wannan DAREN.
Yanzu kunnuwanki sun shirya sauraren wannan cukurkuɗaɗɗen labarin?
Muhijjinatu ta miƙe daga kwancen da take idanuwanta tsaf suka washe.
''Abbu kai nake saurare.
**WATA RANA DADDARE**
**LABARIN ABBUN MUHIJJINATU**
To Abbu ina sauraranka Muhijjinatu ta faɗa tana me duban Abbunta.
Ƙasar AMSAD babbar ƙasa ce dake Chan yankin gabas,kuma babbar ƙasa ce da
duk sauran ƙasashe a ƙarƙashinta suke.
Sunana Sarki Abdullahi bn AbuSufiyan bn Abdulfatta bn Nuhu Bn Abdulƙadir........Kuma nine Sarkin ƙasar nan ta AMSAD............
Abbu dama kai sarki ne?
Bai tsaya bata amsa ba yaci gaba da cewa.
Mahaifina AbuSufiyan Adalin Sarkine mai tsausayi kuma duk sarakunan sauran ƙasashe suna mishi biyayyah sannan babu mai ƙarfin arziƙi irin nasa.
ya daɗe bai samu haihuwa ba matansa huɗu a duniya.
Gimbiya Rahima Mai babbanɗaki,sai Gimbiya Baraka Mai ɗakin gabas,sai Gimbiya Balaraba,sai mahaifiyata Gimbiya Habibata....
Abbu ya ɗago ya dubi Muhijjinatu yace.
''Ina fatan kin fahinci inda labarin ya dosa?
Muhijjina ta ɗago ta dube shi tace.
Ehy Abbu na fahinta,hakan na nufin amsar tambayata da nake yawan cewar muɗin ƴan Adam ne tabbas yanzu na fahinci mu mutane ne ba wasu naui'n dabbobi ba tamkar yadda na saba cewa.
Murmushi yai yace''Dama nace da sannu zakiji duka amsar tambayoyinki.
''To Abbu ci gaba labarin akwai daɗi.
bai ce uffanba yaci gaba da cewa.
''Duk yadda matan mahaifina suka so su haihu,abu ya gagara,domin dukka su uku babu wacce ta taɓa koda batan wata.
Mahaifiyata shekararta biyar Allah ya ƙaddare ta da samun cikina kar kaso kaga murna wajen sarki,tsabar murna saida ya saka aka tara masa sarakunan duka ƙasashe saboda taya sa murna.
Wata tara daidai ta haifo ƙaton ɗanta namiji kyakkyawa ni ne nan balarabe na biyota sak domin ita ƴar sarkin Makkace.
Haka akai ta murna da shagalin haifata,tofa shekarata 1 daidai akayo min ƙane Safwan,shima shekararsa ɗaya tayo masa ƙane Bashir.
Wayyoḷ
Ina wuta kishiyoyinta su jefata?
anyi tsafin an kwace hanyar to amma da yake iyayenta sun shirya mata babu abinda ya sameta.
Tun tashin mu Safwan ya tashi irin yaran nnan marasa tausayi.
Shi kuma Bashir ya tashi irin ƴan ƙaryar nan me mugun son kuɗi....
Tin yana ɗan shekara 16yrsold ya soma neman matan banza da shaye,shaye.
Da dama dangi sun ta'allaƙa kan cewa dangi kishiyoyin mahaifiyarmu suka yi ma ƴaƴanta 2 asiri Safwan da Bashir,dama ni bana shiga harkar su.
To ita dai ta barwa Allah ikon sa.
****
Lokacin da tsufa ya kama mahaifinmmu yana so yai murabus.
daga kan karagar mulki,kowa yasan babban ɗa shine magajin uba.
To ɓangaren Safwan kuwa ya haukace shi lallai shi zai gaji sarautar Sarki.
Abin baƙin ciki matan babanmmu suke daɗa zugashi ya haukace sam bayaji baya gani.
Mahaifiyarmu da Sarki soyayyar da suke gwada mishi ta hana su tanƙwarashi.
da naga abu zai zama tashin hankali haukan Safwan kullum ƙaruwa yake yasa nace a ƙyaleshi.
Indai Sarauta ce ni na haƙura nabar mishi.
Sarki ma bai ja ba ya ƙyale ni nan ya sake tabbatar da cewar nafi safwan hankali.
