ABDUL_MALEEK by miss'Deejarh

Author :  miss'Deejarh Category :  Romance

Chapter   26 / 37

75K to 78K   out of 109K words

sauri yabar gidan Dan bayason tambaya, musammanma akan safnar.
Cak ya sulaiman ya tsaya yabi motar da kallo har bobo yafice daga gidan, kallonsa yadawo dashi akan Safna dake ida share hawayenta.
Rissinawa tayi tana gaisheshi sannan tara6a ta gefensa zata wuce.
Jimana ya sulaiman yafad'i yana kallonta.
Safna tatsaya harya k'araso gabanta suna fuskantar juna, lfy kuwa mike faruwa?.
Babu komai safna tayi magana muryarta nad'an rawa, shiru ya sulaiman yay yana kallonta da nazarin yanayinta, yad'an gyara tsayuwarsa yana sauke numgashi, ya ce, "keba yayar Rahma bace?.
Yayartace, cewar Safna.
To amma miya had'aki da Abdulmaleek? har kike kuka?.
d'ago ido tayi ta kalleshi, bazata iya kallon idonsaba Dan yana mata kamada na bobo, tayi shiru batareda ta iya cewa komaiba.
Ganin bazatayi maganaba ya ce, " to shiga cikin....
Da sauri tawuce batareda ko juyowaba.
Shima binta yayi da kallo cikin mamakin miye tsakaninta da bobo?, bai zargi komaiba Dan yasan bobo dodon matane, bazai ta6a zarginsa da fasik'anciba, amma tabbas akwai wata ak'asa tunda har bobo yafice daga gidan Dan bayaso suyi magana.
Yabud'e motarsa yashiga zuciyarsa cike da waswasi, shima ficewa yayi da zummar zai tambayi bobo inhar sun had'u.

++++++++++
a6angaren bobo kam yana fita office yanufa kai tsaye.
Sakatariyarsa ta gaishesa cikeda salo kamar yanda ta saba, babu k'arya yau wankan bobo yakasheta, datanada dama har pic zata masa.
Turare tad'auka tafesa tareda k'ara kallon kanta amadubi, komai daidai, tagyara zaman siket d'in material d'inta da rigar, shima mayafin aka sake salon yafawa sannan. Tanufi office d'in.
Masinja Kamilu dake la6e yana kallonta Dan yasan dolene indai oga yashigo saitayi gyare gyarennan ya tuntsure da dariya yana fad'in kai iska na wahalar da maikayan kara, kedai awahala zaki k'are yarinya, mutum kamar wannan aii kasan matarsama abar kalloce, tomizai tsaya kallo ajikinki wannan karfata.
Itadai Sakatariya Madeena๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜œ dabatasan masija nayiba tanufi office d'in cikin takun k'asaita da salon yanga irinta d'aukar hankali.
Bobo na zaune akan kujerarsa ta alfarma yana rubuce rubuce sakatariya tayi sallama.
Bai d'agoba amma ya amsa mata, yad'ora dafad'in waye yazo nemana?.
Lissafa masa tafarayi daga k'arshe ta ce, "ad'arare sai Alhaji sunusi da la..
Tak'are maganar da in ina.
Dukda haka bai d'agoba sannan baice komaiba itakuma baice tatafiba.

Araina na ce, " mulki kenan."

Yakai kusan minti 4 yana rubuce rubucensa saida yagama sannan yad'ago yana linke takardar.
Mik'a mata yayi, tamatso tareda rissinawa takar6a.
Yamaida bayansa yakwantar ajikin kujerarsa yana d'an lilawa kad'an, idonsa akanta ya ce, ke yanzu dakikayi shigar mutunci bakijin kinfi kima a idon mutane ba?, amma da ko kunya bak'yaji kisakko kananun kaya kina tallar jikinki ga jama'ar gari da sunan wayewa, wannan ba wayewa bace shashancine, ki kama kanki sai miji nagari yaganki yasoki, shigar banza babu abinda yake jawomuku sai mazan banza suyita bibiyarku dankoba 'yan iskanbane tofa kallon 'yan iska irinsu suke muku, ki kiyaye banason shashanci.
Kaita gyad'a duk kuma sai jikinta yayi sanyi, ta ce, "sir ngd ALLAH yak'ara girma da d'aukaka yatsareka daga sharrin mak'iya.
To amin, ALLAH yasa mudace yafad'a yana d'agowa daga kwanciyar dayayi akujera, yanuna takardar hannunta, wannan takardar kibama Kamilu yakai office d'in Barrister Kamal Abubakar, yatsaya yakaranta yabasshi Reply yakawo min.
Okey sir madeena sakatariya yafad'a tanad'an rissinawa cikeda girmamawa.
Hartakai k'ofa tajuyo sir baka buk'atar wani Abu?.
Kai bobo ya girgiza mata yana jawo laptop d'insa daga cikin jakka.
Itama ficewa tayi tana fad'in OK sir.

