Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Adventure
shi ne ya bani
umarni na zo nan darul uzut na same shi a yau
xinnan” Ko da jin haka sai gaba xaya dakarun suka
mayar da makamansu sannnan suka koma gefe da gefe
90
BAYAN MUTUWA
suka tsaya. Shi kuma shugabansu sai ya mayarwa da
mahayin martanin murmushi sannan yace.
“Biyoni a baya na kaika wajensa”Take ya juya
suka sake nausawa cikin daji shi kuma mahayin ya
sakarwa dokinsa linzami ya bishi a baya.
Sai da suka wuce rukuni-rukuni bakwai na ‘yan
fashi waxanda adadinsu ya kai mutum dubu-dubu
kuma dukkansu a cikin shigar yaqi suke ga tarin
makamai na yaqi kala-kala har da irin wanda mahayin
bai tava gani ba sannan suka qaraso darul uzut.
Darul uzut wata fadace wacce aka ginata da zallar
dutsen wuta, girmanta yafi na gidan sarautar sarki
sairan haka ma kayan qawa dana alatun dake cikinta
sun ninka na gidan sarautar sarki sairan sau goma.
Suna shiga cikin fadar suka isketa cike da barori
da kuyangi mata iri-iri baqaqe da farare kyawawan
gaske tamkar zavosu aka yi daga cikin matan duniya
suna ta hidima da kai kawo. Abin haushi shi ne
91
BAYAN MUTUWA
mutum biyu ne rak a cikin fadar kuma suna zaune
akan karagar mulki baabba guda xaya an tara musu
kayan ciye-ciye dana shaye-shaye iri-iri na alfarma
babu kalar da babu. Ba waxansu bane waxannan
mutanen biyu face Attajiri Huzulu da kuma sarkin
varayi nahiyar gaba xaya wanda ake kira da suna
Ranzalar.
Koda Attajiri huzulu ya hango wannan mahayin
an tsaida shi a farkon qofar shigowa fadar, wanda ya
rakoshi ya kama dokin ya sauka ya juya baya sai ya
miqe yana murmushi ya buxe baki yace “Lalle
marhabun da makanu lallai ina farin ciki da isowarka
akan lokaci, maza ka qaraso nan gareni” Koda jin
haka sai makanu ya saki fuska cikin sauri ya qarasa
wajen su Huzulu, koda ya rage sauran taku huxu ya
qarasa wajen sai ya zube qasa ya kwashi gaisuwa.
Huzulu ya taso da sauri ya rungume shi, sanan ya
janye jikinsa daga cikin nasa kafin ya kama hannunsa
ya ja shi zuwa wata kujera dake kusa da shi suka
zauna.
92
BAYAN MUTUWA
Faruwar hake ke da wuya sai matarnan suka
kawowa makanu abinci da abinsha sama da kala
ashirin suka ajiye a teburin dake gabansa. Nan fa
makanu ya shiga cin abinci da abin sha har sai daya
qoshi sannan ya sha ruwan inbi ya yi gyatsa.
Ko da Attajiri Huzulu yaga makanu ya samu
nutsuwa sai ya bushe da dariya yace “Yauwa yanzu
lokaci ya yi daya kamata ka bamu labarin duk abinda
yake faruwa a cikin gidan sarautar birnin misira da
wajenta” Makanu ya yi gyaran murya gami da gyara
zama yace.
“A halin yanzu Gimbiya lashmin tasa ranar yanke
maka hukunci a bisa guduwa da ka yi daga gidan
kurkuku amma har yanzu shi sarki Raihan baisan
cewar ka gudu ba, ka sani idan wannan ranar ta yanke
maka hukunci ta zo kuma aka zarta da hukunci a fada
to alqadarinka ya karye saboda a wannan ranar
Gimbiya lashmin zata tona maka asiri ta faxi dukan
laifukan da ka aikata a garin na sirri, hakan zai
matuqar zubar maka da mutunci da kuma darajarka”
93
BAYAN MUTUWA
Koda makanu ya zo wajenan a maganarsa sai jikin
Attajiri Huzulu ya soma tsuma, zuciyarsa ta rinqa
tafarfasa kamar zata qone.
