WATA RANA DA DADDARE BOOK 1 BY Aishat Falalu Rimin K'aura

Author :  aishat Category :  Romance

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 18.5K words

dai ina nuna muku bansan komai ba yanzu dai duk ba wannan ba, wacce hanya zamu bi mu gudu kafin gobe?

Zaro ido Rabiya tayi tana kallon Mukasshifiyya.

sassauta murya tayi ta dafe baki tace.
''Mukasshifiyya ki ma daina wannan maganar sam.
Ki duba girma da tsayin katangar masarautar nan ki gani ta ya, ta ina mutum zai iya guduwa?
ke kanki in kika duba tsayin katangar kanki bazai hango tsayinta ba.

Sau ɗaya tak! wani ya taɓa gigin guduwa Sarki yasa aka kamo shi aka yanke mishi ƙafa da hannu kana aka fille mishi kai, kafin a fille mishi kai sai da aka gana mishi azaba kala daban-daban. . . . .



*******
Da sanyi safiya kowacce ta kwaɗa wanka ta cire uniopom ɗinta ta wanke tas, domin al-adar sarki kenan kowacce sai ta wanke kayanta tas kana domin shi
ba'a ganinshi da ɗauɗa.

Domin ita kanta ɗauɗar muddin aka kamaka da ita, to hukuncinta dabanne.


Ƙaton kafet ne aka malala tundaga inda Sarki Safwan ya safko daga mota har zuwa inda bayi suke.

Gefe ɗaya kujera ce haɗaɗɗiya nidai Mom Hummy da na ruɗe cewa nayi kujearar zinari ce🙊🙊🙊

Cikin tafiyar ƙasaita, izzah girman ƙai ƙasaita dik ya tara waje guda. sannan ga , zalunci cuta ƙeta, da sannu dai zakuji waye Sarki Safwan.

Bayi biyar ne gefe, da gefensa, wato dama da hagunsa.

Ɓangare ɗaya kuwa ga wani nan tsaye baya um, baya UmUmm ba laifi shima shiga ce ta sarakai a jikinsa.

Fuskarsa ɗaɗɗaaure domin dama shi baya dariya, wato Sarki Safwan.
Kayan jikinsa da rawaninsa duka baƙine kalar tambarin sarautarsa.

Shi wannan bawan Allah fusakrasa cike take da yalwa , nidai na dasa mishi ayar(????)nayi mamaki da sarki safwan ya iya haɗa wajen zama da wani domin duk sarakunan Nigeria ƙarƙashin ikon S. Safwan suke to shi waye?"

SARKI, SAFWAN ɗaya bayan ɗaya yake bin bayin da kallo kowa ya sarda ƙanshi ƙasa alamar girmamawa.

Wannan bawan da yazo sanar musu saƙon zowar Sarki jiya shine ya miƙe ya soma magana kamar haka.

*Sarki yace ya gaisheku* *kana yace a gaya muku cikin shekarar nan anyi asarar bayi* *A ƙallah guda 50 don haka daga yau ya yarjewa kowanne bawa ya nemi* *baiwa ƴar uwarsa domin ta haka ne zakuyi ta hayyayyafa*
*sannan duk wacce tayi gardama akwai hukunci mai tsauri da za'ayi mata*
*baya ga haka yace bayan mace da namiji to zaku iya neman jinsi*
*wato mace da mace, namiji da namiji*

*sannan akwai horo da azaba ga duk* *baiwa ko bawan da yai wa gwaninsa* *gardama. *

07049138863.

̈̃̈̃Call 07012329134



WATA RANA DADDARE.🖤
🖤 (horror story)☠️

Writing
by
Aishat Abdul-falalu.
(Rimin k'aura).

(Mmn Humaira)



from the writer of

*Ishara. *

*So ko hauka. *

*Shagaltattun duniya*

*And new book WATA RANA DADDARE




https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp


🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_




page 13-14.


**BAYIN ALLAH**

Gaba ɗaya sun shiga mummunan tashin hankalin wannan baƙin zalunci na Sarki Safwan.

