Khaleesat Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 38.4K words

yatsa, murya na rawa tace
hydar shiga kagani, shiga yayi dakin
da
sauri dan atunaninshi wani abu
yasami
matarshi khaleesat ne, amma daya
shiga
dakin abunda yagani yafi komi
tayarmai
da hankali a duniya..
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
2βƒ?5βƒ?



Faisol yagani babu komi a jikinshi,
ga
jini duk falon, sanan ga guntulen
yatsa
akasa gakuma wuka, abu na farko
daya
fara zuwa zuciyan hydar shine ina
khaleesat?? Shiga yayi dakin yaduba
uwar daka bata, yafito kaman
mahaukaci ya duba bayin tsakar
gidan
nanma bata, komawa dakin yayi ya
hango kayan khaleesat riga da zanin
datasa yau da safe, a rude ya dago
faisol
ya kifamai wani irin mahaukacin
mari,
take faisol ya farka daga suman
dayayi
yana kukan azaba. Hydar da
fuskanshi
tai ja gabaki daya. ya shake wuyan
faisol
yace ina khaleesat?? Faisol yama
kasa
magana, hydar yakara dakamai
tsawa
ina khaleesat?? Ina kakaimin
matana??
Mekama matana??
Yanda idanun hydar suka juya
gabaki
daya kaman wanda yasha giya yasa
faisol yakara tsorata, yace hydar
tsaya
nama bayani dalla dalla. wani irin
naushi hydar yabama faisol aciki, ya
hanbareshi akan aciki, ya gwara
kanshi
da bango, hydar dukanshi yake ta
ko
ina, ummi taji dukan yay yawa tace
zulaihat ki tsaya anan karki shiga
dakinan. Ummi tai shahada tafada
dakin.
Rike hydar tayi gam tace hydar
karka
bari fushi yaci gabala akanka,
karkuma
kayi aikin dana sani, karkuma ka
manta
dan sarki kake duka haka, ka natsu
muyi
komi ahankali harya fito da
khaleesat.
Hydar fizge jikinshi yayi daga hanun
ummi, yakara komawa kan faisol
wanda
yadawo kaman mara numfashi
yacigaba
da dukanshi ummi ta fizgo hydar ta
rike
fuksanshi da tafukan hanunta biyu
tace
β€œhydarβ€? β€œHydar β€œHydar kallen, yaki
kallon ummi sai huci yake yana
kokarin
kwace fuskashi.
Ummi takara matse kumatunshi tace
β€œhydar dago kwayar idonka ka
kallenβ€?
da kyar ya iya daga jajayen idonshi
ya
kalli ummi yana huci kaman zaki.
ummi
tace oya furta INNALILLAHI WA
INNAILAHI RAJI’UN hydar da kyar
ya
iya furtawa. Ummi tadauko ruwa
tabashi
yama kasa karban kofin saboda
yanda
jikinshi ke rawa tsabagen zuciya.
Ummi ce takai ruwan bakinshi kadan
yasha yacire kai, ummi tace shanye
takara kaiwa bakinshi yakafa kai ya
shanye still tana rike dashi gam,
saboda
tafi kowa sanin halin dan nata,
ahankali kwalla yafara taruwa a
idonshi,
idonshi yacika taff da kwalla amma
basu saukoba. ummi ta shafa kanshi
tace hydar bar hawayen su zubo,
dan
hakan zaisa zafin zuciyarka ta ragu,
hawayen ya gangaro zuwa
kuncinshi,
hydar ya kifa kanshi akan cikin
ummi
yana shesheka, muryan kuka yace
ummi
ina yakaimin matana?? Ina yakaimin
khaleesat??mai yay mata?? Mai yay
ma
matana??
Ummi wlh inhar wani abu yasami
khaleesat, inhar wani abu yasami
matana saina kashe faisol saina
halakashi, saina…β€? Bakinshi ummi
ta
taushe tace shiiiiiβ€?
[2:27AM, 3/5/2017] β€?+234 803 052 4904β€?: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
2βƒ?6βƒ?



