Hafsat Elham K'iyayya da Soyayya By Billy Galadanchi

Author :  Billy Galadanchi Category :  Romance

Chapter   7 / 18

18K to 21K   out of 52.1K words

Su tsaf,sanda mukaje Kano Hutu ma da ita ta sakamu catering school na kusan 3 weeks har snacks muka koya,a school kuma Nayi food and nutrition da home economics" dariya ta bushe dashi tace "Kai Wannan zancen yamun dad'i yanzu dai dan Allah ki riqa wanka da ruwan miski,kuma had'in magarya da bagaruwa na tsarki ma ba dole se kanada aure ba,kurun ki daure kina had'awa zan aiko miki da butar k'arfe kina saka karan fari a ruwan da Jan miski Harma da farin kisaka ganyen d'od'oya idan baki dasu duk zan aiko miki,karkuma naji kina tsarkin ruwan sanyi wlhy,ruwan d'imi Sune ruwan tsarkin ki,kuma kina yawan wurga karan fari a bakinki seyayi laushi yana hana warin baki kinji?" Godiya sosai tayiwa Aunty husnah sannan tana Ajiya wayar ta yi dariyar mugunta sosai ta gano yanda Aunty Husna keso suci uban Yarima me jiran gado cikin ruwan lolxxx....

Tashi tayi tashige cikin toilet ta watsa ruwa abinta dama tanada farin miski momy ce ta bata kusan kwali uku,ta tsiyaya a ruwan se tashin kamshin miski takeyi tako ina,wata bingilallaiyar riga ta saka pure red me adon red stones agabanta,rigar iya karta gwiwa,gashi ta dameta ta d'ago da dukiyar fulaninta sun leqo waje ta baje gashinta batare data tufke shiba gashi bak'i wuluk se sheqi yake abinka da yar fulanin usul,ya sauka har gadon bayanta,a karonka na farko da ita zaka rantse cewar ba indiya ka gani,wani hula wanda bata rufe tsakiyar kai ta tsakiya ta zagaye kanta dashi ta sako gashin ta baya,janbaki me taken rubiwu ta saka a lips nata ta sanya kwalli me fito da blue color a take ta fara shanawa a fuska ma,kwanar turaren turarenta Na slim girl ta Shafa da sauran Su tomphord woman da daddy's girl ta saka sannan ta fito,a parlor ta taddashi yana zaune yana shan hot coffee yana kallo,cike da takun katsaita ta tinkaro inda yake,kamshin turaren tane ya shaida masa iso warta wurin,cup na coffee dazekai bakinsa ya dakatar yabita da ido,harga Allah be gane taba,murmushin ta me laushi ta sakar masa tace cikin wata hatsabibiyar murya "Ina kwana yaa Abdul dafatar ka tashi lapia" dak'yar ya saisaita tunaninsa sabida seda ma tayi magana ya tabbatar ita d'ince yace "Good morninh wify how was ur night" yafad'a yana kallonta wani wal tayi da ido tace "splendid yaa Abdul,kaifa?" D'an Murmushi yayi yace "Same as urs,u looking so wow" wani far tayi da ido "thank you yaa Yarima,me kake sha?"

"Coffee,will u like some?" Yabata amsa yana kuma tambayar ta, Mik'ewa tayi daga zaman tace "No thank you,lemme prepare something for u to eat" wani Murmushi yayi "for me or for us?" Ya tambaya D'auke da Murmushi a fuskarsa,ita d'inma Murmushi tayi,tace "sure for the both us"

