BAYAN MUTUWA

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Adventure

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 20K words

a mafarki ba a tava zaton cewar zai tava faruwa ba.
Bayan an fice da attajiri Huzulu sai Gimbiya
Lashmin tasa aka sallami kowa a fadar har da saurayi
Amzad kuwa amman kafin ya tafi sai ya faxi qasa a

35

BAYAN MUTUWA

gaban Lashmin ya fashe da kukan farin ciki kuma ya
kama yi mata godiya kamar bazai daina ba har sai da
ta daka masa tsawa a gaban Dakaru da kuyanginta
sannan ya shiga taitayinsa sannan ta dubeshi tace.
“Ban taimakeka domin komai ba sai domin
na kawo sauyi a wannan qasar tamu na kawar da
zalunci na shimfixa adalci, ko kai na kama da rashin
gaskiya sai na hukunta ka, ka sani cewar kaima yanzu
rayuwarka na cikin hatsari saboda haka dolene na
haxaka da Dakaru waxanda za su baka kariya kuma ba
zaka ci gaba da zama a wannan gidan hayan ba” Koda
jin haka sai Amzad ya dubi Gimbiya Lashmin cikin
alamun tsananin damuwa yace.
“To mahaifiyata fa? Wacce yanzu haka tana
can gidan tana jiran dawowata? Kin san cewa ta tsufa
ainun bata gani kuma bata iya tafiya” Koda jin haka
sai Lashmin tayi murmushi tace.
“Kada ka damu tuni tun kafin ma a fara yin
wannan shari’a taku nasa an xauketa an akita can
gidan sarki dake bayan gari, kuma yanzu can za a
kaika wajenta. Na tabbatar da cewar can za ku sami
cikakken tsaro har izuwa ranar da za a kammala
wannan shari’a taku” Koda gama faxin haka sai
Lashmin ta dubi mataimakin sarkin yaqi tace.

36

BAYAN MUTUWA

“Yakai muzainu wannan aikin kane, ka
jagoranci Dakaru xari ku raka Amzad izuwa can gidan
sarki na bayan gari kuma ka zauna tare da shi acan har
izuwa tsawon lokacin dana neme ku” koda jin haka sai
Muzainu ya dubeta cikin tsananin damuwa yace mata.
“Ya shugabata idan sarkin yaqi baya nan
nima bana nan akwai matsala ta tsaro a gidanna fa”
Gimbiya Lashmin tace.
“Ai nasan da haka amman kada ka manta
cewa kafin kafin ma ka isa can inda na aikeka tuni
sarkin yaqi ya dawo daga can kurkuku ko kuma kana
zaton cewa za a kawo mana harin sumame a cikin
wannan xan tsukukun lokacin?” Muzainu ya yi
murmushi yace.
“Aa bah aka bane kawai dai bana son ni da
sarkin yaqi muyi laifi ne a wajen mahaifinki” koda jin
haka sai Lashmin ta yi murmushi tace.
“Ai yanzu ni ce akan karagar mulki ba
mahaifina ba, saboda haka idan ma laifi ne ni za
kuyiwa bashi ba, indai kana tsoron tuggun attajiri
Huzulu ne to ka kwantar da hankalinka domin na
xauki matakan tsaro tsaurara akan hakan”.
Nan take Muzainu ya kama hannun Amzad
ya jashi suka nufi qofar fita daga fadar dakaru na take

37

BAYAN MUTUWA

musu baya. Sauran qiris Amzad ya fice ta cikin qofar
fadar sai ya juyo suka haxa idanu shi da Gimbiya
Lashmin take yaga ta yi masa wani irin kallo wanda
ya ximataushi ya jefashi ciki tsananin, mamaki,wasuwasu, fargaba da rashin fahimta lokaci guda duk su
biyun suka juyawa junansu baya ta nufi hanyar da zata
kaita cikin gidan sarautar shi kuma ya fice daga fadar
yana mai bin Muzainu a baya.
Da sauri, dakaru sun kewaye shi suna gudugudu sauri-sauri.
Lokacin da Gimbiya Lashmin ta shiga cikin
gidan sarauta sai ta nufi turakar mahaifinta sarki
Salhan kai tsaye tana isa babban falonsa sai ta iske shi
a zaune tare da mahaifiyarta a cikin nishaxi suna ciyeciye da shaye-shaye har suna yin soyayya irin tasu ta
manya.
Al’amarin day a yi matuqar bata mamaki
kenan domin a zatonta zata zo ta riskeshi ne a cikin
tsananin fushi bisa abinda ta aikata yau a fada domin
ta tabbatar da cewar tuni labari ya riskeshi. Koda sarki
Salhan yaga Gimbiya Lashmin ta durfafo inda suke
zaune sai ya miqe tsaye zumbur cikin matuqar farin
ciki ya tarbeta yana mai rungumeta gami da sumbatar
goshinta sannan yace.