Wani abin al-ajabi ranar da Safwan ya hau karaga ma'ana aka rantsar dashi da ya hau kujera da an wulloshi da qasa an rasa meye musabbabin abun.
Sau uku ana haka cikon na huɗun ne ni na hau.Koda na hau sai na zauna daram ba abinda ya faru.
sai bushe bushe algaitu wanda ba'asan daga ina yake fitowa ba.
A dole Safwan na kallo na na zama sarki.̇
Ransa ya dugunzuma sosai sai ya soma sakin maganganu yace''Dama munafurcu yasa nace na haƙura saboda ina da abinda na ƙudurwa a zuciyata tofa.
Shekara ta ɗaya akan karaga mahaifinmmu AbuSufyn adalin sarki yace''gagarinku nan''
Allah Sarkiḷ mutuwar sarki ta dugunguza ƙasashe da dama a duniya musamman mu ƴaƴansa saboda ni duk yafi shaƙuwa dani fiye da kowa a yaransa.
Mutane sun san sarki ya tafi yabar copy wato ni domin duka halayensa babu wanda na baro.
Abbu ya ɗanja numfashi yana goge hawaye,tamkar a yanzu mahaifin nasa ya mutu.
ya zuba mata ido kana yace''Muhijjinatu
NI MUSULMI NE CIKAKKKE!!!
a mamakance ta ɗago tace Abbu meye hakan meye musulmi????"
07049138863.
̈̃̈̃Call 07012329134
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
PAGE 20- 21
Bai dubeta ba ya soma da bata amsa.
Addinin musulunci shine addinin gaskiya.
Addinin da manzon Allah( S.A.W)
ya koyarvdamu.
Addinin.Musulunci shine addinin da zaka san mahaliccinka kuma ka bauta mishi.
Addinin musulunci shine addini me tsafta.
Cikar musulunci shine.
kalmar shahada.
Ka ƙiyasta babu abun bautamawa da gaskiya face Allah ,(S.W.A)
sannan ka shaida Annabi muh'd bawan Allah ne kuma manzonsa ne.
Inkai haka ka zama cikakken musulmi.
Sannan sai sauran.Sannan kayi imani
.........
1Imani da Allah.
2kayi imani da manzonsa.
3Imani da mala'iku.
4IMANI da Littafansa.
5kayi imani da ranar tashin alqiyama
6Kayi imani da ƙAddara alkhaiei.
7kayi imani da ƙaddarar sharri.
1Sallah
2Azumi
3zakka
4Hajji
daga cikinsu babu wanda banayi.
Ada ina sallah,ina azumi ,ina fitar da zakka daga cikin ɗumbin dukiyar da Allah( s.w.a.)ya azurtani da ita.
Abbu sallah,amma yaya akayi ban taɓa ganin kayi ɗaya daga ciki ba
Kuma nima baka taɓa koya min ba?
Murmushi yayi yace karkiyi sauri Muhijjinatu da sannu zaki ji duk dalilin da yasa.
*******
Ranar da Sarki ya cikia sati da rasuwa aka ɗaura min aure da mata 4.
Akuma ranar aka nemi ƙanena Safwan aka rasa.
Sati na zagayowa ɗaya ta mutu mutuwar farat.
Anyi sadakar uku ɗaya ta kwanta ciwo kwana 2 ita ma tace gagarinku nan.
cikin wata 1 kaf matan nan saida suka mutu.
Na shiga tashin hankali yadda baki zato kuma duk auren soyayyah mukayi dasu,kuma duka ƴaƴan sarakuna ne.
Ke in taƙaice miki cikin shekara mata 10 suka mutu,duk an chanfani cewar tsafi nake,mutane sun soma tsoron ince ina son ƴaƴan su.
Don haka sai na haƙura da aure na fawwalawa ubangiji al-amarina.
Na yi shekara ɗaya ba mata.
Kwatsam ina zaune wani shararren Malamin addinin musulunci Shekh,Ibrahim ya zo tare da ƴar sa ina zaune fada duk abin duniya ya dame ni.
Maganar da yazo da ita bani ba hatta fadawa sun girgiza,har wasu na ganin kwaɗayi da son abin duniya yasa zai jefa ƴarsa hallaka.
Abinda yace min shine.
