KANWAR MAZA 1&2 BY By Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  Aisha Adam (Ayshercool) Category :  Romance

Chapter   98 / 128

291K to 294K   out of 382K words

kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
Ga Wan ta ba shi da lafiya, Wayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ?wace mata Waya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ?wace Sabir ya auri ?anwar anty aisha ya bata. Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'.

Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.

Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ?asa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ?arshe a nan ?asa ta yi bacci.

Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaWi a ?asan zuciyarsa, dan ?o?ari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan ya?i yadda ya sallama cewar ya faWa soyayya, haryanzu tantama yake yi.

Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta Wauke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba Waya.

Wajen ?arfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a Wakinsa, ta zo a kaita makaranta.
Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.

Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi Wakin nasa.

Ciwon kwana Waya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.

Ta ?arasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe Win jallabiya ta ce "Sannu ka warke?".

Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya ?alau, ya jiki?"

Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?"

Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na Wauka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?"

Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.

"Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ?i amsawa wai sai an yi maka irin taka". Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.

"Barka da wannan lokaci ranka ya daWe, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.

"Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta".

Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.

Sai dai a harabar gidan, ta haWu da Mahmud, yana shirin fita.

Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?".

"Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi"

"Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta"..

Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buWe motar ta shige.

Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya daWe, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne".

Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi.

Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.

Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaSa ta, in ta sai mata abubuwa".

Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a".

"Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde Wan bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu'a da fatan alkhairi"

Ya ce "wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki".

"Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu'a, tsakanin Ammi da wannan matar?" Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa.

"Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?"

A dai-dai nan, ya iso ?ofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru.

Ta ce "Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faWa mata ba"

Ta buWe motar ta ce "Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy" ta nufi cikin makaranta.

Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ?asa, gaba Waya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an Wora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama.
Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ?i auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daWe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba.

Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya Wauki rumaisa zai kaita makaranta.

"Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi ha?uri mana".

"Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haWinsa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti ne da ita ba, kar a cutar da ita*.

Ammi ta ce "Kana da gaskiya, amma na ga ta su ta zo Waya, in sha Allah babu wani abu da zai faru, tun da ka ji sau?i ma, sai ku tafi amma dan Allah kar ka ce zaka yi faWa, kaga ba ka da cikakkiyar lafiya. Kuma ka sani ko a dalilinta komai ya dai-dai ta tsakaninka da Wan uwanaka?"

Kallon idon ammi yake, tuni har hawaye sun cika mata ido.
"Shikenan ammi, ba zan yi magana ba, ki yi ha?uri, amma dole in raba shi da iyalina".

***
Da aka tashi daga makaranta, Adam ne ya zo Waukar ta, saboda ya ji sau?i sosai, ciwon bai kuma tashi ba.

Tana ganinsa ta hau dariya "Ka warke ne ka zo da kanka, da adaidaita sahu zan hau na tafi ai".

Fuskar sa babu walwala, yayi mata banza, ya ja motar suka tafi, sai dai ta ga ya nufi gidansu, maimakon na Ammi, ganin ya na ta cika yana batsewa, ya sanya ba ta kula shi ba, ta cigaba da harkokinta.

Ko da suka je gida, su Asiya suka din ga yi musu sannu da zuwa, suna yi wa Adam sannu, dan baba uwani ta gaya musu, maigidan ne babu lafiya.

Ya wuce Wakinsa ta wuce nata, ta yi wanka, ta kwanta baccin da ba ta samu yi jiya ba.

Sai da aka yi la'asar, sannan ta tashi, taje kitchen ta haWa shayi, ta zuba madara fal da milo, ta dafa ?wai ta ci abunta, sannan ta Wau littafinta, ta tafi Wakin Adam.

Yana zaune a kan kujerar Wakin sa, yana dudduba wasu takardu, ta yi sallama ya amsa mata a ciki, ba ta damu ta je gabansa ta tsaya, ta ce "Albishirinka?"

Ya kalleta ya ce "Ya aka yi?".

Ta nuna masa littafinta, na assignment Win da ta yi, ta zana malaminsu, ta ci 10/10.

Ya Wan kalli littafin da mamaki, sannan ya kalleta, alamar yana jiran bayani.

"In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing Wina, ya Waga littafin ?an ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ?ir?irar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu Walibai masu ?o?ari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa"

?an murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa.

Ya ce "You try".

"Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma ?ar tsana babba, sai lunch box Wina"

Yayi mata kallon ba zaki girma ba.

"Ya naga kana kallona?"

"Mahmud, Ala?arki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka".

"Wai meyasa zaka saka ni a cikin faWa ku? Ni meye nawa yana yi mini kirki, shikenan dan kuna faWa nima sai na din ga jin haushin sa. Jamil, Jabir, Samha ala?ar ka da su bana so, Jamil da Samha, sun wahalarsa da matarka, su meyasa ba ka gaba da su?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

Rasa bakin magana yayi, duk yadda kake tunanin rumaisa ta wuce nan, a zahiri tana da ?uruciya da wauta, but she have a very sharp brain, ba shi da amsar bata a yanzu dan ta ?ure shi.
Amma saboda kar ta ga ta yi nasara ya ce "Ni ne shugaba, a gaba nake da ke, dan haka duk hukuncin da na yanke dole ki bi".

