WATA RANA DA DADDARE BOOK 2 BY Aishat Falalu Rimin K'aura

Author :  Category :  Romance

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 18.3K words

A CIKIN DOKAR DAJI,nemanta amma.Ko sahunta babu.

Bawan Allah zama yai ya zafga uban tagumi..
Yana ta jimami.

Chan gafda Sallar Magriba har ya ɗora alwala,ɗaga idonsa sama wazai gani?

Kwatsam !!!
ba zato ba tsammani ya hango ta ya hangota zaune nesa dashi da ƙatuwar dabba wacce zata kai girman ragon layya.

Ta tasa dabbar gaba sai ci take ɗanya bakinta jaga-gaja da jini,ci take haiƙan yadda kasan kura.


Duk girman dabbar ta kusa cinyeta.
Har ƙasusuwan bata bari ba daga inda yake yana juyo ƙarar taunar ƙashen da zaƙo-zaƙon haƙorata,farcenta kuwa da ta nitsa zata chaɓo tsoka.


Hatta kayan jikinta doguwar rigar laraba da Bilal ya.Kawo mata ita ma.Ta jiƙe da jini caɓa-caɓa.


Koda yazo daf da ita kalamanta yasa ya sandare a tsaye.

''Abdullahi,sai naga bayanka,sai na kasheka!!!

Bana san rayuwarka,sai na kasheka nacinye namanka ɗanye

sai ta ƙyl-ƙyale da dariya kai daji kasan ba muryarta bace.

Adduo'i kurum yake ta maimaitawa a baƙinsa tare da kiran sunayen Allah kyawawa.


Kusa da ita yaje ya tsaya har yau bakinsa ɗauke da addu'a.

Juyowa tayi da jan idonta,sai kuma ta fashe da dariya.


shi kuma sai ya fashe da kuka.

''Muhijjinatu kece a wannan halin,?

Ni Abbun naki abun so da ƙaunarki zaki kashe,kece da cin ɗanyen nama?


yana cikin maganar bai ankaraba,ta ɗamƙo hannunsa ta gantsara mishi wani mugun cizo,wanda har fatarsa saida ta ciro babbar tsoka a jikinsa.


Wata iriyar ƙara ya saki saboda zafi da zogin da yaji,jini ya soma ambaliya.



goshinta ya dafe ya fara da kiran sunan Allah sannan ya fara.

''A'uzubikalimatllahi,tahmati...................

(A page na gaba zan rubutA har qarshe.)


''Bissimillahi Ukuraj Aduwullah.


fisge -fisge ta soma yi amma ƙarfin addu'ar ya hanatsa cutar dashi.

Ihu take sosai a halin yanzu Horronya sak ta koma.Dalilin jinin dake kwance a jikinta,da kuma halittarta da ta sauya kamar ba Muhijjinatunshi ba.

duk addu'ar da ta tari bakinsa ambata yake.

Kuma bata fasa ihu da kururuwa ba......

a cikin hakan ne har barcin ya kamata ta langwaɓe ta soma barci.
Aa
koda ya kwantar da ita sallar Magriba ya soma yi,bayan ya sslamce ya soma rero karatun Al-Qur'ani me girma.




SHIN WAI BAKU TAMBAYE NI INA LABARIN MUKSHFIYYAH BA.

Muhaɗu a nex page insha Allah.


yawan commts yawan typing.

wasu ma ban taɓa gsnin commts ɗinsu a gidannan ba,sharhi na ƙara qarfii.......

WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)


The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*page-17-18.

Wata azabatacciyar ƙara su Sarki Safwan suka ji baƙin aljani ya saki.

baki ɗayansu ɗagowa suka yi daga sujjadar da suka duƙufa suna wa DODO.

Wannan karon harda Alh.Bashir.
Shi kuma ya zo ne domin biyan buƙatarsa ta kama Azkfyyh.

Boka Zaƙawanu shi yazo wajen baƙin aljani yana tambayarsa.

''Me ya same sa yake wannan muguwar ƙara?

dakyar ya iya duban Boka Zaƙawanu,bayan ya bayyana a siffar mutum,yace ''Baka san balain da nake ji ba,don baka iya duban fatata da kaga yadda ta kwaye.

Tinda uwata ta kawo ni duniya ban taɓa jin bala'i da musifa irin wannan ba.

