Author : Billy Galadanchi Category : Romance
fuska tayi cikin d'aga murya yace "Hafsat wlhy I will slap u right away,karki mayar dani a bokin wasanki mana,maza bud'e bakinki Kici abinci" tsorata tayi da yana yinsa wannan ya sanya ta wangale bakin ya zura mata ci takeyi tamkar batason ci,Shikuwa se gimtse dariyar sa yakeyi karta raina shi sanda ta cinye tatas sannan ya zuba mata milk shake ta shanye shima rungumeta yayi sosai ya ce cikin sanyi "I'm so sorry blossom kin saka namiki tsawa" batace masa komaiba sabida bacci kanya ankare harta soma minshari abinta.....
*Baya wata biyar*
Hafsat kam dukta kumbura sakamakon watan haihuwarta daya tsaya,shi tausayi ma take bashi wlhy,ga abin ban tausayinma momy ta hana koda Innah a sanarwa tanada ciki sabida mata basa iya kama bakinsu kuma tana tsoron munafurcin siyasa itama tasan wahalar datasha,dako da adu'ar uwa ta samu, "Blossom me qaton ciki zamuyi selfie" Murmushi tamasa sannan tace " Kaga ni ka matsa zan zauna,wayene zeyi wani selfi yaronka na ciki ya k'ara mun k'aton hanci" Murmushi yayi ya d'aurata akan cinyarsa yace "kinga nifa banasan k'azafi ke d'innan sanda kina yarinya me qaton hanci ma ake ce dake,kurin da kika girmane kika soma packaging kina saka makeup Allah da bazaki ganuba"bata kula shiba ita dai yau sauyi takeji ajikinta na musamman kuma haka kawai ta tsinci kanta da kasa gaya masa,Murmushi yaku mayi
" blossom ya dai zakisha fresh milk ne?" Girgiza masa kai tayi alamar Noo da mamaki ya kalleta yace "Blossom yau kene kike gudun milk Kodai bakida lapiya ne?" Murmushin karfin hali ta qaqalo "Noo I just don't feel like taking it now" Murmushi yayi ya qura mata ido yana nazarinta ga mamakinsa gumi takeyi bece mata komai ba ya gyara mata zamanta ya rungumeta,can anjima seta cafko hannunshi ta riqe gam,saukar da ita yayi yace
"Blossom look @ me" Ba msu ta kalleshi "Are u sure ur alright?" K'walla ta soma yi"I'm not sure yaa Abdul " kamo hannunta yayi "inane yake miki ciwo den?"
"Nima ban sani ba,baya nane tamkar ana datsamun and dts all" bece komai ba ya d'aga ta se asibiti.... Allah Sarki k'uruciya Ashe labor take domin kuwa basufi 30 mnt da isaba ta sunkuco rangadeden yaro sak ubanshi,Abdul dukya gama rudewa,lokaci d'aya ya dauki san duniya ya daurawa yaronnan,batada wani problem yasanya aka sallamesu, waya yayi ya sanarwa momy aikam kan kace meye Wannan gidan sarauta ya d'auka cewar Elham ta haihu,kowa se murna yake Haj Habeeba dakanta ta roqa me martaba a sakawa jinjirin sunan yaronta daya rasu Ibrahim tun yana qarami,hakan kuwa akayi yaro yaci suna Ibrahim ana kiranshi da sultan,dama momy ta turawa Hafsat kanwarta itane ta kula da ita har yaron yayi watanni uku,sannan suka shirya zuwa domin kawowa me martaba da Fulani jikinsu su ganshi.....
*Nigeria*
Ba k'aramin so Abdul akewa sultan ba duk inda zashi tare suke zuwa koma ina ne,ga yaro qarami amma ya shaida ubansa kowa nasan sultan,wani yanmaci lokacin Satinsu biyu da zuwa k'asar Abdul nawa sultan wasa a parlor haryayi bacci anan ya shinfideshi ya Shiga domin watsa ruwa Ita kuwa tana kitchen.......koda Abdul yadawo bega sultan ba kwallawa Elham kira yayi tazo "Blossom kaddai kitchen kika kaimun sultan kinsanfa akwai zafin gas acan" hannu tasa tad'an shafi fuskarta sannan ta yamutsa fuskar "Yana d'akin ka daiko ni ban dauke shi ba" wasa farin girki domin kuwa kaf sun duba ba sultan ba labarinshi ba k'aramar hauka cewa Abdul yayi ba me gadi ya shaqa akan wayaga yashigo yace dashi "wata motace ta shigo irin waccen shudiyar ta Haj,ina ga abokankane domin mazane,ganin wanin yayi ciki ya sanya nashiga ban d'aki koda na fito harsun tafiyarsu" nan take Abdul ya soma kuka bashiba ba Elham ba haka ya kira momy duk aka taru aka Shiga damuwa.