Cikin tsananin fushi ya miqe tsaye zumbur ya
dakawa makanu tsawa yace “Rufe bakinka ko yanzu
na zare takobi na sare maka kai” Cikin hanzari
makanu ya sunkuyar da kanshi qasa ya tsuke bakinsa.
Da ganin abinda ya faru sai sarkin varayi ya miqe
tsaye da sauri ya kama kafaxar Attajiri Huzulu ya riqe
yace.
“Haba Attajiri Huzulu uban ma su kuxi, duk wani
attajiri da ma su mulki a qarqashinka suke, jarumai da
matsafa duka yaranka ne, akan wane dalili wata ‘yar
qaramar qwaruwa zata tayar maka da hankali alhalin
kaine uba kuma uwa ga duk wani mahaluki a wannan
nahiyar gaba xaya, ai tunda wannan labarin ya zo
garemu ba za mu tava barin mutuncinka da qimarka
su zube ba. Dole mu ruguza duka shirye-shiryen
Gimbiya Lashmin kafin wannan ranar ta zo wacce
take son kaika qasa”.
94
BAYAN MUTUWA
Sarkin varayi ya juya ya dubi makanu a lokacin da
zuciyar Attajiri Huzulu ta xanyi sanyi yace “Ya kai
makanu ina son ka sanar da ni yau sauran kwana nawa
gimbiya Lashmin ya rage ta yankewa mai girma
Attajiri Huzulu hukuncin qarshe a fadarta?” Makanu
ya xago ya dubi sarkin varayi yace “Yau sauran
kwana ashirin da xaya” Jin haka sarkin varayi ya yi
murmushi sannan ya juya ya koma kan karagar ya
zauna kusa da Attajiri Huzulu ya dubeshi yana mai
dafa hannunsa yace.
“Ai tayi kuskure data xauki dogon lokaci, ina mai
tabbatar maka, nan da cikar sati xaya rak za mu kawo
qarshen mulkin wannan yarinyar sannan kuma zamu
kama mahaifinta da hannunmu mu kawoshi cikin
kurkukun gidanmu mu voyeshi kai kuma ka xare
karagarsa ka zauna”.
Lokacin da sarkin varayi ya zo nan a maganarsa
sai Attajiri Huzulu ya xan yi murmushi mai kama da
yaqe yace “Faxar wannan qudurin a baki yana da
sauqi amma ka sani aikata shi a aikace ba abune mai
95
BAYAN MUTUWA
sauqi ba, ina mai tabbatar maka cewar wannan yarinya
Lashin ta daxe tana tanayi akaina ba tun yanzu ba tun
tana yarinya qarama, ban san da haka ba sai da
bokayena suka yi bincike akanta suka gano haka, duk
faxin nahiyar nan babu wanda yasan sirrrina sama da
ita kuma ita kaxai tasan lagona wanda idan ta riqeshi
to ta gama da ni, amma riqe wannan lagon nawa
daidai yake data faxa cikin wutar data shekara tana
ruruwa? Nima kuma yanzu na gano lagonta da shi
kuma zan yi amfani na hanata ci gaba da aiwatar da
mugun nufi akaina?” Cikin hanzari sarki varayi yace.
“Mene ne lagonta? Kuma kaima mene naka
lagon?” Sa’ar da attajiri Huzulu ya ji wannan
tambayar sai ya qyalqyale da dariya sannan lokaci
guda ya turvune fuska yace “Ya kai sarkin varayi mai
fadar Darul uzur kayi sani cewar babban lagon
gimbiya lashmin shi ne wannan yaron Amzad wanda
take son ta karve dukiyarsa daga hannuna. Tun suna
yara ita da shi ta kamu da tsananin sonsa sa’adda ya
ceci rayuwarta amma sai sarki ya shiga tsakaninsu ya
96
BAYAN MUTUWA
yiwa Amzad sihirin da ya manta da ita gaba xaya,
kuskuren da sarki ya yi shi ne bai yiwa gimbiya
lashmin irin asirin da ya yiwa Amzad ba don haka ita
bata manta da shi ba don haka kullum a cikin begensa
take dare da rana,matakin daya kamata na xauka shi
ne na saka a sato Amzad yanzu a kawo shi nan,
sannan na saka a sato wata sarqa ta musamman dake
wajen gimbiya lashmin, ita dai wannan sarqa ta
Amzad ce kuma ita kaxai zata nuna masa ya tuna duka
abinda ya faru a baya a tsakaninsu da ita. Ni na san
sato Amzad daga cikin birnin misira abune mai sauqi
a wajen mutanenka, ya kai sarkin varayi ya za ai a
sato sarqar dake wajen gimbiya lashmin alhalin dare
da rana tana wuyanta a xaure, kuma ko wanka zata
shiga kewaye bata cireta? Ko sau xaya bata tava cireta
ba tun sanda ta cire sarqa a wuyan Amzad sa’ar da
suna yara a lokacin da aka rabasu. Idan na samu
Amzad da sarqa na samu cikaken lagonta kuma duka
umarnin dana bata dole ta bi saboda zata iya salwantar
da rayuwarta da mulkinta saboda Amzad.