''Na rantse sai na ɗau fansa akan Abdullahi da ƴarsa,ashe mugun tarko ya ɗana min.

''Kuma wallahi ƴarsa sai ta kashe shi da hannuta,dama me ya rage,na mayarda ita HORROW.

Kuma a halin yanzu bata da abokin gaba sama da mahaifinta...

Alh.Bashir ya juyo ya dubi ɗan'uwansa Sarki Safwan yana tambayarsa.

''Waye Abdullahi,me baƙin aljani ke nufi da maganganunsa?

Boka Zakawanu yace.

''Bashir ka daɗe rabonka da BAƘAR FADA,shi yasa duk abubuwan dake faruwa baka da masaniya.

''Ko wannan zuwan ma da kayi kazo ne da niyyar biyan buƙatar kanka.

Kazo akan biyan buƙatarka ta nemo Azkfyyh,duk da kasan cewa Azkfyyh yar ɗan'uwanka ce.

To ba kowanne Abdullahi ake magana ba face ɗan'uwanku kaida Safwan,domin duk yadda Mariya da Safwan suka baka labari duk baka yarda ba,to maganarsa ake.

Zaro ido Alh.Bashir yai yace.

''Ban gane ba,dama dai dagaske wannan tatsuniyar da na kasa yarda,Abdullahi yana raye?


"Yes of course,hatta da cikin jikin Gimbiya Binta ma an haife cikin,tsaleliyar budurwa a nan tana rayuwa A DOKAR DAJI.
Domin har nan BAƘAR FADA ma anzo da ita.


Bakin Alh.Bashir ya mutu murus ya gaza furta uffan.

Bin Boka Zaƙawanu yai da kallo,zaka hango tsantsar mamaki da al-ajabi a tattare dashi.

''Waye yazo da yarinyar har nan?

''Bakin Aljani shi yaje har DOKAR DAJIN DA Suke rayuwa ya tafo da ita.

''Wanne Daji ne?

"Dajin tsakiyar duniya kenan.Inda babu wani Biladama da ya taɓa giftawa ta wajen.

An ɗaukota a domin sanin sunanta,domin shine passwort ɗin buɗe,kofar get ɗin ƙofar da Abdullahi ya rufe dukiyarsa kuma anji sunan nata.

Cire hula Alh.Bashir yai ya gurfana a gaban Boka Zaƙawanu.


Yace yanzu kana nufin Safwan yasan securityn?

"Eh man,bakin aljani yai mishi tsayin daka har ya gano sunan yarinyar.

''Sunanta Muhijji.........

Boka Zaƙawanu bai rufe baki ba Safwan yai saurin rufe mishi baki.

Da gudu Alh.Bashir ya rungumi Sarki Safwan yana faɗar.

''congratulation my big brother.....

''Ashe mun samo sunan securityn na farko da za'a haɗa da Mukashifiyyah Azkfyyh Haidar,amma me ya hana ka bari Boka Zaƙawanu ya sanar min,koko kafi so naji wannan zazzaƙan albishir daga bakinka?

Ya faɗa tare da fashewa da dariya.

Turɓune fuska Safwan yai yana duban Alh.Bashir tare da yi masa kallon up and down.

Ɓanɓare jikinsa yai daga rungumar da Bashir yai masa.

Kana ya mayar da dubansa izuwa ga Boka.

''Haka mukai dakai,don me zaka sanarwa da Bashir da sirrina?

A dokar aikinmu ba haka mukayi ba.

''Dokar farko da aka saka min,ance nayi ma ƴata fyaɗe nayi,kana aka ce,ƴata Sumayyah,zata koma tamkar mata ta zan cigaba da amfani da ita a duk lokacin da take,priod,a halin yanzu duk sa'adda Sumayyah ke al-ada na sani kuma sai nayi.Mata fyaɗe da jinin.

A haka ta samu juna biyu,aka ce DODO na buƙatar ɗan tayin na bayar...

Ance na mayar da Sumayya tamkar mata ta,kullum sai nayi mata fyaɗe,
baya ga haka ance kullum sai na biyo layar ɓata nazo nayiwa DODO SUJADA daga.

Da ga cikin meke ban aikataba,meye makamancin hakan da Bashir yai?


idan har yana buƙatar sanin sirri,meye ya hana ya aikata wa'innan ayyukan,na Siyar da lahira a siyo duniya?

to ni yanzu duk duniyar nan ban yarda da kowa ba daga kaina sai DODO me sa'a.

