Author : Category : Romance
faɗa haɗe da zaro ido.
''Me kika dawo yi?
Maza kibar gidannan.
Ta faɗa tana duban Mariya Murya ƙasa,ƙasa.
Haj.Nazo muku da labarin inda Mal.Da Azkfyy suke,muddin zaku bani kuɗin.
Wa'inne kuɗi Haj.Ta faɗa?
millon 10ɗin ko.
''Ke ki rufa wa kanki asiri maza kibar gidanan.......
Taje ina?
Alh.Bashir dake saukowa daga saman upstair ya faɗa fuskarsa a turɓune.
Dariya ya kwashe da ita kafin yace.
''Wannan shine tsuntsu daga sama gasassshe.
''Babu inda zata.
Keeee! Ina sauran?
ya faɗa haɗe da zaro ido.
''Dama-dama,labarin da nazo baka kenan.
''Wanne labari? ai kece labarin tunda kinzo hannu bara a fara garƙame ki in yaso sauran kin bayyana inda suke.
Ja da baya Mariya ta soma yi tana faɗar.
''Kamar ya,Azkfyyh bani ce na haifeta ba,kuma bani na sata aikata abinda tayi ba.
Ko Allah baya kama laifin wani da wani.
Kuma kaima kafi kowa sanin yaya muke da Azkfyyh.
Ita kanta bata san waccece ita ba sai kwanannan da munafiki Mal.Kabir ya bata labari,kuma tace sai ta ɗauki fansa akanka,da kuma ɗan'uwanka Sarki Safwan.
Ni dama labari nazo isarwa domin ance ka saka kimanin milyan ɗari ga duk wanda ya kawo labarinta ko na Mal.Kabir.
Don haka kayi gaggawar gano shegiyar yarinyar nan Azkfh.
domin da ita da Mal.Kabir babban burinsu shine su tona maka asiri.
Kuma wai an gano Mahaifin ita Azkfyyr Sarki Abdullahi yana a raye da akwai aljanin dake kawo rahoto.
Ni yanzu kazo muje na nuna maka inda suke,a kamo su sai ka bani millon10 ta na kama gaba na.
hhhhhhhhhhhh!!!!
Alh.Bashir ya kwashe da dariya tare da duban Mariya a ƙasƙance.
Yace.
''Ke! wawiyar ƙauye,wama kike da suna?
''Yanzu duk danginku,waye ke da 1millon ma,bare 10millon?
Cikin mamaki Mariya ke dubansa izuwa yanzun jikinta ya soma rawa.
''Ke yanzu tsawon rayuwarki a ƙauyenku kin taɓa ido biyu da 100k?
"Shiru Mariya tayi tamƙar ta zubo fitsari a wando.
''Amsa zaki bani,domin ni bani tambaya ayi banza dani.
''Aa ta faɗa tana girgiza kai,tamkar wata kaɗangaruwa.
Dariya ya kwashe da ita.
Yakai kimanin minti 5 yana dariya kafin yace.
''Saike mayyar kuɗi kucakar ƙauye za'a ɗauki 10millon a baki jakar ƙauye irin talauci gaki mayyar kuɗi ko?
''To ki ma ajiye milyan goma ina?
''To bara kiji,yanzu ba sai anjima ba zaki ,tashi muje ki nuna min inda Mal.Kabir yske da kuma Azkfyyh.Kuma ƙwandala ba za'a baki ba.
''Kina tunanin ni Alh.Bashir zan ƙirgi naira ɗaiɗai har millon goma na baiwa baƙauya irinki?
To ki farka daga barcin da kike.
Mariya tayi shiru ta maƙure a kusurwar ɗaki.
phone ɗinsa ya fito daga aljihu ya ɗanna lambar dsp.
Ina so a zomin da motar ƴansanda da kuma bataliyar sojoji.
Mariya dake matse da fitsari ta ƙarasa sako shi ji kake zuuuu!!!
