RUBUTACCEN AL'AMARI by AYSHA ALI GARKUWA

Author :  AYSHA ALI GARKUWA Category :  Romance

Chapter   2 / 17

3K to 6K   out of 49.6K words

na gida da woje ,
Ummaru tsiyar ka rigima da mishkilanci ko maganar ka tsada gareta."

Kanshi a k'asa ya d'an lumshe ido har ga Allah shi wannan halin nashi halittar sa ce haka Allah yayishi bai san ya zaiyi ya canza kanshi ba haka yake, a ranshi yace.
"Ya zanyi da Rubutaccen al'amari haka Allah ya halicceni bazan iya canza kaina ba".

Ita kuwa Ummul tuni ta tsuke fuska dan sam bata jin Hamma Umar Faruoq d'in nasu kamar jinin ta haka kuma ya samo asali ne da yanayin halin Faruoq baida shiga harkar da ba tasaba bayi da yawan magana baya kuma son raini da hayaniya yana da girmama na sama dashi har ranshi kuma yake jin son y'an uwanshi a ranshi yana kuma kula da yanayin tarbiyar k'annen shi a matsayin shi na babban yaya,
suma kuma suna son d'an uwansu sai Ummul ce da sam bata ko son su had'a inuwa d'aya da shi.

Tsuke fuska Ummul ta kuma yi jin yadda Hajjajo ke wani bashi kula ta musamman shiko ya wani shareta.

Su Adam da Sadiq da Aliyu da Usman sai murmushi sukeyi.

Shi kuwa yana gama b'allo maganin ya mik'awa Usman tare da bud'e mishi ruwan ya bashi yasha sannan ya had'a maganin wuri d'aya tare da mik'ewa ya fita a hankali yana zuwa bakin kofar woyarshi ta fara tsuwa cikin wani sautin wak'ar India kaal hoh nan hoh sautin ne da ya kasan ce ko ba,a ga Umar Faruoq a wurin ba matukar akaji sautin toh tabbas yana kusa da wurin sauti mai cike da sanyi da tausayi.

A hankali ya fito a barandar Hajjajo ya koma gefen baya kad'an tare da zauna wa kan kujerun dake jere a wurin.

Woyarshi ya zaro a hankali yayi picking ya fara magana a hankali.

Su kuwa a parlour Usman ne ya mik'e tare da cewa.
"Nenne bari in tafi gwadago."

Murmushi ya Sadiq yayi tare da cewa.
"Tab ai kai kam aikin wuya kam baka cikin kai da zuciyar ka take rabi ai sai dai kaje back kana shan rab'a."

Hannun shi yasa ya d'an dafe k'irjin shi cikin lumshe ido yace.
"Da kenan ya Sadiq yanzu nayi lafiya zuciya ta kamar taka take ko buhu zan iya d'agawa."

Adam ne ya d'an kalleshi yace.
"Sai dai buhun kam amman damuwa da firgicin da zuk'atan mu zasu iya jurewa taka zuciyar bazata iya d'auka ba."

Murmushi sukayi baki d'aya ita kuwa Ummul maya finta ta gyara cikin fara'a tace.
"Yauwa ya Usman dama zanje gidan Anty Sadiya dan tunda akayi sallah ban jeba."

Hannu ya mik'a mata tare da cewa.
"Zomu tafi yar k'anwata zan kaiki."

Aliyu ne ya kalli Nenne da sauri yace.
"Nenne kina ji wai zata tafi gidan Anty Sadiya kuma batayi girkin ranaba."

Da sauri Nenne tace.
"Ehh haka nefa Autana kaga har na manta,
kai kam Usman tafi kawai abinka kar ka makara,
Ita Ummul sai tayi girkin rana."

Lokacin d'aya idanun Ummul suka ciko da k'ollah tib hannu ta rink'a yarfawa a hankali tana d'an buga k'afafun ta tare da yin kan Aliyu tana cewa.
"Ma gulmacin yaro dan munafurci Aliyu duk k'asa min ido a rayuwa ta shi yasa wallahi na gomma ce ina school ba mai takura wa rayuwa ta."

Sai ta kuma juyowa gun Nenne cikin muryar lallashi tace.
"Ayyah Nenne na kiyi hak'uri ki barni naje wallahi zan dawo da wuri inyi aikin dare."

