Author : Category : Romance
WATA RANA DA DADDARE BOOK 2COPTL.
WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 1-2.
Tiryan,Tiryan Mal.Kabir ya basu labarin rayuwar Azkfyyh tin daga farko har ƙrshe.
(Tamkar dai yadda Abbu ya baiwa Muhijjinatu,)
Ina fata dai masu karatu baku manta ba,da labarin irin uƙubar da mahaifin Azkfiyyh yasha a hannun Al-h.Bashir,Sarki Safwan.
Mal.Kabir ya ɗora da faɗar.
''Tun washe garin da al-amarin ya faru.
Da gari ya waye dukkan wanda yaje fada babu wanda ake gani face,Safwan.
A matsayin sarki,haka zalika babu mai ikon yin magana.
''Ke in taƙaice muku har yau babu wanda ya tambayi Ina sarki Abdullahi?
"Ina yaransa?
''Ina Gimbiya Binta?
fadawan Sarki Abdullahi. duk sun juye sun koma na Sarki Safwan.
daga ciki babu wanda yai maganar
''Ni dai Mal.Kabir haifaffen garin ƙaraye ne daje jikar kano.
Ni babban Malamin addinin musulunci ne.
Sarki Abdullahi ni malaminsa ne da nake taya shi da rokon ubangiji idan wasu al-amurra sun shige mishi duhu.
Ya roki da na dawo garin da ya ke sarauta....
Girmansa da nauyinsa yasa na amince da buƙatarsa.
Lokacin da Sarki Abdullahi ya kwanta jiyyar rashin lafiya,dafarko dai duk wani sihiri da tsafi da ake yowa nike karyashi.
Da suka lura da irin ɓarnar da nake musu.
A wani DARE ne Alh.Bashir.Kece min yaga bani da sa'na'ar yi ne.
Yana so zai ɗauke ni ya bani aikin yi.
Duk wata zai dinga bani 500k.
A lokacin tana wata tsiya.
Yace yaga Sarki Abdullahi bai ajiye ni a layin fadawa ba,kuma bai bani san'a ba.
To shi zai ajiye ne a boysqeater,idan ma ina so zan iya zuwa da iyalina.
(Abinda bai sani ba abinda sarki ke bani a duk ƙarshen wata ko rabinsa bai bani ba.)
bazan iya yi masa musu ba,saboda sarki bashi da lafiya,sannan duk wata kulawa Bashir na bashi,kuma a iya al-kharin dake tsakanin ni da Sarki banga buƙatar da wani nashi zai nema ba,ina da ita na Qqq. aikatawa.
Kuma nasan idan Sarki ya samu lafiya nayi mishi bayani zai fahince ni.
Ban daɗe da komawa gidan Bashir ba aka nemi Sarki Abdullah k'warai wanbai aka rasa.
Ina zaune yazo min dake Azkfyyh,ba zaki wuce shikara 6yrs ba a dunuiya...
A lokacin ita Mukshfyyh tana da shekara 16 a duniya tasan komai game da labarinku,domin Mallam Abdurrahn ya labarta mata komai.
Kuma mafi munin abun Mukshifyyah tana gidan Safwan ya ajiye ta cikin bayinsa.
Sai Haidar.
Shi kuma yana cikin kulawar Sarki Safwan saboda biyan buƙatar da Safwan keson yayi da Hsidar.
Akwai wani gida cikin DAJI....inda Sarki Abdullahi yasa aka gina mishi ƙofa wacce sunayen ƴaƴansa kaf shine securityn wannan ƙofa,kuma baza buɗe ba sai jinin Sarki Abdullahi ƴaƴansa na cikinsa.
To Haidar kaɗai yasan wannan password.
Babbar matsalar Malam Abdurrahn ya kurumtar da bakin Haidar daga furta magana.
An ƙaishi duk ƙasashen duniya domin ya warke,amma ko ina aka je ba sauƙi sai ga Allah.
b Sarki Abdullah yana Raye koko?
ni nan da kika gani,ni kaɗai zan iya bada wannan labari sai Sarki Abdurrahmn.
Saboda Adduo'in da nake yawan yi shi yasa tsafinsu bai taɓa ni ba.
Domin kafin mahaifiyar Su Sarki Safwan ta mutu harda laya aka saka a bakinta,kinji dalilin da ba wanda ya isa yai maganar inA Sarki Abdullahi.