Sai kai Zaƙawanu,to naga kaima kana shirin cin amanata.

Ya faɗa yana aunawa Alh.Bashir harara,wanda yai zaman yan bori.

Bakin Alh.Bashir na ƙyarma yace.
''Mi kake nufi,kana nufin duk wahalar da muka sha ni dakai ya tashi a banza,sai da daɗin yazo zaka juya min baya.

Dariya Safwan ya kwashe da ita sai da yai me isarsa kana ya dubi Bashir yace.

''Wallahi bacin kana ɗan'uwana da ya rage min a duniya da sai na kasheka,har lahira,kasan ni bana rama al-khari da alkhari sai dai na rama Alkhari da sharri.

Kasan kirarina kenan haka nan kai Amanna dani ka manta koni waye.

Bazan kasheka ba nafi san kullum kaita ƙumsar takaicina da baƙin cikina har ya kashe ka.

Saboda haka ni a matsayin Karen farautata na ɗaukeka.

Kuma yanzu na kamo abin farautar don haka yanzu baka da amfani a wajena.

Tin wuri ka fita hanyata ka fidda rai da samun wannan dukiya ta Abdullhi.

''Wai ma ina ɗumbin dukiyar da mahaifimmu ya mutu ya bar maka zarinka yai yawa Bashir,shin wai ko in ka mutu da kuɗi za'a rufeka ne.?

Cikin Alh.Bashir yai laƙwas.
Yace.

''Yanzu duk wahalar da muka sha a tare haka zakai min?

WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)


The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*page19-20.
Alh.Bashir yace ''Yanzu duk faɗi tashin da muka sha a tare haka zaka yi min?

ƙyal-ƙyalewa da dariyar Mugunta Alh.Bashir yai kafin yace.

''Kai Bashir bara na faɗa maka.Abinda baka sani ba.

Da ga yau babu ni babu kai.

Karka kuskura ka kuma nuna ka sanni,Ko jini ɗaya da muka fito daga yau kar ka kuma nuna ka sanni.

Saboda a halin yanzu ban yarda da kai ba.

Domin kuwa yadda ka yarda ka haɗa kai dani aka kawar da Abdullahi,nima wata rana zaka iya shawarar haɗa kai da wani a domim kawar dani.

Don haka kowa tashi ta fisshe shi.

Zufa ta tsattsafowa Alh.Bashir ya dubi Boka Zaƙawanu yace..

''Ka saka baki,nima fa nayi wa DODON TSAFI biyayyah.

Boka Zaƙawanu ya kwashe da dariya yace.

Ina ni ina shiga faɗan ƴan'uwa, kai da shi ai kumfi kusa.


Kuma dama mu BAƘAR MADARAUTA,bama san zaman lafiya munfi son muga ana zalunci,cin amana rashin imani,kai duk wani abu me kyau bama so munfi san abu me muni.

Don haka muna goyon bayan Safwan 100/100

gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

shida Safwan harda tafi.

Alh.Bashir yace.

''Tinda kaci amanata wallahi summa tallahi sai na ɗau fansa.

Zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa,cikin ƙunan rai da ɗacin zuciya ya soma tunanin irin ɗumbin dukiyar da Abdullahi ya tara wacce kullum yake mafarkin yadda zai hallaka Safwan domin ya.Mallaketa.

Sai da aski yazo gaban goshi sannan maganar zata zama ƙanzon kurege.

ya tuna Imaninsa da kuma lahirarsa duk da ya siyar saboda kwaɗayin dukiya.

Tunanisa idan ya mallaki dukiyar sai yai ta zuwa Hajji da Umara yana istigifari ya karkaɗe zunubinsa.

(Allah sarki jahilci babban ciwo Alh.Bashir kayi kuskure,shin in kaje hajji da Umra Allah ya yafe maka laifin bawa da ubangiji sufa sauran bayin Allah,irinsu Abbun Muhijjinau shin su sun yafe maka?)

kenan duk yadda yake kwana yana tashi da tunanin dukiyar nan abun ya zama ta leƙo ta koma.


Luuuuuuu!!!

Ya sulale k'asa jikinsa ya soma ƙyarma.
Ko hawan jinin farat ɗaya ya kama shi?

