BAYAN MUTUWA

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Adventure

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 20K words

da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya
zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.
okacin da Gimbiya Lashmin ta lura da
gaba xaya fadawa da ‘yan majalisu sun
hallara sai ta yi gyaran murya take fadar
tayi tsit aka saurara domin aji abinda zai fito daga
bakinta. Duk wanda ta kalla sai taga yana muzurai

L

18

BAYAN MUTUWA

gami da haxiyar miyau kamar su tashi su matse
bakinta tayi bayanin dole.
A zuciyarta sai tace oh kaga miyagun banza
kawai so suke suji wata maganar ta sharri bata alheri
ba, domin su san yadda za su qula wani mugun
makircin.
Kawai sai aka ga Lashmin ta fara da yin
murmushi sannan tace.
“Yaku jama’ar wannan birni na sham kuyi
sani cewar mahaifina bashi da lafiya amma duba ba
wani ciwo mai tsanani bane don haka zan ci gaba da
wakiltarsa har izuwa tsawon xan lokaci kafin ya
warware, ina mai yi muku alqawari da cewar zan
tafiyar da mulki bisa adalci kamar yadda mahaifina ke
zarta da shi.
Saboda haka ina fatan cewar ‘yan majalisa da
dukkan dakaru da sauran shugabanni na birni da
qauye za su bani haxin kai kamar yadda suka saba
baiwa mahaifina.
Yanzu take ina son a ci gaba da zarta da
komai kamar yadda aka saba kuma zan saurari qara
guda uku kacal a zaman da za mu yi yanzu, ina masu
gabatar da qara?” Koda jin wannan tambayar sai wani
dattijo daga cikin fadawan ya matso gaba kusa da

19

BAYAN MUTUWA

karagar mulkinta a vangaren hannun dama ya zube
qasa ya kwashi gaisuwa sannan yace.
“Ya shugabata ni ne mai gabatar da qara a
wannan fadar tsawon shekara talatin baya kamar
yadda kika sani” Koda jin haka sai Lashmin ta yi
murmushi tace.
“Gaskiya ya kai Safwan bin ma’aruf bin
kananata, tun kafin a auri mahafiyata kake wannan
aikin. Kai ne ka gabatar da qarar waziri Dulnur wanda
ya kashe amininsa ya aure matarsa kuma ya mallake
dukiyarsa kimanin shekara talatin da shida baya anan
fadar, da taimakon ka ne gaskiya ta bayyana har ka
saka sarki kan’an ya yankewa waziri Dainur hukuncin
kisa aka tsireshi a tsakiyar kasuwa ko ba haka abin ya
faru ba?” Safwan ya risina yace.
“Haka yake ranki ya daxe” Nan take jama’ar
da suke cikin fadar suka kamu da tsananin mamaki
bisa jin yadda Gimbiya Lashmin ta riqe wannan
tsohon tarihin domin lokacin da al’amarin ya faru ba a
ma san zata zo duniya ba.
Lashmin ta dubi Safwan bin ma’aruf tace.
“Karanto mini shari’ar farko na ji a kuma
shigo da wanda ya kawo qarar da kuma wanda ake
qara” koda jin wannan umarni sai Safwan ya miqe

20

BAYAN MUTUWA

tsaye yaje bakin qofar da ake shigowa da masu shari’a
yace.
“Ina attajiri Huzulu da kuma saurayi Amzad a
shigo da su”.
Nan take sai ga wani dogon mutum
ma’abocin kwarjini a cikin suture masu tsada ya shigo
cikin fadar fuskarsa cike da annuri. Kallo xaya zaka yi
masa kasan cewar babu wani abu da yake damunsa a
rayuwa, yana tafe yana murmushi.
Wanda ke biye da shi kuwa wani matashin
kyakkyawan saurayine wanda kana yi masa kallo xaya
zaka gane cewa in ba don talauci ba da bai kasance
ramamme ba kuma da kyawunsa ya ninka hakan sau
uku.
Kai da ganinsa kasan yana fama da aikin
wahala kafin ya samu abinda zai kai bakinsa, biye da
waxannan mutane biyu dakarun fada ne.
Koda Gimbiya da wannan matashin saurayin
mai suna Amzad suka haxa idanuwa karon farko sai
kowannensu yaji zuciyarsa ta buga da qarfi. Cikin
hanzari Amzad ya sunkuyar da kansa qas don kada
qurawa Lashmin idanu ya zama laifi ayi masa wani
hukunci akan haka.