Ke Safwan ba ƙara Azzalumi bane.
Ko Haidar ɗin ma ta ya su buƙatarsa ta biya zai baiwa dodo jin Haidar.
Ko nan ɗin da kuka ga an kawo mu ba kowa bane face Malam Abdurrahmn.
Mallam Abdurrahm ba ƙaramin so yake nuna muku ba a dalilin ku ya tura babban yaronsa saudiyya domin nemo ilimin addinin musulunci.
Dalilin da yasa ya ƙaurace muku shi musulmi ne Mahaifiyarsa kirista ce,to tace duk lokacin da ya taimske musulmi bata yafe mishi ba,kuma sai ta tsine masa.To tsananin biyayyahr da yake mata yasa ya zuba ido yana kallo.
̧
don haka a domin kawar da mulkin zaluncin Sarki Safwan sai kun haɗu ku duka ƴaƴan Sarki Abdullahi,kuma sai kun nemi ilimin addinin musulunci.
Safwan tinda ya hau mulki tsawon shekarunnnan babu wanda ya ƙara jin daɗi.
Mata goma 4 yake aure a duk.Shekara kuma da wata shekarar ta zagayo zai sadaukarwa dodon tsafi da jininsu.
idan matar ta samu ciki da cikin da matar zai baiwa dodo jininsu.
duk shekara iyaye na shiga zullumi,domin duk wanda ya nemi auren ƴarsa ya hana,hukuncinsa kisa ne kuma ya ɗauke ƴar ya aura ta ƙarfin tuwo.
Sannan duk shekara ana neman ƴaƴan gata,ƴaƴan sarakai a rasa an rasa inda annobar ke 6ullowa,basu san Safwan ne
Sarki Safwan baka isa ka bada labarinsa da Rana ba sai DADDARE.Domin baƙaƙen al-jannu dake tare dashi.
To yanzu Azkfy abinda zakiyi shine dole ki tashi ki nemi ilimin addinin musulunci.
Amma kafin nan zan fara koya miki iya addu'in kariya da na fattatakr sheɗanun Aljanu bakin sanin da Allah yai min.
Sannan zanyi sallar istikhara domin neman yarda ga Allah s.W.A.
Domin sanin shin Abdullahi yana a raye koko,bakin iya yarda Allah zai fahintar dani.
Kukan Mariya ya katse su.
Duk shiru suka yi, tare da zuba mata ido.
Don sanin dalilin kukan nata.
share hawaye tayi,tare da duban Azkfiyyah.
''Ki yafe min,ki yafe min,Bansan keɗin abar tausayi bace ba sai yanzu,ki yafe min Azkfyyh.
Azkfyyh ta tashi ta share mata hawaye.
''Mama ba sai kin nemi gafara ta ba,kuma Insha Allah zan ci gaba da dubanki a matsayin mahaifiyata.
Murmushi Mal.Kabir yai ya dube su tare da girgiza kai batare da yace uffan ba.
Ci gaba daba Azkfyyh labari yai.
''Abu na gaba da sarki Abdullahi yai.Muku.
Akwai addu'ar da yai muku,kaf ƴaƴansa babu wanda ya isa yai zina dasu,face mijinsu na aure.
Duk kuma wanda yai gigin hakan akwai gagarumar matsala.
A halin da ake ciki Safwan ya manta da ƴar'uwarki Mksfyyh.
Ya manta da matsayinta domin shi muddin ba mugun nufin shi ba baki da abinda yake riƙewa a rayuwarsa.
ƴarsa ɗaya Sumayyah.
Wannan ne ƙarshen labarin.
Azkfyyh ta sarda kanta ƙasa ta fashe da kuka tace wannan rashin imani na Safwan har ina,domin bazan taɓa kiransa Baba ba.
Sarautar Safwan ta mahaifina ce.
Safwan shi ya kashe mahaifina na kuma ya ƙasƙantar da zuri'arsa.
Wallahi tallahi!!! ''Sai na ɗau fansar jinin mahaifana!...
dole zan nemi ilimin Addinin musulunci domin yaƙi da sheɗanu.Insha Allah sai na shahara a neman ilimi,ko ina sai an san da zama na a duniya.
