KANWAR MAZA 1&2 BY By Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  Aisha Adam (Ayshercool) Category :  Romance

Chapter   71 / 128

210K to 213K   out of 382K words

daga nan"

"And, shi wannan da yayi i?irarin kashe Aliyu da wannan yarinyar, a kai mini shi state CID, sannan a kamo mini yaransa ma, zan bincika wanda ya saka aka sake shi ana tuhumarsa da kisan kai"

Dpo ya ce "In sha Allah ranka ya daWe" baki buWe malam shamsu ya din ga bin Adam da kallo, da mamakin ina suka samo Adam.

Adam ya dubi malam shamsu ya ce "Kai kuma, daga yanzu idan zaka yi gulmar, ka din ga nunawa mutanen unguwar ni, ka ce nine wanda yayi mata cikin shegen ta haifa, ta dawo ya karSi abun sa, idan da wanda zai Wau mataki a kan hakan ?ofa a buWe take. A saya mini shi a ceil, sai na waiwaye shi"

Cikin tashin hankali ya ce "Dan Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama ka yi ha?uri, ka yafe mini, wallahi kuskure ne"

Adam ya ce "Kai Yanzu wannan da ko magana ma ba ta iya yi ba, ba ta san ma'anar abunda ake faWa ba, ta yi maka kama da mai cikin shege? ?addara ?ar ka ce zaka je kana faWar wannan maganar?"

Ya sunkuyar da kai yana girgiza wa.

"Ko da wasa, ka kuma gaya mata wannan mummunar maganar, sunana Adam Sharif Galadima, zaka ga abun da zai biyo baya"

Ware ido malam shamsu ya yi, a radio yake jin sunan Adam, sai kuma ya san shi ne mamallakin katafaren gidan gonar da yake cikin unguwar, cikin tsuma ya ce "In sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, tsautsayi ne"

Duk da wannan abun da Adam ya yi wa rumaisa bai burgeta ba, aka bawa Aliyu kayan sa, suka fito daga station Win, Adam ya rungumo Aliyu suka fito, Usman ya ri?o rumaisa, mai sunan baba ya fito shikaWai ya kama gabansa.

Cikin motar Adam suka shiga, ya kunna suka fita, suna tafe ya ce "Aliyu, dan Allah daga yau komai za ta tsoka no, ku ?yaleta ita kaWai ko zaneta ne ayi, ka ga yanzu haka kurum ta janyo maka kwanan ceil"

Aliyu ya ce "Ba ayi haka ba babban yaya, tuba muke yi"

"Ai ni ko ba a tare mini faWa ba, ina da ?arfi"

"Rufen baki ko na cillaki ta tagar nan" Usman yayi maganar yana nuna mata taga.

Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, Adam da Aliyu kuma suna taSa hira, rumaisa har mamaki take yadda yau Adam ya buWe baki yana magana haka da Aliyu.

A ?ofar gidan su rumaisa Adam yayi parking, Aliyu ya yi ta masa godiya, Adam ya ce "Ka daina wannan godiyar mana, kar ka saka na ji kunya, ai kai nawa ne Aliyu a gaida mama" suka yi musabaha ya fita, Usman ya buWe motar ya fita, rumaisa har ta fita Adam ya ce "Ke tsaya, Ammi ta bani sa?o na baki"

Rumaisa ta Wan yi jimm sannan ta ce "Sunana rumaisa, ba ke ba" yai kamar bai ji ta ba, ya Wauko ledar wurin ammi ya mi?a mata, ta ?are masa kallo ta ce "Ni ammi ba ta ce za a kawo mini wani sa?o ba, ni ba zan karSa ba, duk wani abu da ya fito daga wurinka bana so, balle nan gaba ka ce mini kwaWayayyiya, gidanku da nake zuwa saboda sabir ma, a dole na ha?ura, saboda gorin da ka yi mini, ina ji ina gani ina ?aunar Wana, amma ka saka na yi zuciya na daina ganinsa, ni ba zan karSi abunka ba" ta tsallaka ta shige gida ta bar shi da kayan a hannu.

Ayshercool.
Chat me on what's app, to subscribe yours.
08081012143

PAID BOOK NE, ? 500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.




