RUBUTACCEN AL'AMARI by AYSHA ALI GARKUWA

Author :  AYSHA ALI GARKUWA Category :  Romance

Chapter   6 / 17

15K to 18K   out of 49.6K words

gidan a rufe."

"OK gani nan zuwa yanzu ku jirani kad'an bari in k'arisa aikin dan tare zamu koma cikin potiskum d'in."

"Toh" yace sannan suka koma cikin mota suka zauna.

Jimawa k'adan Hamma Umar d'in ya iso ya bud'e musu gidan nashi suka shiga ,
a take su Abdul suka canza labulayen gidan kab sannan suka kimatsa komai suka shimfid'e carpet masu lau shi da taushi gaba d'aya gidan ya d'auki k'amshin da shek'i ga k'amshin sabon penti ga k'amshin sabbin kayan d'akin ga k'amshin kasan cewar Hamma Umar ma abocin tsabta da k'amshin ne komai yayi ras sai shek'i da k'amshin yake zubawa,
shi kam Hamma Umar yana tunanin me Abba yake shirin yi tunda yasan har yau Ummul bata san da zancen ba haka dai ya bar abin a ranshi tunda shi bashi da yawan magana,
su Abdul na gamawa suka d'auki hanya tare da Hmma Umar..


Suna zuwa gida sallan jumma'a suka tafi,
Bayan an taso masallacin ne Dr Umar ya wuce chemist d'in shi,
Abba kuwa da sauran gida suka dawo,
Itako Ummul zuwa yanzu ciwon cikin ta ya fara tsananta,
tana zaune a parlour Nenne tana d'an juya kai Aliyu ya shigo parlour kallon ta yayi cikin kula yace.
"Sannu Anty Ummul ko inje in kira Hamma Umar ne?."
a d'an wahalce ta harareshi tace.
"Barni in mutun."
Dariyan tsokana yayi sannan yace.
"Kije Abba na kiran ki."

Da sauri ta d'an zaro ido gami da dafe k'irji cikin tsoro tace.
"Ni? da gaske Abba na kirana?."

"Ehh wallahi da gaske ne,
toh menene dan Abba ya kiraki ji yadda kike zaro ido."

"A a wallahi Aliyu Abba baya kirana ko batun makaran ta ne Nenne yake gayawa ta gaya min,
ni dai naji tsoron kiran nan nashi."

"Toh koma dai menene kije maji daga baya."
cewar Aliyu kenan.

A bak'in kofar parlour Abban ta tsaya tare da yin sallama ,
Daddy ne ya amsa tare da cewa .
"Ummul na shigo."

Kai ta sunkuyar cikin jin tsoro ta shiga a hankali can gefen Daddy ta zauna yayin da zuciyarta ke luguje,
a hankali ta gaida su,
sannan tace.
"Abba Aliyu yace kana kirana."

Kallon ta yayi cikin k'aunar y'ar tashi a hankali yace.
'"Ehh ina kiran ki."

Sai kuma duk sukayi shiru,
can dai Abba yayi gyaran murya tare da cewa.
"Ummul ni wayene a gareki?."
Kai ta d'ago cikin k'arin firgici a hankali tace.
"Mahaifina."
Kallon ta ya kumayi sannan yace.
"A duniya bayan mahaifi yarki akwai wanda ya fini sonki?."

Baki na rawa tace.
"A,a babu."

"Na tabbatar kina da sanin cewa shariya ta bani damar zab'a mik'a majin aure ko."

"Ehh."
ta bashi amsa hawaye na bin fuskarta.

Shi kuwa gyaran murya yayi sannan yace .
"Abin da ban saniba ko zaki iya min biyeyya kan zab'in da nayi miki."

Zuwa yanzu kam ta k'asa magana sai kai take gyad'a wa tana wasa da yatsun ta.

Cikin bada umurni Abba yace.
" toh nayi miki miji,
kiyi biyeyya a kanshi ko bana raye shine mijin ki, mahaifiyata da d'an uwana sune shaida,
na bada auren ki ga d'an uwanki Umar Faruoq."

Kalaman Abba sun maida Ummul kurma sun sata wani irin razani da firgici gaba d'aya jikin ta rawa yakeyi bugun zuciyar ta kuma kamar zai b'allo ya fito woje kunya yayi mata wani irin nauyi cikin rawan baki tace.
"Hamma Umar Faruoq?."

Kai Abba ya gyad'a mata tare da cewa.
"Ehh shi d'in dai."

