Author : Billy Galadanchi Category : Romance
ma motsi rikicewa yayi lokaci daya ya kwasheta suka rufa masa baya seda ya sakata a mota sannan ya tuna da key,dagudu yaje d'akin ya had'o da wayanshi da ku d'ad'e,asibitin dasuka kaita ranar ya nufa,da sauri suka karb'eta aka danna mata ox da komai da injections,Abdul se zirga zirga yakeyi dawowa wurin Su Ashraf lokacin sun dawo sallar asuba yace "Waiku kuwa wane iskancinne ya hanaku kirana tun d'azu Idan da wani abin ya samu Yarinyar mutane me zakuce?"
"Yaa munfa kiraka baka d'aga ba,ka duba wayarka" kan wani yayi magana doctor d'in yace "Patient naku ta farfad'o,dama kunsan case na athsma yana sauka da Wannan injection da sauri,sedai ku kiyaye abubuwan dake saurin tayar mata da asthma" da sauri yaje d'akin, yana zuwa yaje wurinta ya riko mata hannu "Sannu Hafsat ya jikin?" Murmushi tamasa tace yaa Abdul zansha ruwa dan Allah" da sauri ya bude robar ruwan dake gefenta ya daga ta,asaman jikinshi ya kara ta ya bata tasha,gani yaye ta lafe ajikinshi ya sanya be d'aga taba yace cikin sanyin murya
"Elly bansan meyasa ba Idan bakida lapiya hankalina gaba d'aya yakan tashi,dan Allah na rokeki ki guje wa duk wani abinda ze kawo miki rashin lapia musamman irin Wannan,nafa Zata mutuwa zakiyi ki barni hankalina ba k'aramin tashi yayiba plss ki dena shan sanyinnan" mamakin kala manshi ne ya sanya ta d'ago ta kalleshi k'wallan datake kokarin tarewa ya sulalo,hannu ya saka ya share mata k'walar ya mayar mata da kanta saman k'irjin sa yana patting bayanta a hankali "Noo plss Elham banasan kina yawan kukannan Alhamdulillah kinji sauqi,koda inda yake miki ciwo ne?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,da sauri yace "sanar mun inane gayamun kinji,ina yake miki ciwo" janye jikinta tayi daga nata,ta kwanta tace "k'irji nane yakemun zafi,kuma se ina jin ribs nawa tamkar iska me sanyi tana Shiga cikin ribs d'in" kurawa dan tsukakken bakin ta ido yayi yanda take magana tana yamutsa fuska dukya gama burgeshi yace "zan sanar wa doctor yanzu I just cnt leave u in pain" Murmushi ta masa tace "Thank you" b'ata fuska yayi da wasa "Sabida na kula da Lapiyar matana kike wani cemun thank you bana so" Murmushi kurun tayi batayi magana ba.
A daddafe suka karasa kwanakin biyu da suka rage musu suka dawo gida da yola,daga kaga Hafsat kasan batada lapia ta d'an rame,ba laipi Abdul yana kula da ita sosai,suna dawowa da kwana biyu ya wuce London......
Abdurrahman Allah yayishi da ilimin Zane tun yana karami,kuma Allah ya daukakashi har girmanshi Zane ba irin wanda bayayi,a London kampanonin dake k'era motoci yake zanawa mota,yayinda har kampanonin builder's yake zanawa gida,a yanzu haka yanada kampanin sa na kansa Abdul builder's dake birnin London,ba k'ananun kud'ad'e yake samu a harkar ba,ya kasance yaro ne d'an k'walisa meji da kansa ga tsananin k'yank'yamin masifa komai nashi CA's dashi.......