38

BAYAN MUTUWA

“Yake ‘yarta kiyi sani cewar yaune nayi
alfahari dake a matsayin ‘yarta wacce zata iya gadata.
Sai yaune na tabbatar da cewar ke jinina ce. Domin
kin cire min qaton dutsen daya danne ni tsawon
shekaru ashirin da biyar, na daxe ina son hukunta
attajiri Huzulu amma na kasa amma ke gashi cikin
daqiqu kaxan kin hukunta shi kuma a lokacin da ya
dace ya karvi irin hukuncin da kika yi masa.
A iya tunanina duk wanda ya mutu shi kenan
komai na shi ya tafi kenan. Nazmir mahaifin Amzad
ya mutu da tsawon shakaru ashirin da biyar dukiyarsa
ta tafi ga hannun azzalumi Huzulu amma yau gashi za
ki dawo da wannan dukiyar izuwa hannun tsatsonsa,
wannan fa shi ne RAYUWA BAYAN MUTUWA sai
yanzu a bayan mutuwar Nazmir sannan iyalansa za su
yi sabuwar rayuwa irin wacce basu tava yinta ba,
domin idan wannan dukiyar ta koma hannun su, babu
sa’ansu a tarin dukiya a gaba xaya wannan nahiyar
tamu.
Lallai kuwa idan kika samu wannan nasara
kinyi abinda har abada ba za a manta da ke ba a tarihin
qasar nan, shi kuma Amzad ba shi da abinda zai iya
biyanki da shi har izuwa qarshen rayuwarsa” Koda jin

39

BAYAN MUTUWA

wannan batu sai gimbiya Lashmin tayi murmushi
sannan tace.
“Akwai abinda Amzad zai iya biyana da shi,
ba komai bane face zuciyarsa da soyayyarsa, burina
kawai ya so ni kuma ya qauna ce ni qaunar da babu
algus a cikinta, ya riqe min alqawari na soyayya har
izuwa ranar da zamu zamo abokan rayuwar juna
domin mu samu zuri’a ta gari” koda Gimbiya Lashmin
ta zo nan a jawabinta sai mamaki ya turniqe sarki da
mahaifiyar Lashmin suka zazzaro idanuwa suka kasa
cewa komai.
Daga can sai sarki ya dubeta yace mata
“Yaushe kika fara ganin Amzad hard a za ki ce kin
kamu da son sa haka?” Koda jin wannan tambaya sai
hawaye ya zubo wa gimbiya Lashmin sannan tace.
‘Na fara son Amzad tun ina da shekara
bakwai a duniya, yakai Abbana shin zaka iya tunawa
da wata rana da yammaci sakaliya sa’adda ka fita
wani rangadi tare da ni” Koda jin wannan batu sai
sarki salhan ya xaga kansa sama ya faxa kogin tunani.
Kimanin shekaru goma sha xaya da suka
gabata sarki salhan ya fita rangaxi a cikin keken
dokinsa tare da ‘yarsa Gimbiya Lashmin a lokacin