Ta Wau littafinta ta ce "Babu biyayya ga abokin halitta wurin saSawa mahalicci, duk da?i?ancina a makaranta, na san wannan, kuma Allah ya yanke rahamarsa ga mai yanke zumunta, Annabi ma ba ya tare da mai yanke zumunci, sai ka din ga jin tsoron Allah wurin yanke jiki kai ma" ta fice ta koma falo ta bar masa Wakin.

Mintuna kaWan ya fito ya fice daga gidan gaba Waya, ya dafe kanta ta ce "Na shiga uku wannan wane irin abu ne, anya kuwa zan iya, ni duk na gaji" tayi tsaki, ta tashi ta je ta ciko roba da gugguru, ta Waukko lemo, ta zo ta saka a gaba tana ci, tana kallon cartoon.

Hayaniya ta ji ana hawowa sama, ta tsaya tana jiran taga waye zai shigo?

Samha ce da Fauziyya, da kuma ru?ayya sai zee ?anwar Samha, baba uwani biye da su, hannunta ri?e da foodflask.

Babu ko sallama suka zo suka zazzauna, baba uwani ta ajiye kwanukan, ta ja gefe.

Samha ta kalli rumaisa ta ce "An samu duniyar da babu a gidan tsoho, an yi Wai-Wai a katafaren gida, da duk dangi babu irinsa" rumaisa ta yi mata banza, ya cigaba da kora lemonta.

Ru?ayya ta ce "Allah wadaran naka ya lalace haryanzu ban ga technology a auren wannan busashiyar yarinyar ba, da ko rantsuwa na yi babu kaffara, ragowar masu garkuwa da mutane ce, sun gama lalata ta" Wan shiru ruma ta yi tana tunanin, me take nufi.

Fauziyya ta ce "Ba wani technology, wula?anci ne kawai, dan Allah dubi Samha ki dubeta, ita ta isa ta kira kanta mace ma wallahi wannan ko a mai aikin samha ba ta isa ta zo ba, kalli bakin shegiya yadda take auna madara, saboda samun wuri, ga ?irjinta fayau kamar faifai ba wata mamora, amma wai ita ya aura".

Rumaisa ta yi gyatsa ta ce "Gidan miji daWi, mussman irin gidan papa, auren mai kuWi daWi ba, na samu promotion, gida babu, na samu a gidan miji" tayi maganar tana lashe madarar hannunta.

Fauziyya ta ce "Ke dalla rufewa mutane baki, tashi ki kira mana Wan uwanmu, mun zo duba shi"

Cikin tsawa rumaisa ta ce"Ba zan kirawo shi Win ba tun da ke ba uwata ba ce"

Samha ta ce "Ke, uban wa ki ke yi wa tsawa".

"Uban duk wanda ya tsargu, ba sunana Aisha ba, sunana rumaisa Mahmud, ?anwar maza, ku tambayi yayan naku wace ni, kawai ku zo ku cika mini kunne, wai ko a? ?ar aiki ba zan zo ba, ai Allhan ba naku ne ku kaWai ba, da ban zo a ?ar aikin ba, sai na zo a matar gida, antynku ce ni, tun da matar yayanku ce ni, ke kuma da ki ke cewa ke ce mace, na ji ni namiji ce, ni duk wadda ta yi mini, wallahi sai ta ci ubanta, babu wata barazana da tashin hankali da ban gani ba, dan haka ba zaku Waga mini hankali ba, ke kuma da ki ke cikakkiyar macen, kin san idan ki ka gama cikar, zubewa zaki yi ki fara tsufa, kin ga ni kuma a lokacin da ki ka fara tsufa na cika ko? Banza kawai"

"Ke! Kina ?ar matsiyata ni ki ke gayawa haka? Kina da hankali kuwa, waye ubanki a ?asar nan, har ni ki ke cewa ubana zaki ci?"

"Eh na faWa, sai na ci ubanki, da ke da duk wanda ya ce zai zageni, ?an fashin daji ma, ba su razana ni ba, balle ku shashashai, gwalagwaje, marasa mutunci, idan tunaninku gayya, ku taron mata ne, ni kaWai dai-dai nake da tunanin maza bakwai".

Ayshercool.










Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?



Ru?ayya ta ri?e haSa ta ce "Kan uban nan, wannan wace irin yarinya ce, mara tarbiyya Binta ta aurawa Wan ta?"

Jin maganar rumaisa ta yi wani iri, yadda ru?ayya ta ambaci sunan Ammi haka kai tsaye kamar sa'arta.

Zee ta ce "Ni wallahi da na san irin wannan abun zamu tarar, da ban zo ba, kawai kun zo kuna zubar mana da mutunci a gaban wannan ?ar yarinyar".