Satinsa uku ga dawo,a parlorn sa yake yana kallo tayi sallama ta shigo kasancewar ya sanarwa feenah Idan tazo part din momy ta Turo masa ita phone nata a kashe yake,har qasa ta durk'usa ta gaidashi,da Murmushi d'auke a fuskarsa ya ce "Zonan ki zauna kusa dani Elham" batayi musuba taje a kujerar da yake ta zauna ya kalleta sosai ya janyo hannunta na dama ya rike yace
"Elham mesa kika mun haka?" D'auke kanta tayi zuwa d'ayan side d'in tace cikin wata murya me sanyi
"Yaa Abdul me na maka" karkatowa yayi gefenta ya daura kafafuwan sa gaba d'aya saman gadon yace "Yanzu ke baki masan me kika munba? sati na uku bana k'asar seki kama wayarki ki kashe gaba d'aya,abin takaicin ma nacewa feenah ta baki waya wai kin tafi gidan k'anwar mamanki,dagaske kin kyauta kenan Elham?" Sosai ta juyo ta k'ura masa ido,tana mamakin yanda yake rero kalamai tamkar da gaske,mutumin dayace ya tsaneta ina ruwansa da damuwa da inda taje" iska ya hura mata a ido,ta gyara zaman ta,sannan ta kalleshi ta k'ara ya mutsa fuskarta tace "kaga nifa sauqi namaka,ina dama ko tafiyar damukayi akan momy kake kulawa dani,yanzu baka gari menene ze dameka danna kashe Wayata beside ni a ganina wanda ka tsaneshi ai sauqin kane idan ya janye jikinshi daga naka" Hannunshi d'aya ya saka ya dafe kanshi yace "yaa salaam,Haba Hafsat wayene yace dake na tsaneki?" Murmushin yak'e ta masa tace "Yaa Abdul kenan,kasani matsalar furuci kenan ka furta akan idona kuma idanuwa na suna kallon naka sanda ka furta hakan na hango tsanar tawa k'arara a idonka da zuciyarka gaba d'aya" hannunta dake riqe a nashi ya matse sanda ta kwallah k'ara yace "Haba mana Hafsat,dan Allah ki dena furta irin wayannan kalaman kinji" kallonshi tayi tace "Ka gani ko yanzu fa ka kasa furta cewar ba k'iyayya ta aranka,kurun kace na dena zancen,naji Kayi hakuri bazan k'araba" juna suka k'urawa ido na yan dak'iku yayinda Abdul ya kasa gane ainahin meyakeji game da Wannan baiwar Allah ita kuwa tsanarsa fall a ranta sunan sa ma bata san ana anbata,shine ya Kawar da shirun dacewa
"An sanar dani kince ke kurun a daura aure bakyasan wani bikin mesa ?" Kallonshi tayi dama taci d'amarar gaggasa masa magana tace "Ba bikin bane banaso auren nakane yake batamun rai wlhy banaso yaa Abdul,zargi na fa kake kuma kace ka tsaneni Wannan wane irin zama zamuyi,yaa Abdul bansan wazan sanarwa ba amma wlhy gabana fad'uwa yakeyi,tsoro nakeji" matsawa yayi kusa da ita ganin tana kuka,ya tallafo ta jikinshi,ita kanta mamaki takeyi yanda bata iya tureshi idan yazo jikinta. yace cikin rad'a "ki dena jin tsoro Elham,kuma gaban ki ya dena fad'uwa I promise to always be by ur side,dan Allah karki badani kowa fa jiran ranar aurena yakeyi,ki saki jikinki muyi bidirin mu kinji?" Bata yi magana ba kamar yanda bata bar jikinshi ba dan kanshi ya janye jikinshi daga nata........ba laifi Elham ta saki jikinta an cashe kuma na narke dukiya a Wannan bikin,sunsha gyara na musamman taciki data waje ba inda basusha gyara ba,fatar Yar fulanin yola se sheqi takeyi, komai iri d'aya aka saka musu ita da Su feenah.....
*Bayan ankai Amare*
Yan matan Amarya sun watse,ya rage Amarya kurun,Abdul ya daukar wa kansa alkawarin baze tab'a barin ya rab'i Elham ba,shi harga Allah kazantar ta yakeji,sannan kuma batada matsuguni acikin zuciyarsa sam,kazar Amarci yashigo da ita a hannu,ya mata sallama,batare da wata kulawa ba yace
"Kici abinci kafin ki kwanta seda safe" daganan be jira cewar taba tafice daga d'akin,kuka sosai Elham tayi a Wannan daren,a ranta tace Wato dama ya kyalenine sabida agama bikin,yanzu nazo gidan na zama banza ko,daga nan ta kudiri niyyar cin ubanshi,kazalika ta dauki alkawarin baze taba ganin bacin rai a fuskar taba.....