Shi yayi imani da Allah ke kashewa kuma shike rayawa,rayuwa da mutuwa duka suna wajen Allah don haka muddin ina san ƴarsa Sayyada Binta to zai bani aurenta.
Mun daɗe muna jayayya nace mishi nifa da na auri mace mutuwa take yace indai ina san Binta to ya bani.
Kuma itama ta amince,don haka amincewa ta kaɗai yake buqata yanzu a ɗaura aure,in bashi sadaki kaɗai yake buqata.
Ba yadda na iya haka na haqura na rungumi ƙaddara.
Ni da mutanena tun mun̵'a qirga kwanakin mutuwar Binta har mukaji shiru.
Shekara guda ta sulluɓo ɗanta namiji aka saka mishi suna Haidar.
Yana shekara ɗaya ta watanni ta haifo mace wacce taci suna Mukasshifiyah.
Bayan an yaye Mukasshifiyya ta haifi Azzkafiyah.
To na haqura da aure tinda Binta ita Allah ya hukunta ta zama matata.
Muna zamanmmu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali..........
Kartseshi Muhijjinatu tayi idonta taf da ƙwalla tace''Abbu ashe bayan ni kana da wasu yaran?
gyaɗa kai yai alamar
''Ehy''
to mu yaya akayi ka nisantamu dasu,Me yasa ka zaɓi rayuwar DAWA?
sannan su sauran ƴan'uwan nawa suna a raye koko?
Kuka sosai Abbu ya fashe dashi yace
SAFWAN,SAFWAN ɗan'uwanane Amma Allah ya isa tsakaninni dashi.
To Abbu har yau banji ka ambaci komai game da Safwan ba amma sai kiran sunansa kake.
yanzu zaki ji komai saurara............
Tun tsawon shikarun da na kwashe ina mulki wajen shekara 5 kenan yarana uku,sai qaramin cikin da Binta ke ɗauke dashi a halin yanzu.
Al-umma najin daɗin mulkina tamkar dai yadda mahaifina ke mulkinasa.
duk tsawon shekarunnan babu wanda yasan inda Safwan yake harni kaina.
Ashe Safwan ya nutsa duniya yabar matarsa da ƴaƴansa ya nutsa duniya neman duniya bokaye ya shiga nan ya fita nan a dole sai ya wulaqantani.
Nida ba laifin da nayi masa.
Cikin shekara 5 ɗinnan ya haɗu da shararrenn bokan da duk duniya anyi ittikafin babu wani boka shaharre matsafi kamarsa boka zaƙawanu kenan,duk wani sheɗanin al-jani to dashi yake aiki duk wani bil-adam ɗin da ya ziyarci boka Zaƙawanu to sunan sa
A SAIDA LAHIRA A A SIYO DUNIYA(wa'iyazu billah)/
Safwan ya sami nasarar haɗuwa da boka Zaƙawanu,tinkan Safwan ya faɗi buqatarsa shi shi bokan ne ya faɗi masa abinda ke tafe dashi.
Boka ZAƘAWANU yace ni sharaɗina kurum zan faɗa maka.
''Safwan sharuɗɗan sune kamar haka-
Dole ne kabar sallah kwata,kwata a rayuwarka,
sannan zakayi zina da ƴarka kuma a cikin azumi.
Sannan zaka sadaukarwa mahaifiyarka dodon tsafi ya zuƙe jininta.
Sannan idan buqatarka ta zama sarki ta cika to zaka mayar da bayinka ƴaƴan sarakuna, ma'ana zaka sato ƴaƴan sarakai su zama bayinka.
kuma duk shekara za'a ba dodo jinin ɗaya daga cikinsu ya shanye.
Idan duk ka cike wa'innan sharuɗɗa za'a nemi sarki Abbdullahi a rasa rashi na har abada.
Zai shiga daji shida matar sa a inda namun daji zasu cinye naman su.
Kuma duk duniya babu wanda zai ƙara tuna Sarki Abdullahi hatta fadawan sa.
sannan abu na gaba da zarar ka zama Sarki zaka maye gurbin masarautar da bakin zane komai zai zama baqi ne,sannan hatta da rawanin ka baqi get ɗin da za'a buɗe a shiga baqi unipoam ɗin bayi baqi sittirarka kullum baqa.
Fadawan ka ma komai nasu baqi.
