Author : Billy Galadanchi Category : Romance
sanar wa momy" sassauta murya husna tayi cikeda rarrashi
"Haba Elham Karki yiwa momy haka mana,kinsan yanda take k'aunarki d'innan Zata iya yanke jiki ta fad'i ga kuma an mata mutuwar Ameer na damunta,dan Allah na rok'eki ki gyara aurenki da kanki batare da sanin kowa ba" nisawa tayi tace "Idan haka ne Aunty ina da shawara"
"To ina jinki Hafsat" daga nan ta zayyane mata komai yanda take ganin za'ayi dashi,ta k'ara da cewar "Aunty wannan ne kad'ai hanyar danike ganin zamu bi,Abdul be kyauta wa kanshi ba aganina kuma beyi jarumta ba amaimakon yayi jarumta ya nemi mafita seya sakarwa yan uwansa ragamar rayuwar sa gaba d'aya"
"To Elham ina fatan Allah ya sanya wannan tsarin namu yayi working kinji" sallama sukayi ta ajiye wayar cike da bacin rai,har kusan kwana ki biyar bata k'ara ganin Abdul a gidan ba da wannan take tunanin bata yanda za'ayi plan nasu yayi working,a maimakon ta kira Husnah,kurun se fushin zuciya ya d'ebeta ta kira momy ta saka mata kuka,cikeda wauta ta gaya mata komai tsaf daya faru,B'acin rai me tsanani ya ziyarci momy,rayuwarta ta b'aci,bak'in ciki ya lullub'e ta hankalinta ya tashi,kuka kawai ta saka ta kashe wayar,a fusace ta kira Number d'inshi.....
Yana office zaune yana tunanin yanda zeyi da Elham so yakeyi yace ze maida aurenta amma yasani bazata aminta dashiba,yana tunanin yanda zeyi rayuwa batare da Elham ba,yanzu ya haqiqancewa kansa rayuwarshi batada wani amfani idan ba Elham,Mema zesa yayi wannan tunanin har ya biyewa san zuciyarsa ya saketa,yana tsakiya da wannan tunanin wayarsa ya soma ringing, gabanshi ne yayi mummunan fad'uwa ganin sunan momy domin kuwa basufi awanni biyu da gama wayar ba,yakuma sani banza bata kai zomo kasuwa,jiki a mace ya d'aga wayar....
"Baba na na gode da abinda ka sakamun dashi na sakar mun mama na da Kayi, ka mayar mun da ita k'aramar bazawara,ka tozar tar dani,baka dubi halin rashin Ameer danake ciki ba ka sakar mun yarinya,me kake so nace da iyayenta? Wlhy ka wulakanta ni fiye da tunaninka,kuma ka sani sena rama da yardar Allah Mamana Zata auri miji wanda ya fika lallai ka Turo mun ita as soon as possible sabida ta sanar dani ba iddar ka a kanta zamanku tare yanzu had'arine Babba ba k'arami ba" kafin yayi magana ta kashe wayar koda ya kuma kira wayarta a kashe gashi feenah bata gida yanzu bare ya kira ta bata,dafe kanshi yayi yata kuka tamkar k'aramin yaro,seda yayi me isarsa sannan ya tashi zuwa gida,d'akin Elham ya wuce kai tsaye ya tarar ta idar da sallah tana adua zama yayi harta idar,juyowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta
"Hafsat mesa kika mun haka? Mesa zaki zab'i had'ani da mahaifiyata? Menene ban miki ba a rayuwa? Sabida kawai ki dauwama a farin ciki na sadaukar da nawa farin cikin,Ashe ban cancanci ki rufa min asiriba? Bayaga haka na gama yanke hukuncin zan kama aure na,Mesa bazaki fara tambaya na tsarin dana mana ba" wani mugun kallo ta wurga masa tace a fusace
"Wlhy Kayi kad'an na kuma zama matar har abada,da kake zancen kama aurenka sekace wata tinkiya kokuma dabba,bakada labarin cewar Na gama idda,dole ne se an sake daura mana aure,kuma bana buk'atar k'arasa rayuwata da ragon namiji,mutumin daze bar ragamar gidansu ta lalace sabida rashin lissafi,aure na ya kare dakai har abada,banida iddar ka kuma Baba me gadi ya kaini islamiyyah,an sanar dani cewar idan idda ta yanke baza'a k'ara komawa aure ba se an d'aura kuma da waninka zan d'aura bada kaiba,na gama dakai har abada" duk girma irin na Abdul kasa daure wa yayi ya saka kuka