Ohon mishi

su dai dariya suka dinga yi suda Boka Zaƙwanu.

***BAƘAR MASARAUTA.)**

ɓangaren Mukashifiyya kuwa tana cikin farin ciki tsantsa.
''Wai ita za'a sadaukarwa DODON TSAFI.

Bayan sun kammala cin abinci

Jamila tai zaune ta zuba uban tagumi.

Mukasffy ta ƙure ta da kallo kana tace.

Miƙewa tayi ta cire mata tagumin tace.

''Jamila wai meye matsalarki?

Cikin mamaki Jamila ke dubanta tace.

''Lallai ma Mukashiffyh kina nufin yanzu har wannan be kai matsala ba?
kina fa jin yadda Sarki yace ƙarshen shekara kece wacce za'a sadaukarwa da DODON TSAFI.

Kuma da alama naga keɗin hankalinki a kwance yake bakya da damuwa.

''Shin haka rayuwarmu zata ƙare cikin zullumi,ke yanzu idan aka tafi dake ni yaya rayuwata zata ƙare "Shin haka zamu dawwama aita ɗibar mu ana baiwa DODO JININMU,TAmkar wasu DABBOBI.?

Mukashiffyah tai murmushi haɗe da guntun tsoki kana tace.

''Jamila har yau baki san waccece niba ko?

to zan sanar miki da sirrin dake baki sanshi ba.

''Na rantse da girman Allah na daɗe ina jiran wannan ranar,ranar da za'a sadaukarwa da tsinanne la'ananne ni wato DODON TSAFI.

''Insha Allahu ni Mukashifiyyah ƴar sarki Abdullahi sai na kawo ƙarshen DODO.walau mutum ne shi,ko aljan ko kuma wata halitta daban.

Kuma sai na kafa tarihi koda bayan rayuwata.

Saboda da haka Jamila kar wannan ya dame ki,kar ya zaunar miki a zuciya,Ki barni da Sarki Safwan ni ko shi shege ya fasa.

ƙur! Jamila ta zubawa Mukashifiyya ido ta gaza furta uffan.

Dakyar ta aro jarumta tace.

''Ki rufa mana asiri Muksfyy ki daina wannan furucin kar kija ayi miki mummunan hukuncin da za'a gana miki azaba kafin a kashe ki.

Har zuciyata nake sonki,da Sarki zai taimake ni da ya musanya ki dani,domin ni bansan yadda rayuwata zata kasance ba idan babu ke.....

Jamila ta ƙarasa da fashwa da matsanancin kuka.

Dafa kafaɗarta Mukashiffyah tayi,tausayin kansu su duka ya kamata na irin shaƙuwar da suka yi.

''Jamila karki ƙara zubar da hawayenki..

akan wannan banzan daliliN.

Kuma da kika ce meye madogarata da nake taƙama.

Bani da kowa banda komai face ubangijin musulunci,wanda yai ni yai Sarki Safwan kuma ya halicci DODON DA suke ikirarin suna taƙama dashi.

Allah s.W.A.shi yace wa bawa tashi in taimakeka,Insha Allah na miƙe,yanzu zaki ga taimakon da ubangijin musulunci zaiyi mini.
Da Sarki Safwan da DODON TSAFI,duka suna rayuwa ne da izinin ubangiji,da Allah yaso ƙwaƙƙwaran motsi ɗayansu bai isa yayi ba.

Don haka ki jira kiga yadda zata kwashe mana ni dasu,kar ki ƙara saka kanki a damuwa ki dogara ga Allah zai isar miki

sannan kiyi tawassali da Annabi muh'd,insha Allah ubangiji zai tsaya miki.


Jamila tace.

''Har naji sanyi Mukashiffyh,nasiharki ta ratsa min dukkanin wata jijiya dake jikina.

To yanzu meye abinyi?....

''Maganar Muksfyyh ita ce abin yi suka ji an faɗa daga bayansu.

Baki ɗaya juyawa suka yi domin ganin me maganar.
̄
Har wayau fuskarsa ɗauke take da kyakkyawan murmushi.

Mukashifyyh ya zubawa ido.

Daf dasu ya ƙaraso ya dubi Mukashiffyh yace.

''Assalamu alaikum.''
har wannan lokacin bai bar murmushin nan nashi me birgewa ba.