Hannu tasa cikin tsoro ta kama kanta ta bud'e baki zatayi magana Abba ya dakatar da ita cikin tsuke fuska yace.
"Tashi ki tafi bana buk'atar jin komai daga gareni ba shawara bace umurni nane wannan."

Tanaji Abba na cewa tashi Amman ta k'asa ko d'aga yatsarta,
sai da taji ya zuba mata tsawa,
cikin firgici ta mik'e ta fita ,
tana fita kai tsaye part d'in Nenne ta ta nufa ,
tana zuwa a parlour ta samu su Ya Usman su ya Adam ya Sadik da Aliyu kai tsaye cikin bedroom ta shige,
Usman na binta da kallon ganin yadda take a firgice.

Tana zuwa ta zauna gefen Nenne dake kan sallaya cikin wani irin yanayin ta kifa kanta kan k'afafun Nenne cikin cushewar sauti ta saki wani irin galabaicen kuka mai cike da tausayi kuka takeyi mai tsuma zuciyar mai sauraro kukan take da sauti,
Nenne kam tana ganin haka tasan me yasa ta kukan gaba d'aya sai zuciyarta ta cika da tausayawa y'ar tata,
su Ya Usman kuma suna jin kukan da takeyi cikin sauri suka shigo d'akin ,
cikin tarin tausayawa Usman ya zauna gefen ta baki na rawa yace.
"Ummul meke faruwa? meya sameki? meke miki ciwon?."

Ba amsa sai kukan da takeyi,
Nenne kuwa tsuke fuska tayi cikin fad'a tace.
"Ke ni tashi a kaina tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina kukan banza bazan kiyi magana ba."

Cikin kuka mai cushe zuciya ta d'ago kanta baki na rawa tace.
"Wayyo Allah wayyo Nenne kiji abin da Abba yace min Nenne wallahi ina son Mustapha ina sonshi yana sona dan Allah Nenne ki bawa Abba hak'uri wallahi ina son Mustapha."

Wani irin dogon tsaki ya Adam yaja cikin buga mata tsawa yace.
"Ai Mustapha yafi miki kowa a duniya tunda har kike kuka da umurnin Abban mu,
ni wallahi kin saman na k'ara tsanar sa."

Juyowa tayi cikin kuka tace.
"Ya Adam kasan da waye Abba zai had'a ni?".
A hatsala yace.
" Na sani mana kuma yafi Mustapha da komai."

Cikin kad'uwa da bugawar zuciya Ya Usman ya kalleta tare da cewa.
"Waye za'a had'a ki dashi?."

Kuka ta saki tare da cewa.
"Ya Usman waifa Abba da Hamma Umar zai had'a ni aure."

Ido Usman ya zaro cikin wani irin yanayin yayi wani irin.....


By
*GARKUWAR FULANI*
妫e啯鎲#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾�