21

BAYAN MUTUWA

Batare da vata wani lokaci ba aka gurfana da
attajiri Huzulu da Saurayi Amzad a gaban Gimbiya
Lashmin. Nanfa fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta
sai da Lashmin ta qarewa attajirin Huzulu da Amzad
kallo, tayi nazarinsu sosai sannan ta dubi Safwan bin
ma’aruf tace.
“Kafin a gabatar da wannan qarar ina son ayi
mini bayani akan matsayin wanda ake qarar da wanda
ya kawo qarar, ina son nasan sana’o’insu,
mu’amalarsu da mutane da koma inda kowannensu ke
da zama” koda jin haka sai mamaki ya kama gaba
xayan jama’ar dake cikin fadar hatta manyan alqalai
kuma na dukan kotunan qasar saboda wannan wani
sabon salone bisa tsarin shari’ar qasar, Lashmin tazo
da shi.
Mai gabatar da qara Safwan bin mu’aruf ya
juya ya fuskanci Gimbiya Lashmin yace.
“Da farko dais hi wannan attajiri wanda kowa
a garinnan ya sani da suna Huzulu yana zaune ne a
unguwar sarakai kuma bashi da wata sana’a wacce ta
wuce siye da siyar da gidaje da kuma bayar da hayar
gida ko gona ko rumfar kasuwa. A cikin wannan
birnin namu na Misra an tabbatar da cewa yafi kowa
yawon gidaje da gonakai da kuma rumfunan kasuwa

22

BAYAN MUTUWA

don haka ko sauran attajirai masu yin harkokin fatauci
kalilan ne suka fishi yawan tsabar kuxi a hannu a
qasar nan gaba xaya.
Shi kuma wannan saurayi mai suna Amzad
bashi da wata sana’a wacce tafi dakon tubalin gini ya
kanje ya nemi aikin dakon tubali yana kaiwa inda ake
gini abiyashi, wannan ita kaxai ce mu’amalar data
haxashi da mutane. A kullum idan ya tashi daga aiki
da yamma da zarar ya wanke jikinshi zai tafi ne izuwa
can gidansu wanda ke kusa da gidan attajiri Huzulu a
unguwar sarakai ya kaiwa mahaifiyarsa abincin da
zata ci. Ita dai wannan mahaifiya tasu ta kasance
tsohuwa tukuf, saboda tsufan ma bata gani da idanunta
kuma bata iya taka qafafunta, ko kewaye zata shiga
sai dai Amzad ya xauketa a hannunsa ya kaita” koda
Safwan ya zo daidai nan a bayaninsa sai Gimbiya
Lashmin ta xaga masa hannu kuma ta tari
numfashinsa tana mai cewa.
“Me yasa kake wuce gona da iri akan bayanin
Amzad, amma sa’adda kake bayanin attajiri Huzulu
sai ka taqaita komai yasa?” Koda jin wannan
tambayar sai idanun Safwan suka zazzaro gaba xayan
jama’ar dake cikin fadarma sai suka kama muzurai.