Ba kowa bane face Sadik.

Idan me karatu be manta ba SADIK shine namijin da aka haɗa da Mukashifyyh.

Fuskarta ba yabo ba fallasa

Fuska ɗaure ta dube shi.

''Me ye kake bukata a wajena?

na kula duk inda nayi idonka na kaina,meye kake nema a waje na?

ko ka ban ajiyar wani abu ne da na manta.

🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_




PAGE 20-21.


Cikin muryarsa me sanyi yace.
''Mukashiffyah amman dai ko sallama ta kin amsa ko?

ko baki amsa sallamata a domin komai ba kin amsa domin amuncin da na nema miki wajen ubangiji ko?

yanzu naji kina wata nasiha,shin ke me yasa ba zakiyi wa kanki nasiha ba,domin kuwa kinsan muhimmancin sallama ga cikakken musulmi ko?

wani banzan kallo ta bishi dashi kana ta murguɗa mishi baki tace.

''Wa'alaikasalam.

Na amsa sai akayi me kuma bawan Allah ?

ta faɗa da ƙarfi.

Mukashifyyh tace''Dama ina so zanyi.Maka wata ƴar tambaya idan ba zaka damu ba.

Zaka hango tsantsar farin ciki a fuskarsa tunda Muksfyh ta bashi wannan babbar kulawa har take cewa zata yi mishi tambaya.

Muksshifyyh abar ƙaunarsa DARE,DA RANA.


''Ina jinki Gimbiya.

Saurin kallonsa tayi jin ya kirata da Gimbiya,amma kuma sai ta kawar da maganar tace mishi.

''Tambaya ta ita ce.
Me yasa lokacin da Sarki Safwan yazo kai baka fito ka tona min asiri a gabansa ba?

''Saboda ina sanki.

tun ranar da na soma tozali dake,naji duniyar nan babu macen da nake so tamkarki, Ina fata zaki soni tamkar yadda nima nake sonki?

maganar ta zo mats wani banbarakwai,wai namiji da suna hajara.


Dariya ta fashe da ita,har ga Allah ya bata dariya.

Wani wawan kallo ta sakar mishi bayan ta tsagaita dariyar.

tace.

''Tun da nake a duniya ban taɓa ganin mahaukacin masoyi irinka ba.

banda tsabar hauka taya kana BAWA INA BAIWA,ka kira zancen soyayyah a tsakaninmmu?

kai da a halin yanzu baka da yancin kanka,haka zalika ni ma bani da ƴanci,taya zamu ƙullah soyyah a wannan ƙasƙancin da muke ciki,idan mun ƙullah soyayyah taya zamuyi aure,idan munyi aure taya zamu iya haifar yara su tashi a wulaƙance tamkar yadda muke hakan kake fata?

Soyayyah ana ginata cikin kwanciyar hankali ne da kuma so da ƙauna.

Ni dakai kullum muna cikin zullumin meye zai faru a gobe.

Duk ajiye wannan gefe,kace kana so na,ni kuma bana sanka,baka daga cikin jerin mazan da nake iya rayuwar soyayyah dasu balle aure ya gifta a tsakaninmmu,ina faɗa maka hakan ne.Idan muna da ƴanci ni dakai.

Don haka ga shawara ni dakai mu rungumi ƙaddarar da Allah s.W.A ya ɗora mana.

Ina fata ka gamsu?

Zaka iya hango bugun zuciyarsa.

Bakinsa na kyarma yace.

''A ko wanne lokaci Allah zai iya juya al-amarinsa.

Karkiyi min haka Mksfyyh ni kaɗai nasan yadda nake azabtuwa da sonki.

Ki tallafe ni Muksfyyh,don girman Allah ki soni.

Kuma da kike zancen bama da ƴanci Allah yasan halin da muke ciki kuma zai kawo mana ɗauki,ina ji a jikina ba zamu mutu cikin wannan uƙubarba.

''Shin kina ganin Allah zai ƙyale Safwan ne,karki manta da tarihin fir'auna mana Allah ya kawo ƙarshensa bare wani Safwan ƙaramin ƙwaro

ina ji a jikina Muksfyyh kece zakiyi silar fitarmu a gidannan insha Allah.

Zubewa yai ƙasa yana mata magiya akan taso shi.

A fusace ta funciko rigar Jamila suka bar wajen.