Sukan mazan gaba ɗaya farin ciki ne marar misaltuwa a zukatansu na ganin zasu samu abinda suke nema a kyauta.

**DOKAR DAJI**

**MUHIJJINATU**
Zaune ta zafga uban tagumi.
A halin yanzu ta gane cewar ita da Abbunta mutane ne ba dabbobi ba,ko kuma wasu launin halittu daban ba tamkar dai yadda ada take zato.

Tsanar Wanda yai silar jefasu a wannan halin yai mata tsaye a ƙoƙon ranta aranta ji take ina ace yanzu tai arangama da ɗaya daga cikinsu wayyo Allah! ai da a take zata kashe su har lahira.''shin su waye ma ɗin ?

dole ne ta ɗau fansar ran mamanta da kuma ƙasƙantacciyar rayuwar da aka jefata ita da Abbunta.
to amma ta yaya?

"Shin waye ummul-aba'isin jefasu cikin ƙasƙantaccen halin nan?

A gaskiya dolene ta koma ƙabarin mahaifiyarta a domin ganawa da wannan sheɗanin baƙin al-janin a domin ya fayyace mata komai.

Dole tana buƙatar jin babban sirrin nan a domin tinkarar koma waye yai musu haka ita da Abbunta.

Zuciyarta taji ta ƙeƙashe a fusace ta miƙe tsaye ta doshi wajen.


Koda isarta tsayawa tayi fuskarta babu alamar tsoro ko razani da ƙarfi ta furta.

''Shin kana ina kana ina baƙin aljani ka bayyana min kanka ''Shin meye ka ɓoye min gani nazo na shirya a shirye nake da ɗaukar koma meya kai nake jira.

Ka fito da sauri bana so na jima kar Abbu yazo ya tarar bana nan zai shiga damuwa.


''hhhhhhhh! hhhhhhh!!hhhhhhhhhh!!!
wata muguwar dariya me mugun sauti ta bayyana.
Dariyar ta karaɗe dajin baki ɗaya abin gwanin tsoro.

A halnkali sautin ya rage amo ya dinga fita sannu,sannu.

A hankali wani baƙin hayaki ya dinga tuɗaɗowa wanda saboda ƙarfinsa Muhijjinatu har rufe ido tayi ya zamana bata ganin komai face hayakin a hankali ya tsaya cak!

hayakin ya dunƙule waje ɗaya kan kwarangwal ya bayyana haɗe da wata baƙar guguwa.

Muhijjinatu ta tsaya cak!
babu alamar tsoro ko razana a tare da ita (to meye abin tsoro ga mutumin da tin buḍewar idonsa a daji yake rayuwa?)

''Muuhhijjjnnatuuuu!!!

bata ammsa ba illah zuba ma baƙinshi ido da tayi a inda yaci gaba da cewa''Mahaifinki ya faye taurin kai,munso mu taimakeshi mu tayashi ɗaukar fansa amma mugun taurin kai ya hanashi.

Ƴan'uwanshi sune silar jefa ku a wannan ƙangin da kuke ciki SARKI SSAFWAN da kuma ALH.BASHIR.

Yan'uwanshi ne na jini Uwa ɗaya uba ɗaya.

Jikin Muhijjinatu na ƙyarma tace''Waye SARKI SAFWAN,WAYE ALH.BASHIR?

''Kamar yaddaukayi miki bayani sune suka rugaza mishi rayuwa su suka ƙasƙantar da rayuwarku A DOKAR DAJI.

Kana nufin Abbu yana da dangi UWA ƊAYA UBA ƊAYA.....?

kafin ya bata amsa wata guguwar ta taso da ƙarfi wannan bame tsoratarwa bace........

**Assalamu'alaiki ya Muhijjinatu.
Sunana Mal.Abdurrahman ni cikakken musulmine kuma rauhanin aljani.
''karki sake ki bishi sheɗani ne yaudarrki zaiyi kansu haɗe yake..cutardake da Abbunki zaiyi kuyi hakuri Allah (S.W.A)shi ya halicceku yana sane da halin da kuke ciki zai kawo muku agaji kinji..Harda sauran ƴan'uwanki duk Allah zai saka muku kinji....