20minute sojoji da ƴansanda sun kewaye gidan baki ɗaya.
koda Mariya taji kuwwa motocin hannu ta ɗora akai tana faɗar.
''Wayyo na shiga uku!!!
Na bani na lalace,ni Mariya.
"Haj.ki saka Baki ki tuna irin zaman amanar da mukayi.
Ki saka Baki yabarni in tafi k'auyenmu.
"Na tuba nabi Allah!!!
Alh.Bashir ya daka mata tsawa yace.
''Ko kakar Hajiya zata zo bata isa ta hanani in yarda naga dama dake ba.
Don haka yau babu me ƙwatarki.
WATA RANA DA DADDARE.
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page page7-8.
Mariya taci kuka har ta gode Allah idonta duk ya ɗashe.
To gadai Mariya a mota zata je ta nuna Azkfyyh da Mal.Kabir.
To Abin har yakai ta soma nadama,dama kwaɗayi da buri yaja mata gashi ta hau motar kwaɗayi ta afka tashar wulaƙanci.
Gashi bata ga tsuntsu bata ga tarko.
Yanzu idan ta faɗi inda Mal.Kabir da Azkfyyh suke aka kamo su ita ina zata?
"Waye zai ci gaba da ciyar da ita
Tunda dai maƙudan kuɗin basu samu ba?
(To ga dai ƴartunubu ana yi kowa ya zama marowac🤣🤣)
tasan ko ƙauyensu ta koma tuwo ma sai ya gagareta.
"Wayyo!!! ni Allah,ni Mariya na jefa kaina a wahala.
Shi yasa ake cewa idan zaka Gina raminmugunta ka gina daidai kai.'
To ita dai ta gina ƙatoto gashi ya afka da ita.
Sai yanzu tai nadamar gaskiya,domin wannan tarkon ba kowa taso ɗanawa shi ba face Azkfyyh.Ashe da ita zai faɗa.
Fashewa tayi da matsanancin kuka me cin rai.
Wani ɗansan da ya daka mata tsawa me razanarwa.
Jikin ta ya soma rawa kef,kef.
****
La'asar liƙis suka isa ƙauyen.
Koda isarsu daf,da ƙauyen musulman da ke ciki suka tsaya sukayi sallah ita kam babu wanda ya damu da rashin yin sallarta.
Koda isarsu ƙauyen da ƴamma liƙis suka isa,motar tayi parking.
Koda tsayuwar mota caaa!!!
Su kayi kan Mariya sun tasa ta a gaba suje ta nuna gidan.
Sumi,sumi kaman tsohuwar munafuka haka tayi gaba suna biye da ita.
har zuwa har zuwa ɗan lungun da gidan yake.
To sai me? duk yadda Mariya ke ƙoƙarin nuna gidan abu ya gagara.
Wayam sunan wani waishi Hassan wayam.
Sudai fili fetal idonsu ke nuna musu.
Daga Mariya sai jam'an tsaro a wajen,domin mutanen garin duk sun gudu,azatonsu kiddinapes ne,domin su suka addabi garin.
Ki nuna mana gidan,Mariya ta goge idonta wai ko cutar makanta ta sameta?
Amma ina haka ɗin dai idonta ke nuna mata.
Ada tabbas taga gidan amma a halin yanzu ita ma taga wayam ɗin.
''Ke duk cikin mu waye abokin ki,ƙauye fa muke ba birni ba balle kice wai kin manta gida.
Ki nuna mana gida ko kuma a yanzu mu chanza miki kamanni.
Kinzo kin ajiye mu anan muna neman gida amma kin nuna mana feli,to cikin mu waye ƙaramin yaro?
Wani fusataccen soja yazo ya hankaɗe kan Mariya yace.
''Ke wai ko kina da taɓin hankali?
girgiza kai tayi ta
"To wallahi bara kije idan baki wuce mun tafi ba sai na bazar dake anan.
kuma sai na mayar dake gari.