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
              24
Zaman dirshan Abdul yayi ya qurawa Hafsat ido ganin ba'a ga sultan ba kwana uku ya sanya ko magana batayi kuma batacin abinci,shi d'in ma ba abincin yake ciba amma dai yafita dauriya kodan kasantuwar sa namijine oho,kyakyawan murmushin k'arfin hali ya sakar mata sannan yace "Blossom na plss kimun magana mana,nace Meyene kike sn ci na girka miki da kaina?" K'ur tamasa da ido kawai batace kanzil ba,hannu ya sanya ya tura hularsa bayan kansa ya shafi sumarsa
"Innalilahi wa inna ilaihiraji'un" itace Kalmar daya keta nanata,tashi yayi yabar wurin batare daya qara cewa komai ba,d'akinshi ya Shiga ya rusa uban kuka tamkar wani k'aramin yaro abubuwan sun had'e masa ga rashin sanin halin da sultan Hake ciki,gashi kuma Elham ko magana batayi bata kuma cin abinci,sanda yayi me isarsa sannan yazo ya dagata cak zuwa d'akin barcinsu,kwantar da ita yayi ya daura kanta saman hannunshi cikeda rarrashi yafara magana
"Hafsat dan Allah ki sassauta wa kanki yau kwanaki nawa bakyacin abinci kuma bakyawa kowa magana,dan Allah na rokeki ki nutsu kiyita adua,wlhy kina k'aramun damuwa ne mara misaltuwa,idan dai baso kike na haukace ba dan Allah Kici wani abin" kuka kawai ta saka ta rungumeshi k'ank'ameshi sosai tayi
"Yaa Abdul Nashiga ukuna har yanzu fa ba koda labarin sultan,wlhy zautar dani zasuyi idan ba'a nemomin sultan ba mutuwa kawai zanyi,me wannan d'an ta tsitsin yaron ya aikata wa mutane,yaa Abdul dan Allah ka taimaka ka nemonin sultan d'ina" k'ara matseta yayi ajikinshi yana jin zuciyar na masa tafarfasa lokaci d'aya kuma yanajin tamkar zuciyarsa Zata Faso k'irjinsa ta fito har cikin b'argonshi yakejin tausayin ta matuk'a wanan damuwar da hafsa ke ciki na cikin abin da ke qara harzuqa Abdul,rarrashinta yashigayi har bacci ya d'auketa"
Wuraren k'arfe d'ayan dare me gadin gidan yaji motsi ana k'ok'arin bud'e k'ofar gate d'in a hankali yazo ya wuce jikin k'ofar gidan ya tsaya wayanshi ya janyo yakira Abdul,ya sanar masa,betashi Elham ba amma sarai taji sanda yake wayar kasancewar dukkanin su bawai baccin sukeba sedai dayake bacci b'arawo ne yakan sacesu wani lokacin suna tsaye a lab'e ya samu nasarar bud'e k'aramar k'ofar gate d'in da buhu D'auke a hannun shi ya ajiye ze juya Abdul yace me gadin ya bishi da gudu me gadin ya bi bayanshi kan yakai k'ofar ya rafka masa uwar sandarsa,take ya fad'i wurin a sume,Shikuwa Abdul da sauri wurin buhun yayi wari ne yabugi hancinsa tunkan ya qarasa bud'e Buhun daurewa yayi ya haska fitilar wayarsa ya qarasa bud'e Buhun "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" itace kalmar dayake ta nanata wa yayinda yayi mutuwar tsaye warin ma ya denaji sabida ganin gawar sultan harta fara zagwanyewa,Elham da tunda yafito take binsa isowa tayi wurin batare da sanin saba,ganin sultan a haka Abdul a tsaye ya sanya ta ture Abdul da hanzari ta wawusheshi,mamakine ya kamata ganin fatarshi ta sab'ule ga uban wari alamomi sun nuna yafi kwana biyu da mutuwa, baka ma gane shine seka kula da kyau,hauka cewa tayi ta soma sambatu kankace meye wannan tafita hayyacinta dak'yar Abdul ya riqeta yana bata baki,kallon shi tayi acikin hasken fitilar wayarshi a daidai lokacinda me gadin ya dawo wurin da gudunshi
