ABDUL_MALEEK by miss'Deejarh

Author :  miss'Deejarh Category :  Romance

Chapter   27 / 37

78K to 81K   out of 109K words

kuzarinta na k'ok'arin turesu domin ku6tar kai.
Ina mutumin naku baiko saurara mataba Dan tuni jikinsa da ruhinsa sun Lula duniyar begen aika aikar dayakeyi, da zafifi yake aikamata sak'wannin soyayyarsa, kafin tafarga yad'auki hanyar mallakarta daga ita har zuciyarta Dan tuni itama tabada kai dukda d'unbin tsoro da fargaba dasuka kanainaye ilahinrin lungun da sak'on zuciyarta.

_Hummm masu karatu nima bara naja camryn 🚶🏻‍♀k'afafuna nanufi wajen angona kuma sarkina mamallakin zuciyarta da ruhina_ *_{Abdus'salam)_* d'ina adon zuciyata😘😂.


_washe gari_
Hummm yaukam na iso amakare Dan natarar har Rahma tagama tsaftace ko ina na gidan, takuma had'a breakfast mairai da lafiya.
Zaune na isakesu a dinning suna karyawa, Rahma da bobo dasun had'a ido saisu sakarma juna murmushi, bobo kam harda d'aga mata gira, takan kauda kai tana murmushi Dan gudun kar Nawal tafahimci wainar da suke toyawa.
Bayan sunci sun k'oshi suka mik'ewa tareda yin hamdala ga sarkin sarakuna mai k'yauta da k'ari.
Bobo yad'auki jakar aikinsa ya rataya, yaukam sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi, Wanda akaima ado da bak'in zare, rigar dakad'an tawuce d'uwawunsa amma yayi d'as aciki kamar kazauna kayita kallonsa,
_Hummm karkuma ka kalla k'ilu tajawo bau, Rahma ta ce, "kana kalan mata miji🤥, my Xoxo ki kalleshi kad'an keda Rano_o😎.
Rahma tasakama Nawal jakarta abaya sannan tad'auki d'an kwandon abincinta suka fito, itama Rahma sanye take da shadda ruwan k'asa mai turuwa zani da Riga, tasaka farin hijjabi har k'asa Asama.
Saida suka fara sauke Nawal a school sannan Bobo yad'auki hanyar gidan Appa.
Juyowa yayi ya kalleta hayateena awajefa zan saukeki dannayi latti.
Itama kallonsa tayi sannan ta kalli agogon motar ta ce, " k'arfe 7:34am yanzu".
Eh nasani, sonake naje office dawuri yau, nayi duk aikin dazanyi zuwa 4 nadawo gida mukasance tare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, ALLAH kana bani kunya.
Murmushi yayi idonsa atiti ya ce, "tom nadaina baki kunya Nusfulhayat d'ina mai kuka, yaya Dan ALLAH kabini ahankali, daddyn Nawal wlhy yauma a kwai zafi, wayyo ummina kizo ki cecen...........
Bata bari yak'arasaba tasaka MASA kukan shagwa6a.
Ohh sorry my cute nadaina fad'a, cikin dariyar shak'iyanci yay maganar.
Maigadi yabud'e masa gate yashiga, ko gama tsayawa da motar baiyiba tafice tayi cikin gida.
Binta kawai yayi da kallo yana murmushi, afili ya ce, "wato idan ka auri yarinya k'arama tana maka ta6ara kaima saika zama ta6ararre, ya shafa sajensa daya kwanta luf, yad'an lumshe ido yana fad'in ALLAH yak'arama ANNABI daraja da fadila da Wasila.
Rahma kin mallake *_Barrister Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i_* gaba d'ayansa da komai nasa, kin mantar dani damuwata gabad'aya, ya ALLAH kak'ara mana soyayyar juna, kakuma nisanta shaid'an daga garemu.

Na ce, " Ameen bobon Rahma.

Fitowa yay shima yanufi cikin gidan, babu kowa afalon sai kamshi dake tashi da sanyin AC.
Shiru yay atsaye yana nazarin gidan, sallamar Baba hansai mai Aiki yasakashi juyowa, ta ce, "a'a Alhaji kaine agidan.
Murmushi yamata sannan yarisina ya gaisheta, baba hansai masu gidan basu tashi bane?.
Khairiyya da khursiyya sun tashi tun d'azu, amma banga Ammi ba gsky.
Okey bara to nawuce office kawai saina dawo.
To Alhaji bazakaci komai bane?.
Ahhh baba nidanake da mata, ai tuni nafita agandu.
Dariyar jin dad'i baba hansai tayi, ta ce, " to madallah Alhaji, ina Nawal da mamanta?.
Nawal na makaranta, mamanta kam tana nan cikin tare mukazo, kud'i yazaro a aljihu yamik'a mata yafice.
Itakuwa tarakashi da k'yawawan addu'oi.