Sororo ya bi rumaisa da kallo, dan ba ?aramin mamaki ta bashi ba, ba ya son mama ta fito ta ce za ta yi masa godiya, dan haka ya shige motarsa ya ja ya bar ?ofar gidan.

Mama kuwa murna ta din ga yi da ta ga Aliyu, nan da nan ta ce Yasir ya Wora masa ruwan wanka, ta kalli Usman ta ce "Ina yake, na yi masa godiya?"

Rumaisa ta ce "Ai ya tafi" mama ta harareta ta yi mata shiru, dan haryanzu ba ta huce ba, da abun da rumaisan ta aikata.

Usman ya ce "Ina sa?on da na ji ya ce ki tsaya ki karSa?"

Ta kwaSe fuska ta ce "Ni ban karSa ba, cewa na yi ya koma da abun sa ba na so"

Cikin takaici ya ce "Dalla matsa ?ar ba?in ciki, ke da ba ro?arsa ki ka yi ba, kawai sai ki ?i karSowa"

"TaS, haka kurum yayi mini gori wataran"

"Uban waye ya ce miki wanda aka haifa a cikin arziki yana gori? Ai idan kin ga mai kuWi yayi gori, to dama matsiyaci ne, daga baya yayi arzikin kuma wata?ila a tsiyarsa zai mutu" ba wani fahimtar abun da yake faWa ta yi ba, ta shiga harkokin ta. Sai dai ta kasa sakin jikinta, duba da yadda mama ta haWe rai, ta?i kulata.

Aliyu ya yi ta basu labarin irin abubuwan da malam shamsu ya din ga faWa a kansu da rumaisa, na Satanci da yadda ya ziga a ka kulleshi, duk ba a same shi da makami ko wani laifi ba.

Usman ya ce "Gajiyayyen wahalalle, irinsu ne masu ?arewa a tsiya, kuma idan bai yi wasa ba, sai na Waga shi na buga da ?asa. Ai ni abun da gayen nan yayi masa ya burgeni wallahi, da ya ce shi ne uban Wan kuma ya karSi abun sa".

Rumaisa ta yi farat ta ce "Yauwwa, na ji ya ce wai shi ne yayi mini cikin, to dama shi cikin yin sa ake yi, yi wa mutum ciki ake yi"

Aliyu ya ce "Bismillahi, ashe haryanzu hankalin da saura".

Ganin kowa ya yi mata shiru ya sanya ta ce "Yaya usy baka bani amsa ba".

"To me zan ce miki, wai ke haryanzu kanki a tukunya yake, baki san meye rayuwa ba, baki san me yakamata ki din ga tambaya ba, Allah ya sa mai sunan baba ya ji ki, shi sai ya baki amsa"

"To me na yi daga tambaya?"

"Idan kun yi auren sai ya baki amsar"

Aliyu ya kalli usman ya ce "Kai fa wasu lokutan sai a hankali, kai ba ka ji kunya ba kake gaya mata hakan?".

"To yaya zan yi mata bayani, ita kai kamar computer abun da ka zuba mata kawai shi ta sani, idan suka yi auren ai aikace za ta gani"

Aliyu ya ce "Kaii usman lafiyarka kuwa? Kar ka gurSata mata tunani malam"

Mama da ke Wakin ta ce "Ke, ki taso ki zo ki kunno mini maganin sauro" mama ta kirata, dan katse waccan hirar da suke yi, dan idan aka zurafafa rumaisan ba ganewa zata yi ba, kuma wani zancen za ta Sallo.

***
Yanayin fuskar Ammi kawai ya kalla, ya san akwai matsala.

A nutse ya ce "Ammi na dawo"

Ta kalleshi, ta kalli ledar hannunsa ta ce "Wannan ledar fa?"

Ya kalli ledar ya ce "Sa?on da ki ka bani ne, ta ?i karSa"

"Saboda me?" Ammi ta tambayeshi cike da tuhuma.

"Ta ce baku yi waya ba, baki ce mata zaki aika mata da sa?o ba, dan haka ba zata karSi abun hannuna ba na zo daga na yi mata gori wataran"

?an jimm ta yi, ta wani fannin rumaisa tana da gaskiya, kuma ammi ta sake jinjina lallai rumaisa tana da tarbiyya.