Ummi ahankali take dukan bayanshi
harya sakko. idanunshi suka washe
kadan, mikewa yayi ummi tace
mezakayi
zoka zauna, yakoma ya zauna. ummi
ta
tashi tadau kayan faisol tabashi da
kyar
ya iya mikewa yasa kayan bayan
yasa
kayan, ummi cikin muryan natsuwa
tace
faisol ina yata khaleesat?? Maiya
faru??
maikuma yahadaku?ina ka kaita?
Jikin faisol yafara rawa saboda
yanda
yaga hydar na kallonshi, hydar ya
dakamai tsawa yace bazaka
fadanmana
gaskiyaba. Faisol cikin daburcewa
yace
wlh yau nikadai nafito tun safe dan
shakatawa, ina zuwa zan wuce ta
kofar
gidanan naga ummi tafito
hartanajan
kofar gida hakan ya tabbatar min da
bakunan kuma nasan baku barin
makauniyar fita ko ina saisa na
shigo
gidanβ€? Hydar yace saikai mata
me??
Yace dama dama naso namata fyade
amma ta gutsiremin yatsa naga
tafita
daga dakin dagudu duk a tsorace
take,
amma wlh banmata komiba, ban
kuma
dauketaba.
hydar zai mike ummi ta rikeshi yace
ummi yanzu ina khaleesat??? Suka
mike
suka fito, Zulaihat tafara taransu
tace
ina kawata ummi??
Hydar ya share hawayen daya fito
daga
idonshi yace zulaihat tsoro yasa
tafita
daga gidan da gudu, yanzu
kauyenan
zamu bincika tass in sha Allah zamu
ganta, in Allah ya yarda batai
nisaba.
Ummi tafita tana shigan makota
tana
tambaya, yayinda hydar yahau
dokinshi
yana zuwa duk wani matattara
majalisa
a kauyen tambaya yake kosunga
wata
makauniya.
Hydar har babban titi yaje ya
tambayi
wasu, wani mai gyaran machine
yace
dazu wata yarinya kakkyawa yar
baka
haka daga ganinta kasan bayar nijar
bace tana dogara sanda, hydar da
sauri
ya sauka daga dokinshi yace eh ita
a ina
ka ganta??
Mutumin yace wlh hatsari takusa
jawowa fadawa tayi titi shinefa har
wani
soja ya mareta, hydar idonshi yay
jaaa,
hydar yace yanzu tana ina, ko kasan
inda tayi?? Mutumin yace wlh
bansaniba, dankoni saida na zageta
amma daga baya muka mage
makauniyace, wlh taban tausayi, sai
kuka take, daga gani kaman tana
cikin
tashin hankali, nidai naga lokacin
data
tsallake titi amma bansan inda
tayiba,
hydar yace nagode dan Allah zandan
daura dokina a wurinan mutumin
yace
to.
Hydar ya daure dokin, jiyake kaman
ya
hadiyi zuciya wani banza ne ya mari
matarshi??

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
2βƒ?7βƒ?



SOJA ya kaita wani babban asibiti
na
nijar mai suna PARAGON CLINIC.
Yana
shiga likitoci suka karbeta aka
dukufa
akanta, soja na zaune abakin kofar
dakin.
Wuraren awa biyu sanan likita
yafito,
da sauri sojan ya mike. DR yace
kabiyoni
office dina. Soja yabishi suka zauna,
soja
yace Dr ya jikin nata?? Dr ya cire
class
din idonshi tareda gyra sarkan cross
din
dake wuyanshi, Dr yace well she is
better
now, but am afraid to tell u dat ur
sister
is disconnected 4rm life. Atsorace
sojaa
ya mike tareda dafe kirjinshi yace
mekake nufi Dr?? Is she dead??
Doc yace calm down, bata mutu ba,
u
know dat Jesus Christ said in
chapter 2,
verse 39 under old testament dat
…β€?.
Soja yace am sorry sir, but am not
a
Christian. Dr yay murmushi yace is
ok,
so as i was saying kanwarka tana
under
coma, soja ya kwalalo ido, Dr yace
agaskiya babu wani ciwo dake
damun
sister naka takamaimai but plz can i
say
something?
Soja yace go ahead, dr yace u know
am a
Christian, kumani in d Christianity
am
4rm Jehovah witness, so abunda na
gane
da kanwarka shine her soul has
gone far,
d gurl is tired of lyf, d only thing
dat will
bring her back to leaving shine taji
sunayen loved ones dinta, kokuma
abubuwan datakeso, kokuma some
story
books, kokuma muryan wayanda
takeso
haka, are u getting me?