40

BAYAN MUTUWA

tana da shekara bakwai kacal a duniya. Dakaru
kimanin xari uku ne ke kwaye da su suna tafiya a
gefen wani daji dake daf da birnin nasu na misra sai
kawai suka ji ana harbor musu kibiyoyi.
Ashe Dakarun sumame ne suka kawo wa
sarki hari. Nan take cikin gaggawa dakaru suka
yanyame keken dokin sarki suka kareshi da manyan
garkuwoyinsu don kada wata kibiyar ta zo ta sameshi
ko ta soki Gimbiya Lashmin.
Ana cikin hakanne sarkin yaqi ya leqo cikin
keken dokin ya dube shi cikin alamun tsananin tashin
hankali yace.
“Ya shugabana maqiyane suka kawo mana
harin bazato, duk yadda aka yi suna da xan leqen asiri
a cikin fadarmu ta haka ne suka samu labarin wannan
fitowar ta mu” Koda jin haka sai sarki salham ya
girgiza kai yace.
“Tabbas zancenka gaskiya ne amma sai
bayan mun tsira sannan za mu yi bincike mu gano ko
wanene wannan munafikin,wai shin adadin dakarun
sumamen zai kai nawa?” Sarkin yaqi yace.
“Ya shugabana sun ninkamu sau uku idan
muka bari suka iso nan suka riskeka bani da tabbacin
kai da Gimbiya za ku tsira, abu mafi kyau shi ne

41

BAYAN MUTUWA

yanzu ku fito mu ruga izuwa cikin daji mu da tsirarun
dakaru inyaso sauran Dakarun mu suyi kamar kana
cikin wannan keken dokin su ci gaba da tsoronsa.
Kafin a cim masu munyi nisa a cikin dajin
mun zagaya tacan mun koma cikin birnin mu” Koda
jin wannan batu sai sarki salham ya dubi sarkin yaqi
cikin fushi yace.
“Yanzu kana nufin mu gudu mubar sauran
jama’ar mu anan a kashe su a banza kenan?” Sarkin
yaqi yace.
“Ai tun tuni sun siyar da rayukan su domin
kare naka dana iyalinka don tsare darajar qasarmu, ka
tuna cewar idan aka kasheka anan cikin dajin tamkar
anci birnin mu da yaqine. Idan waxan nan abokan
gabar suka san cewar sun gama da kai ai kuwa
komawa za su yi suyi gaggarumin shirin yaqi su zo su
baje birnin namu gaba xaya, jinin mutanen mu nawa
ne zai zuba anan? Adadin dukiya nawa ne zata
salwanta, kaga kenan ashe rayuwarka zata kuvutar da
miliyoyin mutane da miliyoyin dukiya”.
Koda jin wannan batun sai sarki salhim ya
yi wuf ya xauki Gimbiya Lashmin ya goyata a
bayansa ya xaureta tamau sannan ya zare takobinsa

42

BAYAN MUTUWA

kuma ya xauki garkuwarsa ya fito daga cikin keken
dokin.
Nan yake shi da sarkin yaqi da tsirarun
dakarun waxanda basufi su arba’inba suka ruga izuwa
cikin daji suka bar sauran dakarun tsaye a gaban
keken dokin suna gadinsa.
Tafiyar su sarki ke da wuya sai ga dakarun
sumamen sun iso bisa dawakansu da yawa. Koda suka
hango keken dokin sarki sai dukkaninsu suka zare
takubbansu suka afkawa dakarun dake tsaron keken
dokin aka ruguntsime da yaqi.
Duk da cewar dakarun sumamen sun ninka
dakarun sarki salhan sau uku sai da aka shafe sa a
guda cif ana baqin gumurzu sannan aka qarar da
dakarun sarki.koda aka gama karkashe su aka leqa
cikin keken dokin sai aka ga wayam. Nan take
shugaban dakarun sumamen ya kurma ihu! Yace.
“Tabbas waxannan mutanen yaudarar mu
suka yi, tun xa zu sarkin misra ya fice daga cikin
keken dokinnan ya gudu ku zo mu bi sawun su” Yana
gama faxin hakan sai ya zaburi dokinsa yabi hanyar
da su sarki salhan suka bi.