Tana fita ta tararda Kamilu zaune akujerar dake gefen tebir d'inta, fuska ta had'e dantasan gulmace ta kawoshi.
Ilaikuwa kallonta yayi yana 'Yar dariya, madee ince dai yau andace oga ya k'yasa?.
Harararsa tayi tareda fad'in ban saniba magananne ni dalla kar6i oga ya ce, " ka kaima sir Kamal, kuma kajira yabaka Reply ka kawo masa.
Mik'ewa yayi yakar6i takardar, to madee bara naje nadawo muyi magana, tunda har yanzu oga yak'i k'yasawa nisaina taya.
Wata uwar harara tawatsa masa, kaidai shashashane Kamilu, yoko mazan duniya sun k'are aibanga abinda zanyi da sakaren namiji irinkaba.
Tab yarinya aii ba'a fuska ake gane sakaran namijiba.
Tsaki tayi tareda mik'ewa wlhy zanje nafad'ama oga baka tafiba.
Da sauri yawuce a'a Madeena rufamin asiri Dan ALLAH, wannan zakin faman yanzu saiya hau kaina aii.
raka bayansa tayi da harara, taja tsaki tazauna tana mita.

Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar yasashi d'aukar wayar da hanzari, gaisawa sukayi tareda tsokanar juna kamar yanda suka saba.
Bobo ya ce, "dama kobaka kiraniba zan kiraka.
To miya faru angon Rahma?.
Murmushi bobo yayi, ya ce, " so inaga anjima zanshigo gidan saimuyi magana atsanake yanzu time d'ina k'urarrene nanda 'yan mintuna kad'an zanshiga wata shari'a.
Okey babu damuwa to saina ganka, nima inada ganawa da Governor nanda minti 10.
Hummm mutumina kuna sha'aninkufa, idan kukayi wasa duk ad'aure zakuje lahira Dan daku ake mulkarmu ak'asarnan.
Dariya Ammar yayi ya ce, "masheranci aii kaima ad'auren zakaje indai hakane.
Can abakinka d'an fatan tsiya sai anjima.
Yanke wayar sukayi suduka suna dariya.
Harzai ajiye wayar saikuma yafasa yakira Rahma.
Tana zaune afalo ita kad'ai tana kallon wani India film, takalli wayarta dake wringing, ganin sunan dake a screen d'in yasakata murmushi, *_Nurulk'albee_*, d'auka tayi muryarta can k'asan mak'oshi tace amincin ALLAH ya tabbata agareka ya *_Nurulk'albee._*
Wata sassanyar ajiyar zuciya bobo yasauke, murya akasalance ya ce, " kema amincin ALLAH ya tabbata agareki my *_Nusfulhayat_*. Ina fata kina cikin k'oshin lafiya da kuzari?.
Alhmdllh sai godiyar ALLAH kam.
Wani k'asaitaccen murmushi yasaki Wanda hartanajin sautinsa akunnenta, ya ce, "nagodema ALLAH da kika kasance cikin k'oshin lfy, kinga kenan yau za'a kar6e ni 100/100 abani kulawa ta musamman awajen barci.
Kamar tana gabansa tafara buga k'afafu cikin shagwa6a ta ce, " nidai a'a wlhy inajin tsoro kuma har yanzu wajen akwai zafi.
Yanda take masa magana cikin shagwa6a yasaka jikinsa yin sanyi, k'ara lafewa yayi acikin kujerar yana shak'ar kamshin turarensa dana office d'in, yakuma narke murya can k'asan mak'oshi haba my Angel kedai kincika tsorone kawai, amma yau kwana hud'u ace haryau anajin zafi?, kodai ana gudunane?.
Hannu tasaka tarufe fuska wai ita kunya kamar tana gabansan, nidai Dan ALLAH kabarmin wannan maganar banaso.
'Yar sassanyar dariya yayi harda shashsheka wadda tasaka Rahma shagala tana saurarensa, ya ce, "shikenan idan nadawo gida zamuyi aii, kafinma nadawo kisaka d'iyarki tayi barci, ummuch๐Ÿ’‹ yamannama wayar kiss, batareda yajira amsartaba ya yanke Kiran.
Lumshe ido Rahma tayi tana murmushi, afili ta ce, ''kai maza sai'a barsu sudai ko kunya basaji?.
Shimadai a can murmushi yayi, yamik'e yana had'a takardu, yad'auki k'atuwar rigarsu ta lauyoyi tareda hular yarik'e sannan yad'akko siririn farin Gil's d'insa yasaka yafice domin gabatar da shari'a...............