Muhijjinatu ta shiga ruɗani bakinta na kyaf,kyaf ta dubi wanda ya kira kanshi Malan Abdurrahman tace.
''ƴan'uwa kuma,dama ina da ƴan'uwa?.........
kafin ya bata amsa baƙin aljani yaɗora da cewar
ka gudu in baka gudu ba zan kira....

Ai kafin ya ƙarasa Mal.Abdurrahm ya ɓace bat.

Baƙin Aljani ya kwashe da dariya yace ƙyaleshi maƙaryacin banza.

''Ni ne zan taimakeki Muhijjinatu asiri sai asiri tsafe sai tasafi hhhhhhhhhh!

"Meye asiri meye tsafi?
Muhijjinatu ta fad'a

Akwai sauran sirrika ma Amma kijira sai WATA RANA DADDARE IDAn tazo mahaifinki ya faɗa miki sirrikan duka to daga ranar zan ɗora miki nawa kije ki jira tazo.

Yana gama faɗar hakan ya ɓace Muhijjinatu tai kira tai kira a domin yazo ya amsa mata jerin tambayoyinta da suke naniƙe a ranta,an kuma ƙara birkita mata lissafi .

jikinta ba laka tabar wajen.
**********

Koda Abbu ya dawo ya sameta salalaf.
Shikanshi yasan akwai damuwa a tattare da Muhijjinatu.


Bawan Allah duk ya kiɗime hankalinsa kacokam ya koma kanta.
Babban burinshi yaji abida ke damun ƴar tilon ƴarsa da ya mallaka a DOKAR DAJI.


damuwar Muhijinatu ɗaya kar Abbu ya fahince ta ina taje kar ya gano ta haɗa kai da sheɗanin da kullum yake gargaɗinta da kar ta sake ta tinkari inda yake.

Sai dai abunda bai sani ba shine zuciyar Muhijjinatu ta ƙeƙashe a halin yanzu bata ji bata gani.

Bayan Abbu ya gasa nama taci ta ƙoshi ta dube shi kana tace''Abbu wai dagaske akwai abun bauta da zai kawo mana agaji ya taimakemu ya saka mana akan cutardamu da akayi,dama akwai shi amma me yasa baka taɓa sanar minba?

koda Abbu yaji haka a take ya faɗi ya soma.ƙirjinsa yai ta fat,fat.




.






https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp


🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_




PAGE 15-16.



KAGA dole ne ka nemo mafita, a halin yanzu yaron nan Haidar kaɗai yasan *securityn*shiga ƙofar get ɗin da dukiyr nan take.
to wai tukun shi boka Zaƙawanu me yace game da rashin maganar Haidar?

Sarki Safwan yace''cewa yai wai bazai taɓa magana ba sai ranar da yai tozali da mahaifinsa Abdullahi. . . . . . . What?

Alh. Bashir ya faɗa a kwai gagarumar mstsala kenan, to ashe bazai warke ba, domin Abdullahi dai baya raye.


ƙyal-ƙyalewa da wata muguwar dariyar ƙeta Sarki Safwan yai yace''banda ƙarya da jahilci irin na Boka zaƙawanu ina Abbdullahi yake a raye wanda ya daɗe da sheƙawa. . . . . Cigaba yai da dariyarsa tamkar bashi ne cikin baƙin ciki yanzun ba.

Alh. Bashir yace wallahi nafika baƙin ciki rashin samun kuɗin nan domin dalilin kuɗin na sadaukar da lahirata na zaɓi duniya amma never ace ba nan ba chan a sake lalubo mafita. . . . .

Ai ni na fi chanchanta da na mallaki dukiyar nan kaifa shuwagabannin ƙasashe su baka, kamafa raina arziƙin govnoni amma duk da haka mugun son abun duniya yai maka katutu ga sarautarka,, Yaya ga zaluntar dukiyar masu kuɗi,haƙƙin ƙasa ka taushe duk sarakuna tsorn zaluncinka suke . . . . . . . .