97
BAYAN MUTUWA
Naji ka tambayi wai mene nawa lagon? Zan iya
sanar da kai nawa lagon amman sai idan kaima ka
sanar da ni naka lagon” Koda jin haka sai sarkin
varayi ya bushe da dariya sannan ya risina gaban
Attajiri Huzulu yace “Tuba nake ya shugabana haqiqa
na yi kuskure kuma ba zan qara ba, yanzu ina neman
izininka a yau xinan zan tura zaqaquran yarana guda
biyu izuwa cikin birnin misira. Mace xaya namiji xaya
su ne Inzal da Karimat. Imzal zai sato Amzad ita
kuma Karimat zata sato wannan sarqa dake wuyan
Gimbiya Lashmin” Lokacin da sarkin varayi ya zo
nan a zancensa sai attajiri huzulu ya yi shiru yana
tunani har izuwa tsawon ‘yan daqiqu sannan ya miqe
tsaye ya yi xan taku uku ya juyo ya fuskanci sarkin
varayi yace.
“Ko shakka banayi Imzal zai iya sato Amzad
amma karimat ba zata iya sato sarqa gimbiya lashmin
ba, idan kuma ta samu nasara satota zan kuwa bata
kyautar dukiyar da babu ita babu talauci har izuwa
qarshen rayuwarta. Maza a kirawo Inzal sa Karimat su
98
BAYAN MUTUWA
yi shiri su tafi izuwa birnin misira” Kafin Attajiri
huzulu ya gama rufe bakinsa tuni an kirawo Inzal sa
Karimat sun bayyana a gaban sarki varayi.
Shi dai Inzal wani kyakkyawan saurayi ne mai
kwarjinin gaske kuma ya cava ado kai da ganinsa
kasan cewa xan sarkine ko wani xan babban attajiri
kuma fuskarsa tana xauke na xauke da alamun mutum
mai tausayi da jin qai sai dai kash akasin hakanne a
cikin zuciyarsa domin mutune mai tsananin mugunta
da rashin imani.
Ita kuma karimat mace ce doguwa mai qirar
kalangu kuma baqar fata. Ba za a kirata kyakkyawa ba
kuma ba za a kirata mummuna ba. Tana da yalwar
gashin kai domin ya zubo har qasan kwankwasonta,
kaurin jikinta madaidaicine ba yabo ba falasa, duk da
kasancewar karima a qarqashin sarkin varayi take ba
zaman kanta take ba, amma jikinta luwai-luwai yake
kamar na jarirai, hakane zai tabbatar maka tana samun
jin daxi da hutu sosai. Karimat tana xaya daga cikin
manya-manya hadiman sarkin varayi wanda ya aminta
99
BAYAN MUTUWA
da su, kuma yana qaunarta yana son ma ya mallaketa a
matsayin matarsa ta uku, amma saboda yana da wani
buri guda xaya wanda ita kaxai zata iya cire masa shi
don haka ya dakata da batun aurenta. Saboda gaba
xaya hadiman sarkin varayi sun san yana sonta don
haka ko kusantarta basa yi, shima sarkin varayin baya
zuwa inda take idan ta zo fadarsa to zata je aiwatar da
wani aiki na musamman.