23

BAYAN MUTUWA

Shi kansa attajiri Huzulu sai yayi fiqi-fiqi da
shi ya kama muzurai yana mai qus-qus.
Gimbiya Lashmin ta gyara zama kuma tayi
gyaran murya sannan ta dubi Safwan tace.
“Tsakanin attajiri Huzulu da Saurayi Amzad
waye ya kawo qarar wani?” Safwan yace.
“Ubangiji Dullas ya taimakeki Gimbiya ai
yaro Amzad ne ya kawo qarar attajiri Huzulu” Koda
jin haka sai Lashmin tayi murmushi sannan tace.
“Ai dama abune mayuwanci attajiri ya kawo
qarar talaka sai dai talakan ya kawo qarar attajiri
saboda har kullum talaka ba zai iya danne haqqin
attajiri ba tunda anfishi sanin komai da kowa kuma an
fishi qima da daraja, maza a karantomin wannan qarar
doming a dukkan alamu zan yanke hukuncinta a cikin
qanqanin lokaci”. Koda jin wannan batu sai hankalin
attajiri Huzulu ya dugunzuma ainun ya buxe baki
kamar zaice wani abu amma sai Gimbiya Lashmin
tayi masa nini da yayi shiru tace.
“Kai ba’a magana a gaban kotu face an baka
izinin yi” cikin alamun kunya da rashin gaskiya attajiri
Huzulu ya yi shiru yana mai sunkuyar da kansa qas.
Mai gabatar da qara Safwan bin ma’aruf yayi
gyaran murya a lokacin da fadar ta suka yi tsit tamkar

24

BAYAN MUTUWA

ruwa ya ci kowa sannan yace saurayi Amzad yana
qarar attajiri Huzulu akan cewa ya kwace masa
gidansa nag ado wanda mahaifinsa ya mutu ya bari a
matsayin bashin da yake bin mahaifinsa, bayan
mahaifinsa ya mutu, baya ga wannan gidan akwai
rumfunan kasuwa guda uku wadanda yace tun kafin
mahaifin Amzad ya mutu ya bashi su jingina kuma bai
dawo da kuxin da ya araba har ajalinsa ya cika.
Bayan rumfuna uku akwai babbar gona guda
xaya wacce ke can kusa da kogin Luzim a bayan gari.
A yanzu haka duk faxin garinnan babu inda ake
noman kayan lambu sama da wannan gona kuma a
tsawon shekaru ashirin da biyar da mutuwar mahaifin
Amzad daidai da rana xaya ba a tava daina noma a
cikin gonar ba kuma duk amfanin da aka samu Attajiri
Huzulu ne yake riqewa.
Bai tava baiwa mahaifiyar Amzad koda sisin
kwabo ba, tun kafin ma ta haifi Amzad saboda tana
xauke da junan biyun Amzad da watanni shida Allah
ya yi wa mahaifinsa rasuwa” Koda Safwan ya zo nan
a bayaninsa sai Gimbiya Lashmin tayi sauri ta xaga
masa hannu tace.
“Dakata haka haba ai wannan shari’ar ta
wuce duk yadda nake zato, ina mai tabbatar muku za

25

BAYAN MUTUWA

mu iya shafe wata guda muna yinta bamu qare ba duk
da cewar za mu iya gano mai gaskiya a tsakanin
attajirin da saurayin a cikin sa’a xaya jal” koda jin
wannan batun sai kowa ya kamu da tsananin mamaki
a cikin fadar.
Su kansu manyan alqalai na qasar sai suka
kasa gano manufar Gimbiya Lashmin da kuma yadda
zata yi ta iya warware wannan qara da kuma dalilin da
yasa tace za a iya gano mai gaskiya a cikin sa a xaya
saboda basuga hujjojin da zata iya amfani da su ba.
Kamar Lashmin tasan abin dake zukatan
jama’a da sauran alqalan qasar sai kawai aka ga ta
miqe tsaye daga kan karagar mulki ta tako kafafunta ta
zo har gaban attajiri Huzulu ta dubeshi a cikin
nutsuwa tace.
“Shin gaskiya ne kana bin mahaifin Amzad
bashin da darajarsa ta kai ta gidansa, rumfunan
kasuwarsa guda uku da kuma babbar gonarsa dake can
bayan gari, gonar da babu kamarta a duk faxin qasar
nan?” koda jin wannan tambayar sai attajiri Huzulu ya
gyaxa kai yace.
“Wannan gaskiya ne kuma ina da shaidu akan
haka gami da rubutacciyar takarda mai xauke da saka
hannunsa da kuma saka hannuna akan duk kuxaxen

