aikin ma nake dubawa yanzu"

Jamil ya ce "Allah ya sanya mu gama da aikin nan lafiya, kalli yadda muke wahala a kan ?asar nan amma ba a gani, kalli aikin da muka yi a kan tsohon ministan harkokin waje, amma dan wula?anci wai kotu ta bayar da belinsa, amma daina maganar ni gaba Waya sai in ji aikin ma ya fita daga kaina" Jamil yayi maganar cikin damuwa.
Adam ya ce "Haba Jamil, bai kamata mu karaya ba, ko da muna yi ba a Waukar mataki, wataran za a Wauka, ha?uri zamu yi mu cigaba da yi, idan ba haka ba haka ?a?anmu da jikoki zasu taso su Waora da bauta babu ranar da talaka zai yi ?anci"

"Kana da gaskiya, amma ni fa na tsorata da batun garkuwa da aisha, anya baka tunanin shiri ne, saboda abun da muke yi?"

"To ba na ce ba, zancenka zai iya zama gaskiya, kuma zai iya zama akasin hakan, duba da yadda dama ?asarmu babu tsaro, kuma kai tsaye garin da babu tsaron ta tafi, dan haka bana zargin kowa"

"To, Allah ya yi mana jagora, ya bayyana gaskiya a duk in da take".

Adam ya amsa masa da Amin.

Rumaisa ba ta yi burki a ko ina ba, sai a ?ofar gidan ma?wabciyarsu, tana tafe tana kuka har ta je ?ofar gidan, ta sauke kayan dutsenta, ta shirya tsaf, ta tattare hijjabinta, ta fara auna manyan duwatsu zuwa cikin gidan nan.

A rikice matar gidan ta fito, a matu?ar tsorace, jikinta ko mayafi babu, domin ganin meke faruwa.
Amma tana buWe ?ofar gida, rumaisa ta sauke mata wata ?atuwar marmara a bakinta, take bakin ya fashe, kan ta yi wani abu wani dutsen ya sauka a goshinta.
Rumaisa ta cigaba da aika duwatsun nan babu ?a??autawa tana kuka, tana faWin "Munafuka, wallahi ba zan yafe miki ba, ni ba ?ar iska ba ce".

Kururwa matar ta din ga yi, tana neman agaji, mutane suka fara taruwa, aka rirri?e rumaisa, amma ta din ga kuka tana ?o?arin cigaba da jifan.

Gidansu rumaisa aka je aka faWa, Allah ya sa usman yana nan, ya je ya dan?ota, tana kuka.

"Meye haka rumaisa, baki da kai ne? Dan me zaki din ga yi wa mutane jifa a gida?"

"Ba ita ta je take gayawa mutane wai na yi cikin shege ba, tana nufin ni ?ar iska ce ina wasan banza da maza" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ?arfinta.

Usman ya ja hannun rumaisa, ba tare da ya ce wa kowa komai ba, ya ja ta zuwa gida.

Hankali a tashe mama ta ce "Rumaisa, kanki Waya ki ka je ki na yi wa mace jifa a cikin gida, tana ta kurma ihu wai a taimaketa zaki kasheta?"

"Cikin kuka ta ce "Wallahi da zan iya sai na kashetan, dan me za ta ce mini ?ar iska? Cikin shege fa yana nufin mai wasan banza da maza".

Mama jiki a sanyaye ta ce "Rumaisa rayuwar duniya ha?uri ake yi, sai ki zo ki gaya mini, ni na Wau mataki"

"Wallahi idan na gaya miki ba zaki Wau mataki ba, cewa zaki yi na yi ha?uri, kuma wallahi ban ha?ura ba, sai ta ga abun da zan yi mata"
Rumaisa ta shige Waki tana kuka, Usman ya ce "Ai wallahi mama ban da kin hana da da kaina zan ci uban matar nan, duk yadda ki ka Wauketa ?a ki ke mutunta mata, amma ta yi mana wannan wula?ancin".

Mama ta ce "Dan Allah usman a rayuwarku ku koyi ha?uri, da ?yale mutane da halinsu, wasu lokutan da kai da rumaisan duk halinku Waya ai".


Ammi kuwa sake kiran mama ta yi, domin ta sake tabattar da rumaisa ta amince, dan ta fuskanci rumaisa ?ar buyagi ce, kar sai ta je ta kaiwa turaki maganar rumaisa ta mayar da hannun agogo baya.

Ta kira wayar mama, mama ta Waga suka gaisa.

Ammi ta ce "Ina maman sabir ne, a bani ita mu yi magana"

Mama ta mi?awa rumaisa waya, ta ci kuka ta ?oshi.

Muryarta a dashe ta amsa sallamar ammi.

Ammi ta ce "Rumaisa lafiya kuwa, na ji muryarki a dashe?".

"Ba ma?wabciyarmu ce ta ke cewa mutane na yi cikin shege ba, ?an unguwarmu suna yi mini kallon ?ar iska mai wasan banza da maza"

Ammi ta ce "Subhanallah, ki kwantar da hankalinki, kin ga yana daga dalilin da ya sanya nake son ayi auren nan, ki yi ha?uri ki manta da su, yau zan je gidan turaki mu yi magana, dama kiranki na yi na sake tabattarwa idan kin amince,

67 / 128