WATA RANA DA DADDARE BOOK 1 BY Aishat Falalu Rimin K'aura

Author :  aishat Category :  Romance

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 18.5K words

Dad ɗinki wayayyen mutum ne sosai kekam kin caɓa. DAma ni.

Farida tace.

''Shi kaɗai ke wayayye Allah ya tsimake ku ya kori Mommy da tuni ta kwafsa mana, kunsan ita rainon ƙyauye ce.

baki ɗaya suka saka dariya.

Shigowar Mariya ya katse su ta ajiye musu ababan ciye, ciye da shaye shaye,
ƴarta Azkafiya tana biye da ita.

Tsawar da Farida ta dakawa Mariya ya katse Azkafiyya daga kallon da take bin ƙawayen Farida dashi.

''Ke wacce iriyar jahilar ƙyauye ce iye?
Uban meye nan kika ƙwaɓa min?

shiru Mariya tayi, ran Azkafiyya idan yai dubu ya ɓaci, kwashe kayan haukanki muje restaurant a chan munyi lunch ɗin.

jikin Mariya na ɓari ta kwashe kayan, ran Azkfiya ya dugunzuma sosai.


na irin wulaƙancin da farida kewa mahaifiyarta. .


**DOKAR DAJI**

Gari ya waye rana ta ƙwalle ƙwall yau Abbu baya zuwa ko ina zamansa zaiyi da Muhujjinarsa susha fira.

Tashi tayi daga kishingiɗar da take tace.

''Abbu!
"Na'am ya Amsa yana kallonta.
Kace Mahaifiyata ta rasu ko?"

gyaɗa kai yai alamar

''Ehy, ta rasu wajen haifarki, kuma ni na binneta da hannuna.

''Abbu ina ne wajen, kuma me yasa baka ziyartattta?

Ya kamata ace nima ka nuna min wajen in dinga zuwa ina ziyartatta, zataji daɗin ganin ƴarta.

''Na tabbata da ace mahaifiyata zata dawo wannan duniyar to zata yi fushi dakai, na mantawa da ita da kayi baka zuwa inda take.

Koko dama bakwa san juna kaida ita, ba soyayyah da ƙauna tsakaninku?
"
"Abbu baka kyauta ma mahaifiyata ba
"Ina so da k'auna da shak'uwa?

Shiru yai batare da yace uffan ba,illah hawaye kawai dake zirarowa a kwarin idonsa.

''Abbu ta kirasa.
bai amsa ba.
Hawayen da ta hango a fusksrsa yasata fashewa da matsanancin kuka me zafi, tausayinsu ita da Abbun ya kamata.

Sai taji me yasa take yawan takura mishi da tambaya?

shi a kullum burinshi ya sadar da ita farinciki ya kyautata mata kullum shine burinshi.

tayi zurfi wajen dogon tunani shima ta ɓangarensa tsananin tausayin zuƙeƙiyar budurwa kamar Muhijjinatu RAINON DAJI. ita kwata, kwata batasan jin daɗin duniya ba, basan farinciki da baƙin ciki ba ba ilimi an tauye mata rayuwa. (nikam nace meye sanadi)

gata duniya amma ita da dabba kusan lissafin su ɗaya ne banbancin ita takasance mutum ƴar Adam, tun da ta tashi tare da dabbobi take rayuwa sune abokanta, an hanata jin daɗin duniya. . . Kullum takure waje ɗaya. . . . .

Muhijjinatu!"
Firgice ta waigo,tare da zuba mishi ido

''Tabbas ban kyautawa mahaifiyarki ba, , ban kyauta ba yadace ace ina zuwa ina ziyartata amma ba laifi na bane. Ina da hujja. .

Ɗan jan nunfashi yai kafin yaci gaba da cewa ''Zan baki labarin rashin zitarta ta da banayi amma kiyi haƙuri akwai RANAR DA ZATA zo WATA RANA DADDARE zan baki labarin zan kuma amsa miki dukkanin tambayoyinki DADDAREN sai dai kafin nan yau ɗaya tashi muje kabarin mamanki in sadaki da ita. Kiga inda na binneta.

Tsantsar farinciki Muhijjinatu bata san lokacin da ta daka tsalle ba ta ta rungushi, kamo hannunta yai suka jera.


**BAƘAR MASARAUTA. **
Jejjere suke kowacensu mazansu da matansu, sanye cikin baƙin unifan baƙi kallo ɗaya zakayi musu ka tabbatar da cewa dukkaninsu bayi ne.