Yanzu ki tashi mu fara sallar istihara A DAREN YAU.
''Insha Allah Azkfyyh ta faɗa tana goge hawaye.
Alwala suka ɗoro,sannan ita kuma Mariya ta kishingiɗa tana barci.
********
Rayuwarsu a ƙauye gwanin daɗi,kuma Alhdullah manya da yara suna zuwa ɗaukar karatu a wajensa.
Azkfyyh kuwa ta dage neman ilimi.Ka'in da na'in.
Kamannin Mallam Kabir sun sauya ba zaka gane shi a yanzu ba,domin yabar gemu.
Sannan Alhmdullah suna cikin rufin asirin ubangiji.
Azkfyyh kullum burinta da buƙatarta ta neman ilimin ta samu tofa daga nan kafcen zai soma.
**DOKAR DAJI**
MUhijjinatu na tsugunne a ƙaton tafkeken kogin inda ruwa ke gudana.
Ta sarda kanta tana wanke gashin kanta
wanda har ya zuba a gadon bayanta.
Kogin da ke cikin DOKAR DAJIN guda biyar ne.
Na farko anan Abbu ke kama kifaye.
Domin ba sai ka shiga ba a ciki daka zura hannunka ma zaka iya ɗamko kifaye.
Kuma kifayen duk manya ne domin guda ɗaya ma idan Abbu ya kamo ba zasu iya ci ba shi da Muhijjinatu.
na biyun kuma ya kasance me ɗanɗanon gishir.Shi kuma gishiri ne dawo,dawonsa.
anan suke ɗibo gishirin da zasu zuba a cikin kifi,ko nama.
Na ukun kuwa kanwa ce ita ma ɓalli,ɓalli ruwan ma ɗanɗanon kanwa gareshi.
Na huɗun kuwa kumfa garshe sosai kamar sabuli,to anan suke wanka ita da Abbunta.
na biyar ɗin kuma ruwa ne garai,garai me daɗin ɗanɗano.
Don ALLAH KUYI HAƘURI DA RASHIN TURO MUKU DA BANYI BA...
Ina makaranta.
Insha Allah typing ba fashi,Allah yasa muna da rai da kuma lafiya.
WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 3-4.
Kammala wankanta keda wuya.
Ta soma iyo,cikin nishaɗi da farin ciki.
ta nitse tayi luff.
Abbu ya iso wajen cikin farin ciki ya tarar da ita,shi ma farin cikin yaji har cikin tsokar jikinsa a duniya babu abind a ke saka shi nishaɗi irin yaga Muhijjintu cikin farin ciki.
''Muhijjintu wanka kike?
Iya fuskarta kaɗai zaka iya gani.
''Zan tafi samo miki nama,mutuminki.
''To Abbu sai ka dawo''
(abinka da wdda bata san tace Allah ya kiyaye ba).
''To ki kula da kanki da akwai sauran gasasshen kifi.
''To Abbu.
Juyawa yai ya shiga daji.
Tafiyar Abbu ba jimawa tayi tsalle ta diro daga kogon,cikin tsantsanr farin ciki.
Ta ɗauko kayanta wa'inda Abbu ya ɗinka mata na fatar dabba tasa ta suturta jikinta.
Tafiya take ranta fes.
Ko ba komai yau zata ji dukknin amsoshinta daga baƙin aljani.
Kai tsaye wajen kabarin Mahaifiyarta ta dosa.
Bata jima tsaye ba ta soma jin sautin mummunar dariyar baƙin aljani.
Ko ɗar ko alamar tsoro babu a tattare da ita.
Ta dube shi a inda ya bayyana da mummunar siffarsa me kan ƙwrangwal yana ta dalalar da gulamar jini.
''Duk wasu amsoshi na same su daga bakin Abbuna.
Naji dalilin WATA RANA DA DADDARE.
''Na san dalilin da yasa muke rayuwa A DOKAR DAJI,naji dalilin ambatar WATA RANA DADDARE.
''Yanzu duk tambayoyina sun dawo gareka.
''Tambayar farko da zan maka ita ce.
''Meye dalilin da yasa kake son taimakon mu nida mahaifina,alhali kana da gudumuwar da ka taka wajen jefa mu a halin da muke ciki a yanzu?.
Ma'ana da kai Sarki Safwan yai amfani wajen cimma burinsa.