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
11
Washe gari bata bude kofa ba se karfe tara na safe,a parlor ta sameshi ta hade sosai cikin wata dress thee green color ,har kasa ba karamin kyau tamata ba,ta watsa pink lipstic dinta se tashin k'amshi takeyi,tana kallonshi ya D'auke kanshi daga dubanta da sauri,itama basarwa tayi tamkar bata ganshi ba ta wuce warta kitchen,bayanta yabi da kallo sannan yayi k'wafa yace "Dolene na d'auki girmana,yarin yarnan Zata rainani,ita kuwa ganin datayi ya shareta yasanya ta kudiri niyyar ramawa, ha d'add'iyar indomie ta dafa se tashin k'amshin curry takeyi tasha kayan lambu,ta soya k'wai da kifin gwangwani a had'e,tafito plate d'aya daman tayi tana wakar jirgin soyayya,cikin parlor d'in tashigo ta daura kan dining ta bud'e fridge ta d'auko lemon gwangwani da ruwa d'aya tazo kusa dashi ta zauna,ta kalleshi da d'an Murmushi tace " Ina kwana yaa Yarima? " yana wani tamke fuska yace "lapia lau" ataikace...murmushin ta kuma yi a ranta tace Kayi da gwana wlhy, tana kai lomar farko ta lumshe ido ta sanya hannu ta Sosa kunne tace "Garin dad'i na nesa wlhy" tana ci tana waqar jirgin soyayya abinta,ahaka wayanta yasoma ringing,saam ce ta d'aga tana ihu abinci a bakinta,saam tace "Banza me kike ci?" Dariya tayi daidai lokacin data had'iye lomar dake bakinta tace "Banza wlhy Wannan had'a diyar indomie damukeci a gida yau ma Nayi,ina loma ina tunawa da Rolex tsinanne Nike kawowa skul amma seya wawushe ya barmu,yanzu kuwa ni kad'ai inci karena ba babbaka" Murmushi saam tayi "beb I'm really missin those days wlhy ina, mijinki?" D'an kallonshi tayi da k'asan ido taga shidinma satar kallonta yake tace "mijina kuma? Ohhh kicemun yaa Abdul,yana nan qalau" tsaki saam tayi "wannan wane irin magana ne Elly watch ur tongue" tsakin itama tayi tace
"Kinga nifa har yanzu Banyi wanka ba so,wlhy jina nake kamar a gidanmu,mantawa nake inada aure ma bare wani abu wai miji" bata rai saam tayi "Dan Allah ki dena karya jiki kinji,ba kyau abinda kike Wannan sirrin Kune be dace kina gayawa koda niba,nidai zancen yayin biki nane an fitar dubu goma sha biyu k'waya uku" ihu tasaka sanda ya kalleta tace "kaji manyan mata maganin k'ananun mata,d'an kara sending mun acc/number dinki plss zan miki sending yanzu,Choo biki on point* dariya sukai sunata hira kan daga bisani suyi sallama,ta zauna ta cinye indomie tatas tasha juice sannan tazo shan ruwa tana d'aga robar ruwan a bakinta ya taso a fusace ya dauke ta shuri atake ruwan ya tarwatse a parlor din, kallon mamaki tabishi dashi,kan tasamu bakin magana yafara masifa
" k'azama kawai,shiya sanya nakejin k'yank'yamin ki wlhy,banda kina yar k'auye kuma jaka menene na saka robar ruwa agaba ki saka ta a baki,bazaki nemo cup ki shaba? Wannan qauyancin nan gaba idan Nayi bak'i a d'aki zan riqa b'oyeki karki yarfani da Wannan halin na yayan kauyawa dakike nunawa" Tunda Elham take bazatace taji abinda ya b'ata ranta irin Wannan ba,ko zagin farko daya mata bekai Wannan baqanta ranta ba,ace mijinka ya kalle kan yace ma y'ar k'auyawa? " Wato iyauenta ne ma k'auyawan plus jaka ita matarsa itace jaka,lokaci d'aya idonta ya ciko da k'wallah take ta fara kuka,murya na rawa tace "Yaa Abdul nice jaka? Nice iyayena suke qauyawa agareka?" Kurun seya wanketa da lapiyayyen mari,yace "ni ban ambaci iyayen kiba karki kuskura ki sauya mun magana kinji na gaya miki wlhy" dafe wurin tayi ta wara ido tana kallonshi zuwa yanzu ta gama tabbatar wa kanta Abdul baze tab'a santa ba,kuma tama fara tsoron sa,sabida tasan wata rana dukna tsiya zatasha,da gudu tawuce d'akinta ta banko k'ofa ko wayarta bata tsaya d'auka ba" acan tafi awa biyu tana kuka dama gwana ce a Wannan b'angaren,indai kukane.Taso ta kira saam setaga tamkar wannan tonon asiri ne agareta,amma fa Elham ta fusata daganan ta dauki k'udirin baze k'ara ganin haqwaran taba har abada, bazata fasa girka masa yaci ba amma fa ko inda yake bazata k'ara zama ba har abada,tsanar sa me tsanani ya addabi zuciyarta,har wani tafarfasa zuciyar tata ke mata, a haka taje ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa jeans 3 quarter da bingilalliyar riga pink colour,Yaukam ba makeup ta kalminma flat aka Saka, murtuke da fuska tafito dama duk fuskar ya kumbura idanuwanta ta sunyi jajir fuskar nan tayi jajir abinka da farar mace,a parlor ta sameshi ko kallonshi batayi ba ta wuce abinta kitchen,rice and stew tayi da salat ta soya kaza ta had'a musu mango juice tun a kitchen ta zuba komai nata a plate takai d'akinta ta dawo ta kai masa Nasa dining,ta zo inda tabar wayar ta,ta d'auka tace "Yaa Abdul abincinka yana dining" ko kallonta beyiba seda ta juya yace "yauwa" murya can k'asa dama yunwa yakeji sosai daurewa kurin yake,ga gogan da masifar k'yank'yami becin girki sena gida....
