WATA RANA DA DADDARE BOOK 2 BY Aishat Falalu Rimin K'aura

Author :  Category :  Romance

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 18.3K words

nake rubutun nan book 1 ne free.




WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)


The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 11-12.̄


Kuka Abbu ya fashe dashi sosai.

Babu inda sautin kukan nasa baije ba.

Abin tausayi,ya kifa kanshi akan gawar Muhijjinatu.

Sambatu kurum yake wata maganar ma bai san lokacin da yake furta ta ba.

(bawon Allah).

''Me zan tsinta a wannan duniyar?

''Na rasa yara na guda uku da na fara mallaka a duniya.

na haƙura har na saba da rashinsu,nazo na gina sabuwar rayuwa da Gimbiya Binta.

Na rasa Matata Gimbiya Binta.

''Na haƙura na sake gina sabuwar rayuwa da ƴata Muhijjinatu.

Ita ɗin ta kasance ita ce duk wani jin daɗina a wannan duniyar.

Muhijjinatu ce farin ciki na !!!

ita nike kallo a matsayin sanyin idaniyata.


''To MUHIJJINATU TA MUTU!!!

"Yanzu meye ya rage min a wannan duniyar?

''Da me zanji?


''Zan kashe kaina,zan kashe kai na tunda kika mutu Muhjinatu.

''Yanzu shikenan ni kaɗai zan cigaba da rayuwa?


''Ina bazan iya rayuwa babu keba Muhijjinatu.

Bazan iya gina rami ina kallo in saka ki ba al-ahalin ni gani a raye.........




''Hhhhhhhhhhhh!!!

Dariyar baƙin aljani.

Cikin razana Abbu ya ɗago ya dubi baƙin aljani.

''Taya baƙin aljani ya iya shigowa nan?
Tabbas sai yanzu ya yarda Sarki Safwan ne ya turo aka kashe mishi ƴarshi Muhijjinatu.

Domin dai baƙin aljani bazai iya shigowa nan ba.

Abbu ya daure ya dube shi yace
''Me ya kawo ka nan,taya har ka iya shigowa nan wajen?

bakin aljani bai ba Abbu amsa ba illah cewa da yai nazo na taimake ka akan yarka Muhijjinatu,wacce Safwan ya kashe.

Dariyar bakin al-jani ta katse sa,ɗagowa yai ya zubawa bakin al-jani ido kana yace.

''Meye ya kawo ka wajena,kunyi silar rabani da dukkan farin cikin rayuwa ta,na haƙura da duk wani jin daɗi banda kowa banda komai sai Muhijjinatu to ita ma ɗin kun kashe min ita.Yanzu ni kaɗai na rage banda kowa banda komai to ku kashe ni nima.

Muddin baku kashe ni ba ni zan kashe kaina.

Baƙin al-jani yace ''Ba cutar da kai nazo yi ba,nazo a domin na taimaka maka,domin Sarki Safwan yaci amana ta shi yasa nake so na rama,na duba naga babu ta hanyar da zan rama sai na ga ta hanyar ka kaɗai ne,nazo na taimake ka akan ƴarka Muhijjinatu da Safwan ya kashe.

''Kai munafuki ne bazan yarda da kai ba.


Baƙin al-jani ya fashe da kuka sosai,yana duban Abbu.

Yace Abdullahi ka yarda dani,

a wannan karon nazo ne a domin na taimakeka.

Abbu yace tayaya?


Baƙin aljani yace Muddin ka yarda da sharaɗina to ni kuma zan taimake ka.

Zuciyar Abbu ta soma tafarfasa ya duba yaga Muhijjinatu rungume a matsayin gawa to me zaiyi,baya ga ya yarda kawai.

Gara ma komai zai faru ya faru,idonsa ya rufe zuciyarsa ta soma tafarfasa.

Tabbas Safwan shine ya kashe Muhijjinatu,domin koda tazo mutuwa sunanshi ta ambata.