Kuma ka kori wa'innan a chanza wasu.
To ina me tabbatarmaka Sarki Abbdullahi da matarsa Gimbiya Binta zasu bar ƙasar nan gaba ɗaya Abbdullahi da matarsa zasu mance kowa kai hatta kansu sai sun mance Abbdullahi zai mance da sarauta sau ɗaya a duniya zai dinga tuna shi waye.
kuma cikin DARE.Ko ya tuna yayi gigin ɗaukar mataki kafin gari ya waye zai manta.
Sannan duk Wa'innan abubuwan ya kasance DADDARE za'a aikata kar ayi komai da safe ko da rana ko da yamma.
Abbu yaɗanja numfashi yana duban Muhijjina.
Hawaye suka zubo mishi babu wacce akafi cutarwa kamarta zarkaɗɗiyar budurwa kamar wannan ace ta kasance RAINON DAJI.̀
ba ilimin addini ba na zamani har gara ƴan'uwanta su sun rayu cikin gata,kuma suna da ilimi sosai kuma sunsan su ko su waye ita kam bata san kowa ba sai dabbobin daji......
Abbu kenan banda Bashir cikin aika aikar?
Safwan shi kaɗai ne ya aikata.
murmushi Abbu yai yace.
''Bashir shine Impomer na Safwan duk abinda nakeyi akan idon Bashir shike sanarwa da Safwan duk halinda nake ciki.
Sai dai shi Bashir ba mulki yake so ba shi dukiyar ce kurum a gabansa duk da dumbin dukiyar da mahaifinmmu ya bar mana gado wacce inda zamuyi ta cinta har ɗiyan,ɗaiyammu bazai talauci ba,ke mubar juya kuɗi kwata,kwata har abada bamuyin talauci....
*****
BOƘA ZAƘAWANU ya ci gaba da gindiyawa Sarki safwan sharuɗɗa kamar haka .........Da zarar matar Abdullahi tazo haihuwa dodo na buqatar jinin naƙudarta.
Safwan yace''Nama bada jinin uwata bare na wata banza uwata ita kaɗai ta ragemin amma na bada jininta saboda in sami duniya.
Uwata ita taci kashi da fitsari na.
Ya matse ƙwallah karon farko da yaji tausayi a rayuwarsa.....
To balle jinin matar maqiyina.
Boka yace sharaɗin qarshe shine zaka duka kayiwa DODO SUJADA,shin ka amince?
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
22-23.
''NA Amince da wannan sharaɗi,kuma zanbiduk wata doka dake ciki, nama amince da sharaɗin barin sallah kwata,kwata a rayuwa bare wannan don haka na amince ni a halin yanzu buƙatata ce kurum a gaba na.
''hhhhhhhhhhhhhh!!!
Boka Zaƙawnu ya kwashe da mummunar dariya.
Kafin Safwan yace uffan tsintar kan sa kurum yai a gaban DODO.
Baƙar halitta ce mummuna bakinsa sai dalalar da baqin Jini yake,kuma gulama gulama,wannan halitta ita Safwan ya faɗi yaiwa sujada(wa'iyazubillah)
Kafin kace me sai algaitu da bushe,bushen sarauta suka dinga watsuwa a ko ina na cikin ɗakin.
Ana busa ana SAFWAN BAƘIN SARKI, ME BAƘAR MASARAUTA, DAGA YAU KAINE SARKI KAINE ME BAƘIN MULKI.
Koda aka gama wanka aka mishi da jini.
ya daɗe ana mishi wanka da jini tsira haihuwar uwarsa.
Gaba ɗaya yalwataccen farin ciki zaka hango a fuskarsa a yau mummunar buƙatarsa ta biya.
Daga baya Boka yace ya rufe idonsa.
Koda rufe idonsa ya buɗe tsintar kansa yai ɗakinsa.
Matarsa tayi mamakin ganinsa amma kuma ba yau ta saba ganin makaman cin hakan ba, duk da cewa tayi mamakin ganin ya koma matsafin qarfi da yaji.
*******
DARE ya raba A lokacin ukun dare ne Sumayya na kwance a saman katafaren gadonta barci take cike da nishaɗi da farin ciki zuciyarta fes bata da damuwar komai.