''Kai Bashir hattara banda kana ɗan'uwana ka isa ka tsaya a gabana kana faɗa min wa'innan maganganun?
ina sarki. . . . . .


dariya Bashir ya kwashe yace''Yaya Safwan kenan sarautar da ka ƙwace da tsiya. . .
Yana gama faɗar haka yabar wajenḷ




**************

Jamila ta dubi Muƙashifiya tace''wayyo mun shiga ukuḷ
yanzu haka rayuwarmu zata ƙare kamar dabbobi ?

Haka banza wofi zai zo ya cuɗanya damu kamar marassa gata?


Muksfy tace.

''Wallahi summa tallahi babu wanda ya isa ya kusance ni banda mijin aurena, Domin. . duk namijin da yai gigin shiga gonata to tabbas ajalinsa ne ke kiransa.

Kuka Jamila ta fashe dashi da ƙarfi, tace Mukassfy inkinsan waccece ni sai kin tausaya min, ga gata ga bayi ina su amma wai ayau nice baiwa marar gata, an sato ni an raboni da mahaifina mai sona NI ƳAR SARKIN GARIN GABAS CE. . Sannan nice ƴa mace duka yayuna maza ne. Kuka Jamila take wiwi. .

Kukan ta ya karaɗe ɗakin baki ɗaya, don haka sukayo caaa

Farisa ta basu labarinta tace NIMA ƳAR SARKIN KANO CE.

Ruƙayya tace ƴar sarkin Katsina gaba ɗaya sai suka gane cewar ashe baƙi ɗayansu duka ƴaƴan sarakain ne.

TO abin tambayar anan shine meye dalilin tara ƴaƴan sarakai da Sarki Safwan yai?


Koda kowa ya gama bada labarinsa tsaf Muƙashifiyyah tace.

Ni nawa labarin yafi na kowa al-ajabi da bugun zuciya da girgiza da razana da kuma ruɗani kunsan koni waccece?

baƙi ɗaya kowa yace''dama mun daɗe munasan sanin labarinki Muksfyyh.

Murmushi tayi kafin tace kunsan wanda ya tara mu anan?
gaba ɗaya kowa ya girgiza kai Alamar ''Ey.

''Waye shi ?
ta tambaye su
"Azzalumi Sarki Safwan.
Uhum'' to ƙanen Mahsifinanene uwa ɗaya uba ɗaya asali ma sarautar ta mahaifina ce ya ƙwata da ƙarfi ya salwantar da rayuwar mahaifina. . . . . . . Cije yatsa Mksfy tayi ta fashe da kuka.


Baki ɗaya kowa ya ɗago yana dubanta a razane har Jamilar ma tana mata kallon ko kin zare?

kuyi manage banda charge ne. . . . .

07049138863.

🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_


PAGE 17-18.


Share hawayen fuskarta tayi tare da yin wani ɗan taƙaitaccen murmushi tace''Nasan zaku ce ko na zare ko?
Garau nake.

Murmshi Mksfy ta yi tace ''Kunsan ban taɓa muku ƙarya ba ko?
Kuma bazan Fara daga yau ba.

Ni Mukasshifiyya bana ƙarya hasalima mun gaji gaskiya a wajen mahaifinmu mai tsoron Allah.

Dalilin da zaku gaskata ni shine''Nasan kunsan Sarki Safwan ko?

Kowa yace

''Ehy''

Kowa yasan shi.

Mukasshifyyah tace ku hararo kamanninshi ku gwada da nawa baku ga kama ba?

Sannan ku hararo kamannina da wannan saurayin Yayana nane Haidar UWA ƊAYA, UBA ƊAYA.

Baki d'aya wajen ya kaure da hayaniya kowa yana faɗar Albarkacin bakinsa.

Sadiya tace''Tabbas hatta hasken fatarku kala ɗaya ne.

Ruƙayya tace tabbas saurayin nan kowa ya ganku dashi yasan kamarku tamkar an tsaga kara.