"That's very good of u" bata kulashiba ta wuce se mazaya mazaunan ta takeyi,da kallo yabi Heeps nata,seda ya had'iya wani yawu me d'aci,sannan ya kawdda kanshi a daidai lokacin da ta b'acewa ganinshi,yace aranshi "Kinada diri Elham sedai bazaki dulmiyar dani ba,Wannan kad'ifirin naki a banza kikeynshi" A gurguje ta feraye dankali ta soye ta had'a kidney sauce ta soya k'wai,ta had'a ruwan tea,ta d'auka taje ta Jere Su a dining, ta zo ta zauna kusa dashi tace "Breakfast is ready" Mik'ewa yayi ba tare da ya kalleta ba yace "Shall we" shi adole ze D'auke idonshi daga kallonta,sabida Shifa ba wai yana santa bane kuma yaga alama so take ta d'aga masa hankali da Wannan k'ayatacciyar halitta me d'aukar hankali,kamar yanda be kalleta ba haka itama ta Kawar da kanta tace "sure" zaman cin abincin bameyin magana harsu ka kammala,dukkaninsu suna tafiya ne da tarbiyar momy ta rashin magana idan anacin abinci,yarigata kammala wa ya kalleta yace "Thank you so much,its soo delicious" Murmushi kurun tamasa ta bar wurin zuwa,parlour d'inta,acan ta baje tana cin kwakwa da dabino data gani a kitchen ta ebo dama cimar tane acewar Sophie G vitamin.....karfe d'aya ta tashiga kitchen koda ma ta duba yabar gidan be sanar mata ba Murmushi kurun tayi tace "A iya sanina dai duk wani namiji me mutunci idan ze fita ko Allah ya kiyaye ze nema agun matarsa amma banda Wannan,tunawa tayi da momy ta d'auki wayarta ta kirata,gaisawa sosai sukayi tace " Ina me gidan naki? " d'an Murmushi tayi cikeda kunya tace "yanzunnan ya fita momy" Murmushi itama Momyn tayi
"Kuyi ta hakuri mamana,kiriqe mijinki hannu bibbiyu na sani dukkanku biyayya kikamun amma da yardar Allah zakuga sakamakon yiwa iyaye biyayya kuma zaku k'aunaci junanku ba kad'anba" godiya tawa momy,Momyn tace "ke Mamana kina da nutsuwa kinga yar uwarki feenah da masifa ta isheni wai aika musu da abinci ba nace aiba wacce ban koyawa girki acikin kuba so bazan wahalar da kaina ba" dariya tayi "momy se hakuri kinsan halin feenah akwai shagwaba" ahaka dai suka sha hira kan suyi sallama.
Fried rice me yawa tayi da meat balls tayi salad na potatoes ta had'a zob'o se tashin kamshin karan fari yake da cucumbers, gidan gaba d'aya ya had'e da k'amshin girkinta,se Wuraren karfe uku ta kammala girkin,wanka tayi ta dauro alwala,tana nan har akayi la'asar ta tashi tayi salla sannan tashirya cikin wani rantsatsen lace pink colour me flowers red aciki,ba k'aramin karbarta yayi ba ya fito da figure 8 d'in tannan CA's da ita ta tufke gashin kanta tsakiya ta fito dashi ta baya,fuskar arna tasha makeup idan ka ganta tamkar ka sace ta ka gudu,uban takalminta me tsini ta saka red ta fito tana tauna chewing gum dake bakinta,sanda tazo tsakiyar parlor d'in takula da Abdul moris da friends d'inshi Su hudu, d'anja da baya tayi sannan ta gaidasu,kafe ta da ido yayi sanda take magana dasu,d'an mitsitsin bakinta yake kallo ga fuskarnan tasha makeup tamkar ta ziyarci wani makeup studio,tace dasu

"Bismillah kuci abinci mana" zayyan ne cikeda zolaya yace "Dama mana kin isa muzo ki hanamu abinci aikinyi kad'an inba haka gobe zamu kara auro wata" dariya tayi har fararen haqoran ta suka bayyana tace "Aini kishiya se idan Anayi a lahira honey da kake gani ba kishiya a tsakanin mu ko ya kace honey?" Tafad'a tana me k'urawa Abdul ido tana dariya, yawunshi ya had'iya yace "Hakane sweery bazan miki kishiya ba har abada" cikin takunta na kasaita tajuya zuwa kitchen wani abokinsu yace da sauri batare dayasan tana jinsa ba"kai yanzu moris tsabar kai d'an iskane Wannan zangad'ediyar zakace bakaso shegen banza kawai" kawai moris seyaji haushi jin ancewa Elham zankad'ed'iya aranshi yace "data saka hijab da bazega surartaba har yace hakan,dining suka nufa Dukkansu ita kuwa koda ta karasa kitchen idonta ya Cika da kwallah aranta tace " Wato Harma friends nashi sunsan ni fankon ashana yafini daraja baya sona,ni ina kokarin nuna musu ana tare shi kuwa ba Wannan a tsarinsa ko?" Da k'yar ta iya saisaita kanta tafito tafara serving nasu tana dan Murmushi, lura Abdul yayi Wannan friend d'in nashi khamis ya matsawa Elham da kallo take yaji wani takaici dabesan dalilin saba,yabi heeps nata da kallo yaga tamkar ita ta dasawa kanta,yace "ki Barshi mana zan saka musu" Murmushi tamasa "Honey lemme just do it,its nothing ai" Noo u go and get us some fresh fruit's for me now" sake masa serving spoon d'in tayi tawuce cikin yangarta,Zayyan ya mikawa spoon din yabi bayanta,janyo hannunta yayi yana Shiga kitchen d'in ya rungumota ta hanyar rik'o k'ugunta ya sanya d'ayan hannunshi ya tallafo kanta ta bayan wuyanta,suka k'urawa juna ido na kusan second talatin itace ta fara d'an yamutsa fuska tana kokarin barin jikinshi,k'ara k'ank'ameta da kyau yayi yace "Elham me haka kikeyi?" D'an wara ido cikeda mamaki ta k'ara yamutsa fuska tace cikin shagwaba "Yanzu kuma yaa menayi" kara matseta yayi jikinshi yace