Ruma ta ce "Oho dai, in ma ?ar cikinki ce ku ta shafa, aka gaya mini cuta sai na faWi mutuwa, haka kurum ti?a-ti?a da ku, ku zo kuna ci mini mutunci. Wai wani kun zo wurin Wan uwanku, yo koma menene, duk ?an uwantakar ta ku, tun da dai ni ta ajiye mussaman yake bani abinci, yake kula da ni, yafi so na"

Samha da takaici ya ?ule, ta mi?e a hasale, tana yin?urin ta ?arasa ta tsinke rumaisa da mari. Fauziyya ta ri?e ta, ta ce "Ba girmanki ba ne".

"Ki cikani Fauziyya, in zuba mata da ha?ora na daki banza, dan ubanta"

Rumaisa ta ce "TaS ki dakeni ki ga yadda ake ?aramin ya?i, wallahi sai yayyena sun yi miki bugun sakwara, bar ganin kin fini girma, ni da maza ma dambe nake ba ruwana da girmanki".

Jin hayaniya ya sanya baba uwani hawowa saman, ta zo ta iskae rumaisa tana ta zazzaga musu rashin mutunci.

Baba uwani ta ce "Haba ke kuwa, ba?inki ne fa, ?an uwan mijinki, ya zaki din ga yi musu wula?anci haka, ai ba haka ki ke yi wa ?an uwanki idan sun zo ba, kuma ba sa'anninki bane "

"Baki san meyafaru ba, dan haka ba ruwanki da ni".

Baba uwani ta dafe ?irji ta ce "Ni ki ke gaya wa haka?"

Rumaisa ta dubi dattijantar baba uwani, ta haWiye abun da ta yi niyyar faWa ta ce "Ba ruwanki da abun da na yi, idan ban saka ki a ciki ba, tun da baki san farkon abun ba, kuma kina goyon bayansu"

Ta Wauki kofinta, ta nufi Wakinta, tare da ce musu "Mahukatan banza kawai"

Tun da ta shige Wakinta, ba ta sake fitowa ba, tayi zamanta tana zane-zane, har aka yi sallar magariba, sannan ta tashi ta yi alwala ta yi salla.

Ta idar da salla kenan, ta jiyo takawa yana kwaWa mata kira, yamutsa fuska ta yi, dan ya tsorata ta.

Fita tayi, ta tsaya ta kalli falonta, an ci abinci an Sata falon gaba Waya, har da fasa mata wasu daga cikin farantai.

Kasa magana ta yi, a fusace ya kalleta ya ce "Meye wannan?"

"Oho" ta bashi amsa.

"Which kind of nonsense is this, ina yi miki magana?" Ya yi maganar a zafafe.

Nan da nan ita ma ranta ya Saci, "Amma dai ka san ni ba ?azama ba ce, kuma ba ka taSa ganin nayi irin wannan abun ba, yadda ka gani, nima yanzu nake gani".

"Wai ne ki Waukeni ne? Sa'anki or what, kina da hankali kuwa, kalli falon nan fa?"

Takaici ne ya ?ule rumaisa ta ce "Ni ba mahaukaciya ce ba, ?annenka da wannan Samhar su ne mahaukata, dan su suka yi haka da falon ba ni ba, tun da dai baka taSa gani na yi haka da gidan ba" ta juya ta nufi Wakinta, ya taka da sauri ya janyota ya mayar da ita falon.

"Idan suka yi haka da wurin, ke ba zaki saka a gyara ba, ko ke ki gyara ba? Ba gidanki bane?"

"TaS, ni zan gyara musu, to wallahi ko kai ne ba zaka yi haka in gyara ba, kai da kake ciyar da ni, balle wasu ?artin banza"

"Shut up! ?annen nawa ki ke cewa ?artin banza? Ki kiyayeni, samo abun gyara ki gyara wurin nan, na baki mintuna biyar kawai. Ki gama ki zo ki gaya mini dalilin da ya sanya ki ke yi wa baba uwani rashin kunya"

Wani irin malolon ba?in ciki ya cunkushe mata zuciya, ba ta taSa tunanin Adam yana da kwarjini, da kima a idanunta ba sai yau, da ta ji tamkar an Waure mata harshe, ta kasa bijire masa, wasu hawayen ba?in ciki suka cika mata ido, amma ta danne, ta zo ta fara aikin gyara wurin.

Ya nemi wuri ya zauna, ta gyara ta kammala, ba ta ce masa uffan ba, ta tafi Wakinta.

Bayanta ya bi, ya tarar da ita a gaban mudubi, ta cika ta batse, ba wani abu take a gaban mudubin ba, kawai tana tsaye, tana sauke numfashi.

Tana ganinsa ya shigo, ta share shi ta cigaba da tsayuwa.

"Me baba uwani tayi miki da ki ka yi mata rashin kunya?"

Banza ta yi masa ta?i kula shi.

"Ina sake gargaWinki, duk abun da zasu zo su yi, babu ruwanki da su, sannan idan ki ka kuskura ki ka kuma yi wa baba uwani rashin kunya, sai na Sata miki rai, kawai kin

98 / 128