Hannu yasa ya sharara mata mari saboda da zafin da yaji na ɓata musu lokaci da tayi.
''Yanzu haka ma ba nan ne garin ba,domin duk wanda ya rayu a katafaren gida irin na Alh.Bashir bazai iya rayuwa a ƙurƙutun ƙauye irin wannan ba.
Rantse -rantse ta soma yi.
Tace.
''Wallahi idan baku yarda dani ba mije ga me gari domin yasan da zaman mu a ƙauyen.
''Muje wajen me garin.
Tinƙis-tinƙis suna biye da ita har gidan me gari.
Koda isarsu jani'an ne ke tambayar.
''Ko yasan Mal.Kabir,tare da wata budurwa Azkffiyh?
(ni kaina ƴar mutan katsinawa nayi mamakin amsar da me garin ya basu.)
Mal.Kabir kuma?
A gaskiya nan garin ba Mal.Kabir mutum ɗaya ne kuma haifaffen garin ne,kuma kaf yaransa bame suna Azkfyyh.
''Ni banma taɓa jin suna irin haka ba.
To ko za'a kira mana su?
Me zai Hana me gari ya dad'a.
****************
**DOKAR DAJI**
Koda ƙarasowar Muhijjinatu bata tsaya wata,wata ba taje daidai inda bishir nan take ƴar guntuwa inda baƙin aljani ya kwatanta mata.
Sannu a hankali ta soma tonewa.
A hankali har ta zaƙulo ƙullin baƙar leda.
Koda ta zaƙulo sai ta mayar da ƙasa ta rufe.
Tasa dutsen inda yake.
Da rana tsakiya Abbu ya dawo.
Da kafaƙin wata ƙatuwar dabbar daji.
Yana tafiya yana nishi.
Ya zauna cikin nishaɗi fira suke sosai.
sai da ya hura wuta gadan-gadan ya miƙe da nufin tafiya yaje ɗauko wuƙa.
Ta jefa wannan ƙullin cikin wuta.(tirƙash!)
Sunci sun ƙoshi.
Suna nan zaune ita da Abbu barci yai awon gaba dasu.
A cikin barcin Muhijjinatu ta soma miyagũn mafarkai.
Na baƙaƙen aljanu.
Cikin mafarki taji baƙin aljani yace.
''Muddin tabi sharaɗinsu zasu taimaketa.
Sannan idan ta farka zata ga hota.
To ta busa wa mahaifinta hodar zai ta yin barci har su gama aiwatar da nufinsu.
Kuma zata ɗau fansa.
Firgigit ta farka idonta yai mata tozali da hodar.
A hankali ta ɗauki hodar ta soma busa mishi sannu a hankali.
Dama barci yake haiƙan.
Wannan hoda ita tasa barcin Abbu ya daɗa tsananta.
Koda shuɗewar wasu mintoci .
Baƙin aljani ya bayyana cikin wata muguwar kama me razanarwa.
''Kin amince zaki yi biyayyah.
''Eh na Amince.
Muhijjinatu ta faɗa.
a ranta sai ta soma tunanin anya tayi wa Abbu adalci kuwa?
Shekara da dama bawon Allah yana ɗawainiya da ita.
yace karta biye ma baƙin aljani amma ta bijeri mishi.
anya tayi mishi adalci kuwa?
''To amma kuma shi Abbu yaƙi yin yadda zaiyi ya ɗauki fansar akan Safwan da Alh.Bashir.
Abbu sai dai kayi haƙuri,amma tabbas sai na kawo ƙarshen Safwan da Alh.Bashir........
Rufe idonki.Baƙin aljani ya katse mata tunaninta.
tofa ita dai Muhijjinatu ta buɗe idonta a wajen da bata taɓa zowa ba tun wanzuwarta A DOKAR DAJI.
Karfe 10 insha Allah zamu Kara posting jiya na Bata lokaci wajen gyaran whatapp .
WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page page 9-10.