Ya kasheta ya kashe mahaifiyarta shi kaɗai ya rage a wannan duniyar....

Muhijjinatu ta mutu!"

kodai mafarkine.


Meye sharaɗin.?


ya faɗa tare da duban baƙin aljani.


**********

**MARIYA.**

Baiwar Allah ta bani tausayi sosai.

Alh.Bashir ya sake latsa lambar Sarki Safwan.

Wannan karon wayar ta shiga.

ɗan takaitaccen bayani yai mishi game da Mariya.

Do da yake da akwai wata laya ta ɓata,wacce aka sarrafa da mugun surƙullen tsafi.

Ita ce Sarki Safwan ya latsa.

Koda ya latsa,a take ya bayyana.

Gidan Alh.Bashir kuma a ɗakin da ya tsare Mariya.

A ruɗe Sarki Safwan ke duban Alh.Bashir yace.

''Kasan Abdullahi yana raye kuwa?

Zaro ido Alh.Bashir yai yace.
''What?

"Abdullahi na raye kuma?

''Kai inposible ne wallahi.

Sarki Safwan yace.

''To da kaina na gani,domin hatta ƴarsa ma na gani da ido na wacce aka tafi da cikinta.I hope understang.

''No,no,Alh.Bashir ke faɗa.

tare da dafe head ɗinsa ya dubi.

Sarki Safwan yace fahintar dani.

Sarki Safwan ya kwashe labarin Muhijjinatu,kaf ya bashi.

Alh.Bashir yace.
''Me yasa kuka ƙyaleta?
Aida kun kasheta a take.

dariya Sarki Safwan yai yace.

''Daɗina da kai kai soko ne har yau.

''Idan mun kasheta ai zai gudu sai dai .............

Dariya Alh.Bashir ya kwashe da ita kana yace.

''Kana nufin ita zata kashe mahaifinta da hannunta?

Gyada kai Sarki SAFWAN yai.

Wannan shine aikin mu.

''Alh.Bashir ya nuna Mariya wacce tai ligif saboda wahala.

Yace gata nan.

Dariya Sarki Safwan yai tare da zuwa kusa da Mariya ya dafata.

Mariya bata kuma sanin ina take ba.

Ta farka ta ganta cikin BAƘIN UNIPOAM.
tare da wasu mutane daban-daban da bata san su waye ba.



**DOKAR DAJI**

ABBU ya dubi Bakin aljani,ya kuma dubi gawar Muhijjinatu.

Tabbas ba tantama Sarki Safwan shi ya kasheta.

Domin da tazo mutuwa shi ta ambata.

Inkwai haka ne.
Babu ta inda Safwan bai kassara rayuwarsa ba.

''Safwan me nayi maka?

ya faɗa da ƙarfi.

Kifa kanshi yai jikinta.

Kuka me ɗaci,me raɗaɗi me ƙuna.
Kai duk wanda yaga Abbun dole ya tausaya mishi.

runtse idonsa yai tare da cizon leɓensa wai ko zai farka daga Mummunar mafarki.

Amma koda ya buɗe ido Muhijjinatunsa ce dai kwance,a matsayin matacciya.

'bakin aljani ya matsa gaf dashi yace.

''Abdullahi,idan ka aminta da wannan taimakon da zanma to,idan baka aminta ba,zan kama gaba na,ni kaɗai na rage wanda zaka ji motsina,idan baka amince ba zan tafi,kuma bazaka ƙara gani na ba har abada.


Abbu ya ɗago ido share -share da hawaye yace.

''Ka tabbatar baka tare da Safwan?

baƙin Aljani yace.

''Mun daɗe da rabuwa da Safwan tinda ya karya mana alƙawari.

Abbu yace.

To na amince da dukkan sharaɗinka,illah ɗaya baazn iya yiwaDODO SUJADA BA.

Baƙin aljaani yace.