Kai Nenne ta girgiza alamun bazata jeba.
Sai hawaye car-car a fuskarta.

Shi kuwa Aliyu dariya ya fara yi cikin jin dad'in ya d'ana mata tarko.

Kanshi tayi a fusace tana.
"Munafuki wallahi sai na dokeka."

Cikin dariya ya zille ya fara gudu ita kuma tana binshi a baya ta kasa kamashi.

Shiko Aliyu gudu yake tare da cewa.
"Yoh ai laifin ba nawa bane tunda bani nace duk randa kika dawo Hutu ko weekend kece zakina yin girki ba,
Hamma Umar Faruoq ne ya fad'a, kuma kice ni zaki daka, kije ki ce mishi bazakiyi girkin ba mana,
ni me nawa a ciki?."

Kuka ta farayi tana binshi tana cewa.
"Ai shima mugun tace kawai ya hanani hutawa a rayuwa ta, ga masu aikin Amman don mugunta yace ni zanke yin girki mugu kawai mai bak'in hali."

Dariya Aliyu ya kuma yi harda yi mata gwalo yace.
"Shifa Hamma Umar yana tausayawa mijin da zaki aurane shi yasa yace ke zakina aikin ,
don karkije baki iya girkiba,
a ga laifin iyayenmu."

Binshi tayi da sauri shi kuma ya nufi woje da gudu yayi gefen da ya hoggo Hamma Umar d'in nasu yana gudu yana juyowa yana kallon ko ta kusa kamoshi.

Shi kuwa Dr Umar Faruoq tun da ya katse kiran woyan da yake yin,
yake jiyo hayani yarsu shi Aliyu a hankali yake tsokanar ita kuwa Ummul sai mita da kuka take yana jin tana ta cewa Aliyu munafuki,
Kalmar da baya k'aunar yaji an suffanta mutun da ita.

Ita kuwa sam bata lura da Hamma Umar d'in a wurin ba.

Shi kuwa Aliyu ya zo dai-dai gaban Hamma Umar d'in ya sule yayi wani irin mugun fad'uwa a k'asan tayis,
gum ya buge bak'in shi a take sai ga jini,
cikin wahala ya saki kuka mai k'arfi, wanda yasa su Nenne fitowa a guje.

Shi kuwa Hamma Umar da sauri ya mik'e ya d'ago Aliyu ranshi a b'ace ya kalli yadda bak'in yaron keta zubda jini,
ita kuma tsayuwa tayi jikinta nata rawa ganin yadda jini yake zuba a bak'in k'anin nata ga wani irin mugun kallo da Hamma Umar ke watsa mata.

Ganin su Nenne sun fito tayi maza tayi bayan ya Usman dan shi kad'ai ne mai kareta su ya Adam ma kullum fad'a suke mata da biyewa Aliyu da takeyi tayi ta jibagarsa.

Ita kam Nenne da sauri ta k'arisa gaban Dr Umar Faruoq da ya tallab'e hab'ar Aliyu cikin fad'a tace.
"Ummul zaki kashe min yaro a banza ga yadda kika fasa mishi baki akan zuwa uguwa."

Ita dai Ummul sai hawaye hannun Usman ta rik'e da k'arfi ganin Dr Umar Faruoq ya kirata da hannunshi cikin rawan murya tace.
"Ya Usman dan Allah ka bashi hak'uri wallahi bazan sake ba Allah ban san zai fad'iba."

A hankali Usman yace.
"Hamma tace kayi hak'uri."

Fuska ya tsuke murya a fad'ace yace.
"Zo nan."

K'ara k'ak'k'ame hannun Usman tayi tana zubda k'olloh,
shi kuwa Usman hannushi yasa a hankali ya b'amb'areta a jikin shi cikin rad'a yace.
"In baki jeba zai k'ara hatsala kije ki k'arb'i hukun cinki."

Cikin zubda k'olloh tayi gaban shi a hankali take taku har zuwa gaban shi tana zuwa ta durk'usa a gaban shi.

A hatsele yasa k'afa ya tureta tare da cewa,
" taso."
Da sauri ta mik'e ta tsaya a gaban shi.
Mari ya watsa mata cikin fad'a ya nunata da yatsa yace.
"Kika kuskura kika k'ara cewa wani munafuki wallahi sai na fasa miki baki,
ke kullum bakya jin magana,
kiyi ta munafurta mutane kuma kece mai halin muna fukan,
kalli yadda kike kuka tun ba'a tab'aki ba, ko shi da kika fasawa bak'in baiyi wannan kukan ba,
kuma kiji daga baki na ba inda zaki je sai shegen son yawo."