"Dole fa ka sauke wannan shan ?amshin, da sarautar ka dawo dai-dai level Win ta, domin ku fuskanci juna kai da ita, dan ba zan lamunci ku yi aure, ku din ga zaman doya da manja ba, kamar wasu ma?iya"

Adam ya ce "To in sha Allah" dan ya rasa mai zai cewa ammin.

Ta sake nisawa ta ce "Sannan na ji abun da ka aikata, Jamila ta zo har falon nan ta nuna ni da yatsa, ka saka mota zaka kashe mata Wa, adam ?iyayyar da ka ke yi wa Wan uwanka har ta kai haka dama? Ka yi yin?urin kashe shi?"

Adam ya yi shiru, ba tare da ?o?arin kare kansa ba.

"Kai a rayuwarka duk yadda nake tausaya maka, da yin iya ?o?arina a kan ka, baka gani ko? Kullum burinka ka tsokano abun da za ayi ta yi mana surutu, saboda wannan zafin zuciyar ta ka ko? Gobe in Allah ya kaimu ka je ka yi masa sannu, sannan ka bata ha?uri, magana kuma har ta kai kunnen wambai yana nemanka"

Dam ?irjin Adam ya buga, ya je ya duba Mahmud, ya bawa Mummy ha?uri, sannan wambai yana nemansa.

Cikin dakiya ya ce "To, in sha Allah duk za a yi" ya juya ya fice daga Wakin.

Ko abinci kasa ci yayi, abubuwa sun yi masa zafi sosai kwanan nan, ya tara ayyuka sosai a office, gashi duk iya binciken da yake ya gano, ko garkuwa da aisha shiri ne ya kasa samun komai, amma wasu daga cikin bayanan rumaisa, na nuni kamar da akwai wani abu a ?asa,gata gardamammiya ya san idan jajjagenta zai yi ba zata yi magana ba, sai ta ga dama. Ga wannan batun auren nasa da ammi ta sako shi a gaba a ?an kwanakin nan, babu damar ya motsa, sai ta yi zancen rumaisa, shi gaba Waya baya farin ciki da wannan auren.
Ga surutan da ake ta yi a kansa a media, kullum ?azafi kala-kala, ayyukansa da ya Wauko kan sace Aisha hankalinsa ya rabu biyu duk yayi sanyi, bai samu sun kammalu ba, tun sa shi ne jagoran aikin.

Ji yayi kansa ya fara ciwo, ga wani irin jiri da ya fara Wibarsa daga zaune, a hankali ya ja jikinsa ya kwanta, gaba Waya bai san ta ina zai fara ba da matsalolin nasa.

***
Yau mama ko sallar asuba ba ta tashi ruma ba, sai da Usman ya tsula mata wayar caji a ?afa ta tashi, ta yo alwala ta yi salla, ta gaida mama, amma maman ta?i amsawa.

"Mama wai dan Allah ba zaki kulani ba?" Ta yi maganar cikin damuwa.

"In kulaki in ce miki me? Ai ki je ki yi rayuwarki ruma nima zan yi tawa, ?a?ana suna bu?atar rayuwata, Sacin ranki ba zai ?arasani ba, na yi magana a samo langa-langa ayi miki Wakinki, dan ba zan cigaba da zama Waki Waya da ke, kina zucguna mini ba"

Ba ?aramin mamaki mama ta bawa rumaisa ba, dan a ganinta mama ta daina sonta, ta tashi jiki a sanyaye, ta je yi shirin makaranta, ta tafi ba tare da ta sake kula mama ba, sai dai abun yayi ta damunta, ga wani irin son ganin sabir da take yi, ga kuma alwashin da ta ci a kan sa.

Ita kanta wasu fitintinun da take yi, tana son ta daina amma Allah ya gani, ba za a taSa ta ta ?yale ba.

Adam kuwa, Yau kamar wanda aka gayawa wani mummunan sa?o haka yake jin sa, komai ba ya yi masa daWi, tasbihi kawai yake yi ko ya samu sassauci, ammi kuma ta sake nanata masa cewar ya je ya aiwatar da abun da ta ce na bawa Mummy ha?uri da duba Mahmud domin komai ya wuce.

Ba a son ransa ba sai domin cika umarnin ammi, ya nufi sashin Mummy.