Soja yay shiru yana cewa a
zuciyanshi
wanan rikakken arne ne wlh, Dr
yace
abunda ke damun kanwarka
ordinarily
shine soul (ruhi ko masu karatu??)
yay
nisa da jikinta, abu daya zai dawo
da ita
shine kotaji muryan wayanda
takeso, ko
taji sunayensu, kokuma wani abu
daya
taba burgeta, so zanyi advising
naka da
kana yawan karanta mata novels
haka..
Zaka iya zuwa ka dubata sojaa yace
to.
Yana shiga dakin, yaga khaleesat
kwance
ansa mata kayan asibiti a jikinta, ga
oxygen abakinta, idanunta abude
amma
ko kyaftasu batayi tana kallon sama,
ga
numfashi tana saukewa kadan
kadan.
Soja yace yarinya, dan Allah karki
mutu,
fight 4 ur lyf, nasan abunda likita
yafada
wanan karyane dan katon arnene, i
know dat ur soul is with u, but u
have to
fight proven him wrong, ki nunamai
ur
soul is with u, abunda yake fada
imagination dinshine kawaiβ€?.
*****
Kaman yanda akeda kungiyoyi a
musulunci, irinsu izala, darika,
shi’a,
ahlu sunna, dadai sauransu hakama
arna keda nasu.
Kamansu Jehovah witness, redeem,
Baptist, Catholic, dadai sairansu,
dafatan
kun gane masu karatun novel
dinan??
Shi wanan Dr din acikin Christianity
shidan kungiyar JEHOVAH WITNESS
ne.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
2βƒ?8βƒ?




HYDAR na sallakawa titin, yayi saitin
inda mai gyaran machine ya
nunamai,
gabaki daya hydar yadawo kaman
mara
hankali, bini bini yana goge
hawayen
idonshi, wani warwaro daya gani
kusa
dawani katon kwata yasa yakarasa
kusa
da kwatan da sauri.
Tsugunnawa yayi yadau warwaron
yana
karema warwaron kallo, bazai manta
wata ranan yana gida dukansu suna
tsakar gida yaga Zulaihat ta cire
warwaron daga hanunta tasama
khaleesat tace kawata gashi nabaki
wanan, da sauri ya share hawayen
idonshi da dan murmushi a
fuskanshi
dan wanan alamune na cewa
khaleesat
na within dis area, waige waige yake
ko
zaiga wanda zai tambaya, wasu
samari
ya hango su uku suna fira yakarasa
wurinsu da sauri.
Sallama yay musu yace dan Allah
kunga
wata makauniya a wurinan?? Daya
daga
cikinsu yace mallam tabbas ni
naganta
dan saida na taimakama wani soja
muka
cirota daga kwatanchan ya nunama
hydar kwatan. Saboda fadawa tayi
ciki,
wani hawaye yakara zubowa daga
idon
hydar yace ko kasan inda sojan ya
kaita?? Saurayin yace mota yasata
yace
mana bari yakaita PARAGON CLINIC,
hydar ya kara share hawayen
idonshi
yace nagode.
Samarin sukace ka kwantar da
hankalinka insha Allah lafiyanta
kalau,
in sha Allah zaka ganta. yace tom
nagode, ya tare texi dama yanada
dari
500 yahau yace mishi paragon clinic
zaka kaini.
SOJA na nan zaune gaban khaleesat
yana
kare mata kallon, tunani yake yanzu
ina
zaiga iyayen yarinyar nan? Ya zaiyi
da
ita?? wayanshi ne yay kara. ya ciro
wayan daga aljihu, mikewa tsaye
yayi
yasara alamun dababban mutum
yake
magana, yace oga dama wlh wata
yarinyaβ€?.. To Allah huci zuciyar
oga,
ganinan to, bari nabiyo flight nazo
abujan direct. ya katse wayan da
sauri
yafita daga dakin yatafi office din
dr.