**Masu buƙatar farkon book 2 da kuma* ƙarshe wato book 4.*
*400ne kacal.*
*A wannan Accout ɗin.*
*Aisha Abdullahi fcmb.*
wannan page na turo shi domin ciyar wasu bayin Allah da suka turo min kuɗin novel jiya whatapps ɗina ya samu matsala.Idan kunga wannan page kuyi min magana sai na saku paid group.
don Allah masu biya akan in turo musu ci gaban lavari da hausa ba nake rubutun nan book 1 ne free.
Bata taɓa tozali da wuri irn wannan ba tin wanzuwarta A DOKAR DAJI.
Waige waige Muhijjinatu ta soma yi tamkar baƙauye yaje birni.
Wajen dai ya kasance komai nasa baƙi ne,komai dake cikin wajen.
A hankali ta ɗaga kanta sama ko ina kan ƙwarangwal ɗin mutane ne birjiki.
Ɓangare ɗaya kuwa wasu mutane ne gasunan suna ta yiwa wata ƙatuwar BAƘAR HALITTA sujada.
Baƙa mummunar gaske.
Muhijjinatu ta zuba musu ido.
Yaune karon farko da taga kalar halitta tata da ta Abbu.
Ashe dama akwai kalarsu?.....
Dube-dube ta Soma yi wai ko taga BAƘIN ALJANI ta tambayeshi dama akwai me kama da ita ita da Abbunta?
Dariyar da aka kece da ita,ita tasa Muhijjinatu waige-waige domin ganin me dariyar.
''Lale-lale da ƴar Sarki me jiran ɗaukar fansa.
Taji wata murya ta faɗa...........
Koda ta kalle me maganar sai taga mutane ne bila adadin sunata zagaye ta.
Suna dariya hhhhhhhhhhhh!!!
Koda Muhijjinatu taji an kirata da ƳARSARKI me jiran ɗaukar fansa,sai wani mugun farin ciki ya ziyarci dukkanin wata gaɓa dake jikinta,sai ta ƙara gaskata baƙin aljani.
Cikin ranta tace.
''Hakanan Abbu yaƙi yarda da baƙin aljani.
Ashe baƙin aljani taimakon mu zaiyi?
Ashe ba cutar da mu zaiyi ba haka nan Abbu yaƙi Amanna dashi.
Tabbass idan na ɗauki fansa zan birge Abbu.
Ta faɗa cikin tsabar farin ciki.......
''Duƙa kiyi wa DODO SUJADA ya sa miki Albarka.
Cikin zumuɗi ta ɗurkusa tayi sujada tamkar yadda taga sauran sunyi mishi.
(Allah sarki Muhijjinatu baiwar Allah)
Koda ɗagowarta daga sujadar taji an fashe da dariya.......
Gabanta yai wata ƙara daram!!!
domin irin murya ABBU TAJI.
koda juyowarta domin ganin me dariyar Da baya da baya ta soma ja domin tsantsar kamar da ta hango jikin sarki SAFWAN TAMƘAR ABBUNTA.
Banbancin Abbunta fari ne tass shi kuma SARKI SAFWAN BAƘI NE.
''Yammata yaya sunanki?
''Muhijjinatu!!!
Ta faɗa jikinta duk yai sanyi.
Wata muguwar dariya ya kwashe da ita yace.
''Idan na chanka daidai sunanku,da za'a rubuta a jikin ƙofar nan ya kasance.
''MUHIJJINATUL-MUKASSHIFIYHA...AZKAFIYYAH HAIDAR.
''Tabbas yanzu na gano sirrin.
"Ina Abdullah?
Ya fad'a tare da zuba mata ido.
''Waye haka?
"Mahaifinki.
"Abbu na?"
"Eh.
"Yana Nan.
"Hhhhhhhhhh!!!
''Kinsan koni ɗin waye?
A'aa.
"Sunana SARKI SAFWAN,kuma ni ɗan'uwan mahaifinki ne,uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya....