To amma me ya kawo haka?
Jamila ce mai faɗar hakan ta gyara zama tana mai fuskantar Mkshfyy.

''Kina nufin Sarki Safwan bayan rasuwar mahainki ya gaji sarautar, to amma me yasa yabarki matsayin baiwa matsayinki na ƴar'ɗan uwansa ba.

don Allah Mkshfyy muna san sanin labarinki .

Ɗagowa tayi ta dubesu tace.
''Zan baku labarina, amma labarin masarautar nan bazai yuwu ba da rana, ko da safe ko da yammaci.

To sai Yaushe?
Jamila ta fad'a

Sai DADDARE domin masarautar nan tana da wani BABBAN SIRRI wanda bazai faɗu ba da rana, amma ku jira lokaci yana zuwa, amma yanzu ba zs bane abinji wannan iftila'in da ya faru shine abin ji wajen mu.



*****DOKAR DAJI****

MUhijjinatu tsaye daodai inda guguwarnan take idonta ƙur akanta tace.

''Kai waye?
Kuma me yasa ba'a bada labarin SAI DADDARE?

"hhhhhhhhhh!!!

Kamar dai koda yaushe wannan mummunar dariyar ƙwarangwal ɗin ya fashe da ita.

Yace "Muhhiijjjinnahhh!!!""

zan taimakeke, amma na faɗa miki dole ne sai ya baki labarinnan sannan zan dasa miki daga inda na tsaya.

kije ya faɗa miki sirrin DARE.
Zan taimakeke.
''Kayi alƙawari muddin babana ya faɗa min zaka taimake ni ka dawo min da Mamana?

''Ehyyyy nayi Alƙawari muddin kema kika bi sharuɗɗan mu.

Kuma ba zaki ɗauki fansa ba saida izinin mahaifinki.

Zaro ido Muhijjina tayi tace''Mahaifina bazai taɓa amincewa dakai ba hasalima ya tsaneka!!!

"Nasan da haka ai akwai dubarar da za'ayi mishi.

''Wacce dubara ce?"
Dole ki mutu ki dawo

In MUTU, kuma INDAWO, kaman ya?

"Hhhhhhhhhhhhhhh!!!!

Nifa sheɗanin aljanine bana tsoron Allah, uwata ta tsinee mini ubana ya tsine mini, sheɗanci babu kalar da ban iya ba.

Da zarar kin mutu, to zai fusata sosai sabida a halin yanzu duk duniyar nan kece kaɗai sanyin idaniyarsa kece kaɗai yake gani yaji daɗi to kinga muddin yaga gawarki to zai yadda yabi mu mu tsafa shi domin ɗaukar fansa.

''Kin amince?


Ehy''

Na amince da sharad'i

Muhijjinatu ta faɗa fuskarta ba tsoro ba razana.


**

Cikin gaggawa ta baro wajen baƙin aljani ta doso sansaninsu.

Cikin fargaba ta iso, tsoronta kar Abbu yazo ya tarar bata nan bata san wacce amsa zata bashi ba.

Tin tashinta bai taɓa zuwa wani waje ya dawo ya tarar bata nan ba.


Aikam gabanta yaci gaba da bugawa ganin yadda taganshi tsaye ya zuba mata ido.

''Muhijjinatu daga ina?

Ammm! Umm!
Baiwar Allah bakinta bai saba da ƙarya ba duk ta gigice.

Katseta ya kuma yi.

"Daga Ina Muhijjinatu?

"Abbu naje ganin tsuntsaye ne.

Dama kina zuwa dubo tsintsaye?
"Ki sani cewar tuni tunin duniya ake mutuwa, kuma duk wanda ya mutu bazai taɓa tashi ba sai ranar tashin alƙiyama.

Mutuwa ɗaya ce tak!
Kuma shikenan bazai dawo ba,Kuma kowa zai mutu,kowa Sai ya mutu Kuma duk Wanda ya mutu bazai dawo ba.


Kef, kef jikinta ya katse da ƙyarma shikenan Abbu ya gano ta.