"Kinganki kuwa,kalli jikinki Elham mesa baki saka hijabi ba? Kinga mazancen fa se kallonki suke" tsuke bakinta tayi sannan tace "Yaa Abdul to yanzu kuma baza'a kalleniba,kurun sabida kai ka tsaneni kowama so kake ya tsaneni?" Shiru yayi kuma be saketa ba yana nazarin kalamnta,cikin sigar rarrashi yace

"Elham ki dena cewar wai na tsaneki,ba kyaufa kina cewa wai na tsaneki nifa mijinki ne" kara tsuke fuska tayi tace "kaga bafa ni bace nace haka Kaine da kanka kafad'a so yanzu me kakeso nace? Ni plss ka sakeni" sassauta riqon daya mata yayi yace cikin sigar rarrashi "Amma dai kin sani cewar ai ke matar aurece,dan Allah ko mayafi ne kisaka mana" gyad'a masa kai tayi alamun to,tama Zata sakinta zeyi se kurun ya kasa danne kwad'ayinnsa ya manna mata Sumba a kunci sannan ya saketa....juyawa kurun tayi tana mazaya masa k'ugu tana rangwa d'a anan ya tsaya amace......Koda dare yayi a parlor ta sako riga da wando na bacci gajeren wandon me aljihu ya fito da Heeps dinnan,ta baje gashinta me kyau kwantacce tazo ta zauna suna kallo tanashan fura daya kawonmata ba mewa wani magana,se Wuraren sha d'aya tamike tace "yaa Abdul I'm Danma sleepy,off to bed good night" Murmushi yamata "Bazaki bari film dinnan ya kare ba mu tashi tare?" Murmushi tayi ta cura hannunta cikin gashin kanta,tayi wata tsayuwa ta Turo k'afarta d'aya gaba tace tana yamutsa fuska"karka damu yaa Abdul bancinnan da gaske yake,idan ka tsayar dani wlhy anan zan maka bacci,kuma na tsani a tashe ni ina bacci" gyara kishingidar sa yayi "Bazanma tashe kiba cak zan d'a gaki zuwa room naki" tab'e baki takumayi ta yamutsa fuska tace "I will not like that either, so just lemme go,good night" bata jira cewar saba ta juya,tun a parlor d'inta ta rufe da key,beji dad'in hakan ba yaso tayata bacci yau,yayinda a d'ayan bangaren ta kudirta baze tab'a Shiga sashinta da sunan bacci ba"

Tir k'ashi muje zuwa to,koya Wannan zaman ze zama,kuci gaba da kasancewa da alkalamin mom Nu'aiym.
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