Yana shiga yasami dr yana rubuce
rubuce, sojaa yace Dr inada matsala
wurin aikina suna kirana, head
quarter
dinmu na sojoji yana abuja, ana
nemana
acahn yanzu. so inason transfer
natafi
da yarinyar abuja, Dr yace shikenan
zan
baka bari nasa ayi arranging
ambulance
dazai kaiku airport, sojaa yace to.
Yakoma dakin khaleesat, matsar da
kujeranshi yayi kusa da ita yace
yarinya
kiyakuri, gwara natafi dake abuja
inkaiki asibiti mai kyau achan, wlh
bazan iya barinki wurin arnen Dr
dinan
ba, gwara natafi dake abuja
hankalina
zaifi kwanciya dan bansan ranan
dawowana nijar ba, inyaso inkin
warke
nadawo dake nijar nakaiki wurin
iyayenki,.. Dr ya shigo yace oga
everything is ready yanzu kaje
kabiya
kudin komi da komi sai ku iya
tafiya,sojaa yace to.
Anfito da khaleesat ana gungurata
kan
gado har aka kaita waje daidai
lokacin
da za’a lankwasa gadon asata a
cikin
motan ambulance HYDAR ya bude
get ya
shigo asibitin,
abinda idonshi yafara tozali dashi
khaleesat yagani kaman gawa za’a
sata a
motan ambulance ga kuma sojan
da’ake
fada mishi a gefe tsaye kusa dawani
likita, maiya sami khaleesat?? wani
jiri
jiri yafara ji, kwata kwata yakasa
daga
kafanshi yakarasa inda suke,
hanunshi
ya daga yana pointing dinsu
bakinshi na
kokarin furta kha..kha..lβ€?
leeβ€?.s..at..
amma bai ida karasa sunanba
yafara
ganin duhu duhu…β€?
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
2βƒ?9βƒ?



Idanunshi sukafara juyawa,
yafarayin
baya baya alamun zai fadi, kaman
ancema sojaa ya juyo, da sauri ya
taba
Dr yace Dr gawani patient zai fadi,
ganin
yay baya zai fadi yasa da gudu soja
yakarasa bakin get inda Hydar yake,
soja yay maza ya tareshi yafadi a
jikin
soja sumamme, ahankali bakinshi
na
fadin β€œmy jidda”my jiddaβ€? saikuma
yakarasa sumewa, sojaa ya girgiza
kumatun hydar yana Dr do
something.
Dr ya juya yakira mutanen dasuka
gama
sa khaleesat a motan ambulance.
Gadon da aka dau khaleesat akai shi
aka
sake gungurowa aka kawo wurin
soja da
Dr suka daga hydar sukasa akan
gadon
wani ajiyan zuciya hydar ya sauke,
wanda hakan yabama soja da Dr
mamaki. Dr yace take him to my
office,
sanan ya juyo ya mikama sojaa
hannu
yace safe journey, sojaa yace tnx. Dr
yawuce office da sauri shikuma
sojaa ya
shige motanshi yayinda motar
ambulance da khaleesat ke ciki ke
binshi
abaya.
Suna kaiwa airport sojaa yayma
khaleesat komi baisha wahalaba,
saboda
transfer latter dayakedashi. yakira
wani
yaronshi yabashi motanshi ya komar
dashi, haka aka gungura khaleesat
har
cikin jirgi suka daga sai
abujaaaaaaaaaaaaaaa.
Taimakon gaggawa ake bama hydar,
Dr
yasamu ya farfado amma sai
yacigaba
da bacci.
Su ummi da zulaihat sun zagaye
gidajen
kauyen kaf amma babu khaleesat,
zulaihat kuka wiwi take, itakanta
ummi
karfin hali takeyi haka taja hanunta
suka dawo gida, amma shiru shiru
hydar
har shabiyun dare bai dawoba,
ummi
kuka take amma a zuci sai addu’a
take
Allah ya dawo mata da danta lpy.
Ranan
ummi bata iya runtsawaba
hankalinta
yatashi to ina hydar ya shiga ne??
Tashi
tayi ta dinga salloli tana addu’a
Allah sa
duk inda yake lpy shi lau. har gari
yawaye.