Saɓanin da da ya kasance a tarihin masarautar unifoam ɗin bayi kore ne shar amma dai muje zuwa muji dalililn da ya sa yanzu ya kasance baƙi wuluƙ!

Mukashifiyya dake zaune taji an dafa kafaɗarta.
Ta juyo don ganin waccece.
Jamila ta dubeta ''Mukasshifiyya tunanin me kike?

''Ba komai Mukashifiyya ta faɗa batare da ta juyo ta dubi Jamila ba.
''Jamila tace ''Kin cika girman kai''Shi yasa kowa ya fita harkar ki.
nikaɗai na damu dake kowa sai yace kin cika girman kai. bakya sakewa da mutane.
Mukashifiyya bata ce uffan ba illah miƙewa da tayi ta miƙa kwano aka zuba mata shinkafa da wake dafa duka, wacce fara ce ƙal, ba mai ko ɗis, haka zalika ba kayan miya. Sannan ita suke ci DARE DA RANA. .
bayan an zuba mata kamo hannun Jamila tayi suka zauna saman ɗan damalin dake wajen.
Su biyu suna zaune Mukasshifiyya tace

''Jamila bawai bana san sanar miki damuwata bane Aa''ni bani da girman kai daga yau zan dinga sakewa da kowa a gidannan bakusan ni bani, shi yasa kuke ganin kmar ina da girman kai. Tausayinn kai na da ku nake na ƙuncin rayuwar da aka saka mu a ciki.

Yanzu damuwar da tafi damuna ita ce Ƙarshen shekara yazo, lokacin SADAUKARWA DODO da jinin wasu daga cikin mu yayi damuwata da fargabata.

''Shin wa za'a ba Dodo?
''Fata na ya kasance nice na gaji da ganin baƙin ciki kullum ana kashemu kamar dabbobi.

Ina tausayawa duk wacce ya kasance ace ta zama rabon DODON TSAFI.

Wannan rashin imani na SARKI SAFWAN ya ishe ni.

Shiru Jamila tayi.
kafin ta jero mata tambayoyi.
''Don me zakiyi wa kanki fatan mutuwa?
"Shin bakya fatan ki sake saduwa da iyayenki?
"Don me Zaki zab'i mutuwa a yanzu,alhali dukkaninmu muna fatan kawo k'arshen sarki safwan.

Mukashifiyya ta fashe da kuka. Kuka haiƙan me cin rai kafin ta dubi Jamila tace.

''Jamila ku kuna fatan sake saduwa da iyaye a wannan duniyar saɓanin ni da na banbanta daku fatana shine nabi iyayena a inda suka tafi.

Bani da uwa da uba bani da kowa a wannan duniyar. . . . . .

''Bangane ba


''Shin daga sama kika faɗo.
A''a nidai nasan an ɗauko ni a wani DARE,tsintar kaina nayi na ganni nan.
A wannan BAƘAR MASARAUTAR a wani
lokaci DADDARE.

Jamila tace gaskiya maganarki ta rikitani ta damalmala min lissafi

''Amma dai muci abinci tukunna.

Kowaccensu kwanon shinkafa ta j awo
suka soma ci hannu baka hannu kwarya domin sai sun galabaita da yunwa ake basu abinci.



**DOKAR DAJI**

''MUHIJJINATU wannan shine kabarin mahaifiyarki'' anan na binne ta.

Matata BINTA. Abar sona, abar ƙaunata DARE DA RANA. . . . . . . ƙaryane baka santa, baka ƙaunarta, da kanasanta da ka ɗaukar mata fansa. . . .

''Kaasheeta akaayii''

jikin Muhijjinatu ya soma rawa.

''Abbu Waye?

be bi takan tambayarba yace

''Abbu mubar wajen nan.

''hhhhhhhhhhhh!!!"

''Abbu kana faji ance Mamata kasheta akayi, kuma za'a ɗaukar mana fansa''

"Abbu meye haɗinka da wannan Baƙar guguwar?

"Wacce ce mahaifiyata,Kaima waye Kai nima waccece?

ka amsa min karon farko a rayuwarsu da ita.

Ya daka mata tsawa da ƙarfi.

''Ki wuce muje nace''......

07049138863.





https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp






🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_




9-10.

''Babu inda zamuje, mu tsaya a ɗaukar mana fansa.

''Me magana ka bayyana kanka.

Wata muguwar dariya me haɗe da baƙin sauti ta bayyana.

"Muhijjinaaa!!!"

me maganar ya faɗa.