  *Wannan shafin nakine Lil sis queen Miemie,Allah ya albarkaci rayuwar ki Ameen*

                          12
A d'akinta takasa yin kuka, tunanin irin rayuwar datakeyi da Abdul take tana mejin tsoron kalar zaman dazasuyi idan har tabar k'asar ita dashi kurun, sukuku ta wuni ranar ba karamin tashin hankali take cikiba,da magrib suka shirya zuwa gidan a b'angaren momy suka sauka,kayakyawar tarba tamusu,sunsha hira ko wannensu ya ware ya nunawa momy ba matsala a tsakaninsu,daganan suka wuce part d'in Fulani Habiba then suka wuce part d'in me martaba, ya musu Nasiha sosai akan zaman lapia da mutun ta juna kuma sun d'auka har zuci agabanshi,koda zasu tafi sarqar gwal ya baiwa Elham dalleliya me dauke da zobuna da awarwa raye,ta zuba godiya ba adadi sannan suka fito kai tsaye wurin mota ya nufa da ita sanda taga da gaske yake sannan tamkar zatayi kuka tace "Yaa Abdul bamuje mun gaisa dasu Innah da Baba ba" wulakance ya kalleta
"Au Baba me gadi wai,ina kinga da kanshi ya gaidani sanda muke shigowa kuma ai shine ya bud'e mana gate sabida duty d'insa ne,Kedai daki kaga ya dace ki gaidashi kije bazan hanaki ba,amma ni shi yake gaidani kuma Kema kin shaida hakan" wani bak'in cikine ya tarnak'owa Elham har wani d'aci takeji acikin yawunta haduye yawu tayi masu zafi sannan tace "Na sani ai Yaa Abdul bata yanda za'ayi me mulkin duniya ya gayar da me gadi,dama bance ka gayarda me gadi ko matar saba, amma y'ar me gadi ita ai tasan darajarsa kamar yanda tasan iyayen kowa,ta sani Babba babbane,sabida koba dan sun haifeta ba dole ta girmama Su" tana kaiwa nan ta juya,shi kuwa ya k'ura mata ido yana nazarin kalamanta....gaskiya Abdul akwai mugun hali,suk kalar zugae da khamis ke masa ai shima yanada hankalinsa be dace yanawa Elham haka ba....

  Bayan kwana d'aya suka cira zuwa Lagos,har suka shirgi ba mewa kowa magana, ita ykamma tunda yaqi zuwa gaida iyayenta bata k'ara koda gaidashiba shikuwa ya nuna mata ko'a jikinshi,Suna hawa hanya gogan ya soma bacci ya daura kanshi a saman kafadarta,acikin baccin ya daura dayan hannushi saman cin yarta,ita dai batayi kokarin hanashi ba a haka har suka yi landing, hannunta ta saka tad'an bubbuga cibyarshi firgigit ya farka ganin shi ajikinta ya sanya duk yaji nauyi,shine ya rigata Mik'ewa yace muce, a hotel suka sauka d'aki d'aya ya kama musu badan yasoba,sedan yayiwa momy alk'awarin bazewa mamanta nisa ba har abada, Suna Shiga ta wuce  Bathroom sabida ta gaji towel nata ta dauka a jaka yana kallonta tashige labulen d'akin ta daura towel d'in ta dabe wuce duwawu kadan ba,ta fito ta shige wankan,tana fitowa tazo Shafa mai,koda take zuwa ya dawo dagashi se gajeren wando,girjinshi faffad'a ga wani yalwa taccen lallausan gargasa kwance luf a ilahirin jikinshi se sheqi sukeyi,farar fatarsa ta kara nuna wa acikin bakin gashin tayi luf luf a jikinshi,gabanta ne yayi mummunan wannan karo na farko data fara ganinshi a haka,dan sauri ta dauke kanta tazo tana Shafa mai,haka kurun yaja mata tsaki yace

"Ke menene haka? Meye na zama daga ke se wannan towel bakida kunya ne ko bakisan bakida mara ba da tsirarara ba" kallonshi tayi batace k'alaba taci gaba da murza man shafawarta tamkar bada ita yake magana ba,k'wafa yayi ita kuwa tayi Murmushi,can kuma ta taso tazo kusa dashi ta sunkuya ta juya masa baya,sassauta towel d'inta tayi tace
"Yaa Abdul plss ka shafamun a baya yana mun k'aik'ayi" kamar yace baze yiba se kuma ya lak'uci man ya murza a hannunshi,taushin lallausan hannunshi sanda ya sauka a wuyanta tad'an b'ank'are bazatace ga abinda taji ba awannan yanayin,yanayine na musamman da bata taba tsintar kanta acikiba me wuyar fassara,hakan take awurin Abdul tunda yake beji skin me santsi da laushi irin na Elham ba,Shafa man yake yana lumshe ido yakuma kasa dena wa sanda taga ze rikitar da ita tace cikin wata murya "Yaa Abdul har yanzu?" Lum sassun ida nuwansa ya sauke akanta yace "sorry network news nake kalla hankalina yana can" Murmushi tamasa tace "Tom na gode" wata hatsa bibiyar rigar bacci ta saka me had'e da wandonta iya cinya zip ne ta gaban rigar se faman janshi takeyi ya sak'ale tamkar Zata fasa kuka tazo kusa dashi