''Tambaya ta biyu me yasa baka bayyana a siffarka,walau mutum,ko aljan sai dai kazo a hayaƙi ko kuma kazo da kai kurum?
''Tambaya ta uku ''Meya sa baka zuwa
har inda muke nida Abbu sai dai ka tsaya wajen kabarin Maman?
Dariya ya kwashe da ita marar ɗaɗin sauti yace.
''Kin gama tambayoyin naki koko?
"Muhijjinatu ta gyaɗa kai alamar
''Eh,na gama kai nake jira.
''Amsar tambayrki ta farko shine-Dalilina nasan taimakonku shine,
Ni sheɗanin aljani ne kowa ma zan iya dafamawa a domin na samu ABOKIN TAFIYA.........
''Tafiya Ina?
Muhijjinatu ta katse shi.
Dariya ya kwashe da ita kana yace ba sai na baki wannan amsar ba,domin banasan tambaya cikin tambaya.
Muje tambyarki ta biyu.
''Ni ba mutum bane fatalwa ce.
FATALWA kuma,meye FATALWA?
fatalwa ita ce mutum ya mutu ya dawo.
Ya dawo kuma?
''Aini Malam Abdurrahman yace duk wanda ya mutu ya koma ga Allah bazai taɓa dawowa ba.
''Ke ƙyaleshi maƙaryaci ne,nace ki daina biye mishi,inda ba'a dawowa ni ya'akayi na dawo?
''Abbu na da kuma Mallam Abdurrahm sun ce duk wanda ya mutu ba zai dawo ba.
''Ni nayi miki alƙawari zan dawo miki da mahaifiyarki wannan duniyar.
''Ke share wannan muje a maganar mu ta gaba.
Dalilin da yasa bana zuwa dai,dai wajen bukkarku shine.
''Akwai wani kafi da Mallam Abdurrahmn ya kafe,to duk wanda yai yunƙurin taimakonku ba zai iya zuwa wajen ba,yafi san yazo kullum yana zuba muku ƙaryar banza da wofi.
''To Abbu ya yarda dashi yace Shiɗin taimakommu zaiyi.
''Ƙarya yake,me yasa idan da taimakon ku zaiyi tun wuri bai mayarda ku,masarautar kuba,ya sada ku da a halinku sai dai kullum ƙaryar banza da wofi.
Saboda haka ni ina tausayinku kuma zan tsaya muku muddin kuka bi sharuɗɗa na.
''Zan kashe ki kuma na dawo dake,zan miki fiffike ki tashi sama kije har BAƘAR FADA inda Safwan ke mulki ki kashe shi.
Sannan bayan kin gama da Sarki Safwan ki dira gidan Alh.Bashir shima ki kashe shi,sa'annan daga baya na ɗaukeki keda mahaifinki na mayar dake gidan sarautarku.
Cikin zumuɗi Muhijjinatu tace.
''Ta yaya hakan zai faru?
''Idan kin yarda kin bi sharaɗina.
''Meye sharaɗin??
''Zaki yi wa DODO SUJADA.
Kuma ni zan ɗauke ki na kai ki kuma DA TSAKAR DARE.
''To NA AMINCE!!!
Muhijjinatu ta faɗa fuskar ta ciki da farin ciki da annushuwa.
''To amma ta yaya zaka iya ɗauka ta TSAKAR DARE,al hali kai baka iya zuwa inda nake rayuwa nida Abbu
"To kece kaɗai zaki iya ɗauke kafin da Mallam Abdurrahm ya kafe a waje.
''Ni bansan wani kafi ba kuma bansan inda ya ajiye ba.
''Amma na amince da sharaɗin tabbas zanwa DODO SUJADA.
kuma zan tono inda abin yake muddin ka sanar min da inda yake ɗin sannan ni kuma ka amince muddin na biya maka wa'innan buƙatun nima zaka biya mun nawa buƙatun.
''hhhhhhhhhhhhh!!!
Mu bama saɓa alƙawari.
Ya faɗa cikin muryarsa mai muni.
''To yanzu faɗa min ina abin yake wanda zan tono?"
''Dai dai farkon ƙofar zaki ga wata itaciya to a kusa da ita zaki ga wani ƙaton dutse a jiki to ki mirgina dutsen nan zaki tone,anan aka birne abin.