''Ka tuna cewa ada kai SARKINE me cikakken iko kana rayuwa da matarka da ƴaƴanka cikin farin ciki.

Amma rana ɗaya Safwan ya datse wannan farin ciki ya kassara rayuwarka A DOKAR DAJI.
Ka tuna cewa ada har ka haƙura da farin ciki ka zaɓi zama da Muhijjinatu.

To ita ma an bibiyeta an kasheta.
Yanzu babu abinda ya rage maka face ɗaukar fansa...

Ka ɗauki fansa akan Safwan idan ka ƙyaleshi yaci bulus kenan.


saboda ɗan durƙushin da zakayi wa DODO ya baka nasara shine ba zakayi ba?


Zuciyarsa ta shiga kokonta.

Abbu ya dubi baƙin aljani.

Yace ''Taya ka iya shigowa anan alhali akwai kariya a wajen wacce duk wani baƙin sheɗani bazai iya ƙetareta ba?


baƙin aljani yace''A yanzu ni ba sheɗani bane shi yasa kaga na iya ƙetarowa na shigo kasan cewa duk wani macuci bazai iya shiga ba,wannan ma alama ce da zaka gane ni ba macuci bane.

Abbu yace komai zanyi don in ɗau fansa akan Safwan amma bazan iya yiwa DODO SUJADA BA.

Cize baki bakin aljani yai yaga dai kar wannan dama ta suɓuce.

Ya dubi Abbu yace''Rufe idonka.

Da ƙarfi ya runtse idonsa.

Baƙin aljani ya shiga aikin hallakar da Abbun Muhijjinatu,'innalillahi wa'inna ilairraji'una.

Minti 5 ba'ayi ba da rufe idon Abby baƙin aljani ya dage yana ta jero tsafe-tsafe..........


Kwatsam!

Ba zato ba tsammani wata zazzakar murya ta hargitse wajen ta ruɗarda baƙin aljani ta zaburar dashi,ya rikice yA gigice.

''Auzubillahi minasshaiɗanirrajim.


''La i'la ha illah hu,wahdahu lashari kalahu,lahul mulku,walahul hamdu,wa huwa ala kulli shai'n kaɗir.

La haula wala ƙuwwata illah billahi la'la
la'ha illhahu wala naabu du illah iyyahu lahun ni'imatu walahul fadlu walahul sana'ul,hasanu la'ilaha 'illahu mukulisina lahuddina walau karihal kafiruna.

Allahu la'ila ha illahuwa Alhayyul-Qayyim-latakuzuhu-sunnatuw.
Wala na'um lahu ma fissama wati wama fil ardi manzallazi yash fa'u indahu illah
bi'zinihi ya'alamu ma baina audihim wama khalfahu-wala yuhiɗuna bi shai'in-min ilmihi illah bi masha'a wasi'a kursiyyu hussamawati walardi wala yu'udu hifzuhuma wahuwal aliyyul Azem...


Tangal-tangal bakin aljani ya soma yi
idonsa da fuskarsa suka jeme waje ɗaya.

Zafi,ƙuna azaba ta addabeshi,fuskarsa duk ta kwaye ta jeme waje ɗaya.

Wani irin ihu ya saki me Razanarwa

Kyakkyawan saurayi ya bayyana kyakkyawa tsaye ya zubawa Abbu ido.

Ɗurkusawa yai ya zubawa Abbu ido yace.

''Innalillahi wainnah ilaihirrajiuna,Allahumma ajirni fimusibati wa akhalifni kharan minha.

Duban Abbu yai yace.
''Ina iliminka,ka tuna kai hardataccen qur'ani ne.

''Shin ina tunaninka ya tafi,me zaisa ka biyewa sheɗani ya ɓatar maka da imaninka?

''Shin ka manta da tarihin annabi yunusa?

"Shin ka manta da tarihin annbi Yusuf?