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 9闁愁煉鎷�

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾虫#鍐ㄧ3妫e啫纾�



*Alhamdulillah ala kulli halin nayi tafiya lfy na dawo lfy yanzu zanci gaba da typing insha Allah har k'arshe*



```NI na jinjina muku y'an KADUNA bamai rabani daku jama'ar KANO kui hak'uri ga shafinku ya iso mun jinjina muku reedars damu writers daku d'ayane bamai rabu daku sai Allah kui hak'uri ga pagenku ya fito kanawa sunce mini GARKUWAR a baya kinyi wani kuskure duk novels da kinkayi a social media dad'in su yayi ta kewaya nahiya sun shiga sak'ok'in Nigeria shin meyasa kika ware hausawa bakya yin novels da su sai FULANI? Hausawa ne sukayi min wannan tabbayar shaidar suna k'aunata gaba d'aya, NIKO NACE MUSU , dole naje duk inda rebo yake dan bani Rena masoya na kuma ban raina ranar da novel yayi mini ta sanadi an sannu garuruwa INA alfahari da Gombe Taraba ADAMAWA YOLA gida nake tun fari su sukayi mini GARKUWA妫e啯顫� tunda nazo a cikin y'ay'an Adam duk ajizi an sanshi da kuskure kuyi hak'uri novelna na gaba da hausawa yana nan tafe, dan ni garin mosoya nisa bai mini da na fad'a kuma yanzu ina tuni Allah ya kaddara in zamto Zuma dana fito ai tayi mini sansani, yau hak'uri zan bawa hausawa dan sunfi so na tsaya tamkar gini, RABBI nufeni silar novel da zanyi mutan k'asarmu su zauna lfy,
Forko mutan KANO zanai kira wanda fagen nema basa jira maza da mata Manya da k'ank'ana a gsky na sansu da Hattara sunce nazo naga yadda abin yake sannan na tabbaya ni sukayi jira na mori so da k'aunar da suke mini sannan sunce na dage fannin k'irk'ira妫e喚妾#鍐╊潰Kanawa wannan shafi naku ne```





*Y*ayi mata wani irin kallo cikin tarin mamaki da jin zafi a ranshi murya can k'asa yace.
"Ummul duk wannan kukan kina yinshi ne dan an had'a auren ki da Hamma Umar?
Ummul duk wannan zafi da tarin bak'in ciki dan an shigar da Hamma na cikin rayuwar ki ne kike haka?."
Sai kuma yayi shiru tare da dafe k'ahon zuciyarshi a hankali cikin jin jiri ya koma baya kad'an ya zauna ido ya rumtse da k'arfi sannan ya jingina da jikin gini,
numfashi ya rink'a furzarwa da sauri-sauri yana mai cushewar tunani.

Ita kuwa Ummul cikin kuka tace.
"Na tsaneshi na tsani Hamma Umar bana sonshi duniya da lahira ko fuskar sa bana k'aunar gani,
Hamma Umar ba abinda yake jazamin a rayuwa sai bak'in ciki ya zame min bak'in jakada a rayuwa ta."

K'ara ta saki da k'arfi tare da dafe fuskar ta jin wani irin zazzafan mari da ya Sadik ya zuba mata cikin huci da zafin rai ya nunata da yatsa murya a hargitse yace.
"Ki kula kisan furucin da zakiyi ki san waye Hamma Umar wallahi a kanshi zamu iya miki komai,
shi Mustapha ko tare kuka fito duniya bake ba shi."

Kife kai Ummul tayi a bakin gado ta saki wani irin kuka mai cike da zafi a zuciya kuka mai cushe zuciya gaba d'aya jikin ta sai b'ari yake lokaci d'aya ciwon mararta da ciki da k'ugunta suka taso a tare,
kuka take cikin tausayawa kanta da Mustapha.

Gaba d'aya sukuwa shiru su kayi cikin jin sautin kukan ta, ya Usman ne yake tunani a ranshi
tabbas Ummul akwai kuna a ranta akwai zafi da ciwon rabuwa da masoyi,
sannan ga cushen mak'iyi da akayi mata,
har cikin ranshi yake tausayawa mata,
a sashin zuciyar shi kuwa,
yana jin zafi da bak'in ciki da takaici yadda Ummul ta tsani d'an uwanshi mafi soyuwa a gareshi.

Nenne kuwa itama shiru tayi tana jin sautin kukan y'ar tata har cikin ranta take tausayawa mata,
amman a zahiri tafi jin dad'in auren Ummul da Umar akan ace da Mustapha dan ita Nenne tana son Umar da Usman tamkar yayanta na cikinta bata son abinda zai b'atawa Usman rai da yanayin ciwon sa bata k'aunar taga damuwa a fuskar Umar dan shi jigone mai burin samawa kowa farin ciki shi baya shiga sabgar daba tasaba,
shi ba a gane matsalar sa dan ba fad'a zaiyi ba duk halin da yake ciki dan shi mutun ne mai kunya da zurfin ciki da kara da kawaici shiyasa bata son abinda zai cutar da Hamma Umar d'in,