43

BAYAN MUTUWA

Suma saran dakarun sai suka rufa musu baya
suka rinka tsala gudu tamkar dawakan nasu za su tashi
sama.
**
Al’amarin sarki salhan da sarkin yaqi da
tsirarun dakaru kuwa tunda suka fara gudu basu tsaya
ba, cikin sa a kuwa suka hango qofar birnin misra
daga can nesa tazarar kimanin zango xari.
Nan take farin ciki ya lulluve su suka qara
gudun su, sai daya kasance bai fi sauran taku baifi
saba’in ba tsakaninsu da bakin qofar garin sai kawai
suka hango dakarun sumame acan bayan su kaxan sun
durfafo inda suke a guje bisa dawakai.
A daidai wannan lokacin Nazmin mahaifin
Amzad ya dawo daga gona yana save da fatanya a
kafaxarsa kuma yana riqe da hannun xansa Amzad
yaron da bai wuce shekara tara ba a duniya.
Lokacin da su sarki salhan suka waiga
bayansu yana goye da Gimbiya Lashmin suka hango
dakarun sumame a bayansu sai suka qara qarfin
gudunsu, koda ganin haka sai dakarun sumamen suka
soma xana kibiyoyi akan baka suna harbinsu kuma
suna daxa kusanto su. Nan fa suka soma yiwa dakarun

44

BAYAN MUTUWA

sarki salhan xauki xai-xai suka riqa faxuwa qasa
matattu.
Har ya kasance sauran sarkin yaqi da sarki
salhan kaxai suka rage a raye suna ta gudu. Tun daga
nesa sarkin yaqi ya riqa qwalawa masu gadin qofar
gari kira yana basu umarnin su buxe qofar amma da
yake masu gadin basu shaida ko su wayeba sai sukaqi
buxe qofar.
A wannan lokacin Nazmir da xansa Amzad
kuwa na daf da isa bakin qofar birnin Misra.koda suka
jiyo gudun mutane biyu a bayansu sai suka waiwaya a
firgice, take Nazmir yaga ashe sarki ne da sarkin yaqi
suke wannan gudun na ceton ransu, kuma ga dakarun
sumame can a bayansu sun durfafo sauran qiris su
cimmasu, kawai sai Nazmir ya juya yana dakawa
masu gadin tsawa yana musu ishira cewar sarki ne fa,
nan take masu gadin suka yi sauri suka buxe qofar.
Amman kuma sai masu gadin suka kasa
fitowa domin kawowa sarki xauki saboda ganin
yawan abokan gaba domin idan suka fito za a samu
galabar shiga cikin birnin.

45

BAYAN MUTUWA

BAYAN MUTUWA 4
Kawai sai gani aka yi kibiya ta soki sarki a
cinya ya kife qasa, Lashmin dake goye a bayanshi sai
ta faxi qasa ta riqa mirginawa izuwa baya can wajen
da maqiya ke tahowa tana ihu, shima sarkin yaqi sai
kibiya ta soke shi a gadon baya ya kife qasa.
Koda ganin abinda ya faru sai Nazmir ya
saki hannun xansa Amzad ya ruga da gudu izuwa inda
sarki yake kwance ya sunkuceshi ya azashi a kaxarsa
ya ruga da gudu dashi izuwa cikin birnin misra ko
tunawa da batun xansa bai yi ba.
Shima yaro Amzad sai ya ruga da gudu ya
xauko Gimbiya Lashmin a kafaxarsa ya nufi qofar
birnin misra, yana gudu ana harbor masa kibiyoyi har
kibiya guda ta soke shi a hannu sai ya yi matuqar
dauriya yaci gaba da gudu a haka jini na zuba a
hannunsa ga lashmin a kafaxarsa yana layi jiri na
xibansa amma sai daya shige cikin qofar birnin.

46

BAYAN MUTUWA

Sarkin yaqi ne ya qaraso da qyar da gudu
yana faxuwa yana tashi har ya shiga cikin qofar, ai
kuwa yana shiga sai dakarun dake tsaron qofar garin
suka yi sauri suka mayar da qofar suka rufeta kuma
suka hau kan ganuwa suka xana kwari da bakansu.
Koda ganin haka sai dakarun sumamen suka
yi tirjiya, bisa dole suka kaxa dawakansu suka juya da
baya cikin baqin cikin rashin samun nasarar kashe
sarki salhan.
A cikin birni kuwa ranga-ranga aka xauki
sarki da sarkin yaqi aka tafi da su izuwa gidan sarauta.
A lokacin wani bafaxe ya zo ya fizge
Gimbiya Lashmin daga kan kafaxar Amzad sai tayi
wuf ta fizge wata qaramar sarqa dake wuyan Amzad
ta dubeshi cikin murmushi tace.
“Har abada ba zan mance da kai ba, ka zo
gidan sarki ka amshi sarqarka a hannuna, ni kuma zan
saka maka da abinda yafi komai daraja a wajena”.
Tana gama faxin haka sai ta riqa xagawa
Amzad hannu shima sai ya rinqa xaga mata hannu har
aka hau kan doki da ita aka ruga da gudu suka qule ya
daina hangota, a sannan ne mahaifin Amzad ya kama
hannunsa ya jashi suka nausa cikin birni.