''Yanzu da banzo ba shikenan kai ma ka hallaka,a bisa yaudarar da akayi maka,an tsorata ka da mutuwar Muhijjinatu,alhali Allah mai rayawa da kashewa bai ɗauki rayuwar Muhijjinatu ba,Muhijjinatu tananan a raye..........

Zaro ido Abbu yai.Ya cimimiye rigarsa.

Kana ya girgiza Muhijjinatu,yaga dai sandare take.

''Taya zaka ce bata mutu ba alhali duk alamun gawa sun tabbata a tare da ita?

"Sannan Kai waye.?

Murmushi yai yace.

"Sunana BILAL,BN ABDURRAHAM.

Wata zabura Abbu yai tare da miƙewa tsaye........


ku daure ku siya ayi tafiyar nan daku in kin shirya siya mu haɗu a pc.

Mun shiga book 3 a paid group.


Kuna ta haɗani da girman Allah book 2 to ga sadaka kadan dg bokk 2 in kin biya zan baki cigaba hade da 3-4 kar ki tsaya sister ki siya ki wuce wajen.

Mu haɗu a pc.Zamu gyara sister.

07049138863.

WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)


The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 13-14.


Wata iriyar zabura Abbu yai ya̧ce.

''BILAL!!!

''Don me zaka ce Muhijnatu bata mutu ba Alhali ba yau ne na soma ganin mutuwa ba.?


Bayan da ka kasance jini Mal.Abdurrahm da bazan taɓa yarda da kai ba.


''To kai ɗin ka kasance jinin mutanen kirki.

Murmushi Bilal yai kafin yace.

''Muhijjinatu bata mutu ba!

"Shiru Abbu yai,sai ya dubi gawarta kuma ya dubi Bilal.

Bilal ba ɗauki dogon lokaci ba ya kwashe dukkaninn labarin kaf,ya baiwa Abbu.

Da binciken da Muhijjinatu ta riƙa yi da zuwan da tai tayi har baƙin aljani ya yaudareta.

Kai ƙarshe dai Muhijjinatu,har Dodo tayiwa Sujada,kuma taga ɗan'uwanka Safwan.

Mu cire batun yiwa dodo sujada.

Domin dai ita Muhijjinatu.

bata san komai ba da ya shafi addini.

''To kaifa?

''Kuma ita tayi hakan ne a haukanta wai don ta samar muku da farin ciki ta ƙwatar muku yancinku.

To baya ga haka Muhijjinatu ta cire kafin da Abbana ya saka maganin sheɗanu.

To a yanzu halin da ake ciki shine.
''Ƙaƙule wannan kafin yasa suka ƙara jirkita maka tunani,aka ƙara ƙulla wani mugun asirin,mafarin kenan har zuciyarka ta karkata ka amince da baƙin aljani,tabbas da akwai wannan kariyar da hakan ba zai faru ba.


Dalilin da yasa nace maka ƴarka Muhijjinatu bata mutu ba shine.

Sunyi amfani da wani sinadarin tsafi.
Wanda ke ɗauke numfashin mutum na tsawon kwana ɗaya da yini ɗaya.

Abbu yai shiru ya zuba mishi ido ba tare da ya fahinci inda zancen nasa ya dosa ba.


sannan idan ta farka zata farka a haukace,to za suyi amfani da wannan damar wajen sarrafata ta yadda zata iya KASHE KA da hannuta,sannan daga baya suma su kasheta.

To yanzu karɓi wannan maganin.
Ingataccen ruwan zam-zam ne na saudiyyah.

da aka karanta surorin alƙur'ani a ciki.

Sannan sai wannan maganin maganin karya sihirine kafiyyen.

babban malami na ya bada na kawo maka,Insha Allah matsalarka Insha Allah da kayi amfani dashi,dukkanin sihirin dake jikinka zai warware a take,da izinin Allah.


''Tashi ka fara da Bissimillah.

Abbu ya karɓi maganin ya soma shan ruwan zam-zam mai ɗauke da adduo'i.