Abbu ya ɗaga hannu ya shararawa Muhijjinatu mari.
dafe wajen tayi saboda zafi.
Fisgota yai yace muje.
ruƙota yai gam yajata keeyyy!!!
Suka bar wajen.


***


"Farida kinyi ƙyau sosai wannan wanka sai ina? kamar zaki gasar kyawawa

''Allah ko Mommy?"
ƙwarai da gaske''
Washe baki tayi sosai take farin cikin yabon da Mommyn tayi mata.

ina ma yadda kike kyakkyawa haka ma zuciyarki''
turɓune fuska tayi.

''Kai Mommy mi kuma nayi?
"Jiji dakai da wulaƙanta ɗan adam.
ki bar wannan halin farida, da talaka da mai kuɗi duka Allah yai su, kuma duka matsayinsu ɗaya illah wanda yafi tsoron Allah.
Dudu nawa duniyar take.* (duniyar da za'a barta me ya kawo* haɗama???*
*Rayuwar da zata ƙare ina farin ciki*??
*jikin da zai zama gawa me ya kawo ɗagawa?*)
"Don haka kisan abinda kikeyi Farida duniya bata da tabbas, wata kil talakan da kake wulaƙanta wa a duniya ranar gobe shine zai fara shiga aljanna.

Duk wannan zantukan da Haj. Zainab keyi Farida najinta har yanzu bata ce uffanba.

dubai abaya ta saka kalar sikyblue
a gaban Haj. Zainab tabar ɗakin fuskarta sam ba annuri.

A tsiyace taja motar a gaban wani shararren shagon alawowi ta parking ɗin motar ta ta shiga.

Ta jima tana jibgo alawowi da chaculate kala, kala masu daɗin dandano.

Kana daga ƙarshe ta hau mota, tana direving tana taunar chachulate, tana lumshe ido irin tana cikin nishaɗin nan.

Koda ƙarasowarta gida bakin get, tai hon, tai hon, amma maigadi barci kurum yake da ƴar radionsa tana ta yi.

A fusace Farida ta fito daidai inda yake zaune yana barci.

A zabire Farida ta ɗaga bencin ta maka da ƙasa, Mal. Kabir yai wata irin super ƙasa bakinsa ya dafji ƙasa, haƙorinsa na gaba ya tsalle ya faɗi, jini yai tsartuwa.

Cikin fushi tace ''Uban me kake?

''Saboda gaka matsiyacin banza da wofi
har lokacin barci gareka, har hutu ke akwai ga mutum talaka?

talaka baya da yanci baya da galihu idan ba zaka iya ba akwai matsiya ta da yawa irinka.

Tana gama faɗar hakan ta kama gabanta.



'Mariya matarsa ta fito ranta a matuƙar dagule tace.

''Malan yanzu haka zamu ci gaba da zama da wa'innan mutanen cikin wulaƙanci haka , dubi yadda ta zubda maka haƙori ƴar cikinka.

Azzkafiyyah ta fashe da kuka tace ''Wallahi mun gaji da wannan wulaƙancin kuma sai mun ɗauki fansa.
mu tashi mu bar musu gidanan mu huta.

Mal. Kabir ya ruƙota yace.
''Nutsu Azzakafiyyah a domin ki muke zaune a gidannan badon keba da tuni nabar nan mutunci na yafi haka. .
Inaso ki ɗauki fansa Azkkafiyyah.
Ki jira lokaci zaki san komai yau da gobe.

Azkafiyya tace Baba Me kake nufi?

dafe kai yai yace. ''Wash!

ruƙoshi sukayi suka bar wajen abin gwanin tausayi.


**DOKAR DAJI. **


''Abbu kayi haƙuri dole ne ka bani amsar tambayata.

''Me yasa baka ziyartar kabarin Mamata?.
Shiru yai ita kanta ta fitar da ran zai bata amsa chan ya ɗago yace.

''Wannan mummunar maganar da kika ji ita ce amsar maganar. . .


A naso a saka ni cikin harkar TSAFI ne inba haka ba ba'a mutuwa a dawo. Dukkanin wanda ya mutun ya tafi kenan har abada.

Suna so su tursasani na bisu na dawo da gawar mahaifiyarki a wannan duniya.
Anaso a sarrafata ta miƙe ta ɗauki FANSA akan wa'inda suka aikata mana haka.

Amma ina so ki DUNƘULE maganar waje ɗaya ki jira ranar tazo, wato WATA RANA DADDARE. zan warware miki komai.

Kan Muhijjinatu ya toshe waje ɗaya ta dubi Abbu tace ''Meye amsar WATA RANA DADDARE?