''Zaki ganshi ƙulle a baƙar leda.
Da zarar Mahaifinki ya kunna wutar gasa nama sai ki faƙaice shi ki toye abin.
Kiyi sauri gashi chan ya kashe wata ƙatuwar dabba yana ƙoƙorin juyowa gida.
Cikin hanzari Muhujjinatu ta juya cikin tsantsar farin ciki tabar wajen.
vv vv vv
** ** **
Azkfyh ta dage neman Ilimin addinin musulunci,gari,gari take zuwa koda yaushe ƙaton hijab da niƙaf jikinta.
A ƙyauyen da suke rayuwa har islamiyyah ta buɗe tata ta kanta tana koyawa yaran garin.
Yau bayan ta dawo daga koyawa Islmiyyah ta shigo gida ta tarar da Mal.Kabir zaune yana tilawar Qur'ani.
Har ƙasa ta tsugunna tana gaisar dashi.
''Malan Ina yini''
''Lafiya ƙalau Azkfyyh.
''Yaya karatun?
"Alhdullah.
''To Masha Allah.
''Idan kin ajiye littafan ina so zamu yi magana.
''To Baba ta faɗa tare da juyawa ɗaki.
Mariya dake kicin tana kwashin tuwo ta auna mata harara.
Wanda ke nuni da cewa tuban nata dai na muzuru ne.
Bayan fitowar Azkfyyh.
Ta zauna gefen Malan tana faɗar.
''Malan gani.
''Azkfyyh da fatan dai kina istiharar da na baki ko?
''Eh.Malam duk DARE ina yi.
''To masha Allah me kika fahinta.
Malam ina yawan mafarkin wani mutum da kuma budurwa cikin tsananin ƘUNCI da kuma wani MUGUN DUHU a baibaye dasu.
Kuma abinda na fahinta ina ji ajikina makusanta nane mutanen.
Girgiza kai yai kafin ya ɗora da cewa.
Jabir.bn Abdullahi Allah ya yarda dashi shida mahaifinsa yace.
*manzon Allah tsira da amince su tabbata a gare shi ya kasance yana koyarda mana sallar istihara (neman zaɓin Allah) a cikin dukkanin al-amurranmu,kamar yadda yake koya mana sura daga cikin alqur'ani yakance idan ɗayanku yayi niyyar yin wani al-amari to yayi sallah raka biyu bata farillah ba sannan ya nemi zaɓin Allah.*
''Tabbas maganarki gaskiya ce nima na fahinci wani Abu.
Tabbas Sarki Abdullahi yanan a raye be mutu ba,sannan wannan budurwa da nake gani ita ce suna na farko password ɗin buɗe ƙofar da dukiyarku ke ciki........
...................MUKASHIFIYYAH AZKAFIIYH HAIDAR.
mu haɗu a nex page.
DA DAMA SUN ROƘI DA NA ƘARA MUSU KODA PAGE 1 ALBARKACIN SOYYAYAR DA KUKE WA BOOK ƊINNAN GA SADAKAR PG 2 NAN KU DAURE KU SIYA 400NE KACAL.
Ina mamakin masu bina ta pc suna cewa please book 2 bayan tun a farkon labarin nace na kuɗi ne.
400 ne kacal.
9187153012
Aisha Abdullahi
fcmb.
Karku bari a baku labari.
Ina Mommyn Ilham naji ki shiru,keda hajara.Adawiyyh mmn al'amin ayeesha.
Zainab mmn yusu kai kuna yawa fa ku.Marmatso kuzo ayi tafiyar nan daku kar ku bari a baku labari....Ana ta biya amma naji ku shiru an soma biya an barku baya......Ku matso to gadai sadaka.
tunda aka shiga paid kunyi luff abunku.
WATA RANA DA DADDARE.
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 5-6.
Amma kuma a ko ina suke suna cikin matsala.
''Tabbas suna cikin tsananin buƙatar addu'ar mu.
Azkfyh ta dubi Mal.Tace.
''Insha Allah zan ci gaba da Addu'a.
Sai dai yaya za'ayi na haɗu da ɗan'uwana Haidar da kuma Mksfyyh?
Mal.Kabir yace.
''Ganin Haidar da kuma Mkshfyyh ba ƙaramin abu bane,sai dai suma ki bi su da Addu'a.