Rahma kam koda tashigo taga falon babu kowa saita wuce d'akinsu khursiyya, cikeda ihun murnar ganinta suka tashi suka ruk'unk'umeta, akan gado suka zube suna dariya.
Daga nan hira suka farayi.
fitar bobo badad'ewa safna tafito daga bayi, dama tana wanka sanda Rahma tashigo.
Rahma ta gaisheta, da k'yar ta amsa, itakam batabi takantaba Dan abunda su khairiyya suke nuna mata ya d'auke hankalinta.
Khursiyya ta ce, "aunty Rahma wai waya kawokine?."
Ya Abdulmaleek mana Rahma tafad'a tana dariya.
Kai yana ina?.
Inaga yakoma Dan yace dama bazai shigoba sauri yakeyi.
Ajiyar zuciya Safna ta sauke aranta ta ce, "yagama guje gujensa yazo yasameni daram.
Sudai su Khairiyya dabasusan tanayibama hirarsu suketa zugawa suna kwasar dariya kamar wasu k'awaye.................




*_💃🏻Taka rawar gani akalla kome kayi kanka duniyace, mai jimirin zama cikinta, shike zuga kansa d'an magori._*

(zancenka haka yake nura m inuwa😎).











*_luv u oll_*
*_(((S)))........2017_*

👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
🅱🅾🅱🅾


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_yau gaisuwar da shafin duk nakune sister Fertymerh xarah & Nafi Anka, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, bilyn Abdul na gaisheku tareda bobon Rahma._*
_I Luv you manya manya😘😂_
6⃣2⃣

Sai wajen k'arfe biyar su bobo suka dawo gidan, kamar had'in baki suka dawo kusan lokaci d'aya suduka hud'un, bayan kowa yafito daga motarsa suka gaisa cikeda k'aunar juna.
Ya Hamza ya ce, "lallai gida yafara kar6ar bak'i irin wannan hayaniya.
Dariya sukayi gabad'aya, ya ishaq ya ce, " tokumu k'arasa ciki..
Cikin falon suka nufa suna 'Yar hirarsu da dariya.

Na ce, "masha ALLAH, biki ya kankama Dan falon yad'an cika da bak'i wad'anda suka iso yau, ga hayaniyar yaransu ya ishaq daketa wasa da yara sa'anninisu bak'i.

Su bobo suka rissina suna kwasar gaisuwa, kowa kallonsu yake cikeda sha'awa, bayan gaisuwa aka ta6a 'Yar hira da tsokanar juna, shidai bobo banda murmushi babu abinda ya iya, dama haka yake ko tsokanarsa kakanni sukeyi iyakarsa murmushi, amma baya iya maida murtani, saidai 'yan uwansa idan suna kusa su kare masa.
Yanzuma wata 'Yar tsohuwa ke tsokanarsa, ta ce, " mai sunan Alhaji wai kaidai kana nan babu canji?, maganama wahala take maka bare dariya?.
Nanma murmishi kawai bobo yayi kamar yanda yasaba baice komaiba.
Ya sulaiman ya ce, "Hajiya iya aii maganar Abdulmaleek tsada gareta saikin saya da kud'i.
Yo sule mizanyi da maganarsa nikam barema na siya, wannan sai matarsa dai amma baniba.
Dariya suka saka gabad'aya falon.
Bobo Yakama gemunsa nagayu yana shafawa fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik'e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, " Hajiya iya kinga kin koreshi?.
Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k'irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund'un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi.
Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik'e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund'un Dunkum! Kana inane?.
Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak'i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke.
Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d'akin suna dariya dacigaba dakiran dund'un Dunkum.
Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund'un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?.
Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, "halan faratun tsohurcan ce tafad'i sunan nan?.
Ammi dake k'unshe bak'i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k'aniyarka wace faratun?..
Uhhhchch bobo yafad'a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi.
aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k'ara kai masa wani rankwashin.
Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak'i kamar wani k'aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi.
Sudai su ya hamza dariya suketa masa.
Ana cikin haka Appa yashigo d'akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska.
Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da 'yayanta?, Appa yafad'a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak'asan kafet ne zaune.
Bak'i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan.
Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?..
Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k'afafun Appa, yad'ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye.
Babana mikayi ake maka dariya haka?.
Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund'un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya 'Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo.
Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund'un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d'ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa.
d'agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad'a idan za'a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo.
Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai.
Ya sulaiman ya ce, "haba bobon Ammi garadai kafad'a anan komai ya wuce.
Hum'im ban yarda da wayonba a can zan fad'a dankuji ehe.
Kaga sulaiman barsa yafad'a d'in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad'a, muce INA yayansu Amarya Dund'un Dunkum.
Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a.
Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k'ok'arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d'azun sunajin diramar family d'in, kowa sai kunshe bak'i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik'eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d'akin.
Ya Hamza ya ce, "ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky.
K'asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya.
Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak'i da hannu, ba k'aramin birgesa tayiba.
Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k'aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba.
Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai.
Mik'ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje.
Appa ya ce, " a'a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k'aunar sirikan nasu masu kamala da dattako.
Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik'e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida.