''Yaushe ne zata zo?
"Yaushe zata zo?"
"Yaushe zata zo?"
ta faɗa game da fashewa da kuka.
da gudu Abbu ya ruga ya ɗauko sharɓeɓiyar wuƙa ya dasa a maƙogwaronsa yace.

''Muhijjinatu na lura ni ɗaya nake kiɗa na inyi rawata, ni kaɗai na damu da farin cikinki, ke bakyasan dukkan abinda nake so, dukkan abinda kike so a doron duniya ƙoƙari nake naga na samar miki shi.
Da kinsan irin ƙunci da ƙuna da raɗaɗin da nake ji da zarar kinyi min maganar jin muɗin su waye, nace kiyi haƙuri akwai RANAR da zata zo DADDARE, zan sanar miki zakiji komai har ma abunda baki tambayeni ba.

ina san dukkan abinda kike so amma tinda kikaga banbaki labarin nan ba da akwai dalili, to amma tinda kin gaji dani da rayuwata kin gwammaci ki kashe ni da kanki domin da kiyi min wannan tambayar gara ki ḍaɓa min wuƙa a maƙogwaro in huta.

Ya ɗan ja numfashi kafin yaci gaba da cewa ''Nasan ba zaki iya kashe ni ba mafarin na yanke shawarar gara ni na kashe kaina da kaina tinda kin gaji dani A YAU ZAN BAR MIKI DUNIYAR.

''Zan kashe kaina Muhijjinatu''
da gudu ta miƙe ta ruƙo shi da ƙarfi.

''Abbu na tuba, na tuba Abbu!!!"
''Ka yafe min kayi min afuwa.
''Bazan kuma ba!
sai kuma ta fashe da kuka.
tausayinta ya kamashi. Shima sai ya fashe da matsanancin kuka me ɗaci me ciwo me tafe da baƙin ciki, su duka biyu sai suka rungume juna suna kuka sosai.
bai san lokacin da yai jifa da wuƙar ba.
Kuka suke wiwi su duka ba mai rarrashin wani daga bisani shi ya koma rarrashin muhijjinatu.

Ɗauƙarta yai cimak ya shiga ɗaki da ita ya ɗauƙo kayan marmari dangin Apple da banana da kankana ya yanyanka da baki ya dinga bata tana ci yana mata labari mai daɗi sai gashi ta murmure. . . Sun koma tamkar basu ne ke kuka a yanzu ba.

Kwanciya tayi ya jawo bargon fattar dabba ya lulluɓeta yace-
''Muhijjinatu zanje na kamo mana kifi.

''To Abbu ka dawo lafiya''
ƙyaren katakon ya jawo ya rufe ƙofar ya tafi kogon kamun kifi.

Tafiyarsa babu daɗewa ta soma barci, barci ne me tattare da miyagun mafarkai barkatai, mafarki ne dai akan mutumin nan mai mummunar murya, me tsoratarwa da razana shine ya dawo mata.

Cikin barcin ta ganshi yana cewa ''Muhijjinatu ki bamu haɗin kai zamu dawo miki da mamanki ku ci gaba da rayuwa. ''kar ki biyewa mahaifinki domin shi bai damu da ita ba ke kuma mamanki ce ki bamu haɗin kai.
''kin amince koko?

Kafin ta bud'a Baki ta Bashi amsa ta farka a firgice.
tambayoyi daƙare a cikin zuciyarta tabbas akwai lauje cikin naɗi.
Duk yadda akayi da akwai abinda Abbu ya ɓoye mata tanasan tasan koma meye.


*****DOKAR DAJI. ****
Lallai ya zama dole ta koma kabarin mahaifiyarta, dole ne taje ta binciko me ke wakana a wajen.
Tinda Abbu yaƙi bata labarin dole taje wannan sheɗanin aljanin ko ma fatalwa ne shi ya bata labarin, to Amma ta wacce hanya?
Murmushi tayi da ta tuna mafita ta tuna *hanyar da zata bi don gano gaskiya. *

07049138863.


https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp


🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_

Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)

The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_




PAGE 11-12.

''Shin meye alaƙar Abbunta da wannan baƙar guguwar?
dole ne na bi ƙwaƙƙwaf na gano gaskiya.

Muhijjinatu dai tana daga kwancen nan dai zuciysrta nata saƙa mata abubuwa da masu ƙyau da akasin haka.

''Dole ne naje ga ko waye, dole ne na amince da ko waye. Muddin zai dawo min da mahaifiyata na rayu da ita in rayu da ita da mahaifina a waje ɗaya.