*****
BawAn Allahr nan yaban tausayi Jamilan ta faɗa tana duban Mksfhy.

''To ko ke zaki aure shi ne?

A'a me yai zafi shi ba wuta ba,ai bani yace yana so ba.

**************

UKUN DARE tsakiyar DARE duk sun mimmiƙe kowa na tsaka da ji daɗin barcinsa,mazan dake gidan duk sunzo sun biya buƙatarsu kowa ya kama gabansa yana runtsawa DARE mahutar bawa.

kukan mutum ya farkardasu baki ɗayansu.

Ɗaya-bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajensu suna zowa domin ganin waye ke kuka a irin wannan lokaci TSAKIYAR DARE?

''Baƙuwar baiwa ce!
kowaccensu ke faɗa.

Da alama tasha duka,jibi yadda jikinta ke fitar da jini.Kuma babbar mace ce.

Kowanne marar imanin yai mata wannan duka haka?

ko daga ina aka ɗaukota?

Allah sarki!
yanzu haka an rabata da Mijinta da ƴaƴanta.
Kai Sarki Safwan ya cika cikakken azzalumi.

Jamila tashi muje mu taimaka mata kinga bata hayyacinta.

Saman gado suka ɗorata,har gari ya soma haske suna zaune kusa da ita duk sunyi jugum-jugum sunkai su ashirin.

Sai da gari ya fara haske ta farka tana ta faman wurwurga ido.

''Na shigangaɗi ni Mariya ina ne nan?
baki na yaja min bala'i wayyo Allah na!

Alh.Bashir wallahi ƙauyen da na kaika nan Azkfyyh da Mal.Kabir ke rayuwa.

Surutai barkatai dai ta dinga yi kala,kala.

Sunan Azkfyh da Mariya ta ambata shi ya kashewa Muksfyyh jiki,ta rasa me ke mata daɗi a duniya,Azkfyyh Mal.Kabir Alh.Bashir duk suna yazo ɗaya.
Anya ba ƴar'uwarta Azkfyyh ba,domin tana gidan Alh.Bashir ɗan'uwan mahaifinta kuma Mal.Kabir me gadi aka ba Azkfyyh.

To ita wannan macen daga ina take?

Sauran ƴan daƙin su suka ci gaba da kula da Mariya,Mukshfyyh kam ta lula dogon tunani.


Haka Mariya ta dinga surutai da ɗuma ɗumai har wani DAREN ya kuma yi duk ta hana su runtsawa.


To nidai nace saida safen ku.

Yau nayi typing over ina jiran commts da sharhi kafin gobe muji yacce zata kaya da mariya bayan haka mariya na gaisheku.



🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_






PAGE 23-24.




Da garin Allah ya waye ba laifi Mariya ta tashi cikin nutsuwa.

Jamila ta karɓo musu kalacin koko,Harda na Muksfyyh dake kwance tamkar marar lafiya.

Tunda Mariya ta ambaci sunan Azkfyyh wani tsohon tabo ya taso mata.

Jamila ta miƙa wa Mariya kunun tana me umartata da ta tashi tasha.

Kawar da fuskarta gefe tayi.

Ta dubi Jamila tace.

''Don Allah a ina nake nan?
Cikin shesshekar kuka take maganar,idonta yai luhu,luhu,tsabar kuka.

Jamila ta sinnar da kanta ƙasa tace.

''Mama kisha kunun idan kin kammala zan miki bayani.

Kurɓa ɗaya tayi wa kunun da ƙyar ta haɗiye,ba sugar ko miskala zarratin.

''To ko gidan yari ne nan ɗin?
domin taji ana cewa abincin gidan yari ba daɗi.

to ai kuma gidan yari taga gandiro ba,amma nan bata ga alamar gandiroba ko ɗaya ba.

Wata ajiyar zuciya ta saki me ɗaci.
.Ta gangaro izuwa katifar Mukshfyyh,wacce ta tsunduma tunani.

Mukashiffyh na kwance ji tayi kawai.An kamo hannunta.

''Mariya tace.

''Yarinya Don Allah ki sanar min a ina nake ita waccen taƙi ta faɗa min gaskiya.

Ta faɗa tana duban Jamila wacce ta zage tana shan kununta.

Kamo hannuta Mksffy tayi,bata san sa'arda hawaye ya wanke mata

4 / 7