KANWAR MAZA 1&2 BY By Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  Aisha Adam (Ayshercool) Category :  Romance

Chapter   82 / 128

243K to 246K   out of 382K words

kwalliya aka wuce da ita wurin biki.

Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ?awayenta.

Rumaisa gaba Waya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan ?ar yarinyar takawa zai aura?.

Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ?awayen amarya.

Babu zato babu tsammani, sai ga ?an mazan mama sun dira a wurin, da shigar ?ananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.

Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.
Yasir ya ce "TaS, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?"

Ta Wan kwaSe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ?ai?ayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan Sata kwalliyar"

Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau"

Mamaki ne ya kama ?an wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.

Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ?ara gyara cake Win da yake kan table.

Rumaisa ba ta taSa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.

Gaban table Win ya ?arasa, kusa da iman ya Wauki ?ar ?aramar wu?ar yanka cake Win, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buWe bakinta, ta buWe kaWan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ?anwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake Win idonta ya cika da ?walla.

Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haWe rai ranar aurenta"

Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ?o?arin yin abun da zai kwantar mata da hankali.

Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba Waya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a Sangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haWa ido, gabanta ya faWi.

?arshe dai da su aka gama partyn, suka Wauki ?anwarsu suka yi gida.

Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.

Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.

Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.

"Me ki ke jira baki tafi gida ba?"

A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho".

"Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command.

Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.

Ayshercool
08081012143
What's app only please

*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*


Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.

Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a Waki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.
?an uwa sai bawa rumaisa ha?uri suke yi.

"Meye haka?" Ya faWa a kausashe.

Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daWi za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi"

"Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya"
Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar Wakan mama.

Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba Waya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.

***
Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.
Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta Waga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.

"Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?"

"Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?"

"Babu Waya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?"

A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest"

Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ?ure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ?afarsa ba zaki hango ba, let's join hands together"

Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faWin "Shashasha kawai".

Iman ita kaWai a Wakinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faWi, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.

?angaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. TaSe baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.

Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.
Ta wuni a uwar Wakan mama, tun ?arfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ?arfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.
Ma?wabta na ta mamakin wani hamsha?in ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.

A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ?i tsayawa.

Mai kwalliyar ?awar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.

?arshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.
Ya je ya tarar duk an yi wa ?awayenta kwalliyar ban da ita.

Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?".

"Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka.

Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi".

Adam dai ya ?ule ?arshe, Bashir ne yayi ta bata ha?uri, sannan ta tsaya aka yi.

Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri Waya da na Adam.

Hauwwaliya har da tsalle, tana koWa rumaisa.

Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.

A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haWe cikin shadda iri Waya, hatta huluna da agogo iri Waya suka saka, motar na tsayawa, ta buWe ta fice ta nufi wurin su Usman.

Abdallah ya din ga Waukar rumaisa a hoto.

Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da Wan hasken da ba zai ishemu ba"

Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki"

Bisa ga al'ada, ?awayen amarya da ?an uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ?ar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ?a da uba.
Abun ba ?aramin ?ayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ?ar mitsitsiyar yarinya.

Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maro?a da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.

Rumaisa ta kalli yadda hall Win ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba Waya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na Wibarta.

Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya ri?e hannunta, sai da ta Wan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ?o?arin Waukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ?o?arin ?wace hannunta daga na Adam amma ya ri?eta sosai.

Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ?anwar zaratan maza har bakwai.

Iman ce ta fito stage, ta karSi mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.

Jabir ba ?aramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ?ar talakawa mara kunya.

Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ?awayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.

Dangin su Adam sun so su farfaWi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya ri?e gulmarsa.

Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta Wau ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin ?an mata.

'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta.

Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ?awar amarya an sha Wauri, ?ar ba?a kyakykyawa.

Iman ta ?arasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku Waya, koda yake na san yaya Aliyu"

Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske, ?ar balarabiya ya aka yi ne?".

Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa".

Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri Waya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ?amwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi ha?uri da ita, idan aka taSata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza "

Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taSa haWata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.

Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.

Jabir ya ?araso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ?arasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane".

"Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan Wazu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaSa.

"Yes na ji, zo mu je dai, ko na Wagaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a Waura auren da namu"

Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.

Suna yin gaba ya hau ta da faWan, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta Waga kai suka yi ido huWu, da sauri ta koma cikin wurin dinner.

KwaSe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya Wan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".

"Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta ?arasa maganar bilha??i za ta yi kuka.

"Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?"

Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ?i fasawa, wayyo mama ni na gaji"

A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faWa.

Mc kuwa koWasu kawai yake yi, saboda shagwaSa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga ya?e, dan kar a fahimci wani abu.

Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.

Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?"

"Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare"

"Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.

Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya Webi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.

Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.

An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta Waga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.

Hatta ammi ta je wurin, an yi mata li?i sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi li?i.

Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata li?i, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu.

Adam ma basarwa yayi, ya din ga yi mata li?i, kuWi ba kaWan ba, ta din ga kallonsa ta ga ko yana sane, amma ya?i kallonta kar ta yi wani shirmen. Babban abun da ya fi burgeta, shi ne fareti, da kuma crossing sword Win da abokan aikin su Adam suka yi musu.

Gajiya kam rumaisa ta yi ta, dan har gyangyaWi ta fara, da ?yar take iya buWe idonta, ga takalmi mai tsinin gaske a ?afarta.

Sai sha Waya da rabi na dare aka tashi, rumaisa tana ta sauri ta bi su yaya Abubakar, amma takawa ya sakata a gaba zuwa motar da suka zo.

Tana shiga ta zauna ce "Wayyo Allahana, na gaji"

Ya kalleta yayi shiru, basu je ko ina ba ta hau bacci, gaba Waya ta kife masa a jiki, kai da jin yadda take sauke numfashi ka san ta gaji da yawa.

Sidi ya ce "Sir amarya ta gaji da yawa"

Adam ya ce "Gashi har ta yi bacci"

Sidi ya ce "Allah mai iko, ba zan manta scene Win da ku ka yi making, ranar da ku ka fara haWuwa ba, and she's now your wife"

Adam ya ce "Shhhhh, a daina tayar da wannan maganar"

"Sorry sir"

Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya Waukar pose Win ta, ya buWe, ga sababbin kuWi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya ri?eta a hannun sa.
Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya.

A ?ofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ?araso, ya sauke glass Win motar, gaba Waya suka ?araso.

"Ta yi bacci fa" ya faWa yana kallon Usman.

Usman ya ce "Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar ?ar kaza".

Adam ya Wagata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi.

Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ?anwarsa a kwance a jikin wani ?ato. Takawa ya Waga kai suka haWa ido da shi, ya wani cukule fuska.

Aliyu ya zura hannunsa, ya Wauko rumaisa gaba Waya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce "Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karSa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai"
Aliyu ya ce

82 / 128