HYDAR har yanzu bai tashiba, Dr na
zaune gefenshi yana kallon
kakkyawan
hallita irin hydar, yasan cewa ya
dade
yana aiki a nijar amma baitaba
ganin
matashi mai kyau da kwarjini kaman
hydar ba, ya shagala da kallon hydar
yaga kafafunshi na motsiβ€?.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
3βƒ?0βƒ?



Dr ya matsa kusa dashi ya rikemai
hannu yana cewa in d name of d
father,
d son and d holy spirit wake dis
man up,
jiyayi an fizge hannu ya bude
idonshi
yaga ashe hydar ya farka.
Hydar ya ballamai harara tareda
cewa
wt did u tnk u are doing?? Dr yay
murmushi.
Hydar yay maza ya sauka kan gadon
yayi hanyar fita yana waige waige,
Dr
yabishi abaya.
Har waje hydar yaje ya tsaya daidai
inda yaga ana sa khaleesat a mota
jiya
yay shiru, Dr yace menene young
man??
Hydar ya juyo yace jiya na ganka
anan
tsaye, tareda wani sojaa, saikuma
wasu
mutane suna kokarin sa wata
yarinya
cikin motan ambulance. Dr yace yes
is
me, any problem?? Hydar yakara
matsowa kusada Dr yace ina kuka
kaita
yarinyar ita nake nema she is my
wife.
Dr yay mishi wani irin kallo yace to
maisa tabaro hanunka?? Hydar yace
is a
long story all i need to know now is
where is she?? Ina kuka kaimin
matana?? Yana maganan kwalla ta
cikamai fararen idonshi.
Kallo daya Dr yamai yasan ba karya
a
zancenshi, tabe baki yayi yace well
wanda yakawota told me dat she is
his
sister, yanzu kuma ana nemanshi a
wurin aikinsu a abuja so yanemi
transfer abuja suka tafi.
Hydar yace wot?? Yay shiru yana
tunani
to wanan shine yayan khaleesat
hydar
data taba fadamishi?? Saikuma yace
nooooo, aitacemin yayanta Dr ne,
dago
kanshi yayi zaima Dr magana amma
yaga Dr haryabar wurin. bin Dr yayi
har
office ya cakume Dr.
Yace kufitomin da matana, dat man
is
lying,he is not her brother. Dr yaji
shaka
yafara kokarin kwace kanshi yace
let go
off me, ni police ne dazansan ba
wanta
bane?? Shiya kawota asibitin. hydar
yadaga hannu ya kifamai mari yace
u
must be very stupid.
Dr daga murya yayi yace security da
sauri suka shigo office din. yace
take him
out of my office, he is mad hala
saisama
matar ta gudo daga gidanka. da
kyar
suka bambare hanun hydar daga
wuyan
Dr aka fita dashi wajen gate.
Saida ya dade a wurin sanan ya
shiga
mota yatafi gida, yana shiga gida
ummi
ta tareshi tana hydar a ina ka
kwana?
amma bai iya cemata kalaba
dakinshi ya
shiga yafada kan katifa yay shiru
hawaye nabin kuncinshi.
Ummi ta shigo ta daura kanshi akan
cinyanta tana shafa kanshi ahankali,
saida hawayen idonshi suka tsaya
sanan
tace hydar ina khaleesat?? Kallon
ummi
yayi yay shiru yakasa amsa mata
ummi
ta goge kwallar idonta tace hydar
yimin
magana, ina khaleesat?? Hydar yay
shiru. Ummi kuka taci sosai ranan
dan
hydar yaki magana. Tashi tayi taje
taja
ruwa daga rijiya takaimai bayi ta
dawo
dakin tace hydar tashi kai wanka
kasan
yau kanada class ko, nanma kurama
ummi ido yayi batareda yace kalaba
sai
hawayen dakebin gefen idonshi.
Ummi tai kuka karshe tashi tayi
tabar
dakin, dan tasan ba karamin abune
zai
maida hydar hakaba, Allah dai yasa
ba
mummunan abu hydar yajiba.
SOJAA suna sauka a airport din
abuja
wayanda sukazo daukansu ne yasa
na
tsorata na gudo…β€?
[2:31AM, 3/5/2017] β€?+234 803 052 4904β€?: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
3βƒ?1βƒ?