Lokacin da karimat da inzal suka tsaya a gaban su
sarkin varayi, attajiri Huzulu ya yi arba da ita sai ya ji
ya kamu da tsananin sha’awarta don haka bai san
lokacin daya qura mata idanu ko qiftawa baya yi ba.
Sai da sarkin varayi ya tava hannunsa ya yi firgigi
kamar ya tashi daga bacci sannan ya basar sarkin
varayi ya yi murmushin qarfin hali.
“Amman wannan hadimar taka mai kyauce”
Sarkin varayi ya murmushi yace “Ai wannan ne aiki
na qarshe da zata yi ta zama matata”Koda jin haka sai
jikin Attajiri Huzulu ya yi sanyi ya kauda kai ga barin
100
BAYAN MUTUWA
kallonta, shima sarki varayi yace “Ya ka ganta? Zata
iya wannan aikin ko ba zata iya ba?”.
Attajiri Huzulu ya yi murmushi yace “Ai da ganin
kura zata ci mutum” sarkin varayi yace “Ta qware
wajen iya qissa da shirya makirci ga iya magana na
turata izuwa qasashe saba’in da biyu ta jagoranci
gagarumar sata a masarautun amma ko sau xaya ba a
tava samun rashin nasara ba, karimat mace ce mai
tsananin sa’a aduk abinda ta saka a gaba, wannan ce
sata ta saba’in da uku na kuma yi mata alqawarin shi
ne aikinta na qarshe wanda zan ‘yanta ta na
aureta”Koda sarkin varayi ya zo qarshen maganarsa
sai murmushi ya suvuce wa karimat ta kamu da
tsananin farin ciki amma a farin cikinta babu batun
aure da sarkin varayi domin shi ne mutum na qarshe
data tsana a duniya, ba komai ya saka ta tsaneshi ba
face tun tana da shekara shida a duniya ya xaukota
daga qasarsu bayan ya kashe iyayenta ya kwshe
dukiyarsu, ya tafi da ita ya baiwa matarsa ita ta riqeta
ta riqa bata horo na koyon sata, yaqi da jarumta a haka
101
BAYAN MUTUWA
ta girma ta cika shekara ashirin da xaya ta zama
gagarumar varauniya mashahuriya.
Abinda sarkin varayi bai sani ba ko yaushe da
dare sai karimat ta yi mafarkin abinda ya faru ga
iyayenta tun tana shekara shida, amafarki tana ganin
lokacin da sarkin varayi ya zare takobi ya sare
mahaifiyarta da mahaifinta ita kuma tana zaune tana
kuka ya sureta ya fice da ita daga cikin gidan tana ihu
tana kiran sunan iyayenta. A kan idanunta sarki varayi
ya saka aka cinawa gidansu wuta ya qone qurmus. A
qarqashin zuciyar karimat ta ci burin cewar komai
daxewa sai ta xauki fansar ran iyayenta a kan sarkin
varayi.
Sarkin varayi ya dubi inzal da karimat yace “Za
ku tafi izuwa birnin misira yanzu kai zaka sato Amzad
wanda ake shari’arsa da maigirma Huzulu ita kuma
karimat zaki sato mana sarqa wuyan Gimbiya lashmin,
bana son ku shafe sama da kwanaki bakwai a cikin
birni ba tare da kun kammala aikinku ba, maza kuje
sarkin gida ya baku dawakai da guzuri yanzu ku tafi”
102
BAYAN MUTUWA
Da jin haka sai Inzal da Karimat suka rusuna sannan
suka juya tare ficewa daga cikin fadar. Fitarsu ke da
wuya sai attajiri Huzulu da sarkin varayi suka dubi
juna suka bushe da dariya farin ciki saboda ji suke
kamar buqatarsu ta gama biya.
Wannan shi ne abinda ya faru a fadar sarkin
varayi, fadar da ake yiwa laqabi da darul uzur inda
attajiri huzulu ya vuya bayan ya gudu daga babbar
kurkuku na birnin misira.
A can birnin misira kuma lokacin da sarki yaqi ya
baro gidan sarauta bayan ya gana da gimbiya lashmin
sai zuciyarsa ta cika maqil da wasi-wasi gami da
103
BAYAN MUTUWA
firgici. Ba komai ne yasa ya tsinci kansa a cikin wasuwasu gami da fargaba. Ba komai ne yasa ya tsinci
kansa ba face tunanin hanyar fa ya kamata yabi ya
samu nasarar taimakon lashmin domin ta cika burinta.