"Kaga yaa Abdul kalli sultan na,sun kashe shi fa kalli mutuwar wulakanci,kalli yana warin gawa kalli yanda fatar jikinshi ya zagwanyewa daga jikinshi, anya kasan wahalar da yaronnan yake sha kuwa?? Wlhy baka sani ba cewa akayi damu gawa zafi takeji idan ana mata wanka ma,kalli sultan fatar shi duk a sale kalli idonshi,wlhy zafi yakeji yaa Abdul ka tasheshi mana,sudais na be mutuba wlhy" jijiigata yayi yace "kiyi hakuri Elham dan Allah ki nutsu mana,kiyi hakuri kinji" batace komai ba ta k'ura masa ido,se kuma ta kwashe da dariya cikeda hauka tace
"Mesa ba zaka tasheniba ina bacci, yaya zaka barni ina bacci ina wannan mugun mafarkin, dan Allah yaa Abdul muje ciki mana" ganin tana wannan abin ya tsoratar dashi matuk'a....miqewa yayi shima ya kamo hannunta "Elham na plss mana me haka?? Ki nutsu kiji ni da kyau haquri zakiyi kinji k'addara ta riga fata an rigada an cucemu se hakuri" dukan k'irjinshi tayi "so kake kace dani wai ba bacci nake yiba,da gaske kake wannan sultan nane wannan,kalli fa da kyau wlhy wannan kalarshi tsanwa ne ni kuwa sultan na fari ne qal" kurin seta sake saka kuka,a haka ta sulale a wurin bata koda motsi.....me gadin ya kalla yace "waye wancan"
"Wlhy yallab'ai sale ne?" Da mamaki ya kalleshi yace "wane salen kake magana?"
"Sale dai sale wanda ka sani yallab'ai" d'aga Elham yayi zuwa mota yazo ya kai gawar sultan ma yana matsar kwalla,yace da me gadin ya fara d'aure sale sannan ya watsa masa ruwa,zashi asibiti ya Turo police anan d'in........
Sosai Abdul ya girgiza jin cewar kan Elham ya tab'u saka makon wannan abin daya faru da ita,sosai abinda ta gani ya girgiza ta Baza suce bazata warke ba amma fa sam Baza suce ga tsawon lokacin dazata d'auka ahaka ba,sedai abinda Allah yayi,kuka Abdul ya sakawa momy sosai sam zuciyarsa bazata iya d'aukar wannan abin ba,wanda ya kawo gawar kuwa anyi anyi dashi Amma sam yaqi magana....
A firgice Elham ta farka tana kurma uban ihu tana sambatu "Wai cewa suke dani Sultan ya mutu ni sam sultan d'ina be mukuba yaa Abdul me shine shaida agabanshi nabashi mama yasha,se kuma tasaka kuka tasoma kokarin kunce d'aurin da aka mata, sosai ta baiwa Abdul dake kusa da ita tausayi yasoma sharar k'wallah " Wlhy sun kasheshi kisan wulakanci fa ko binnewa beci albarkacin suka masa ba,gaskia nima sena kashesu,kuma bazan binne suba sesun dawo k'asusuwa sena mayarda su...sekuma ta kwashe da dariya...Abdul barin d'akin kurun yayi cikin tsananin k'unan rai ilahirin mutanen dake d'akin kuka sukeyi na matukar tausayawa Elham.
Mom Nu'aiym.