"Elham wlhy bazan iya rayuwa batare dake ba,kuskure ne nayi kuma na gane kuskurene plss give me a second chance" dariya ta kwashe dashi "Off course I can give u one big another chance to destroy my life" matsawa yayi kusa da ita yace
"Ba haka bane Elham,wlhy kece rayuwata gaba d'aya, banajin zan iya rayuwa baki" ka tayi magana wayarta ya soma ringing, dauka tayi taga yaa Ibrahim ne,d'agawa kurin tayi,t wani shagwabe murya
"Yaa Ibrahim dan Allah fa tun yaushe na kiraka shine se yanzu kake kirana?" Daga d'aya bangaren kuma Murmushi yayi najin dad'i yace
"Kiyi hakuri Rose kinji,inata aiki ne yanzunnan na shigo gida go lunch ban ciba" K'ara langwab'e murya tayi tace "Yaa Ibrahim kai kuwa seka riqa wani tunamun da yaa faruk na,shine yake kirana da Rose" Murmushi yayi shi yakasa gane kan Elham yanzu kuma tace dashi wai aurenta ya mutu,kuma batada Idda dama auren dole akayiwa dukkansu
"Ehn love one tintin Kodai yanzu da yaa faruk za'ayi aurenne?" Dukda tasan cewar Abdul bawai yana jiyo me Ibrahim ke cewa bane,amma seta tsinci bakinta da furta Kalmar "Bazan kuma aure a gidan sarauta ba,indai yaa faruk ne na hak'ura gaba d'aya, kawai dai sunanne yake zuwarmun da good memories damuka kasance a tare,he's such a nice person,nasan da ace Shina aura,da Banyi zaman zawarcin k'uruciya ba a yanzu,baze tab'a saki naba sabida yana sona sosai"
"To kiyi hakuri wata rana se labari,idan na kammala abinda nake zanyi kiranki" sallama sukayi ta wuce bathroom kai tsaye tana me jin zafin yanda zuciyarta keso ta bata kunya akan Abdul,mesa takejin tausayin sa ne?" Wannan itace tambayar data kasa samun amsarta tuni.....
Juyin duniya Abdul yayi amma Elham takasa bashi fuska,hasalima zagine ke Shiga tsakaninsu,a haka a rikice ya dakatar da duk abinda yakeyi ya kwaso ta suka dawo Niger.......
Zagi na wulakanci momy ta masa,yashiga magiya amma fir taqi saura rarsa,iyayenta sunyi bak'in cikin wannan wulakncin sedai wannan karon a wurin momy ta dawo da zama gaba d'aya,d'akin feenah shine ya zama nata,hankalin Abdul be kara tashiba seda yaga har me martaba Fushi yake dashi, shirya wa yayi yaje fadar me martaba,a durk'ushe yake agaban me martaba yana kwasar gaisuwa,daga gaisuwar kuwa me martaba yamata banza,seda ya raina kanshi sannan yace
"Abba dama nazone akan zancen Hafsat,dan Allah a taimaka a dawo mun da ita,tunda saki daya ne,Inshaa Allah,wannan kuskuren baze sake faruwa ba" yafi mintuna sha biyar da gama magana me martaba be kulashiba,ga bahalin cewa komai,se can yace
"Ina so kasani,mahaifiyata Hafsat ta kasance me rauni tun kafin zuwan tsufanta kasancewar batada lapia ko kadan,mahaifiyar Elham itace ke d'awainiya da ita kasancewar a b'angarenmu bamuda macen dazata kula da ita,bata tab'a gaji yawa da kulawa da itaba kazalika bata tab'a karb'ar sisin kwabon mu na ladan d'awainiyar da take da ita ba, alokacin datake fama da matsananciyar rashin lapiya Asabe baro mijinta take ta dawo ta kwana a wurinta,itace da kanta ta samo mata maganin hausan datayi ta sha harta samu lapiya,tafara tafiya bayan tayi shekaru takwas bata taka k'afafuwanta,sabida yaa d'aukar Mahaifiya ta matsayin mahaifiyarta tana haihuwa ta sakawa yarta suna Hafsat!!! Yarinyar da shekara da shekaru Allah be basu haihuwaba se daga bisani suka haifeta,soyayya me tsanani mahaifiyata keyiwa Elham wanda wannan shaida ne kowa yasani" "shiru yayi yad'anja fasali sannan yaci gaba