A wannan lokaci yana tafiyane yana ta sauri domin ya
isa gidansa ya zauna yayi tunani mai zurfi domin
samun mafita kwatsam sai yaga mutum tsaye akansa
nan take zuciyar sarki yaqi ta buga da qarfi tsaya cak a
inda yake suka fara kallon-kallo da mutumin dake
tsaye a gabansa.
Ba wani bane wannan mutum face sarki Raihan
wato mahaifin gimbiya lashmin cikin alamun tsananin
mamaki gami da tsoro sarki yaqi ya qaraso kusa da
sarki Raihan ya zube qasa ya kwashi gaisuwa sannan
ya miqe tsaye ya dubeshi kansa na sunkuye cikin
biyayya yace “Ya shugabana mene ne ya fito da kai
daga gidan sarauta ka shigo cikin gari a wannan
lokacin? Sa’ar da sarki Raihan ya ji wannan tambayar
sai ya yi ajiyar zuciya sai yace “Na xauki karagata na
baiwa ‘yaarta a ranar data hau ta yi abinda na kasa yi a
104
BAYAN MUTUWA
shekara ashirin da biyar tunda ta sami nasarar kawar
da babban maqiyina daga cikin birnina amma kuma ta
tsokano mana tsoliyar dodone, na samu labarin cewar
atttajiri Husulu ya gudu daga kurkuku, tunda na samu
wannan labarin na kasa ci da sha kuma na kasa bacci,
saboda nasan cewar qarshen mulkinmu ya zo kuma
adalci ga talakawa ya qare ni da duka zuri’arta da
dukkan masu biyayya a gareni ta su ta qare domin
attajiri Huzulu ba zai barmu muci gaba da rayuwa ba,
ko dai a murqushe qasarmu gaba xaya ko muyu ragas
mu da attajiri Huzulu da jama’arsa
Yanzu dai kaine kaxai abin dogarot a shin zaka
iya taimakon ‘yarta akan aiwatar da shirinta na daqile
attajiri Huzulu? Abune na siyar da rai domin babu
tabbacin nasara a cikinsa, abune mai matuqar wahala
idan kana ganin ba zaka iya taimakonta ba to ina da
zavi na biyu, shi ne dani da gimbiya da duk masoyana
mu bi dare mu sulale mu gudu mu yi qaura daga
garin”.
105
BAYAN MUTUWA
Lokacin da sarki ya zo nan sai hankalin sarkin
yaqi ya dugunzuma ainun fiye da kowanne lokaci ya
rasa abinda ke masa daxi a duniya ya yi shiru suna
kallon juna har izuwa tsawon daqiqa biyar daga bisani
kuma sai sarki yaqi ya kalli sarki cikin nutsuwa yace.
“Ya shugabana nan ba wajen da za mu yi wannan
maganar bane, saboda babu sirri kuma ka yi ganganci
da kake fitowa daga gida a irin wannan lokacin saboda
maqiya za su iya sakawa a saceka” Sarki raihan ya yi
murmushi yace “Babu wani maqiyi daya fini sanin
birni misira da kuma mutanen da suke cikinsa, nasan
hanyoyin da zanbi ba tare dana haxu da wani tsautsayi
ba, duk wani baqo da zai shigo garinan ina ganinsa
kuma ko da zai voye fuskarsa sai da na ganka yanzu
sannan na buxe fuskarta koma na gama nazarin
wannan wurin da muke tsaye. Yanzu mu wuce izuwa
gidankaa domin mu zauna mu tattauna tabbas akwai
shawarwari da zan baka za su yi matuqar taimaka
maka”.
106
BAYAN MUTUWA
Sarki Raihan yana gama faxar haka sai ya xauki
mayafin dake kafaxarsa ya xora akan fuskarsa ya rufe
fuskarsa da shi yadda idanunsa kaxai ake gani sannan
ya kama hannun sarki yaqi ya jashi suka nausa cikin
gari izuwa hanyar da zata kaisu gidan sarki yaqi.