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
              25
Zaman nutsuwa sukayi a gaban me martaba suna sauraren abinda zece yayinda yayi mintuna biyar suna saurarensa batare da yayi magana ba se can yayi gyaran murya xanna ya gyara zaman alkyabbar sa yace cikin nutsuwa
"Abubuwa da dama sun faru a wannan masarautar,kuma sanin kanku ne wayannan abubuwan ba masu dad'i bane,dukda yake sace sultan da akayi bawai acikin nan Gidan aka shigo aka sace shiba amma sarai ganin sale da gawar jaririn ya sanya mun tabbatar cewar daga wannan masautar ne,tunda kuwa sale shekararshi kusan talatin da biyar koma fiye da haka anan gidan, koda ya zo nan shekaru nsa basu wuce sha biyar ba har tsufa yazo masa gashi muna tare,yanzu wannan d'anyen aikin ya janyowa mahaifiyar sultan kamuwa da cutar tab'in hankali,tofa ku sani na rantse da Allah mabuwayi duk wanda na kama dasa hannun shi aciki ko waye shi saina hukuntar dashi,sale na nan na saka an kawo mun shi a masarautar nan da kaina zan bincikeshi yana nan a tsohon prison na masu laifi a masarauta gobe da yardar Allah zan bashi azaba mafi muni da Zata saka yayi magana koda beso ba, Mamana kuwa idan visa dinsu ya zama ready zuwa wani watan zan turata India adubamun k'walwarta" jin yayi shiru Haj habiba tace "yallab'ai har yanzu munkasa gane dalilin kirannan da aka mana,bansaniba ko satar da kisan jinjirin ya shafi nida iya laina ne?" Wata mahaukaci yar tsawa ya daka mata wacce a lokaci d'aya ta razanar da ita matuk'a bama itaba d'auka cin mutanen dake wurin
"Wlhy Habeebah zan nuna miki isa da k'arfin mulkin dana keda shi,idan baki saniba na sanar miki cike nake dake FAM kuma wlhy bazanci b'ata lokaciba wurin ganar dake kuskurenki kinji na fad'a miki,maza tashi ku bani wuri dukkanku" jiji a sab'ule dukkansu suka mik'e se adu'o i sukeyi na tonuwar asirin duk wanda ya aikata wannan mummunan aikin..... Wuraren k'arfe biyu na dare me martaba har lokacin be runtsaba yana nan yana zagayen gidan shida fadawanshi guda biyu, B'acin rai sam baya barinshi bacci tun faruwar wannan mummunan abin,muryar dayaji ne ya sanya ga dakatar dasu da hannu tare da nuni da hannu akan cewar su dakata
"Kaga burshi Me martaba fa na sanar maka da gaske yakeyi wannan karon,so yake ya dauko mana rigima,sabida haka wannan babbar damace agaremu dawowar da akayi da sale gida prison na nan gidan,zuwa zakayi ka bashi zab'i Kodai na mallaka masa dukiya me yawa ya koma inda ba wanda ya sanshi kokuma ka kasheshi" kallonta burshi yayi yace " Haj nifa nasan halin saleh,yanda yasha burin adama dashi idan an samu nasarar kashe Yarima faruk yahau baze tab'a barin wannan masarautar ba,ki bani dama kurun na kasheshi" shiru yad'an ratsa wurin kan tace
"Burshi wlhy kaga nifa harka da kisan kai ba santa nake ba,sanin kanka ne ko sultan d'innan bawai da gangan na kashe shiba hasalima dan kanshi ya mutu nida bansan a kashe kowa,ko yayyun Yarima ai gidan marayu na kaisu bana san harka da kisa karka kasheshi adai fitar dashi daga garin kota karfin tuwo ne" Sosa sumar sa yayi "Barin je in sumar da masu gadin in jashi kawai mubar nan" baya da baya me martaba ya koma seda burshi yayi gaba sannan suma sukabi bayanshi acan suna kallonshi ya wurga wata farar Leda yaja da baya had'e da toshe hancinsa,daya daga cikin fadawan dake tare da Sarki ne ya koma ya tashi wasu bardawa shi kuwa me martaba da daya suka lab'e wani wuri,shida sale suka fito sad'ad'a suka wuce Sarki ma suka bi bayanshi suna zuwa gate se gani sukayi fadawa sun zagayesu take aka kama Shegu......
Koda momy taji komai a bakin me martaba gigicewa tayi ta saka kuka dak'yar ya riqeta akan kartaje wurin habeeba har wannan lokacin ita habeeban batasan an damqe su sale ba kuma bata masan me martaba Yaji komai ba police kawai ya sanya akawo su zasu mata tambayoyi dole se ta fad'i inda takai yaran farko Wato yayyun Abdul sannan tayi bayanin zancen sultan menene laifinsa na sace shi kuma menene laifinsa na kasheshin da tayi......."