haka yasa take ji a ranta dole zata iya juya d'iyarta tayi mishi biyeyya.

Ya Adam kuwa wata iriyar kunyace ta rufeshi ganin yadda a gaban Usman Ummul ke kuka kamar ranta zai fita dan an hada ta Aure da Hamma Umar,
kunya yake ji ya Ummul zata nuna bata son d'an uwan shi alhalin shi a koda yaushe cikin nuna mata kulawa da gata yake.

Ya Sadik har cikin ranshi yake jin tsanar Mustapha tunda a kan Mustapha ne Ummul take furta kalaman k'iyeyyar Hamma Umar d'in nasu haka kuma yake jin zai iya yiwa Ummul ko wanne hukuncin matuk'ar zatayi wa Hamma Umar d'in rashin da'a.

Auta Aliyu kuwa abokin fad'in Ummul kuma kaninta mai tausayawa mata ganin yadda take kuka ba wanda yake lallashin ta gashi dama ya Usman ne mai kareta kuma yau shima fad'an ya shafeshi,
kawai shima Aliyu sai hawaye yake zubda wa a hankali ya matso kusa da Ummul d'in murya na rawa yace.
"Ayyah Anty Ummul kiyi hak'uri kibar yin kukan haka."

Cikin tausayawa kanta da kanta ta fad'a jikin Aliyu kanta ta kife kan cinyar shi ta saki kuka mai cushewar sauti,
shima Aliyu sai hawaye car-car yana jin tausayin ta a ranshi,
cikin kuka tace.
"Aliyu yau kowa baya sona duk an tsanani sabida Hamma Umar ! sannan an rabani da Mustapha sabida Hamma Umar ! Auta kalli yau ya Usman ma fushi yake yi dani sabida Hamma Umar! kalli ya Adam da ya Sadik ji suke kamar su kashe ni sabida Hamma Umar! Abban mu da Nenne duk basa sona a yau sabida Hamma Umar!
Aliyu ba wanda ya tausayawa min sai kai."
sai kuma ta saki wani sabon kuka.

Ya Adam ne yayi kanta cikin nunata da yatsa murya a fad'ace yace.
"Kifa dena cika mana kunne da kuka wallahi in ba hakaba zan tattakaki."

Ya Sadik kuwa tsaki yaja cikin zuciya yace.
"Kiyi duk yadda kika ga dama ya rege naki tunda bakya ganin alkhairi zab'in da iyayen mu suka yi miki,
Mustapha ne dai bazamu bashi auren kiba."

Daga nan suka fice ita kuwa Nenne tsaki taja ta fice ta shiga kitchen ta kama aikin ta,
Aliyu kuwa tafin hannushi yasa yana gogewa Ummul d'in k'olloh dake bin fuskar ta,
shi kuwa ya Usman zama yayi kusa da Ummul d'in daketa murk'ususu tana ta cike lips d'in ta zufa na keto mata tako ina sai kukan da takeyi cikin raunin da wahala.

A hankali ya kalleta cikin sanyi ya d'an yi murmushi yace.
"Ummul khairi banyi fushi da keba ,
ki sani ke tawace kamar yadda Hamma Umar yake nawa ni Usman Ku duk nawa ne ba Wanda zank'i a cikin Ku kiyi hak'uri k'anwata kiyiwa kanki da Hamma na addu'a Allah ya muku zab'in abinda yafi zamewa alkhairi a gare Ku."

Kai kawai ta juya tana mai azabtuwa da ciwon cikin da tarin damuwa.

Shi kuwa Usman haka yayi ta bata baki ,
Amman ina Ummul bata ma san yana yiba,
ganin haka yasa. Usman ya fita kai tsaye parlour Hajjajo yaje,
cikin sanyi yayi mata maganar abinda ke faruwa,
kai ta d'an jinjina cikin k'arfin guiwa ta kalli Usman tace.
"Ku kanta na d'an wani lokacin ne zatayi ta bari ta saduda ta zauna da Umaru cikin aminci,
aini naji kukan nata zuwa ne bazan yiba,
dan inta ga ana damuwa da kukan nata dayin lallashin ta toh bazata bariba ku fita sha'anin ta."

Ido ya tsurawa Hajjajo cikin sanyi yace.
"Hajjajo indai Hamma Umar na son wannan had'in toh ina farin ciki da auren nan domain farin ciki B'iyayen na shine nawa."

Haka suka d'an tattauna kan zancen.

Itako Ummul tunda suka waste suka barta take kuka kamar zata had'iyi zuciya ta mutu,
Aliyu yayi ta lallashin ta amman ina dan abin ya had'e mata ga ciwon ga bak'in ciki,
haka Aliyu sai ya fito yaje kitchen ya dawo gunta yana ta sintiri ya kasa zama.

Haka har dere yayi Nenne kam ko ta kanta bata kuma biba dan inta tsaya kusa da ita tana jin tausayin d'iyar tata,
ta dai sa abinci Aliyu ya kawo mata,
ita kuwa Ummul yau abincin bazai ciwuba.

9:00 pm har yanzu Ummul tana kuka ne hannun ta dafe da mararta da k'ugunta akaro na biyu Aliyu ya shigo cikin tausayawa yace.