Sojoji kusan su biyar naga sunzo
daukanshi, shiga cikin mota yayi
already
wata motan ambulance tazo akadau
khaleesat aka saciki, wani babban
asibiti
ya kaita a abuja mai suna AMAZING
GRACE HOSPITAL private asibiti ne,
likitocin wurin turawa ne nan aka
kwantar da khaleesat saida yagama
komi
sanan ya ajiye wani soja ya dinga
gadinta shikuma ya koma ya shiga
mota
yatafi headquarter dinsu inda ake
nemanshi.
HYDAR yadawo ba uhm ba uhuhm,
baya
fita ko ina, lesson dinma yadena
zuwa,
hunting ma yadena zuwa, bayama
kowa
magana, abin duniya yay ma ummi
yawa ga hydar ga zulaihat duka sun
dawo marasa lpy. Ita kanta karfin
hali
take dan yanzu tagane khaleesat
tazama
jininsu, bata a gidan yanzu gidan
yadena dadi, gidan yadawo fanko.
FAISOL tunda yakoma gida yake
rashin
lpy, mai martaba hankalinshi yatashi
yaga yatsan danshi a gutsure, yay
tambayan duniya amma faisol ba
bakin
amsawa saboda yanda bakinshi ya
kumbura ciwo ya cakashi.
Yau kimanin sati daya kenan da
tafiyar
khaleesat, yaune kuma za’a fara
waec.
Ummi ta debo ruwa takaima hydar
bayi
ta dawo dakinshi ta xauna kusa
dashi
tace β€œhydarβ€? yadago kai ya kalleta
tace
yaune zakufara waec katashi kayi
wanka
katafi, girgiza kai yayima ummi
batare
dayace komiba.
Ummi itama idonta ya cika da
kwalla,
tace hydar kayakuri kaje kayi
jarabawan
khaleesat zata dawo wata rana
insha
Allah kaji. kulle idonshi yayi batare
dayace komiba. ummi tagama
magana
da wa’azin tafita hydar na zaune,
alwala
tayi tafara sallan nafila tana rokon
Allah
yadawo da hankalin danta jikinshi.
Hydar na zaune dakinshi yay shiru
idonshi a lumshe babu abunda yake
gani
sai fuskar khaleesat, tuna ranan
data
taba cemai inaso kazama soja abun
yatuna yamike ahankali yace
khaleesat
inhar burinki ne nazama sojaa koda
baki tare dani, koda shine abu na
karshe
dazanyi aduniyanan saina zama
sojaa
kallon agogo yayi yaga saura 30min
afara paper da sauri ya shiga
wanka.
Yana fitowa yasa kaya yay kyau
kaman
bashiba, ya shigo dakin ummi yana
murmushi yace ummi natafi,
mamaki
kaman zai kasheta tace to hydar
Allah
yabada sa’a bazakaci abinciba??
Yace
zanyi lattine saina dawo zanci,har
zaure
tarakashi sanan ya tafi πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
3βƒ?2βƒ?



ABUJA
Har yau babu wani improvement a
khaleesat, likitoci kullum suna kanta
amma ba’a samun cigaba ko kadan,
kullum sojanan yana zuwa dubata
dan
har matarshi mai suna Farida da
dansu
marwan yakawo sun ganta, farida ta
tausayama khaleesat sosai dan har
kuka
saida tayi.
NIJAR
Alhamdulillah hydar ya kammala
waec
da jamb dinshi a tsawon wata biyu,
result yafito yaci da kyau yay
applying
NDA shima sunanshi yafito dan
yaune
ma zaitafi Nigeria, zaije chan
kaduna
makarantan Nigeria defense
academy
( NDA ).
Da sassafe ya shirya ya shigo dakin
ummi sai murmushi yake dan gani
yake
dazaran yaje Nigeria zaiga
khaleesat,
haka yakeji a ranshi zaiga
khaleesat,
ummi tace hydar ka shirya? yace eh
ummi, tace hydar maisa kazabi
Nigeria??
Akwai makarantan sojoji na nijar
maisa
bazakaje wurinba kaga kana
kusadamu,
yace ummi zan nemo matana a
Nigeria
ne. tace to abu daya zan fadama
shine
kariki gaskiya, amana, da takwa,
karka
zamo mai ha’inci, kakuma dunga
taimakom duk musulmin dayake
bukatan taimakonka, inhar karike
wanan dabi’an hydar tsawon 2 years
dinan dazakayi wlh saika zama
babban
sojaan da akwai sojoji dasukai
shekaru
goma basu sami mukamin ba.