Ta goge hawayen fuskarta tace.
''Insha Allah Malam komai zai zo ƙarshe da izinin Allah.
Mariya dake laɓe tace ''Duk zaku ci ubanku daga ke harshi,ni dai ba haihuwa nayi dashi ba balle in takura don ya shiga matsala.
******
Da sanyin safiya Mariya ke tambayar Mal.Kabir zata je ƙauyensu ta'aziyya.
Koda ya tambaye waye ya mutu?
sai ta soma ƴan kame,kame.
''Ubangiji ya maido ki lafiya.
Amsar da ya bata kenan.
Sumi-sumi ta wuce ta soma shiryawa.
Azkfyyh da ke gefe.
Tace.
''Mama Allah ya tsare.
Wata uwar harara ta gaura mata aranta tana jin mugun haushin Azkffyh da tayi silar da suka bar cin cima me daɗi.
Wajen ƙarfe ɗaya na rana Mariya ta isa birnin tarayyah.
Da yake ƙauyen da suke bai da nisa da abuja.
Daidai ƙofar shiga birnin tarayyah,me idon Mariya zai gane mata?
Faskeken hoton AZKFYH da na mijinta Mal.Kabir.
Tamkar wani governor da shugaban ƙasa.
Wani me siyar da Maclen ta tsayar.
Ya ɗauka siye zatayi har ya soma daɗin baki,irin na ƴan tallah.
Sai kuma tace.
''Bawan Allah tambaya nake.
Far'arsa ya mayar ciki.
Yace.
''Ina jinki.
''Don Allah domme aka kafe hotonan mutanenchan?
ta faɗa tana nuna hoton Mal.Kabir da Azkffy.
''Ko kin sansu ne.
Ya faɗa yana dubanta.
Girgiza kai tayi alamar.
A'a.
Yace to baki ga abinda ke rubuce ba?
Marairaicewa tayi.
''Yaro banyi karatun boko ba.
Yace to 1millon ga duk wanda ya kawo su.x
Zaro ido tayi warwaje.
millon10 fa kace.
Murmushi yai yace.
''Me ce ce 100millon ga Alh.Bashir ɗan'uwa ga Sarki Safwan?
jikin Mariya na ɓari tabar wajen.
Ba tare da ta kuma ce mishi uffan ba.
Sai da tayi nisa ta saki doguwar ajiyar zuciya haɗe da faɗar.
Tirƙash!
''Mariya keda talauci kunyi hannun riga.
10millon ai har na mutu ba zan cinye ta ba.
Cabɗijannan!!!
Ada nayi niyyar Azkfyyh kaɗai zan towa asiri,to yanzu har Malan ɗin ma yai ta kansa.
Al-qur'an bazan bar Millon10 ba.
In yaso in ya sake ni sai inzo birni in gina ƙaton gida in samu saurayi in aura in ta rayuwata.
Kila ma har haihuwa sai nayi.
Bari ma in zubar da kayan nan nawa.
Nan take Mariya ta zubar da wa'innan kaya duka,nata.
a ranta tace.
''Ni da zan shiga sabuwar rayuwa me zanyi da tsummokarai.
''Kai tsaye.
Napep ta faɗa.
Gidan Alh.Bashir.
''To waye ma me san ɗan'uwan baƙin azzalumi Safwan ba?
**
Tin a bakin get ta gane cewar an kuma tsaurara tsaro a gidan domin sojoji ne fululu ta ko ina.
''Keeee!
Wajen wa kika zo?
bakinta na kyarma wajen faɗar wajen Hajiya.
''Dama ni ƴar aike ce naje ganin gida kuma yanzu na daw.
''To zaki faɗa mana kaɗan daga sirrikan gidan?
''Ehy,domin ni da babban Albishir nazo akan wa'ind Alh.Ke nema..
What?
''Da gaske kike?
shiga daga ciki ya faɗa yana zare jajayen idanuwansa.
Koda isarta ƙaton falon farko.
Haj.Ta tarar zaune tana kallon shirin kwana casa'in a ƙatuwar Tv.Plasmar da ta mamaye bangon ɗakin.
Da sallma ta shiga.
''Wa'alaiki'salam,Haj.Ta faɗa tare da zubawa me shigowar ido
''Mariya ta