" Anya Abdurrahman kayiwa Mamana adalci daka saketa da k'uruciya? Bakada labarin matsalar da wannan sakin ya jamun awurin Mahaifiyata akan na bada auren takwararta akan mijin dabe dace da ita ba? To ka sani gangan cin danayi abaya bazan k'ara maimaita irinshi ba har abada,Elham ta kawo mana yaron dazata aura me suna Ibrahim kuma mun bashi aurenta nanda sati biyu masu zuwa" zabura yayi tamkar wanda aka tsikara ya saka kuka agaban mahaifinshi
"Dan Allah Abba kamun rai,na rokeku kubani wata damar nayi alkawarin zan gyara kura kuraina,na baya,zan kula da ita zan rayu da ita cikin Aminci" Murmushi me martaba yayi irinna manya yace
"Abdurrahman ka rigada kafara haduwa da darasin rayuwa, da wannan zakasan muhimmancin tunani me zurfi kafin yanke ko wane irin hukunci" da kuka yabar wurin..... Sanye take da doguwar rigar less ash color tayi rolling da red d'in mayafi,fuskar nan tasha makeup tamkar babu abinda ke damunta,nan kuwa tunanin Abdul ya tayar mata da hankali matuka,tarasa nutsuwar ta gashi sam ta gayya ta gayyato Ibrahim a rayuwar ta bata taba zaton cewar ze gabatar da kanshi da sauri har hakaba, Dukda bata sonshi, amma a yanda Abdul ya wulakanta ta Zata koyawa kanta san Ibrahim ko yaya ne......kamar wanda k'wai ya fashewa aciki haka yake tafiya,a garden yazo ya sameta zauna kusa da ita,waigowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta gaba d'aya,cikin sanyi murya ya furta
"Hafsat zuwa nayi muyi magana akan zancen aurenki da naji,dan Allah ki taimakamun karki barni" wani malala cin Murmushi tayi tace
"Kamar yanda Kayi dogon nazari akan sakina kafin ka sakeni,haka nayi dogon nazari akan auren masoyina Na haqiqa,Abdul bakada hurumin dazakace wai na fasa auren shaqiqina na dawo hannun wanda bema san darajar iyaye na ba,inaso idan mafarki kakeyi toka farka,sabida bazan tab'a auren kaba" k'ura mata idonshi yayi da suka sauya launi zuwa jajaye yace murya na rawa
"Hafsat nasani ban miki adalci ba ko kadan,kuma ban isa in hanaki komaiba,nasani wannan hukuncin dakika yankemun Na cancanci wanda yafishi,zan miki fatan alkhairi idan har kika zab'i yin hakan amma wlhy duk halin dana Shiga kece sila,mutuwa zanyi ada na hakura dakene sabida wasu yan dalilai,yanzu kuwa bayan munyi aure mun rabu na fahimci kece rayuwata tsaf zan mutu idan nayi rashin ki my Elly,ina miki....se kuma tari ya sarqeshi janyo handkerchief yayi ya tare wanda atake ya soma aman jini,gigicewa Elham tayi ganin wannan tashin hankali tazo ta riqeshi " Yaa Abdul Sannu,meke faruwa da kaine? Aman jini na Shiga uku " ganin fa be kulata ba kuma gashi se aman yakeyi ya matukar tayar da hankalinta,a rikice taje part d'in momy ta sanar mata,a tare sukazo aka kwashe shi zuwa asibiti Elham se kuka takeyi wanda ita kanta bata san kona meye ba,tsoro takeji karta rasa yaa Abdul d'inta wannan aman jini idan yayi irin shi so biyu toko tabbas tsaf mutuwa zeyi dominnko ba abinda ze hana wa jininshi tsiyayewa ta tas.....abin mamakin kuwa shine yanda doctors suka tabbatar musu cewar lallai daga zuciyarshi har b'angaren ulcer lapiyarshi qalau,me martaba be yadda ba yasanya aka masa general check up nan ma Lapiyar shi qalau.....haka ya shafe kwana ki goma cur besan inda kanshi yake ba idan kuma yasoma aman jini baya tsayawa seya kusa amayar da yayayen hanjinshi,Elham ita kad'ai setaje d'akinta tayita kuka daba tasan dalilin shiba,Gashi me martaba yace aurenta ba fashi sora kwana ki 4 tunda ba biki za'ayiba daurin aurena kawai kuma Abdul bashi bane angon kazalika ba waliyinta bane da har za'ace ajira warkewarsa,a yanzu an dawo dashi gida sabida likitoci basu gane komai ba,inda ake zargin asiri aka masa,momy dukta ya mutse ba itaba ba Elham ba,a haka ranar d'aurin aure tazo ba amarshi haka aka gangama daurin auren......