Dana nahoreka dajin tsoron Allah,
ka
kiyaye sallolinka biyar, ka nisanci
sabon
Allah ka kula da kanka kuma. ya
rungume ummi, ummi ta fashe da
kuka
hydar ya share mata hawaye yace
ummi
nai miki alkawari zanyi amfani da
duka
abunda kikace sanan ya saketa.
Kallon zulaihat yayi wanda ta rakube
a
gefe tana matsar kwalla murmushi
yayi
yabude mata hannayenshi, da gudu
tazo
ta rungumeshi itama tafashe da
kuka da
kyar ya lallasheta, kallonshi tayi
tace
yaya hydar plz inzaka dawo ka dawo
min da kawata kaji? yay murmushi
yace
i promise, daganan tadau ghana
masgo
dinshi suka rakoshi har zaure.
Fadawan sarki ne suka ga sun shigo
gidan suna huci kusan su 50, hydar
ya
daure fuska yace lpy?? Sukace sarki
yace
ataho daku yanzunan.
Ummi ta dafe kirji tace maimu kayi
kuma?? Wani bafade yace zakuyi
bayanin uwar maiyasa kuka
guntulema
yarima faisol yatβ€?. Bai karasa
magananba hydar ya wankamai
mari,
yace uwata kake zagi? sauran
fadawan
suka kama ummi, sukace koka wuce
mutafi komu nakasa mahaifiyarka
yanzu, hydar zai kara magana ummi
tace mutafi hydar. haka aka kamasu
har
fadaβ€?.



πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


🌹 *_KHALEESAT_*🌹
πŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌπŸ™ŽπŸΌ


```Maman Abd shakur```


_PAGE_
3βƒ?3βƒ?



********BAYAN 5 YEARS.***
Ayaune HYDAR ya kammala
karatunshi
na sojaa, inda yasami babban
mukami
as CAPTAIN HYDAR MUHAMMAD.
Har
hawaye saida yayi lokacin daya
shiga
office dinshi xama yayi kan kujera
yace
khaleesat all dis are 4 u, but plz
khaleesat where are you?? Ina kika
shiga
abin kaunata?? Zuciyata kadan
tarage ta
fashe.. waynshi ne yay kara,
yadauko
wayan ganin zulaihat ne yasa ya
dauka.
Murya arude tace yaya hydar ummi
batada lpy, hawan jinin ta yatashi,
plz
kaxo mukaita asibiti arude yamike
yana
too, to ganinan. zaran keys din
motanshi
yayi yafita.
β€?.Kasancewar lokacin damai
martaba
ya aika akirasu hydar faisal
yafadamai
khaleesat ce ta guntulemai yatsa
shine
mai martaba yacema hydar su tttara
subar garinshi yakoresu, haka suka
hada kudi suka shiga mota sukazo
kaduna. Da kyar hydar yasamu
yakama
musu daki daya anan kaduna sanan
shikuma ya shirya yatafi
makatantanshi
anan jaji kadunaβ€?.
Yana kaiwa katafaren gidansu direct
dakin ummi yawuce, yaga Zulaihat
sai
kuka take ta daura ummi akan
cinyanta,
hydar da sauri yakarasa wurin ya
rike
ummi yana ummi naβ€? ummi naβ€?
ahankali ta iya bude ido amma babu
amsa, kallon zulaihat yayi wanda ga
dukkan alamu wanka tafito tana
daure a
towel sai kuka take, Hydar yace ya
isa
zulaihat jekisa kaya kizo mukaita
asibiti,
tashi tayi tashiga dakinta tazira
doguwan riga tadau hijab dinta
tafito,
tazo gaban hydar tace yaya hydar
zip,
saida yajamata zip din rigan sanan
yadau ummi yasa amota suka tafi
FMP
clinic kaduna.
Suna zuwa suka tarar da baban
likitan
dake duba ummi baya gari, wani
likita
ne yadubata saida yafito hydar ya
bishi
office, likitan yace hawan jini

4 / 13