Sai ya kuma watsa mata mari tare da cewa.
"Ki wuce kiyi cikin gida ki fara akin ki tun wuri."

Baki na rawa tace.
"Toh"

Ta fice ta tafi tana kuka Usman ne yabi bayan ta da sauri yana lallashin ta har saida ta d'an huce ya kalleta cikin kulawa yace.
"Allah ya d'aiyiba."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ya Usman Ina sonka."
fuskarta ya shafa tare da koikoiyan muryar Nuru yace.
"Allah ya d'aiyiba

Dariya sukayi baki d'aya sannan ya fice ya tafi.

Hajjajo kuma da Nenne da su ya Adam parlour Nenne suka bita,
Nenne da su ya Adam fad'a suke mata,
ita kuwa hajjajo lallashinta take yi.

Shi kuwa Dr Umar Faruoq yana rik'e da hannun Aliyu har suka shiga parlour su,
kan kujera ya kontar da Aliyu dressing na wurin yayi mishi tare da bashi maganin ya sha,
sannan ya kunna mishi A,C da TV.

a hankali Aliyu ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya tare da lumshe ido,
lokacin d'aya yayi bacci,
shi kuwa Dr Umar Faruoq wonka yayi tare da kimtsawa ciki shigarsu irin ta manyan doctors sai k'amshi yake zubawa ya fito ya nufi katafaren chemist d'inshi mai suna Baba aura chemist dayake kusa dasu,
yana zuwa dai-dai bakin wurin yayi wani irin.......





By
*GARKUWAR FULANI*

[6:47AM, 9/20/2017] ‪+234 706 196 7803‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Page 3⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Wannan shafi d'ugguruggum dinshi naki ne ke kad'ai Mamyn Najmah ina al'fahari dake ina sonki har cikin raina Allah ya bar zumunci ngd da k'aunar ki gareni 😘😍🤝*



*A*jiyan zuciya tare da lumshe ido,
ganin mutane da suke cike a harabar bakin chemist d'in mata da maza manya da yara,
cikin ranshi yake fad'in,
"Allah ya bashi ikion dubasu baki d'aya".
Fitowa yayi cikin nutsuwa ya nufi wurin da ya kasance wurin zaman shi a ko wacce rana matuk'ar dai ya shigo potiskum toh shi baya samun hutun weekend d'in.

Yana isa yaranshi da ke aiki chemist d'in suka yi mishi barka da safiya,
sannan ya zauna ya fara duba marasa lafiyan d'aya bayan d'aya yana mai basu kulawa yadda ya kamata duk da ba sakin fuska yake yiba amman a fili za'a gane fuskarsa mai ciki da tausayi ne da jink'an marasa lafiyan,
dan bashi da surutu maganar sa a k'aiyade take .

Haka ya yayi ta dubasu har zuwa azahar daga nanne ya tashi tare da sa yaran nashi suka rufe chemists d'in sannan sukayi alwala suka nufi masallaci dan yin sallan a jam'i.

Bayan an idar da sallah su suka koma bakin aikin su shi kuma kai tsaye gida ya nufa dan gaba d'aya ya gaji ga yunwa ga baccin da yake ji.


Ita kuwa Ummul bayan ta shiga kitchen ta fara aiki kenan ,
woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan sautin kiran kawai ke shaida mata Mustapha ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara magana a woyar,
gas d'in ta kashe sannan ta fita cikin takunta mai cike da nitsuwa,
kai tsaye ta nufi part d'in kakarsu Hajjajo bedroom ta wuce tana zuwa ta d'ale kan gadon ta mai rumfa cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba,
Ido ta lumshe cikin sauk'e ajiyar zuciya tace.
"Habeebi"
"Na'am."
Yace mata tare da cewa.
"Ummul kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in banji muryar ki na awa 3 ba Ummul ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki."

Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa tace.
"Ya Habeebi ka kontar da hankalin ka Ummul taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin raina ko bacci nake fuskar ka itace k'awan yata."