Al’amarin Gimbiya lashmin kuwa bayan sun rabu
da sarki yaqi ta shiga turakarta sai ta shiga sabon
tunani mai zurfi inda ta ji cewar babu abinda take so a
cikin faxin duniya sama da mallakar Amzad a
matsayin abokin rayuwarta. Nan take ta tambayi kanta
a cikin zuciya tace ta yaya zan kwato dukanin dukiyar
Amzad daga hannun Attajiri Huzulu a cikin kwanaki
biyu kacal? Ta yaya zan gani inda attajiri Huzulu yaje
ya voye na saka a kamoshi a gurfana da shi a gabana a
tsakanin yau zuwa gobe? Yin haka abune mai wuya
amma kuma ai mulki ba wasabane. Me mulki yana yin
komai indai abun mai yiwuwane a doron qasa.
Matakin da zan bi ya zama dole a gobe a zo da Amzad
fada na ganshi ya ganni kuma na tuno masa da koni
wacce a gareshi, mataki na biyu a daren yau dolene na
107
BAYAN MUTUWA
gana da babban bokan attajiri Huzulu wato boka
zallazi domin ziyara zan kai masa ta bazata tunda
shima nasan lagonsa lallai zai taimakamin akan attajiri
Huzulu koda gama aiyana wannan al’amarin sai
gimbiya lashmin ta qwalawa ilela kira ta shigo turakar
da gudu ta zube qasa a gabanta, lashmin ta dubeta tace.
“Mike tsaye muyi magana ki kalleni ido cikin ido”
Da jin haka sai Illela ta miqe ta dubeta cikin nutsuwa
Gimbiya Lashmin tace.
“Ina son a cikin darenan na kai ziyara can bayan
gari wajen boka zillazi a sirrance ba tare da wani ya
ganmu ba, kece kaxai zaki rakani, bana son a ga
fitarmu daga cikin gidanan ko dawowarmu sannan
kuma ina son mu tafi da akwatinan ta lu’u lu’un sarki
ki riqe mu tafi da ita” Koda jin wannan maganar sai
Ilela ta firgita ainun jikinta ya kama rawa a lokacin da
idanunta suka zaro tamkar tayi arba da mutuwa tace.
“Haba ya shugabata ki sani ya shugabata duka
dukiyar sarki babu abu mai darajar wannan akwatin ta
108
BAYAN MUTUWA
lu’u lu’u a duk nahiyar nan gaba xaya, shin saceta
kike so muyi?” Gimbiya Lashmin ta girgiza kai
alamar cewar ba haka ba tace.
“Fansa zan bayar a matsayin raina dana Abbana da
kuma amzadm ki sani ba domin komai boka zulazi
yake taimakon attajiri Huzulu sai saboda ya yi masa
alqawarin cewa da zarar ya karvi karagar gidannan zai
bashi akwatin lu’u lu’un sarki. Ita kuma wannan
akwatin babu mai tavashi da hannunsa ba tare da
hannun ya guntule ba har sai ya zama sarki garinan
duk wanda ya mallaki wannan akwatin zai zama duka
nahiyar babu mai kuxinsa, kuma dole sai mai mikin
garin ya xauketa da hannunsa ya damqa maka sannan
zaka ci gajiyarta. An turo varayi sama da dubu ashirin
izuwa gidan sarautar domin su sace wannan akwati
amma dukansu da guntulallen hannu suke komawa, ki
sani idan na xauketa na saka a cikin jakarnan ta akwati
zan iya baki ki riqe, duk abinda nake buqata nasan
zaki iya shi yasa na umarceki da ki ruga kije ki
aiwatar da shirye-shirye na wannan fitar da za mu yi a
109
BAYAN MUTUWA
cikin wannan dare” Ba tare da wata gardama ba Ilela
ta risina tace.
“Angama ya shugabata” Cikin hanzari Ilela ta juya
ta fice, ita kuma Gimbiya lashmin sai ta juya ta shiga
cikin turakarta ta soma shirin fita.
Al’amarin Inzal da karimat da xan saqo makanu
suka baro fadar Darul uzu amma da ya rage sauran
baifi tafiyar rabin sa’aba