Sannan nayi alƙawari sai na ɗauki fansar duk wanda ya kashe min mahaifiyata.

Ahalin yanzu na fahinci muɗin mutane ne ƴan adam bamu kasance ɗaya daga wata halittar ba.
To Amma meye dalilin mu na keɓancewa a dokar daji?
wannan amsa sai Abbu.

Dole na jira sai WATA RANA DADDARE kamar yadda yake faɗamin.

********

Gudu take falfalawa sosai kamar wacce zata tashi sama.

Ba zato ba tsammani taga tsohuwar a gabanta.

Ƙuuuu!

Cikin hukuncin Allah tasa giya motar ta tsaya.

Cikin musifa da bala'i ta fito fuskarta ko kaɗan ba annuri bala'i kawai ke cinta.

''Ke wacce iriyar tsohuwa ce mai karanbanin tsiya salon kija na taka kiki
ki ɓata min tayar mota. Ki jazamin azumin ba gaira ba dalili.

''Na rantse bacin ina tsoron lafiyata data bisa kanki zanbi in wuce.
gobe sai inga kin fito, don haka tsohuwa aje gida a koyo wayo da hankali.

duk wai'nnan zantukan da Farida keyi tsohuwar nan bata ce uffan ba.

Ido kurum ta zubawa Farida.

Farida tace. ''Ki matsa zan wuce. . . . .
Shiru bata tanka ba hakan ya fusata Farida ta juyo a fusace da nufin ta zo ta jefar da tsohuwar. Kwatsam!!! ta nemi tsohuwa ta rasa.

Hakan ko kaɗan bai tsorata Farida ba bai kuma girgizata ba illah dariya da ta fashe da ita a ranta tace.

''Tsohuwar banza ko mutum ce ke ko aljana duk zan iya dake ni zakiyiwa siddabaru.

Nikam MmnHummy nace anya Farida kina da hankali kuwa.



**BAƘAR MASARAUTA. **

A ƙallah zasu kai kimanin mutum ɗari biyu mata da maza, bayi kowacce sanye cikin uniofoam baƙi wuluƙ!

Abinda ke ɗaure min kai ni Aishat shine har yau banga wannan sarki mai baƙar masarauta ba.

Jamila da Mukasshifiyya suna zaune, lokacin hantsi ne, dukkanin bayin mata da maza kowacce na al-amurran gabanta.

Wani gajeren bawa baƙi yazo yana sanar dasu cewar ''Sarki yace a sanar musu gobe i war haka yana nan tafe.

Koda ya gama jawabinsa sai ya bar wajen dama shi ba ya ɗaya daga cikinsu.

Mukashifiyya ta dubi Jamila tace-

''Mugun baƙin ɗan saƙo kenan baki ga duk bayin dake wajen nan ba kowa ya sha jinin jikinsa ba?

Jamila ta ɗaga kai ta kalli bayin gaba ɗaya kowa yai saranda.

Ǧyaɗa kai tai tare da zubawa Mukasshifiyya ido tace.

''Me hakan ke nufi?
Tabbas naga wasunsu ma kuka sukeyi.
Mukashifiyya tace.

''Ai mun shiga uku!
''Zuwan sarki ba alkhairi bane. Domin
kowa anan cikin fargaba yake.

Zuwan Rabiya ya katsesu da kukanta tazo.

Jamila ta duba tace ''Jamila kece baƙuwa
gobe war haka mun bani.

Zuwan Sarki Safwan bala'i ne da musifa.
Bai da imani ko misƙala zarratin sannan
zuwan shi abune me nuni da sabon Ʌeq́s da zai kunno.

Sai ya gama azabtar damu matanmu da mazanmmu sannan ya ɓullo da mugunwe ƙuḍirin dake danƙare a zuciyarsa

Lokaci yayi da zamu sami yancin kai.
Tin ina ƴar shekara 10yrs aka ɗauƙoni.

A ƙallah na share shekara 20yr anan ḄAƘAR MASARAUTA har na fitar da rai da rayuwar ƴanci na fitar da rai da sake farinciki nasan ada ina cikin gata ina da uwa da uba, amma a halin yanzu ko na fita bansan taya zan sake tozali da iyayena ba, bansan hanyar da zanbi in gano su ba. Kullum zaluncin srki Safwan ƙara ƙamari yake.

Mukasshifiyya tace.
''Rabiya kenan duk wannan zantukan nasan dasu, kawai

2 / 7