"Ummul naje na gayawa Nenne baki da lafiya Abba kuma yace kije gun Hamma Umar ya duba ki."

Kai ta kuma kifewa kan kago ta ci gaba da kukan da sautin shi baya fita dan muryar ta ta dashe,
Ya Adam ne dake zaune a parlour Nenne jin Abinda Aliyu ya fad'a yasa shi mik'e wa ya shigo bedroom d'in cikin tsuke fuska da bada umurni yace.
"Ke mike kije Hamma Umar d'in ya duba baki,
kin zauna kin wuni kuka shin kukan zai miki magani ne?
ki mik'e ko nace."

Cikin kuka dabin umurnin mahaifin nata da Yayan nata da tsoron ya Adam d'in ta mik'e cikin wahala hannun ta damk'e da mararta ta fice tana kuka,
kuma Ita da kanta ta san in Hamman ya mata Allurar tana jin sauk'i,
cikin kukan ta nufi part d'in su Hamma Umar d'in.

Shi kuwa Hamma Umar duk kukan da Ummul keyi yana ji dan lokacin da tafara kukan yana parlour Hajjajo jin kukan yayi yawane gashi yaji bala'in da su Adam ke mata yasa ya zame jikin shi ya dawo parlournsu cikin sanyi jiki ya konta kan kujera yasa tafin hannushi ya rufe fuskar sa,
zuciyar shi cike da tausayin Ummul ,
yana koncen yaji sautin kukanta a hankali yana ratsa parlour cikin rawan murya yaji tana sallama,
ido ya lumshe cikin jin zafin kukan da takeyi ga kunyar da ta rufeshi,
a hankali ya amsa mata sallamar,
Ita ko da zuwa yanzu ko tsawonta bata iya mik'ewa,
a sunkuye ta shigo parlour hawaye cike a fuskar ta da tayi jazir da kuka ida nunta duk sun kumbura,
a hankali ta durk'usa gaban kujerar da yake konce cikin kuka da rawan murya tace.
"Abba yace inzo kamin al..! alluran da kake min."

Shiru yayi zuciyar shi cike da tausayin ta gaba d'aya yake jin haushin kanshi tunda sana dinshi take irin wannan kukan.

Ita kuwa ganin bai kulatan ba ta saki kuka mai cike da raunin gaba d'aya jikin ta rawa yakeyi,
jin yadda take kukan ne ya mik'e cikin sanyi bedroom ya shige yana zuwa ya had'a allurar, sannan ya dawo parlour yana zuwa gabanta ya k'afa guiwowin shi a k'asa kan carpet suna fuskan tar juna,
kanshi a sunkuye yasa hannushi ta bayan ta a hankali ya murza siket d'in atampa dake jikin ta,
ita kam Ummul ido ta rumtse da k'arfi zuciyar ta cike da tsanarsa a ranta,
fuskarta ya d'an kallah sannan ya zira bakin allurar a cikin jikin ta,
k'ara ta saki cikin kuka da zafi ta fad'a jikin shi.

Ido ya rumtse da k'arfi sannan yasa hannushi d'aya ya matso ta cikin sanyi da raunin murya yace.
"Kar kiyi inji miki ciwon ki nitsuba ba zafi."
kuka ta kuma fara cikin dashewar muryar,
shi kuwa idoya lumshe sannan ya k'ara saita allura a hankali ya rink'a cusa ruwan a jikin ta,
yanayi a hankali yana ce mata .
"Sorry."
Ita kuwa jin zafin yadda ruwan ke ratsata yasa ta ya matso shi ta rik'eshi gam,
yana gamawa ya zare allurar sannan a hankali ya tureta baya ya janye jikin shi,
ya mik'e kenan ya kalli Usman dake dafe da bak'in k'ofa ya zuba musu ido sai kallon suyake cikin wani irin yanayi.

Ita kuwa yana tureta ta mik'e cikin jin jiri ta ratsa gefen ya Usman d'in ta wuce.

Tana fita Hamma Umar ya kawo hannun Usman d'in cikin tsantsar kulawa ,
kan kujera ya ajiye shi sannan ya d'auki maganin shi yazo ya bashi yasha,
a hankali yace.
"Usman gobe zamuje gun Ammin mu."
murmushi Usman yayi sannan yace.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin"
yace sannan suka she ga bedroom d'in a tare sukayi shirin baccin su.

Washe gari da safe bayan sun gama shirin su tsab sannan suka shiga cikin gida a parlour Nenne suka zauna bayan sun gaida Nenne suka fito parlour Hajjajo suka wuce suna zuwa Hamma Umar d'in ya shiga kitchen d'inta da niyar zai d'auki cup,
Sai kuma yayi baya a hankali ya tsaya a bakin kofar yana jin abinda Ummul ke fad'a,
ya Adam da Hajjajo dake bayan kitchen d'in ma suna jin abinda take fad'in ta window ita kuwa cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Nayi alk'awarin har Abadan.....


By
*GARKUWAR FULANI*




棣冩憫棣冨磳棣冨磳棣冨磳棣冨磳棣冨磳棣冨磳棣冨磳棣冨磳

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page

6 / 17