Kana ya sha maganin.

5minut da faruwan hakan wani fisgaggen barci ya sarƙe shi tamkar wanda yai maye.

Nan take ya bingire ya soma barci.

Ya kwashe kimanin minti ashirin ya farka da wani mugun aman jini,wanda da jini ya faɗo baƙaƙen layu zasu biyo baya,bawan Allah amai yake tamkar zai amaye ƴaƴan hanjinsa.

Nishi yake sosai ya galabaita iya galabaita.

An kwashe minti 10 yana wannan wahalar daga bisani ya ɓingire yana nishin wahala.

Sai da Shakh.Bilal ya tabbatar a yanzu ya ɗan samu relief.Ya matso kusa dashi yace.

''Yaya kake jin jikinka?
"Alhdullahi sai godiya ga Allah mai kowa mai komai wanda ya ƙagi ruhinA.

''Ambatar sunan Allah da Abbu yai yasa Bilal yaji wani mugun daɗi ya ziyArce shi.


ya ɗaga hannu yaiwa Allah godiya,domin komai da izinsa yake wanzuwa.

yana cikin tunanin yaji Abbu ya ɗaga hannu yana ta gidiya Ga Allah mahalliccin kowa.

Gora Shakh Bilal ya miƙa mishi yace.
''Je kayo Alwala.

Lokacin da tsugunna yana Alwala kuka ya fashe dashi,domin rabon da yaga yai alwala a rayuwarsa tun kafin wannan MUMMUNAR ƘADDARAR ta faru dashi.

Sai da Bilal ya kamo shi ya riƙesa yaCe.
''Kayi haƙuri tabbas asiri gaskiya ne ga mai yinsa domin yaci annabi s.A.W.
Ka sani wannan Al-amarin an rubuta maka shi cikin littafin ƙaddarar ka.


shimfiɗa mishi sallaya.Sannan yace.

''Kayi sallah raka'a biyu ka gode wa Allah.


Lokacin da ya zauna ya dinga rere karatun Alqur'ani shi kansa mamaki yake.

''Anya shine?


To ni ma Maman Humaira banga abin mamaki ga ikon me sama'u da ya ƙagi cuta kuma ya sanyo maganinta.
domin shine me kowa me komai.

bayan salamce sallar ya fara da yiwa Annabi salati,yai istigifari,yaiwa Gimbiya Binta Addu'a.
Allah ya jiƙanta da rahma.

(Ya Allah ya jiƙan humairata da rahma.Allah ya haɗa fuskokin mu gidan Aljannah.Har yau ina kewarki My dauther😭😭😭😭)


Hannuwa ya ɗora ga abinda yake cewa.

*''Tsarki ya tabbata a gareka ya* *Allah.tare da yabo a gareka,Albarkatun* sunanka sun *yawaita.*
*Mulkinka da girmanka sun ɗaukaka*
*babu abin bautamawa da gaskiya sai kai*

*Na juya fuskata ga wanda ya ƙagi halittar sammai da ƙassai*

*ina me karkata ga addini na na gaskiya*
*Kuma ni bana daga cikin mushirikai*
*lallai sallata da rayuwata da mutuwata na Allah ne,ubangijin talikai.*
*babu abokin tarayyah a gare shi*
*kuma da wannan aka umarce ni kuma ni ina daga cikin musulmai*
*Ya Allah kai ne sarki babu abin bautamawa da gaskiya sai kai.*
*kaine ubangijina kuma ni bawanka ne*
*na zalunci kaina,kuma na tabbatar da zunubi na* *dukkaninsu,babu me gafarta zunubi sai kai*