Sai dai da ya tambayi Fauziyya, ta ce masa suna Wakin Mahmud.

Kai tsaye bai jira wani iso ba, ya shiga sashin da Mahmud yake, yana zaune a kan gado, an Waure ?afarsa da bandeji, da alama ?ashin ?afar ya taSu, amma ba irin so serious Win nan ba.
Mummy na gefen Mahmud tana takura shi ya ci abinci.

Mummy ta wani haWe rai, Mahmud ya yi wa Adam kallo Waya, ya mayar kan abincinsa, aka rasa wanda zai amsa masa sallamar da yayi.

Hakan ba ?atamkn ?ulara da shi ya yi ba , ya ji kamar yayi ficewarsa, amma ya san makircin Mummy.

Ya dubi Mummy ya ce "Na ji baki ji daWin abun da ya faru ba, am sorry for it, shi kuma Allah ya bashi lafiya" ya juya zai fita Mummy ta ce "Dan Allah Adam wace irin ?iyayyace kake nuna mana haka? Har ka taka Wan uwanka da mota, meyake damunka ne?"

"Ba mayar da magana, ko bibiyar tarihi na zo mu yi ba, na baki ha?uri kar a sake saka mahaifiyata a duk wani abu da zan yi, ni na yi laifi ba ita ba"

"Amma Adam ni kake gayawa haka? Da na isa da kai, ko giwa ta nuna maka ina da muhimmanci a wurinka ai da ban tunkareta ba, kai zan yi wa sanin yi maka maganar ba shi da amfani, ba zaka saurara ba ya sanya na sameta".

"Kuma shine har da gayawa wambai? Idan haka ne maiyasa maganar ba ta tsaya iya nan ba?"

"Magana ake yi ta rai fa adam, yin?urin taka shi da mota ka yi".

Mahmud ya ce "Mummy ki ?yale shi dan Allah, kin san abnormal yake, kuma ko da ya takani da mota, za a iya Sugewa da cewa ba shi da lafiyar ?wa?walwa, sai dai zan sake Waukar nauyi, gidan jaridar fallasa su wallafa cewa ka yi yin?irin takani da mota ka kashe ni" Mahmud yayi maganar cikin zunzurutun izgilanci.

A zafafe Adam ya juyo, ya Sarar da kayan abincin, ya sha?e Mahmud zuciyarsa na tafasa.

Mahmud ya kalli cikin idon Adam ya ce "Ka daina jin haushi idan an ce baka da lafiyar ?wa?walwa, duk mutumin da bai iya sarrafa fushinsa ba, ?wa?walwarsa babu lafiya ".

"Kai adam, ka cika shi kar ka kashe shi mana, jama'a ba kowa a kusa ne?" Mummy ta fara kwarmato.

Sanin cewa mutuncinsa zai sake zubewa, muddin aka sake zuwa aka gansu a yanayi mara daWi shi da Mahmud, kuma ran ammi zai sake Saci, ya sanya shi sakin Mahmud, ya fice da sauri.

***
Ma?wabta suka yi ta shigowa yi wa mama jajen abun da ya faru, na kama Aliyu, sai dai a wannan karon mama a tsorace take da mutanen, dan kar su je su yi musu wani sharrin.

Rumaisa ta saba sa ta dawo, mama za ta ce mata, ga ruwan wanka ta wanke wannan gumin da ?arin ranar, idan an gama abinci ta ci ta yi salla ta tafi islamiyya, amma yau ta dawo ba ruwan wanka, ga mama ba ta kulata ba, haka ta yi abun da zata yi ta tafi islamiyya.

A ?a'ida, ta kan ci abinci sau huWu zuwa sama a rana, ba wai abincin take tsayar da hankalinta ta ci ba, zaSe-zaSe ne da ita, ga irin cin abincin yara take yi, tana ci tana wasa, ko da ta fara ta ce ta ?oshi. Kullum ta dawo daga islamiyya sai ta ci abincin yamma, sai dai a yau Win ma mama ba ta ajiye mata abincin ba, gashi bata mayar da hankali ta ci na rana sosai ba, bugu da ?ari ta ga mama ta Wora tuwo a matsayin abincin dare.