Sumayya ita kaɗai ce ƴa a wajen Safwan
tana kwance cikin daɗin barci ta tsinci kanta cikin baƙon al-amari shin mafarki ne ko gaske,zafi da zogi da raɗaɗin da taji yasata fasa gigitacciyar qara wacce tasa ba arziƙi mahaifiyarta fitowa.
Tirƙash!
ai ba Sumayya ba hatta mahaifiyar ta daskarewa tayi daga tsayen da take ganin Safwan mahaifi ga Sumayya kwance saman ta yai mata kaca,kaca,reaping na wulaƙanci.
Cikin kuka Sumayya ke faɗar
''Daddy nice,nice Daddy Sumayya fa ce.
Maman Sumayya,Wacce ta faɗo ɗakin fujajan daskarwa tayi, daga tsayen da take.hannu aka ta fashe da kuka ta soma cewa
''Alh.Me yassmeka?
Sumayyace fa ƴa ƙwal da ka mallaka a doron duniya.
ita ce kayi mata fyaɗe?
Safwan ya miƙe fuskarsa ko alamar razana da ruɗani babu babu alamar nadama ko da nasani a tare dashi fuskar sa sam ba tsoron Allah.
Buƙatar sa ta duniya kurum ke gaban sa.
Cikin kuka mahaifiyar Sumayya tace.
Ka sake ni a yau ɗin nan a kuma yanzu.
''Bazan tona maka asiri ba,saboda innna tona maka asiri Sumayya na tozarta,amma ka sani zama na da kai ya qare,wallahi,kuma Allah ya isaḷ tsakanin ni dakai ka jira yaumatubulasra'i insha Allah Allah zai bi mana haƙƙinmmu.
Safwan ya kwashe da dariya yace idan ana saki dubu nayi miki,kuma rufin asiri kar ki rufa min ki sane duk duniyar nan banga ubanda zanji wa kunya ba babu shi,ke ko me martaba zai dawo duniya yaga wannan aika,aikar bazan taɓa damuwa ba.
Sumayya ta safko daga saman gado tana tafiya tamkar ƴar kaciya,tace ''Mommy don Allah zan biki.
Safwan ya tillata saman gado,har goshinta ya dafji qasa.
Yace
''Babu inda zaki dake tazo?
Mahaifiyar Summayya ta dube ta idonta na sharar da hawaye tace''Sumayyah ki tuna Allah yana tare dake!!!
daga haka ta juya.Sumayya ta kifa kanta ƙasa tana kuka wiwi.
********
Kwana biyu da faruwar hakan Mahaifiyarmu ta mutu sakamakon aman jini.
Daga rashin lapiyar mahaifiyarmu kuwa ni kaina na kwanta jiyya.Rashin lapiya sosai.
Duk wata qasa da kika sani an kaini domin sanin ciwo na amma ina.
A shefa duk ciwo na ya danganci sheɗancin Safwan,ko mata na da sukaita mutuwa shike bada jininsu wa dodon tsafi ita ma Binta kafin na aureta mahaifinta babban malamin addinin musulunci ya shiryata tsaf.
Da ayoyin Allah kuma anyi anyi asha jininta yafi qarfinsU.
Haka ma yaranta sunfi qarfin dodo.
Safwan yabar sallah kwata,kwata a rayuwarsa ya zaɓi duniya fiye da lahirarsa wa'iyazibillah.
A ɓangarn Bashir kuwa duk wani asiri naci shike bani shi sai ya fake da yana bani kulawa dangane da ciwona kana kuma duk wani duk wani asiri na bisnewa Safwan ke bashi sai yazo ya bisne.
Koda wasa Safwan bai taɓa zuwa dubani ba.
Wai mutane me yasa muka ɗauki dogon buri muka ba duniya al-hali rayuwar qanqanuwa ce.
Shi Bashir munafinkin ɓoye ne bai taɓa nuna min ƙiyayyah a gabana ba Safwan shi ke nuna min ƙiyayyah da gaba da hassada.
MASARAUTAR ASAD.
Babbar masarauta ce kuma duk wani sarki dake duniyar nan Yasan da zamanta,kuma ƙarƙashinta yake masarauta ce me dumbin tarihi kuma a tarihinta ba'a taɓa sarkin da aka sha wahalarsa ba duk sarakunan da suka shuɗe a dalai ne masu tausayin talaka.