*ka shiryarda ni bisa ga mafi kyawun ɗabi'u*
*babu wanda yake shiryarda mafi kyawunsu sai kai*
*ka gusar da miyagun su daga gare ni*
*babu wanda zai gusar sheɗanu a gare ni sai kai.*
*na amsa maka na sake amsa maka da biyyah bayan biyyah a gareka.*
*kuma arziki naka ne ya Allah.*
*alheri naka ne ya Allah*
*sharri kuma bana danganta shi dakai*
*ka kareni ka tsare ni da sharrin abinda ka halitta walau mutum ko aljan*
*masu bibiyata da masu bibiyar zuri'ta.*
*Ya Allah ka kare ni,ka kare min zuri'ata*
la'ilaha 'illahu muhammadurrasullihi s.A.w.
Astagafurrallahullazela'ilaha'illahhuwa alhayyulQayyimu wa atubi ilaihi.

Kuka ya fashe dashi sosai.
Saman sallayar ya kifa kansa yana sujada kuka yake me ciwo.


WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
( horror story)


The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*page-15-16.


Shakh Bilal bai dakatar dashi ba,sai da yai kukansa ya godewa Allah.

Ido ya zuba mishi a zuciyarsa yana tausayinsa.

Tinda yake bai taɓa jin labarin wanda aka ƙuntatawa irin Abbu ba,kuma wai uwa ɗaya uba ɗaya.

''Ya Allah ka saka mishi kaine mafi chanchantar wannan sakayyar ya Allah.

miƙewa yai ya isa wajen Abbu ya dafa kafaɗarsa yace.

''A wa ɗaya ta rage min in tafi ɗaukar karatu.

Dama.Malamin mu da ƙyar ya amincewa Abba na da ya bada ni aro domin inzo in taimake kafin in kammala karatuna,domin ya hango ƙatuwar matsalar dake tafe da kai.

Kuma cikin hukuncin Allah na kammala zan tafi.

Duk lokacin da na dawo,dani da ƴaƴanka zamu haɗa ƙarfi da ƙarfi a domin kawar da BAƘIN MULKIN SAFWAN,yanzu dai komai naka ya dawo hankalinka bazai kara ɓacewa ba.

zaka ci gaba da ibadunka,zaka ci gaba da sallah azumi da duk wani aikin ibada,saidai ba zaka iya zuwa cikin gari ba har yau saboda akwai sauran sihirin da bai ƙarasa karyewa a jikinka ba,saboda lokacin da aka ɗibar min ba zai bari mu ƙarasa sauran aikin ba,amma Insha Allah lokacin da zan dawo gaba ɗaya za'ayi ta ta ƙare ko mu ko Safwan.

Kuma Muhijjinatun ka za ta tashi Insha Allah.



Sai Abu na gaba Mahaifina yana gaisheka,Abbu yai murmushi yace.

''Allah sarki MalAbdurrahm kace nima ina gaishe shi......

Shek Bilal yace ''To ni zan tafi sai hwaɗuwa ta biyu.

Abbu yAce ''Ubangiji ya bada sa'a Allah ya bada ikon yin abinda aka je nema.

Bilal yace.

''Amin ya ɓace.

**************

Abbu ya juya ɓangaren da Muhijjinatu take.
yaga bata da banbanci da gawa.Wai amma a haka Bilal yace tana da rai.
''To Allah kenan me rayawa kuma me kashewa,me sauko da cuta kuma ya safkar da maganinta.

Farar jallabiya da bilal ya kawo mishi irnta larabawa da hula ita ya ɗauka ya zira.

Zubawa Muhijjinatu ido yai,kafin sannan ya zauna ya dinga karanta Ayoyin Al'ƙur'ani,Ayatul-kursiyyu,da kuma ƙarshen suratul-baƙara,wato amanar rasulu.

Bai gushe ba ya dinga addu'ar Allah ya tashi kafaɗun Muhijjinatunshi.

''Allah kaine mafi girma,kuma kaine mafi buwaya,kuma.Kaine nake jin tsoronka Ya Allah,ina neman tsarinka dani da ƴata dake kwance rai a hannunka ya Allah,Allah ka tsaremu,ka karemu daga sharrin ɗan'uwana Safwan da sheɗanun da ke biye dashi Ya Allah.