Basu dawoba saida akayi isha'i.
Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik'o rigar bobo.
Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba.
Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, "sakarmin Riga.
Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika "alk'awari.
Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, " alk'awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata.
Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, "bobo kana wulak'antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k'iyayya tsakanina da 'Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina..... Takasa k'arasawa saboda kuka dayaci k'arfinta.
Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k'ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d'auketa.
Yad'an lumshe idanunsa yabud'e akanta, kinga tashi yafad'a cikin muryarsannan mai dad'i da amo.
Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta.

A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo.
A'a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq.
Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can.
Ammi ta ce, "Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar.
Akunyace Rahma tamik'e, zata fita Appa yafito shima daga d'akinsa, ya kallesu ya ce, " a'a INA mukarram d'in?.
Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi.
To Aida kun k'yalesa babu dad'i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad'iba malam salen, daga yau kar a k'ara haka kunji?.
Insha ALLAHU Appa baza'a sakeba suka had'a baki wajen fad'a.

Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad'owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?.
Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k'arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, "yana tareda baba suna hira awaje.
Appa ya ce, " kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin.
Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, "to Appa."
Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k'osar dashi, d'akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak'in ciki, jitake gaba d'aya yau tatsani bobo dakomai nasa.
Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak'e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa.
Ayya sannu yafita ko?.
Eh ya fita aii ruwa naita sakawa.
To sannu, muje muci abinci ko.
To kawai tace mata suka fito falon k'asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa.
Aunty Sameera ta ce, "a'a INA safna wai?.
Da sauri Rahma ta ce, " tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH.
Dariya sukayi gaba d'aya, aunty rasheeda ta ce, "wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak'i bobon mu, madai gani ko guy d'in nata yafishine haka?.
Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak'e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad'auki so ta d'ora masa ayanzun.
Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad'iba, amma jitake kamar tana cin magani.

Safna da bobo kam suna lambu zaune, bobo ya d'aure fuska kamar bai ta6a dariyaba Dan ganin yanda Safna takafeshi da idanu tamkar zata cinyeshi.
d'an tsaki yaja yana kauda kai daga kallinta, ke kinga inada abunyifa nazo nan nazauna, kuma matata banaso taduba bata ganniba Dan haka miye maganar taki?.
Dukda maganarsa ta 6atama safna rai, musamman dayace bayaso matarsa taduba taga bata nan amma saita danne ta matso hawaye tana shashshekar kuka.
Hannu ya d'aga mata, kinga ba kuka na tambayekiba fa malama.
Share hawayenta tayi, ta durkusa agabansa guywa ak'asa tana cigaba da hawaye, Abdulmaleek pls kasamo mana mafita, nidai nasan kaima kana sona, idan zaka iya daurewa wlhy ni bazan iya jurewa ba ka taimaki rayuwata karta salwanta akan sonka.
Wani murmushin mugunta bobo yayi, ya ce, "tabbas ina sonki amma so na 'yan uwantaka, irin Wanda nakema khursiyya da khairiyya.
So na gsky irin na soyayya da tsan tsan k'auna da begen juna, mai ratsa jijiya da ruhi da 6argo mutum d'aya tak nakemashi, itace Rahma, my Nusfulhayat d'ina, farin cikina uwar 'yayana, sarauniya mai sarautar dukkan zuciyata da duk abinda ke cikinta.
Safna kamar yanda na gaya miki wannan zaman shine zai zama zama na k'arshe tsakanina dake, kuma itace zata zama magana ta k'arshe tsakanina dake wadda ta danganci wannan, zan baki shawara kuma zan miki nasiha, idan kin d'auka kin huta, idan kin watsar ke wahala, nidai ALLAH yagani nafita hak'k'inki amatsayina na d'an uwanki musulmi.
Zamansa yagyara yana mai k'ara tattara nutsuwarsa waje d'aya.
Cikin murya mai nuna muhimmancin maganar dazaiyi ya ce, "Safna!.
d'agowa tayi tana kallonsa amma bata tankaba.

Ya ce, "Safna ina d'aga mini

27 / 37