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
18
Tun asuba ta farka taga baya nan,ga alama ma sallaci yaje ita d'inma sallah taje tayi,ta wuce kitchen kai tsaye ta d'aura musu egeg yam with beef paper soup, ba jimawa ta kammala ta hada masa coffee ita kuma ta had'a kayan tea nata ,a dining ta Jere komai ta wuce toilet kai tsaye tana idar wa ta fito ta shafe jikinta da mai tafara sanya sure spray follewed by body splash nata,ta bayanta ya rungumota ta na tsaye ajikin mirror d'in rufe idonta tayi jin saukar hannunshi saman breast nata, dukda a saman towel ne seda taji wani yarrrr,bata gane menene yake mata yawo a duk sanda ya rab'eta irin haka,jikinta ta janye da sauri ta sadda kanta k'asa,hannunta ya janyo ta dawo jikinshi ya manna mata hot kiss a wuya yace "Elham na,ina kika Shiga ina ta nemanki?" Murmushi tamasa
"Ina kitchen ne ina had'a breakfast"
"Dama yunwa ya addabeni oya saka kaya da sauri muje muyi break fast d'in" yaudai Hafsatu kasa koda motsi tayi bazata iya saka kaya a gabanshi ba,kallonta yayi ganin tayi tsaye ta sunkuyar dakai
"Bakiji ba nace ki shirya mu tafi ko" d'an ya tsanta ta saka a baki tace "Yaa Abdul ka bani wuri to mana,zan sameka a dining d'in" Murmushi yayi ya fice batare da yayi magana ba,yau ma sanda ta bashi abincin yaci sannan suka dawo parlor a saman cin yarta ya d'aura kanshi shi adole wai ga mara lapia, ita kuwa kunyarshi take ji matuka yanzu......
Tun da safe Hafsat ke fama da wani matsanan cin ciwon kai amma bata sanar masa ba da rana ma haka ta daure ta girka masu spaghetti da miyar Hanta kurun se ice tea, zuwa yamma kam Hafsat jiki ya tsananta domin kuwa kasa yin girki tayi,Shikuwa baya gidan yaje ya gaisa da mahaifanshi kasancewar jikinshi yayi k'wari.....sosai momy taji dad'in ganinshi agidan Ras da shi tace
"Mamana fa? Ina fatar tana lapia?" D'an Sosa kunne yayi yace "Tana nan lapia lau momy tace ma na gaidaki ai" Murmushi tayi "To Babana kadaiji tsoron Allah ka kula da yar mutane tsakanin ka da Allah dan Allah na rokeka karka kuskura ka wula kanta musu 'ya,sunmaka halacci sosai"
"Inshaa Allah momy zan kiyaye komai da kika ce zan kula da ita" al Barka ta zabga masa ya tashi ya fita......Koda ya dawo Elham bata parlor kuma yaje kitchen bata nan,kai tsaye bedroom nata wuce ya tarar ta k'udundune a bargo se rawar sanyi takeyi,da sauri ya Hau saman gadon ya d'an yaye duvet d'in
"Hafsat lapia dai meya sameki?" Kasa bashi ansa tayi kurin dai taci gaba da zubar da zafafan hawaye,dagota yayi ya d'aura ta saman cinyarshi yaji jikinta zafi rau "Hafsat plss Sanar dani meyake damunki haka,jikinki zafi fa sosai" dak'yar ta iya cewa "Kainane yakemun masifar ciwo sarawa yakeyi tamkar ze rab'e gida biyu" kan ya kama yaji zafi rau yace "subhanallah Elly tashi muje asibiti,bazan barki gida da zazzabi haka ba gaskia" kasa cewa dashi komai tayi da kanshi ya saka mata doguwar riga ya kinkimeta se asibiti, zazzab'in cizon sauro ne ke damunta aka mata aluurai aka bata magunguna suka dawo gida abinsu,salar isha ma dak'yar tayi tayita ya samu tasha tea kawai suka koma d'aki suka kwanta,janyota sosai ajikinshi ya rungumeta yanata rarrashi nta se hawaye kurun takeyi sabida ita kad'ai tasan yanda kanta ke masifar Sara mata,har bacci ya d'aukeshi ita bata rutsa ba,can Wuraren karfe ukun dare kukanta ya tasheshi,"Hafsat har yanzu kanne?" Cikin kuka tace "yaa Abdul dan Allah ka k'ananun kaina ciwo yakemun sosai