''Ke jahila ce ta cikin DOKAR DAJI.
bakisan komai ba banda dabbobi da tsuntsaye,haka zalika bakisan masoyi ba balle maƙiyi,baki gane fari balle baƙi.
Keda namun DAJI.banbancin ku kaɗan ne ke ƴar Adam ce,su kuma dabbobin DAJI Ne.
saboda haka yanzu zan sanar miki daƙiƙanci da kuma wautarki ta DABBAR DAJI.
''Shi mahaifinki yasan gaskiya shi yasa ya hanaki bin baƙin aljani,da yake shi hankalin rayuwar da yai cikin gari na ɗibansa.
Ke kuma kin kasance RAINON DAJI CE ke.
To a taƙaice da baƙin aljani yaudarki yayi.
Bari kiji taƙaitaccen labarin.
Da farko dai ''Baƙin aljani ya sami labarin Abdullahi be mutu ba.
Shi yasa amma Mallam Abdurrah na shirin taimakonku shi yasa yaje yakai ƙarar Mallam Abdurrahmn wajen Mahaifiyarshi.
ita kuma ta dakatar dashi daga taimakonku.
to ya tura ɗanshi ƙasar saudiyyah a domin nemo ilimin karya mugun sihiri da tsafi.
To kafin ya dawo muke so ke mu yaudareki,tunda shi mun kasa galaba akanshi.
Don haka ki sani cewa ke da kanki zamu
sarrafaki,da hannunki zaki kashe mahaifinki.
Wannan sujada da ki kayi wa DODIN TSAFIN MU duk tana cikin sharuɗɗan aikin.
****** *******
Wani ɗansanda ya dubi me gari yace.
''To ko za'a kira mana sh?
me zai hana me gari ya faɗa
jim kaɗan aka zo da Mal.Kabir.
Mai gari ya dubi Mariya ya dubi Mal.Kabir ɗin da aka kira,wanda yai tsuru,tsuru bawan Allah kunsan baƙauye da tsoron ɗan sanda.
Sai da Mai gari ya ya kwantar
mishi da hankali.
Yace ya kwantar da hankalinshi.
''Babu abinda zai faru.
''Mai gari ya dubi Mariya
''Wannan shine?
Girgiza kai tayi idonta shaɓe-shaɓe da hawaye.
Mai gari ya dubi Mal.Kabir yace.
Zaka iya tafiya.
Jikinsa na ƙyarma yabar wajen.
Mariya ta fashe da kuka ta dubi maigari.
Tace.
''Mai gari kaine fa nemar mana gidan da zamu zauna nida shi ka fa tuna.
Mai gari yai jim yana san tuna wani abu amma ya manta.
komin yai yunƙurin tuna wani abu zuciysrsa tamkar ansa sarƙa an ɗaure ta.
koda taga me gari yai shiru ta ɗora hannu aka ta ƙurma ihu tana faɗar.
''Nashiga uku!!! ni Mariya.
Gulma da kwaɗayi ya ja min bala'i da musifa.
To tinda ba Zaki fad'a ba yanzu sai ki tashi mu koma.
Keeeey!!! suka jata tamkar akuya.
Mai gari yana tambayarsu yaya akayi amma ina sunyi nisa basa jin kira.
Koda aka kira Alh.Bashir cewa yai azo mishi da ita domin in taji wuya a wajensa ta faɗi gaskiya.
Ta ɓangaren me gari sai da suka riga suka tafi ya tuna da Mal.Kabir baƙo.
To amma kuma zuciysrsa ta nan na ɗe ba zai iya kiran Mal.Kabir ɗin ba.
kuma ya tuna shike da ƴa Azkfyyh.
Malamar Islamiyyah.
**********
Baiwar Allah Mariya har ta bani tausayi.
Tayi nadama tayi nadama.
Wani ƙeɓantaccen ɗaki Alh.Bashir ya kaita.