26

BAYAN MUTUWA

da ya zo ya karva a hannuna da zumar zai biyanio
kafin cikar wani wa’adi na kwanaki har ajalinsa ya
riske shi bai gama biyana waxannan kuxaxen ba shi
dalilin daya saka na riqe gidajensa, gonarsa da
rumfunansa na kasuwa” Koda jin wannan batun sai
Gimbiya Lashmin ta gyaxa kai kuma tayi murmushi
sannan ta sake duban attajiri Huzulu tace.
“Shin kuxaxen da mahaifin Amzad ya karva
a hannunka duka ya karve su ne a rana guda ko kuma
ya karve sune daban-daban akan ko wacce kadara
tasa?” Hazalu yace.
“Ai ya karve sune daban-daban, misali
lokacin da yake so zai gina waxannan rumfuna na
kasuwa guda uku bashi da kuxin aikin sai ya zo
wurina na bashi rancen dinare dubu xari biyu da
arba’in bisa sharaxin cewa idan ya kammala ginin zai
bayar da hayar rumfar duk wata zai riqa bani dinare
dubu hamsin har tsawon wata shida a sananne zai
kammala biyana, a watan farko da zai fara biyana
wannan kuxin ajalinsa ya same shi, tsawon shekara
guda ba a bani ko kwabo ba.
Duk sanda naje wajen matarsa na nemi
haqqina sai tace dani itama ba a bata ko sisi ba ta ma
san a hannun wa rumfunan suke ba, ya shugabata

27

BAYAN MUTUWA

kinga kenan na tafka asara na tsawon watanni shida
kuma inda kuxina a hannuna suke da sun ninka kansu,
bisa wannan dalilin na riqe duk kadarorinsa a
maimakon kuxaxena daya karva na fitar da matarsa
daga cikin gidan na zuba ‘yan haya a ciki.
Dangane da yadda aka yi na mallake
rumfunan kasuwarsa kuwa guda uku shi ne bayan ya
karvi wannan kuxin na farko dinare dubu xari biyu da
arba’in, a tsakiyar watan da zai biyani ya sake
dawowa ya ranci dinare dubu xari biyar ya sayi irin da
zai shuka a wannan gona tasa wadda ya gada a wajen
ubansa kuma ya biya ma’aikata suka nomata bisa
sharaxin cewar bayan yayi girbi zai biyani dunare
dubu xari takwas. Har bayan shekara biyu da
mutuwarsa ba a bani kuxina ba, bisa wannan dalilin na
riqe takardun rumfuna guda uku.
Ana I gobe zai rasu Mahaifin Amzad ya sake
dawowa gareni ya ranci dinare miliyan xaya ya sayi
raquma,alfadarai da jakuna waxanda za su riqa safarar
amfanin gonarsa izuwa qauyuka da birane dake cikin
qasar nan kuma ya biya ma’aikata da za su yi masa
wannan aikin rabin wahalarsu tun ma kafin kaka ta zo,
da sharaxin wata biyu da shuxewar kaka zai biyani
dinare miliyan xaya da rabi, sai da aka yi kaka uku ba

28

BAYAN MUTUWA

a bani ko dinare xaya ba, bisa wannan dalilin na riqe
gonarsa ta zama tawa”.
Lokacin da attajiri Huzulu ya zo nan ciki
dogon jawabinsa sai kawai aka ga hawaye yana
zubowa daga idanuwan Gimbiya Lashmin nan take ta
dubi Attajiri Huzulu cikin alamun tsananin fushi tana
mai daka masa tsawa tace.
“Tabbas ka cika shugaban azzaluman duniya,
da farko dai na yarda cewar mahaifin Amzad ya ranci
duk kuxaxen da ka faxa a hannunka bisa amincewar
zai biyaka kuxin ruwa to amma idan aka yi la’akari da
irin kuxaxen da aka samu a rumfunansa na kasuwa da
kuma gonarsa a wannan tsawon shekaru ashirin da
xaya ai kaci ribar data ninka kuxin daka bashi sau
dubunnai.
Kawai don kana binsa bashin kuxaxen da
gaba xaya adadinsu bai haura dinare miliyan biyu ba
sai ka cinye masa gaba xayan dukiyarsa wacce a halin
yanzu idan idan qiyasta darajarta za a yi darajarta tafi
dinare miliyan xari biyar sannan kuma dukiyar ta
haura miliyan dubu goma.
Sannan kuma kowa a garin nan ya sa ni kafin
ka mallaki rumfunan kasuwa da waxan nan gonakin
baka da jarin daya fi dinare miliyan biyar amma yau