wlhy,kuma ka matsamun k'afana suma suna mun nauyi saramun komai yakeyi" haka ya tashi yamata kamun kai yashiga mata tausa sosai har jikinta ya sauka atake ta fara had'a gumi se bacci me nauyi yayi awon gaba da ita,adu'a yashiga yi mata seda yaji ana kiran Sallar asuba sannan fa yaje yayi alwala a d'akin yayi sallah sannan yaje ya soya kwai da plantain ya hada ruwan zafi,koda ya dawo d'akin ta farka amma bata tashi ba,hawa saman gadon yayi ya tab'a jikinta yaji ba zafi "Sannu Hafsat Kindai ji sauqi ko?" Murmushi ta sakar masa tace
"Naji sauki sosai,amma daga kwance ina ganin jiri"
"So nake namiki wanka sekici breakfast naki" zaro ido tayi waje tace "Allah ni zanyi da kaina" cikeda shagwab'a tayi wannan furucin har tana shura k'afa,be tsaya wani gaddama da itaba ya fara cire mata kaya jikinta yanayin yanda take jujjuya jikinta ne yafi tafiya da imaninsa tsirara ya mata sannan ya d'aga ta cak ya nufi ban d'akin da ita,acikin bahon wankan ya tsunduma ta ya sab'e ta tatas,se sussune kanta takeyi,da kanshi ya Shafa mata mai ya saka mata kaya ya daga ta se dining,shine ya bata abincin sanda ta k'oshi sannan ya ci Nasa,bayan sun dawo parlor se tausa yake mata tun tana lumshe ido har bacci b'arawo ya saceta se farkawa tayi ta ganta a cikin faffad'an girjinshi me cike da gargasa suna baccin a tare,kasa motsi tayi karta tada shi ta koma ta kwanta.....
*Bayan sati Biyu*
Jikin hafsat ya tsananta matuka,tasha maganin malaria kala kala amma duk a banza ciwon kai ne ya sakata a gaba babu k'auk'utawa,ganin haka momy ta kaita private hospital, duk ta rame tayi bak'i sabida azabar ciwon kai ko idonta bata iya d'agawa gwajin farko suka gano tana d'auke da cikin sati uku!!!!!! Agaban momy suka zo sukace da Abdul"Congratulations sir,ur wife is 3 weeks pregnant, Baza kuga daidai ajikinta ba se ta wuce trimester d'inta so se hakuri zamu bata magungunan dazasu taima kawa ita kanta da cikin dake jikinta" mutuwar tsaye Abdul yayi dagashi had Elham d'in yayinda momy se murna takeyi 'yarta nada ciki,Zata samu jika dama gashi feenah haryau shiru!!!!!!! Kai tsaye gidansu yace a amai dasu ze kula da ita,hakan kuwa akayi can aka sau kesu, Elham har lokacin kuka takeyi magungunan da aka bata ma watsar wa tayi, tarasa Inda Zata saka rayuwarta taji sauqi,a take ma taji ta tsani kanta tama kasa tunanin daya dace tayi, a d'akinshi taje ta taraddashi a zaune tana kuka ta duqa kusa dashi tace
"Yaa Abdul wlhy summa tallahi ka yarda dani ba namijin daya tab'a sanina a 'ya mace,dan Allah Kayi hakuri" wata muguwar harara ya fara sakar mata sannan yace "A ruwa kika sha cikin dan kutmar uba? Wannan shine sakayyar soyayyar danake miki Hafsat? K'iyayyar daki kemun har takai matsayin da Zakije kiyi zina da aurena akanki? Wato sanda aka daura auren mu banida lapiya maza kikaje kina bi ko? Dukdan sabida bakya sona,cikinki sati uku ya nnuna cewar kinada igiyoyina akanki kikaje kina watsewarki da wanina,Allah ya isa ban yafe miki ba wlhy" kukan tane ya tsananta tace murya na rawa
"Wlhy na rantse maka yaa Abdul bansan komai ba game da wannan cikin,ban tab'a aikata zinaba tun ina gidanmu balanta na kuma da aurena" shaqo wuyanta yayi yace "Baki tab'a zinaba a ina kika samo wannan d'an shegen? Wlhy Sekin sanar mun waye ubansa,sabida kinsan bazan iya gayawa momy da duniya abinda Ki kayiba shine yasanya kika zabi tozartar dani har haka Elham?" Sakinta yayi ta fadi cikin d'acin rai ya soma kukan