SAFWAN.
Yaiwa ƴarsa fyaɗe.
Safwan ÿaiwa ƴar cikinsa fyaɗe.
Safwan ya baiwa dodon tsafi jininn mahaifiyarsa.
Safwan yabar sallah kwata,kwata a rayuwarsa.
********
Yau wata na 2 da kwanciyata jiyya kuma ayau ne na warke tangaram.
Abin mamaki ba kuma wani yazo ya bani magani ba ba kuma likita ya duba ni ba ikon Allah kenanḷ
ko fadawa duka sunyi mamakin wannan al-amari sauqi kwatsamḷ
da yamma ina ɗaki naji sallama.
''Assalamu'alaikum.
Mamaki ya kamani nasan dai ni ni kaɗai ne to sallama daga ina?
ni da ƙofa take garƙame da jamlock.
Ido na ne yai min arba da farin mutum dogo,sanye yake da farin tufafi.
Kafin ince uffan yace''Sunana Mal.Abdurrahan.
Ni rauhanine cikakken musulmi.
...Nazo ne na sanar maka cewa ka yarda da ƙaddara wannan jarabawace tana daga cikin ƙaddarorin da ubangiji ya aiko zasu sameka ka sani cewar cikakken musulmi shine wanda Allah ke jarabta,Manzon Allah S.A.W yace duniya sijinil.Muminin wa jannatul kafeeroon. ...
Ayau sabuwar sauyi zai riskeka zaka rabuda ƴaƴanka sarautarkan wannan duk ƙaddararka ce domin kafin Allah ya halicce mu ya halitta annabawa kuma duk ya jarabcebsu to mu su waye da Allah bazai jarabce mu ba?
nan Mal.Abdurrahman ya kwashe labarinnan kaf ya faɗa min game da ƙullin da Safwan da Bashir kemin yaci gaba da cewa na para bibiysrsu don na tsimake ka to mahaifiya ta tace Muddin na sake taimakon musulmi Allah ya isa bata yafe min ba,ita ba musulma bace mahaifin musulmi ne kuma ya mutu.
Ina mata biyyah ina gudun fushinta
Yarona Bilal ilimin shi bai kai na yaƙi da sheɗanun aljanun da aka haɗaka dasu ba,amma zansa ya dinga bibiyarka sannan zai shiga duniya neman ilimin addinin musulunci a domin ya tayaka yaƙi dasu.
.........Yana gama faɗar hakan ya ɓace.
Mal.Abdurrahman,Mal.Abdurraham.........Naso ma ƙwalla mishi kira amma inq....Bazan iya tafiya nabar ka ba idan na tafi wajen wa zani? ban san kowa ba sai kai Abbu..
Amma Abbu idan mutuwar tazo me zai hana ka lallashe ta ka faɗa mata da gani sai kaine muke rayuwa, don haka ta ɗauke mu rana ɗaya nasan zata tausaya mana......Shiru yai ransa yana ƙissima rashin ilimi da jahilcin muhijjinatu sai tausayinta ya ɗaɗa ka mashi.
yana jin a ransa a kowwanne hali zai shiga sai Muhijjinatu tayi ilimi ta san kanta.
Dubanta yai yace.
Mutuwa saƙone daga ubangijin musulunci ke aiko mala'ika a azara'ilu ba magana yake ba bakuma a ganin lokacin da yake zowa sai dai kawai ya zare rai ya tafi,kuma baya ƙetare maganar ubangiji.
gyaɗa kai tayi kurum batar da ta gamsu da maganarsa ba tace.
To Abbu ci gaba da bani labarin yaya akai da sauran ƴanu'uwana kuma ta yaya kukayi rayuwa da mamana a DOKARDAJIN NAN?....
Daga wannan page ɗin a page na gaba za'a dawo labarin ma'ana labarin Abbun Muhijjinstu zai ƙare zamu dasa daga inda muka tsaya.
Idannnaga commts over zamu takarkare labarin zuwa anjima zan kara
page 1
in mai kowa mai komai ya kaimu gobe zamu ci gaba da dawowa labari.
Kuma book 1.ya kusa ƙarewa.A page 49-50.Shine book 1
sauran page ɗin har zuwa page 200 shine paid.Allah ya bada iko.
karku manta yawan page zai saka mu ƙara page ɗaya da