Mustapha kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na ratsashi har cikin k'ahon zuciyarshi,
yayin da ita kuwa Ummul take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar kasan cewa a haka suna musayan zantukan so masu sanyi,
ji take matuk'ar babu Mustapha a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita.

Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna,
ita kuwa Ummul gaba d'aya ta manta da wani batun girkin da aka sata,
haka yasa tayi ta woyarta sune basu katse hirar ba sai 12:23 pm tana katse kiran kuma bacci ya kwashe ta,
bata farka ba sai yanzu da taji muryar Hamma Umar a parlour HaJajjo.

Ita kuwa Nenne dama ta shiga mak'o tansu duba mara lafiya so batasan me Ummul tayi ba.




*Asalin dengar takan su, Zuriya d'aya ce duk su jikokin Alhaji Umaru shuwa'arab ne*


Alhaji Umaru Shuwa'arab asalin sa shi da matarsa Rabi'atu Hajjajo kenan su Shuwa'arab ne asalin ma zauna garin patiskum cikin unguwar tudun wada yamma da fce,
kowa yasan shuwa'arab kyewawane kuma masu jin larabci ne,
Alhaji Umaru da Hajjajo suna da yaran su 3 duk mazane babban d'ansu Alhaji Ibrahim Umar shuwa sai k'anneshi biyu tagwaye ne Hassan da Husaini sun tashi cikin gata da tsantsanr k'aunar juna,
Alhaji Ibrahim shine babba kuma ya kasan ce mutun mai tausayi da k'aunar k'annenshi yana musu so mai tsanani,
iyayensu kuwa sun basu tarbiya mai inganci tare da ilimin addini da na zamani
sun tashi cikin tsabtacecciyar rayuwa,
da kulawar iyayen su bayan sun girma ne Alhaji Ibrahim yayi aure ya auri matarsa Amina ba fullatanar potiskum d'in,
mace mai mutunci da kara da sanin ya ka mata,
bayan anyi auren bada jimawa ba Allah yayiwa Alhaji Umaru Shuwa rasuwa,
daga nan ragamar gidan ya zama a hannun Alhaji Ibrahim yake ya rik'e k'anneshi da amana ya basu dukkan abinda uba zai bawa ya ranshi sunci gaba da karatu su .

Yana zaune da matarsa da mahaifiyar shi a gidan shi da k'annenshi baki d'aya,

Ranar da Alhaji Umaru Shuwa ya cika shekara d'aya da rasuwa a ranar Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta fari tas kekyawa dashi mai kama da babanshi,
ran suna yaro yaci sunan kakanshi Umar Faruoq kenan.

Yaro ya tashi cikin gata da kulawan mahaifiyar shi da kakarshi da k'annen mahaifinshi Hassan da Husaini,
yaro mai farin jini da kwarjini.

bayan shekara 4 Alhaji Ibrahim, yayiwa k'annenshi Aure rana d'aya,
suka tare a gida jen da ya gina musu a gefen nashi.

Bayan watannni 5 da auren Khadija matar Hassan ta fara laulayin cikinta na fari a lokacin kuma Amina matar Alhaji Ibrahim itama tana da cikin d'anta na biyu,
matar Hussani kuma bata da ciki tukun ,
Bayan wani lokacin Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta na biyu mai suna Usman a lokacin Umar Faruoq kuwa ya cika shekara 5 da y'an watanni, Khadija matar Hassan kuma ta haifi d'anta na fari mai suna Adam wanda tsaka ninshi da Usman kwana 12 ne Usman d'in ya girmi Adam da kwana 12 haka yaran suka tashi cikin shak'u da juna ko mai tare akeyi musu,
Umar Faruoq ya tashi da k'aunar k'annenshi.

Usman da Adam suna da shekara d'aya a duniya Allah yayiwa Alhaji Ibrahim maifin Umar da Usman rasuwa.

Rashuwa da ta shiga jikin Hassan da Hussain da Hajjajo sunyi kukan rashin d'an uwansu wanda shine madadin mahaifinsu a garesu.

Amina matar Alhaji Ibrahim mahaifiyar su Umar wacce yaran ke karanta da Ammi tayi kukan rashin mijinta da rabuwa da yaranta dan tana gama ta kaba ta koma gidan iyayen ta,
Alhaji Hassan wanda suke kira da Abba ya karb'i Umar da Usman ya dank'asu a hannun matarsa Khadija wacce yaran ke kira da Nenne sannan kakarsu Hajjajo itama tana gidan suka taru suka raini yaran cikin kulawa da tsantsar gata ta yadda su Umar basu san zafin maraici ba.