***********

A gogon da Shake Bilalu ya kawo mishi da ita yai amfani wajen dubar lokacin sallar asuba.

A sujadarsa ta ƙarshe ya daɗe yana kuka yana neman gafarar Allah s.W.A.Me kowa me komai maƙagin sammai da kuma ƙassai.

A kan Allah ya dube shi ya baiwa Muhijjinatu lafiya.

ya nan zaune har gari ya soma haske.

Idinsa ƙur ya zubawa Muhijjinatu,ido kuma bakinsa bai dai na ambaton Allah ba.

Tamkar a mafarki haka yaga Muhjjinatu tana motsi....

Cikin farin ciki ya ajiye casbahar hannunsa ya tafi har inda take.

''Muhijjinatu !!!ya kirata da ƙarfe cikin zumuɗi.

Sannu a hankali ta soma ƙoƙorin buɗe idonta.
Ruƙota yayi,farin cikin tamkar wanda akayiwa albishir da gidanaljanna firdausi.


Abin mamaki koda ya riƙe hannunta wani zafi yaji ya soke shi da ƙarfi.
Sauri yai ya duban hannun nata.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una ya faɗa,domin ba komai ya gani ba face yatsunta sunyi zaƙo-zaƙo tamkar na Hirror.


Koda fara kalmatusshadar da Abbu yai.
Sai yaji ta ƙwartsa wata muguwar tsawa.

Tsawar da ta hargitsa dodon kunnensa,amsa kuwwar tsawar har dajin saida ya amsa.

Addu'a yake sosai.
Abu na gaba mafi muni da ya kuma dugunzuma bawon Allah nan Idonta da yai jawur,tamkar barkono.
Yai wani irin mugun ja,idan kayi mata kallo ɗaya ba zaka kuma kallonta ba.

hannunnan nata chaƙo-chaƙo tasa a daidai tsakiyar dokin wuyansa ta cafƙo wuyansa.

''Sai na kasheka!!!

"Sai na kasheka!!!

Abinda kawai take ambata kenan.
''Ya ilahi.

saboda azaba tari ya soma yi ƙuful'ƙuful.


da ƙyar ya iya buɗar baki ya soma karatanta.

''Wattaba'u.......
Ya ɗora da wassafati Aya 5
Suratuljinni5
Baqara-aya 5
(Suna maganin Aljani da izi nin Allah tin da safe kafin aci komai ake tofawa a ruwa a Sha.)

jin addu'on da yai mata yasa ta lanǧwaɓe ta soma barci,tana jan wani mugun munshari tamkar wani katon da yai aikin ƙarfi ya gaji.

Sai a yanzu ya soma tunanin maganar Shakh Bilal da yace Akwai babban al-amari a tare da Muhijjinatu,kenan wannane al-amarin?

Tirkash!..


sai yanzu ya gano hikimar Shakh Bilal wajen karya sihirin mantau ɗin da aka yi mishi,hakan yana nufin inda yana yadda yake sai dai Muhijjinatu ta kasheshi a banza,ita kanta batare da tasan ta aikata hakan ba.

Domin dai babu me maganin sheɗanu face Ayar Allah.

Ya sake duban ta a yanzu kuma wani gurnani take tamkar dabbar daji.

Gata nan shamɓal sai barci take,a halin yanzu farcen da yai zaƙo,zaƙo ya koma yatsunta lafiya lau suke.



Al-Qur'ani yaje ya ɗauko ya soma rera karatun Suratul-baQara.


chan ya juya kansa ya yana karatun sai da yazo wajen Wattaba'u sannan ya dakata ya rufe Al-Qur'anin.

Koda juyowarsa ba Muhijjinatu ba labarinta.

''To ina taje?
Wacce ya bari kwance tana barci.

Tun rana yake gararamba

3 / 7