47

BAYAN MUTUWA

A lokacin da sarki salhan ya zo nan a
tunaninsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi Gimbiya
Lashmin yace.
“Yanzu ashe tun daga wannan ranar da
Amzad ya ceci rayuwarki kika kamu da son shi?”
koda jin wannan tambayar sai itama Gimbiya Lashmin
ta zubar da hawaye sannan ta zura hannu aljihun
rigarta ta fiddo wannan sarqa ta Amzad ta nunawa
sarki tace.
“Qwarai kuwa tsawon waxannan shekarun
ina ajiye da sarqa Amzad kuma ina begensa a cikin
zuciyata dare da rana. Tambayar da nake son na yi
maka mene ne ya hana Amzad zuwa wajen da nake ya
karvi sarqarsa dake hannuna? Mene ne dalilin daya
saka duk sa’adda nace kasa aje a nemo Amzad da
mahaifinsa sai kace har izuwa tsawon waxannan
shekarun kace an halaka shi, nima kuma ka saka aka
tsare ni a cikin gidan sarauta baka barina na fita sai da
sharaxin wajen da zani nan xin zanje, ka hanani
samun sakewa da zan yi bincike akan sa har zuwa
girmana.
Tabbas ka jefani a cikin kurkukun soyayya
wanda yafi rijiya gaba dubu, ka sanya min xaci a
zuciya wanda yafi azabar fitar rai, kuma ka dusashe

48

BAYAN MUTUWA

min hasken idanu da baqin ciki da yafi dare duhu,
tsawon shekaru sha xaya kenan ban ga masoyina ba
Amzad rabona da shi tun ina da shekaru bakwai a
duniya sai yau da aka gurfanar dashi a gabana domin
na yi masa shari’a da azzalumin attajiri Huzulu.
To ka sani ko ka bani amsar tambayoyina ko
kaqi a yau xinnan sai naje na baiwa Amzad sarqarsa
wacce na cire a wuyansa tun muna yara a ranar day a
ceci rayuwata. Ko kana so ko baka so yakai Abbana
sai na cika alqawarina a gareshi na bashi abin da yafi
komai daraja a wajena kuma ba komaibane face
soyayyata da kuma aurena”.
Lokacin da Gimbiya Lashmin ta zo nan a
zancenta sai shima sarki sairan ya ji hawaye sun
suvuce masa don haka sai ya kamo Gimbiya Lashmin
ya rungumeta a qirjinsa yana kuka yace.
“Ki gafarta min yake ‘yarta kiyi sani cewa
akwai dalili mai qarfi wanda yasa na raba rayuwarki
da Amzad xan Nazmir waxanda suka ceto rayuwarmu
a tare kuma a lokaci guda, dalili kuwa shi ne bayan
anyi mana magani ni da sarkin yaqi wato an cire
kibiyoyin dake jikinmu an sa mana magani don kashe
dafin kibiyar sai kawai muka ga bokana wato Darzas
ya baiyana tsulum a gabanmu.

49

BAYAN MUTUWA

Boka Darzas ya dubeni cikin damuwa yace
“Ya shugabana kayi sani cewar ba wani bane ya turo
dakarun sumame su kasheka ba face sarki zardar na
birnin mailus, kuma munafikin da ya sanar da su
cewar zaka fita yawon rangaxi ba wani bane face
bawanka yunus mai kula da dawakanka na hawa,
musamman sarki mailas ya siyar da shi izuwa fa
farakenku suka zo dashi nan qasar,kai kuma ka siye
shi a matsayin bawa har ka aminta da shi, saboda
qwazon shi a wajen aiki da qwarewarsa wajen kiwon
dawakai.ban gano wannan sirrin ba sai yanzu da zan
zo wajenka na yi bincike akan kawo wannan harin.
Abu na gaba da zan sanar maka kar ka sake
kabar wata alaqa ta soyayya ta qulu a tsakanin
Gimbiya Lashmin da Amzad xan Nazmir waxanda
suka ceci rayuwarka xa zu a qofar birninnan daga
hannun dakarun sumame, domin bincike ya nuna ba
za su tava zama abokan rayuwar juna ba, kuma
qarshen soyayyar tasu tana qunshe da baqin ciki a
gare su da duk masoyansu” Boka Darzas yana gama
faxin haka sai ya vace vat.