29

BAYAN MUTUWA

an wayi gari babu mai cinikin gidaje da gonakai
wanda ya fika qarfin jari.
To idan baka sani ba yanzu ka sani cewar
wannan matsala taku kai da Amzad tun ina yarinya
qarama na san da ita. Ansha kawo wannan qarar
gaban mahaifina amma sai wasu daga cikin ‘yan
majalisarsa su sa a kori qarar a baka gaskiya, badan
komai ba sai don kana binsu izuwa gidajen su a
sirrance xaya bayan xaya kana shaka musu cin hanci
na maqudan kuxaxe.
Na daxe ina jiran wannan ranar da zan samu
damar cikakken bincike akan wannan qarar na
qwatowa Amzad da mahaifiyarsa haqqinsu amma ban
samu ba sai yau, ka sani babu cuta babu cutarwa, kaje
ka zo da duk takardu da kuma shaidun bashin daka
baiwa Mahaifin Amzad, shima Amzad zai zo da irinsu
waxanda mahaifinsa ya mutu ya bari, bayan an zo da
su kotu zata saka a yi lissafi na iya adadin hakkinka
daya kamata a biyaka a cikin dukiyar da mahaifin
Amzad ya bari sannan ayi lisafin a gani, tsakanin kai
da shi wane zai yiwa wani ciko a tsawon waxannan
shekaru ashirin da xaya” Koda jin wannan batu sai
Attajiri Huzulu ya taqarqare ya kwarara uban ihu
tamkar mahaukaci sabon shiga.

30

BAYAN MUTUWA

Sannan ya kalli Gimbiya Lashmin cikin
tsananin fushi da qiyayya yace.

BAYAN MUTUWA 3

‘K

e yarinya ce abinda mahaifinki
yabarshi a rufe baki isa ki tona shi
ba...” Kafin Huzulu ya gama rufe
bakinsa tuni Gimbiya Lashmin ta sharara masa mari,
ta dubi wasu dakaru uku dake tsaye kusa da shi tace
musu.
Koda ganin wannan al’amari sai hankalin
lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya
kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi,
babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar
mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko
da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa
sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani
ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma
Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba
kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da

31

BAYAN MUTUWA

za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar
hankali a rayuwarta
Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba
da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu
tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar
dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta
gidan sarautar.
Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai
kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin
fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da
ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake
zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta
fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya

32

BAYAN MUTUWA

zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.
Koda ganin wannan al’amari sai hankalin
lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya
kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi,
babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar
mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko
da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa
sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani
ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma
Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba
kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da
za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar
hankali a rayuwarta
Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba
da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu
tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar
dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta
gidan sarautar.

33

BAYAN MUTUWA

Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai
kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin
fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da
ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake
zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta
fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya
zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.

34

BAYAN MUTUWA

K

awai sai sarkin yaqi ya miqe ya qwalawa
dakarunsa kira, nan take sai ga Dakaru sama da
mutum xari uku sun rugo izuwa gabansa Lashmin ta
sake duban sarkin yaqi tace.
“Idan kuka kai shi can kurkuku ku sanar da
cewar kar abar kowa ya kawo masa ziyara koda kuwa
iyalansa ne kuma koda mai kawo masa abinci kada ya
shiga wajensa shi kaxai kuma sai an tabbatar da cewar
an cajeshi yayin shigarsa da fitowarsa.
Sarkin yaqi ya risina yace “Angama ya
shugabata” Nan take aka tusa qeyar attajiri Huzulu
aka fice da shi daga cikin fadar a wulaqance abin da
ko

2 / 7