"Yaa Abdul dan Allah ka rufe mun zip d'innan mana kaga fa se janshi nakeyi amma mak'ale" d'agowa yayi ya sauke idonshi daidai cikinta,flat tommy d'inta ya k'urawa ido yace aranshi "wannan Yarinyar anyi yar duniya" Tasowa yayi tsaye ya janyota ya manna jikinsu tamkar ze maidata ciki sannan ya d'an matsa kad'an ya kamo zip d'inta a maimakon ya ja zip d'in seya cura hannunshi cikin rigar ya shafi tommy d'in ta murya k'asa k'asa yace "Hafsat wai nikam yaushe rabonki da saka abinci a cikinnan,jifa yanda ya lafe" hannunta takai saman Nasa dake kan cikinta take ta k'ara masa wani shock ya D'auke numfashi tace "Yaa Abdul meye haka? Dan Allah ka dena banaso" idonshi da suka sauya launi sabida azaba ya sauke mata yace "Menayi kuma?" Shagwabe wa tayi "Dan annabi nidai ka rufe mun zip d'in yunwa nakeji" dakyar ya iya rufe zip d'in,a wahalce ya koma ya zauna,juyawa tayi tana dariyar mugunta a ranta tace "Indai ina duniya kuma muna tare seka duk'awa me gadi da ahalinsa wlhy" Har takai kofar fita zuwa parlor dake d'akin ta dawo

"Yaa Abdul I'm hungry fa" k'ura mata ido yayi yace "Nasani yoghurt zakice kina wanka na saka an kawo miki" D'an lumshe ido tayi tace "But yau har da gasasshiyar kaza irin me d'awafi d'innan zanci plss,wasu lokutan idan akayi wa Baba megadi albashi yakan siyo mana" k'irjinshi seda ya doka jin abinda tace sarai ya sani dashi takeyi yace "Shirya mu taka anan bayan hotel nasan ana saidawa" da sauri ta wani daka tsalla tace "Yauwa bara na saka hijab kin na" Murmushi yayi yafara tariyo tsallen datayi yanda mazaunan ta ke girgiza san ransu,Shifa harga Allah ya kusa ajiye zancen Khamis gefe, idanma asiri suka masa aiba laipi bane danya kusanci matarshi kumama koda zasu rabu ai Gara yasan ya Mora,beside kyautuwa ma yayi a karya taba sakin matarshi,tunda ai zab:in momy ce,da wannan tunane tunanen har tace "Yar megadi na jiran Sarki me jiran gado,nafa kimtsa" beji dad'in maganar taba amma seya basar ya Mik'e kawai ya zura jallabiya rsa ya ce "muje" haka suka jeera suna tafiya ba mewa wani magana acikinsu,suna karya kwanar layin ya rik'e hannunta,kallon shi tayi batace komai ba,acan suka siyo suka k'aro juice suka juyo,har suka iso ba wanda ke magana,anan suka bace tare suka cin ye kazar tatas,mikewa tayi ta wanke baki ta dawo ta haye gadon ta kwanta abinta cikin nutsuwa bacci barawo shine ya sungumeta suka ware..... Ba ita ta farkaba se Wuraren karfe biyu na dare dama tana tsammanin zuwan period nata,aikam ciwon mara me tsanani ne ya tasheta,a razane ta tashi sai kuka,se Innah take kira tana yarfe hannaye,a k'asa ya kwanta dama saman carpet acikin bacci yaji kukanta ya farka da sauri yazo ya dagata ya daurata akan cinyarsa
"Hafsat lapia menene ya sameki haka" tana kuka tace "Yaa Abdul na Shiga uku mtrl pain ke damuna mutuwa zanyi" tsoro yaji sosai ya rasa me ze mata,acikin rudu yace "Me ake baki Idan yana miki ciwo ne?" Kasa ansashi tayi tayita kuka se tambayoyi yake mata amma sa. Ta kasa amsashi sabida azaba,kan kace me wannan tafara amai me tsanani da gudu take zuwa toilet yin aman,a haka har kusan asuba dawowa tayi ta kwanta akan cinyarsa duk ya damu tanata kukan,hannu ya sanya yana d'an patting bayanta a hankali,da kad'an yaji shiru koda ya duba tayi bacci sosai ta bashi tausayi yalwataccen gashinta duk ya baje ya rufe mata fuska se gumi take had'awa hannu ya saka ya janye mata gashin a hankali ya sunkuya ya sumbaci goshinta yace "sorry my wife, u will soon be well" kasa d'agata yayi ya barta anan tana bacci nta har bakwai ta gota sannan ya lallab'a ya ajiyeta ya je sallah,kuma dawowa yayi kasan cewar flight nasu se dare ze tashi ya sanya ya shige cikin jikinta ya rungumeta sosai suka ci gaba da baccin Su,har cikin ransa

7 / 18