Nenne kuma bayan ta haifi Adam ta kuma haihuwa yaran 4 Sadiq sai Sadiya sai Rabi'atu wacce take takwarar Hajjajo ce amman suna kiranta da Ummul khairi sai kuma d'an autanta Aliyu.

Yaran sun tashi cikin k'aunar juna baka gane cewa Nenne ba ita ta haifi su Umar ba,
Sai dai kowa da halinsa dan shi Umar mishkili ne baya wasa da yara kuma kasan cewarsa shine babba a family d'in su yasa k'annenshi suna girmamashi
shi kanshi Umar yana jin haushin yadda yake halinshi, yayinda hakan ya jamishi kiyeyyah a uzuciyar Ummul ita kuma gani take yana takura rayuwarta a, zahiri Umar yana jin zafin yadda wasu lokutan ake gaza gane cewa wannan halin fa ba yin kanshi bane Allah ne ya halicce shi a hakan.

Sun tashi cikin gata da kulawa inda Umar a yanzu haka shi babban doctor ne yana d'aya daga cikin yerdeddun governor damaturu shine doctor dake duba lafiyar governor nasu kuma shine babban doctor dake aiki a general hospital damaturu,
Usman kuwa shi accounter ne sai .

Sai
Adam Airforce ne yanzu haka a Kaduna yake
sai in yazo ziyara.

Sai Sadiq shi kuma yana aiki a ministry of justice.

sai Halimatu Sadiya ita kuma nurse ce tana aiki anan cikin garin potiskum.

Sai
Ummul khairi ita kuma bayan ta gama primary school d'in ta aka jona mata secondary school GGC damaturu inda ta koma cikin damaturu da zama a cikin makaran ta,
yayin da shi kuwa Alhaji Hassan Abban Ummul kenan shi yana aikine a offishin gwamna a damaturu hakan yasa Abba yana da gida a can inda yake zama yana aikin shi sai alhamis ya taho week end cikin garin patiskum d'in,
hakan yasa idan anyi hutu Ummul takan zauna a gidan shi dake gidan jen maikata na ministry of works and housing dake gashua road damaturu dan jira ya gama aikin sa sai su tafi tare su koma cikin potiskum tare.

A hakan ne wata rana Ummul ta fita ita da k'awayen ta suna d'an zagawa cikin uguwar,
anan ta had'u da Mustapha saurayin da suke soyayya a yanzu haka,
shima yazo gun abokan shine a unguwar,
dan shi Mustapha gidan su na commissioners quarters dake Maiduguri road damaturu,
haka sukayi ta soyeyya in sunyi hutu yana zuwa har gidan su Ummul d'in dake potiskum,
Haka yasa
ya saba da ita ya saba da y'an uwanta suna yiwa juna so mai tsabta.

Shi kuwa Umar sosai ya zuba ido kan lamuran Ummul, gashi in Abba baya nan kusan shine uba a gidan,
so yana tsanani sa mata ido dan kare tarbiyar ta ita kuwa hakan yasa ta k'ara tsanarsa da jin tsoronshi,
dan baya mata da sauk'i.

Usman kuwa mutun ne mai fara'a da sakin fuska yana watsa da kawo dan shi ko da Abba wasa yake mishi kamar kakanshi,
haka yasa Usman ya kasance wani jigo na gidan in ya fita ko na awa d'aya ne sai anyita ceki yarshi,
shi da Umar kuwa suna yiwa juna wani irin so mai tsanani Umar yana k'aunar Usman fiye da komai a rayuwarshi suna yawan kaiwa Amminsu ziyara a gidan kakannin su.

Usman tun yana k'arami ya tashi da ciwon zuciya mai tsanani inda Abba da Daddy Hussain in Abban kenan sukayi ta jin yarshi,
a haka abin tashi hankali da fari an gane cewa zuciyar Usman tana da d'an hujin dake sashi ciwon zuciya so anyi ta bashi kula,
amman kuma Usman na girma abin na k'aruwa haka yasa zuciyarshi ta zama ta tsage ,
dole aka fitar dashi Egypt so acan akayi

2 / 17