Hannun Elham acikin na Abdul ya qurawa fuskarta ido data kumbura tayi ja jajir se sheqi takeyi na wahala bacci takeyi sakamakon allurar baccin da aka mata sabida ta samu nutsuwa tamkar matacciya lokaci zuwa lokaci takan kwab'e fuskarta tamkar me shirin yin kuka kota yamutsa fuskar wanda dana hakan d'abi'ar datane,tausayinta sosai yakeji se adu'a yake ta tofa mata haka yakeyi daman dare da rana bashida aikinyi se zaman mata adu'a yana sharar k'walla,yau kusan wata d'aya kenan da faruwar wannan al'amarin kuma har yanzu bata sauya zaniba, Haj Habeeba dai a binciken da akayi dukkanin yayyun Abdul datakai orphanage susu biyu sun rayu acan sedai gabaki d'ayansu sun bar orphanage d'in sunyi aure da yan uwansu na wurin sun fara aiki, ba kad'an ba momy tayi kuka ace kana d'an Sarki ka b'uge da rayuwar gidan marayu tsabar san kai irinna Habeeba da rashin imani,abin bak'in cikimma wai D'ayan me suna jabir Allah ya masa rasuwa yabar matarsa da yaronsu d'aya,se kabir ne aka samu wanda yayiwa Habeeba Allah ya isa cikin buhu buhu........A hankali ta bud'e idonta ta sau kesu akanshi Koda suke a lumshe,a wahalce tace "Yaa Abdul yunwa nakeji sosai ka bani wani abin,se inajin jikina tamkar wata mara lapiya" da sauri ya miqe jin tayi magana irinta masu hankali da sauri yazo ya d'agata yace "me kikeso Kici blossom?" Narkewa tayi ajikinshi sannan tasaka masa kuka "wai yaa Abdul da gaske ba mafarki nake ba sultan naga gawarshi jiya??" Qara qanqameta yayi yace yana kukan shima "Blossom kiyi hakuri ba mafarki kikeba,haka Allah ya tsara abinshi" wani kukan ta kuma fashewa dashi me ban tausayi...
*Dan Allah Kuyi hakuri da wannan yan kwana kinnan bana samun zama*
Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*
Billy Galadanchi
Haske writer's Asso💡
Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).
              26
Sosai me martaba yayi murnar samun Lapiyar hafsa,matsala d'aya ne ta kasa kwantar da hankalinta abincinma taqi ci yanzu tunda aka tabbatar mata da mutuwar sultan kuma a hanyar data ganshi take kuka,me martaba da kanshi ya shirya yaje asibitin domin har wannan lokacin asibitin basu sallameta sunce se sunga yanda jikinta ya qarayi,a saman kujerar da masu zuwa duba marasa lapiya ke zama anan me martaba ya zauna ya fuskanci Hafsat sosai ya tattare nutsuwar sa akanta yace bayan yayi gyaran murya
"Mamana yaya Lapiyar jikinki? Ina fatar kin samu sauqi?" Sunkuyar da kanta tayi qasa cikeda kunya sannan tana hawayen data kasa tsaidasu tace
"Naji sauqi ranka ya dade jiki Alhamdulillah" sake yin gyaran murya yayi yace "Na sanar miki karna kumajin kin kirani da wani sunan bayan daddy,Aini mahaifinki ne" murmushin k'arfin hali tayi cikin hawayenta tace murya na rawa "To daddy" shiru ya d'an ratsa d'akin na wani lokaci kan yace "Mamana ko kinsan cewa Allah mahaliccin dukkan komai shine da kanshi yake rayawa kuma shine yake kashewa alokacin dayaso kuma yayi muradi,kamar yanda yake Talauta wa a sanda yazo yakuma azurta a sanda yayi muradi,kana ya fitar da rayayye a cikin matacce kuma ya fitar da matacce a cikin rayayye?? Shin kokinsa ubangiji shiya keda iko akan dukkan kuma shine qadirin ala manyasha'u,kokina labarin cewar agaban idona akayiwa mahaifina yankan rago?? Shin Hafsatu bakida labarin cewar acikin k'addarori na rayuwa taki k'addarar ta fad'o ne acikin mafi sauqin d'auka?? Labari ya riskeni cewar tunda Allah ya baki Lapiyar ki bakyacin abinci bakida aiki se kuka,Anya Mamana kinwa adalci kuwa? Anya Hafsatu kin godewa Allah akan manya manyan ni'imominsa akanki? Ashe ba wani babbar ni'ima bane Allah ya baki na samun lapia ba sanda kika Zata ba? Ashe ba babbar ni'ima bane agareki kin tashi kiga dukkanin Dangin ki suna farin ciki da samun Lapiyar ki?? Shin ko kinsan cewar mutane da dama dasuka samu irin matsalar ki a rayuwa suna nan suna yawo akan titi,bola da juji Nanne makwancinsu, abincin su a bola ruwan shansu a bola