******

A yau ma kamar kullum Farida ta fito cikin shiga ta al-farma ta shiga motar Daddynta.

Sunyi hon, hon, shiru ba me gadi ba alamarsa.

Zaune yake yanata barci. . . . Cikin fushi Farida tazo ta ɗaga hannu ta sharara mishi mari.

A zabire ya miƙe firgigit.

fitowar Azkafiyya kenan daga cikin gida.
Gaba ɗaya gigicewa tayi ta saki wata iriyar ƙara. .

Aikam batai wata wata ba isa tayi daidai inda Alh. Bashir yake tsaye ta kam daddage iya ƙarfi, bai zata ba Farida ma bata zata ba AZKAFIYYA ta kwasheshi da mari.

wayyoḷ Bala'i
Farida ta gaza cewa uffan, Alh. Bashir ya gaxa cewa uffan.

Azkafiyya ta ruga da gudu bayan Mal. Kabir.

Ruƙota yai yajata suka nufi boysqeaters.

Da gudu ya isa ya iske Mariya zaune tsna cin ɗumame yace Mariya ''Mun shiga ukuḷ
Azkafiyya ta mari me gidannan Alh. Bashir.
Gwalalo ido Mariya tai warwaje.


ɓangaren Farida kuwa mamaki Al-ajabi ta cije yatsa wai ko barci take?
Amma da zarar ta farka Alh.Bashir mahaifinta tsaye mamaki ya kasheshi.

wai ƴar matsiyata ce ta dallara wa mutum me kuɗi irin ubanta mari.
Tiƙashḷ

''Na rantse da girman Allah a yau sai kin gwammaci mutuwa da rayuwa dagake har matsiyatan iyayenki kuma sai hannunki ya rabu da gangar jikinki.

''Wallahiḷ Wallahiḷḷḷ.

Yau zaki shiga musifar da bala'i na gidan duniya. . .

kKafin kace me sojoji sun cika gidan sun zagaye ko ina.

Farida tsaye tana ba sojoji Umarni.
''Ina so da Uwar da uban ku yi musu ligif.
Ita kuma ƴar ina so ku tsinko min hannunta. . . . .



Zama tayi ta kame akan kujera tana jiran a tsinko mata hannun Azkfiyyh a yau sai taga ubanda ya ɗaure mata gindi.

Zamanta ba jimawa sojan yazo yake sanar mata an duba boysqeaters ba kowa,ba komai hasalima tamkar biladama bai taɓa wanzuba a wajen.

''Babusu kaman wasu Aljanu?
''Ranki ya daɗe zaki iya dubawa.

To ta ina suka bi?
Duk fa an kukkule ko ina kai never ,,Hannu ta ɗora akai ta fasa kururuwa,sojan ne yazo yake bata haƙuri akan karta damu suwaye su?
da har zasu gagaresu gano wa a wannan
duniyar.

Tofa duk wata social media an ɗora hoton Azkafiyyah M.Kabir da kuma kyautar maƙuḍan kuɗaɗe ga duk wanda ya gansu ko ya san inda suke.


tofa. . . . . . . . .



duk group ɗin da basa commts wannan ne last page ɗinmu.


07049138863.

̈̃̈̃Call 07012329134


🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_



PAGE 19-20.




**A DOƘAR DAJI **
**TOFA**

'
DARE ya raba sosai MUHIJJINATU na tsaka da barci me daɗi.

ABBU Ya taso ya yaye bargon da ta lulluɓa dashi .

Yace Muhijjinatu tashi !
Tashi!
Yau Zan baki labari, A DAREN YAU ta tabbata duk amsar da kike buqata tana cikin wannan DAREN.

Cikin magagin barci tace''Abbu wannan wanne kalar labarine da ba'a ba dashi sai DADDARE.?"

Toshe mata baki yai yace''Idan kika bari wannan damar ta wuce sai kuma nan da shekara A WANI DAREN kar ki kuma cewa komai amsar da kuma sirrin duka suna cikin

3 / 7