Haka kwana ki suka shud'e har sati biyu kowa tasa ta fissheshi yakeyi,tunda tazo gidan bata tab'a Shiga side d'inshi ba koda tashiga dariyar data kwana biyu ba tayiba ta dinga tsulawa tamkar wata zautacciya har tana rik'e ciki,ba wani abu bane ya bata dariya irin yanda taga komai Nasa a har gitse ga boxers da singlet nashi tsilli tsilli masu datti,laundry basket nashi gwanin ban tausayi,kan gadonnan kuwa tamkar inda akayi yaqi,sosai ya bata mamaki ace duk iyayi da tsafta irin nashi d'akinshin a haukace, a ranta kuma tace "Laifi nane ai its my duty wlhy,Harma naji kunyar kaina sosai" komawa sashenta tayi ta saka wandon maza irin k'ananun nan masu yanka ata gefen cinyoyi,wanda da kad'an suka wuce duwawunta,ta sako vest baqa tafito sosai ta gyare d'akin ta turareshi da turarukan masu daukar hankali,tashige ban dakin sanda ta wanke boxers din da singlet duk sannan ta wanke ban d'akin a ranta tace "Ko matar malam jabir ai da haka ta ciwo kansa"# wani haske Ummie Aisha. Tana idarwa tafito daga part d'in a parlor d'inshi suka had'u da sauri ya dauke kanshi itama haka ko kallon shi batayi ba tace " Sannu da zuwa yaa Abdul" a wulakance yace "Me kikemun a d'aki kokuma wata k'ulallaiyar ce yanzu" yafad'a a maimakon ya am sa gaisuwarta ,Ras taji gabanta ya fad'i sosai da sauri ta d'ago ta kalleshi sarakan kukan se hawaye,ita yanzu sosai yake bata tsoro wlhy,murya na rawa tace "Bafa abinda na maka part d'in na gyara kurun" juyowa yayi jin muryarta na rawa yace "Ubanwa ye yace dake ina bukatar hakan,Wato dariyar dakika ga ina miki shine har ya baki damar ki saka k'azamin hannun ki kina damkar mun kaya ko?" Mamakinta ne ya karu waiita yake kira k'azama,batasan yaa akayi ta tsinci muryarta da furta "Kayi hakuri plss yaa Yarima" tsaki yaja yayi gaba,ita kuwa d'akinta ta wuce se nana tawa kanta takeyi "Bazakiyi kuka ba Elham kin gaji wlhy,koda bazaki ramaba ki nuna masa cewar be damekiba,kuma karki fasa neman ladarki" a haka da k'arfin hali ta share k'wallar ta,Shikuwa a haukarshi wai basanta yakeyi ba wani asiri ta masa yake jin sha'awarta,wannan kuma ba wanda ke zugashi se abokinshi dakesan yayi kuskuren sakin Elham shiya aure Wato khamis,kuma yayi k'udirin baze dakata ba harsai ya cimma burinsa......Acan ma ta manta wayarta batare da wata farga baba bayan tayi wanka tasha gayu ta nufi part din,da sallamarta ta Shiga ta sameshi yayi d'ai d'ai a kan gadon yana danne dannen wayarsa,be ansataba itama kuma bata damuba ta dauki wayarta ta juya harta kai k'ofa yace "Ke zonan" gabanta ne ya fad'i jin yakirata da ke,lokaci daya kuma taji ranta yabbaci,Wato har takai baze iya kiran sunan taba?" Jiki a mace ta juyo ta tsaya wurin gadon batare datayi magana ba,cikeda isabba tare daya kalletabba yace "Visa naki ya zama ready,nanda kwana ki uku zamu wuce London ki shirya kayanki,kuma yau da dare zamuje gidan me martaba ki musu sallama gobe zamuje gidan Su momy ki musu sallama jibi da sa sassafe zamubi jirgi mu sauka a Lagos, Friday zamu d'aga zuwa London" shagwabe wa tayi,wanda itafa harga