50

BAYAN MUTUWA

S

arki Salhan ya dubi Gimbiya Lashmin
ya ci gaba da magana “Bisa wannan
dalilin tun daga wannan ranar na
sanya hijabi a tsakaninki da Amzad har mahaifinsa ya
rasu ban bari kun sake ganin junaba. Ki yafe min yake
‘yarta, lallai ki yafe min na yi miki babban laifi amma
son da nake miki ne gami da son ganin kyakkyawar
rayuwarki a gaba yasa na yanke wannan hukunci”.
koda sarki salhan ya zo nan a zancensa sai
Gimbiya Lashmin ta fashe da matsanancin kuka,
al’amarin daya karya zukatan iyayenta kenan suka
kamu da tsananin tausayinta.
Don haka sai mahaifiyarta ta janyota ta
rungumeta a kan qirjinta tana mai rarrashinta tana bata
baki har izuwa tsawon ‘yan daqiqai amma bata daina
kukan ba, daga can sai Lashmin ta janye jikinta daga
cikin na mahaifiyarta ta miqe tsaye ta dubi sarqa tace.
“Ya kai Abbana kayi sani cewar babu wani
qarfi wanda ya isa ya dates so na gaskiya a tsakanin
masoya,addini ko sihiri, dukiya ko talauci,wuya da
daxi basa raba masoya sai dai mutuwa da qaddara. ni
banyi imani da dukkan abinda bokayen ku ke faxaba
muddin ya shafi soyayyata, idan kuma har abinda suka
faxa ya zama gaskiya to na yarda na mutu akan qirjin

51

BAYAN MUTUWA

masoyina domin shi ne abinda ya fiye min komai farin
ciki a rayuwata” koda gama faxin haka sai Gimbiya
Lashmin ta miqe tsaye da sauri ta juya ta fice daga
cikin turakar mahaifiyarta na kwala mata kira amman
ko waigowa ba.
Koda ganin haka sai mahaifiyar tata ta miqe
da sauri da nufin taje ta ruqo ta amman sai sarki ya yi
wuf ya runqota ya dakatar da ita yace mata.
“Kar ki kuskura ki dakatar da zuciyarta da
take ruruwa da wutar soyayya, domin daidai take da
mahaukacin zakin da ya fusata a cikin daji a lokacin
da yake fama da tsananin yunwa,kinsa cewa idanunta
a rufe suke zai iya banke kowa” Koda jin wannan
batun sai mahaifiyar Lashmin ta koma ta zauna kusa
dashi ta xora kanta akan qirjinsa a lokacin da hawaye
ya zubo mata shi kuma ya qanqameta a jikinsa tana
mai cewa.
“Haqiqa ‘ya tayi gadon ubanta akan zafin
soyayya ko kuwa ka mance ne da yadda muka mallaki
junanmu, mun sha baqar wahala da gwagwarmaya?”
koda jin wannan batu sai hawaye ya suvutowa sarki
salhan yace.
“Zan iya mancewa da komai na rayuwata
amma ba zan iya mancewa da tarihin soyayyata ba

52

BAYAN MUTUWA

yake matata, a duniya banga abin da yafi soyayya daxi
da haxari ba, kuma babban kuskure da mutum zai yi a
rayuwarsa shi ne yace zai shiga tsakanin masoya”
Koda jin wannan batun sai hankalin mahaifiyar
Lashmin ya dugunzuma ainun ta janye jikinta daga na
sarki suka fuskanci juna ta dubeshi cikin alamun
tsananin damuwa tace.
“Wai shin yanzu kana nufin kenan zaka
kyale Lashmin ta yi soyayya da Amzad xan Nazmir
alhalin kasan cewar qarshen soyayyar tasu mummun
qarshe ne da mugun baqin ciki?” Koda jin wannan
tambayar sai hawaye ya sake

3 / 7