Ya ajiye.
Azaba ta gidan duniya gana mata ake.
Lambar SARKI SAFWAN ya latsa da nufin kiransa.
amma wayar a kashe take.
***WATA RANA DA DADDARE (horrow story)**
**MUHIJNATU**
Tunda na mallaki sunanki na riga na zama me kuɗin duk duniya.Hhhhhhhhhh!!!.
Zaro ido tayi tare da mamakin wai yau gata ga Sarki Safwan.
dubansa tayi tace.
''To ya akayi shi baƙin aljanin ya kasa faɗa maka sunana alhali ya sani?
Dariya ya kuma kwashewa yace.
''Shi baƙin aljani ke duka Aljanu ma,halitta ce me muguwar mantuwa.Duk lokacin da yaje DOKAR DAJI.
To da ya ɗauko sunanki kafin yazo nan BAƘAR FADA. ya manta....
To kai a ina masarautarka take?
Dariya dai ya kuma kwashewa da ita.
Yace.
''To ko Abdullahi zaki faɗawa yazo ya ƙwace sarautarsa.
Girgiza kai Muhijjinatu tayi tace.
''Aa Abbu ba zai iya rayuwa anan ba.Abbu ya haƙura da duk wani jin daɗin duniya.
Muhijjinatu ta juyo wajen baƙin aljani.
Tace.
''Na roƙe ka ka mayar dani wajen Abbu tunda ba zaka iya taimako na ba.
Ba tareda baƙin aljani ya bata amsa ba.
Sarki Safwan ya dubeta yace.
''Har kin haƙura da ɗaukar fansar?...
"Ke yanzu ƙanƙanuwa dake,har kina da hikimar ɗaukar fansa akaina?
to taho ki ɗauki fansar.
''Ashe dai Abdullahi.
Na kashe maciji ne ban sare mishi kai ba.
''To yarinya munyi amfani dake ne a matsayin karen farauta.
Dama mun ɗauko ki a domin sanin sunanki.
''To amma bara kiji wani abu da baki sani ba munsan sirrin password.
Ɗin da ake nema.
Don haka ki sani Ke ce zaki kashe mahaifinki da hannunki,sannan kema in kashe ki,in kashe Haidar.Duk wani ɗigon jinin Abdullahi,sai ya ƙare a DORON DUNIYA.
''Ke so nake mai wanda
yasan Abdullahi ma ya ɓace a duniya sai tarihinsa ya shuɗe.
Muhijjinatu tace.
Abbu yace akwai ubangijin musulunci kuma baya barci kuma yana kallo.
Kuma baya barin Azzalumai irnka.
''To wai me Abbu yai maka ka kassara mishi rayuwa.
''Ke rufe min baki baki kai matsayin da zan tsaya baki amsa ba...
Abinda dai zan sanar miki shine.
''Daga yau zaki zama BAƘAR SHEƊANIYA.....Kuma HORANYA............
Baƙin aljani.Aljani taho ka soma aiki.
Muhijjinatu bata anƙara ba.
BAƘAR GUGUWA ta rufe mata idanuwa ruf.
Bata ganin komai,tara-tara ta dinga ganin komai ya koma mata tamkar wacce tasha giya....
tara-tara ta dinga ganin komai.
''Shin suma tayi koko?
Dariyar baƙin aljani ta garame BAƘAR FADA gaba ɗaya.
Baƙin aljani ya dubi Sarki Safwan yace.
''Ka daɗe kana ƙin yarda da maganata da nace ma Abdullahi na nan a raye to gaka ga ƴarsa da aka haifa cikin DAJI.
Ya nuna Muhijjinatu dake kwance tamkar gawa.
Na sanar maka tin ranar da yabar gida naci gaba da bibiyarsa.
Sarki Safwan yace.
''Ayi min afuwa.
Dariya baƙin aljani yai kana yace yanzu shirin mu zai soma.