Allah bata masan tanayi ba tace "yaa Abdul dan Allah kamun rai,bikin saam next week fa,kabari idan aka gama mana" wani mugun kallo ya wurga mata,yace a fusace yana mike wa tsaye"wai nikam a zatonki zaki yaudareni da Wannan shagwabar munafurcin,kinga bokanku be Ciba shine zaku zomun ta wannan hanyar,wlhy wannan tafiyar ba fashi,kar kuma ki yarda wai sabida inaso zanje dake,takura ni akayi wlhy,banza kwad'ayayyiya danla can matsa ki bani wuri" tayi alkawarin bazata kuma yin kuka agabanshi ba wannan ne ya sanya ta masa murmushin yake wanda akace yafi kuka ciwo tajuya batare datayi magana......
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
10
Abdul se zirga zirga yakeyi a d'akinshi ya kwasa bacci,ya rasa dalilin daya sanya zuciyar sa keta faman azalzalarsa akan yaje gun Hafsat,yanaga koba komai zataji sanyi,betab'a jin abokanshi sunce sun kwana d'aki daban daban da matansu ba musamman sabuwar Amarya, haka dai ya hakura ya kwanta dukda a wannan bacci sam be dauke shiba, da safe ma yaso Shiga d'akinta amma seyaji nauyin yin hakan....a b'angaren Elham kuwa Wannan rashin shigowar da safe ba k'aramin b'ata mata ranta yayiba,kuma ya kara nuna mata cewar ita da banza basuda maraba ko kad'an,sosai kuma taji ta qara sanarsa,tasani da faruk d'inta ne baze tab'a yi mata haka ba,wata k'ila ma sam zumud'i baze bari yabar kusa da itaba,kuka ta zauna ta saka ita kad'ai bame rarrashinta,tana Tsakiyar kukan wayanta ya soma bulayin neman agaji,dagawa tayi taga saam ce aminiyar ta da kukan ta d'aga bata boye mata komaiba,saam cewa tayi mata "Kinga ina gidan Aunty Husnah dama tace Zata baki tips na horar dashi sabida haka bara na bata,idan kina kuka kinma damu kenan" wayar aka baiwa Aunty Husna suka gaisa tace
"Kinga Hafsatul Elham share hawayenki,yanzunnan zan saving digit naki a waya zanna riqa d'auraki akan service wlhy se yamiki magiya akan gwiwowinsa kekuwa alokacin zamu nuna masa cewar tabbas shayi ruwane,zamu tauna tsakuwa sabida aya taji tsoro kazalika zamu jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya jal,Abu na farko danakeso dake shine ki cirewa rayuwar ki qiyayyar sa sabida mijinki ne zawarci masifa ne,sannan kuma qiyayya jafa'i ne wlhy, komai zece da iyayenki kansa yayiwa Allah ne masani,yanzu sanar dani kina da k'ananun kaya?" Tana share majina tace "Ea dama ni nafi shiri dasu da dogwayen riguna" Murmushi Husna tayi tace "Yauwa yar gari,inaso ki cire abinda yake halla ka matan hausawa Wato kunya,ki rataye a kwandon shara,mijinki Ne ba haramci ko tsirara kika fito masa,Ki fara dannan guntayen riguna da wanduna da d'amammun kaya kina rafka uwar kwalliya,na sanki da yalwar gashi ga jiki me daukar hankali,lallai ne ki rama wulakancin daya miki idan ya kawo kanshi domin dolenshi ma yazo,karki kuskura ya gane kinci ciwo,kuma ki masa girki na wuce sa'a,ina fatan dai kin koya agida kosai nazone?" Dan Murmushi ya sub'uce mata tace "A wurin momy Fulani ba kalar girkin daban koyaba,har na turawa ma sanda take a k'asar waje tana koyamun,kuma Alhamdulillah na dauke