Ba ta kula kowa ba, sai kukanta suka jiyo a Waki, Usman ya le?a, ya tarar ta kwaso kayanta, tana ta ninkewa tana zubawa a bagco tana kuka, kamar mai shirin yin yaji.

Cikin mamaki ya ce "Ke! Meye haka?"

"HaWa kayana nake yi, cikin dare idan kowa yayi bacci in bar gidan nan, tun da dai ba a ?aunata" maimakon ya ji haushinta, wata uwar dariya ce ma ta kama shi.

"Waye ba ya ?aunar ta ki?".

"Ba mama ce ba, ta daina kulani, wallahi duk faWan da aka yi da ni nice mai gaskiya, ya za ayi ace in sayo sigari? Kuma dan meyasa wannan shamsiyyar zasu din ga ce mini ?ar iska, sai ayi ta yi mini abu ba zan rama ba"

Usman cikin salon tsokana ya ce "Gaskiya babu daWi kam, yanzu to ina zaki tafi?"

"Tun da ba a sona a gidan nan, katsina zan koma wurin ?an bindigar, wurin su barde, au ashe an kashe barde to dai daji zan koma na yi bukka na zauna a ciki" ta yi maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

Usman kamar ya shiWe dan dariya, Aliyu da su Huzaifa kansu dariya suke yi mata.

Aliyu ya ce "Mama ki yi biko, saboda ke za ayi yaji"

Mama ta ce "Idan ta tafi nima na huta, Allah ya raka taki gona, ku ?ara mata kuWin mota".

Jin furucin mama ya sanya ta sake tunzura tana kuka ta ce "Shikenan, bakomai"

Ta Wauko bagconta tana kuka, Huzaifa ya ce "Allah sarki rumaisa, zamu yi kewarki sai a darul salam" ta sake fashewa da kuka.

Yasir ya ce "Rumaisa a yafi juna, Duk in da ki ka je ki zauna lafiya da mutane, koda yake ai kin ce a bukka zaki zauna ke kaWai, Allah ya kiyaye hanya ga wannan" ya baya naira Wari. Ta saka hannu ta karSa, suka cigaba da tuntsra mata dariya, ita kuma bil ha??i da gaske barin gidan za ta yi.

Ta waiwaya tana kallon mama, ta ga mama ko a jikinta, jajjagenta ma take yi, ta nufi hanyar soro.

Abdallah ya ce "Yarinyar nan fa ba hankali ne ya game jikinta ba, bari na bi bayanta.

Ta dafe kayanta ta fita waje, ta tsaya tana tunanin wace hanya za ta bi, kamar sama sai ga mai sunan baba.

Ya kalleta ya ce "Meye haka? Ina zaki? Kukan me ki ke yi?" Ya jejjero mata tambayoyin.

"Tafiya zan yi" ta faWa tana share hawaye.

A kausashe ya ce "Zuwa ina?"

"Mama ba ta so na, kowa ya tsaneni shi ne na ce barin gidan zan yi, an bani kuWin mota ma" tayi maganar tana nuna masa kuWin hannunta.

Takaici ne ya ?ule mai sunan baba, gaba Waya rumaisa ba ta da wayo wasu lokutan cikin takaici ya ce "Dalla wuce ko na mareki"
Za ta yi Magana, ya daka mata tsawa zai kai mata duka, ta taka da gudu ta koma cikin gida.

Abdallah da ya biyo bayanta kuwa, dariya kamar zai shiWe.

Mai sunan baba ya biyo bayanta zuwa gidan, su Usman ya saka a gaba ya din ga yi musu masifa, saboda sun bar rumaisa ta fita, ba sa tsoron ta yi wani wurin.

Mama ta ce "Ka daina yi musu faWa, ita ta haWo kayanta ta ce barin gidan za ta yi"

Mai sunan baba ya yi wa rumaisa wani mugun kallo ya ce "Zaki wuce ki ajiye kayan nan, ko sai na zaneki, idan ki ka bar gidan, wurin uban wa zaki je, mara wayo" sumi-sumi ta shiga ta ajiye kayan a falon mama.

Har dare suna yi mata dariyar abun sa ta yi, wanda hakan ya sake tunzarata.

Mama tana kallon rumaisa ta tada kai da kayanta, ta ?i yin shimfiWa ta kwanta,

71 / 128