*****
Tsaye suke suna zagayenta da ƙwarya da layu a dukkanin hannayensu.
Hannayenta gaba ɗaya suka tsartsarga suna dinga cusa baƙaƙƙen layu.Kana aka ɗinke.
Sannan aka dinga kwarara mata jini a jiki.Suna wasu kalar surutai.
Zaɓal-zaɓal jikin DODO ya dinga yi...
Yana aman gulamar jini.
Baƙin aljani ya dubi Sarki Safwan yace.
''Ankammala komai.
''Wannan yarinya sai ta kashe ubanta da
hannunta kuma zata riƙa tafiya bisa sarrafawata.
Dariya suka kwashe gaba ɗaya...
Kana Safwan. ya zubawa Muhijjinatu ido.
Wacce numfashi kaɗai ke yawo a jikinta.
***DOKAR DAJI**
Ɓangaren Abbu kuwa yanata barci,barcin asara koda farkawarsa firgice ya farka,yai mamakin iya tsawon lukutan da suka kwashe suna wannan mugun barci shida Muhijjinatu.
Ɓangaren muhijjinatu ya waiga yaga barci take haiƙan.
Jijjigata ya soma yi,amma ko motsi bata yi.
''Muhijjinatu. Muhijjinatu.
Ya soma kiranta.
Duk jijjigar da yake mata bata motsi amma kuma tana numfashi...
Tayi sandar-dar tamkar gawa.
Duk da cewa tsakiyar DARE ne yaso ta tashi,amma dole ya ƙyaleta.
******
Washe gari da safe,kuwa har rana ta fito
Muhijjinatu bata motsi.
Hankalin Abbu ya dugunzuma sosai.
Ga wani mugun zafi da jikinta yai.
DAJI ya kusa ya sassaƙo itaciya yazo ya zafka.
Har yau dai idonta a rufe yake bata motsi.
Rungume ta yai ya soma bata a baki,amma kuma bakin kulle yake gam.
Kuma maganin baya shiga a bakinta.
Zama yai ya zuba uban tagumi,hankalinsa yakai ƙololuwar tashi.
''Shin meke damun Muhijjinatu?
to wasa wasa ƙaramar magana ta zama babba.
yau kwanan Muhijjinatu uku kenan a kwance.
Idan ka dubi Abbu yanzu ba zaka gane shi ba,domim kamanninsa sun ɓace bat.
Saboda muguwar rama.Abinka da bafullatani.
Abu dai har sati ɗaya kullum jiya iyau.
Duk sassaƙen da yake sassaƙowa a banza.
WATA RANA ya tafi sassaƙo wata itaciyar da yake saka ran Muddin Muhijjinatu tasha to kowacce cuta ce zata rabu da ita.
Koda ya dawo tarar da ita yai samɓal.
ta mimmiƙe.Idanuwanta sunyi tsaye komai dai irn na gawa.
Hatta numfashin babu a tattare da ita komai ya tsaya cak ya daina aiki a jikinta.
Koda ya ƙare mata kallo bata da banbaci da lokacin da yaga gawar mahaifiyarta.
Wata kalar razanniyar ƙara Abbu ya fashe da ita yace.
''Wayyo Allah na.
Tinda kika mutu Muhijjinatu nima zan mutu!!!
zan kashe kaina na gaji-da duniya.
Ahalin yanzu banda kowa banda komai,komai ya ƙare min dole nima na kashe kaina banga abinda zanyi A duniyar nan ba.
mu haɗu a nex page.
**Masu buƙatar farkon book 2 da kuma* ƙarshe wato book 4.*
*400ne kacal.*
*A wannan Accout ɗin.*
*Aisha Abdullahi fcmb.*
wannan page na turo shi domin ciyar wasu bayin Allah da suka turo min kuɗin novel jiya whatapps ɗina ya samu matsala.Idan kunga wannan page kuyi min magana sai na saku paid group.
don Allah masu biya akan in turo musu ci gaban lavari da hausa ba