*_luv you oll_*.
*_(((S))).........2017_*

๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿ’ปtyping........

โฃ *_ABDUL-MALEEK_*โฃ
_โ€ข{๐Ÿ…ฑ๐Ÿ…พ๐Ÿ…ฑ๐Ÿ…พ}โ€ข_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_masu karatu bara namuku gulmar Xoxo da 'Yar ficika,๐Ÿ˜Ž hummm Xoxo cedai Xoxo cedai da Yar Ficika, saimukaje gidan Hafsat Rano aka kawo mana gasashshiyar kaza da lemo๐Ÿ—๐Ÿน๐Ÿพhummm ina gaya mukudai, shikenan dai shikenan dai, sai.....๐Ÿ™Šum bara nayi shiru kar zarah Bukar da hajja sufad'a musu gobe su sassambad'i k'eyata alungu๐ŸŒ, kekuma Rano saura kifad'a eheโ™€๐Ÿ˜._*
_๐Ÿ˜‚luv you so much, my sweet sisters, Hafsat xoxo, Hafsat Rano, 'Yar Ficika & Zarah Bukar, hajjace, Ayusha ilyasu, gaisuwa agareku dafatan Alkairi._
๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ.

6โƒฃ1โƒฃ

*_5:12pm_* bobo yamik'e tareda harhad'a takardun dazai buk'ata agida, yacire laptop d'imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had'a komai yakashe kayan wutar office d'in sannan yad'auki rigarsa ta lauyoyi ya sak'ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad'a yafito.
Da sauri Kamilu yataso yana fad'in oga kafito?.
Nafito kamilu, zan wuce gida kuma.
Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d'in hannun bobo ya kulle k'ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k'arfe hud'u da rabi yake sallamarta ita.
Saida yashiga motar sannan yad'ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine.
Dariya Kamilu yayi yabud'e mortar yashiga yana fad'in oga ai damunar tafara kankamane, nanda 'yan satittika zakaga ruwa yafara wadata.
Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k'arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin k'ira'ar shriek Abdurrahaman sudes, har k'ofar gida yakai Kamilu yamik'a masa kud'i yana fad'in gashi asaima uwargida kaza.
Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k'ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k'yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa.
Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki.
Ganin hadarin nak'ara tasowa yasaka bobo k'ara gudun motarsa cikin 'yan mintuna k'alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi.
Rahma tana kichin Dan k'ok'arin had'a abincin dare taji ana kwankwasa k'ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan.
Batayi gaggawar bud'ewaba saida ta ce, "wayene?.
Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak'e murya kamar mace ya ce, " nice hafsat Xoxo budurwar bobo.
Gabantane yafad'i gakuma wani k'ululn bak'inciki aranta, cikin masifa ta ce, "ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo.
Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik'ani.
Yo ya kasheki mana, Rahma tafad'a ak'ufule tareda juyawarta kicin.
Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik'ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k'ofar kichin abud'e take ta baya, yana turawa tabud'e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi.
Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad'an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo.
Dariya tabashi danganin kishi k'uru k'uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, " yawwa.
K'arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi.
Lfy kuwa?, naganki haka?.
Lfy lau tafad'a tana nufar cikin falo.
Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d'insa yayi danta d'an jike yaja kujerar dake kicind'in ya zauna yana cire takalminsa.
Rahma tadawo kichind'in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d'agoba saida yagama cire takalmin yad'ora k'afarsa fara Sol Asama.
Rahma ta ce, "azuciyarta, hummm jik'afa kamar ba'a takata ak'asa........
Bobo yad'ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin ak'ofar falo tsaye kamar mace?.
Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba.
Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?.
Hawayen datake mak'alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, " bakai tazo nemaba, kuma ta ce, "budurwarkace ita.
Yaso ya shek'e da dariya amma saiya dake, yamik'e da Sauri yana fad'in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin 'yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon.
Rahma taduk'e kanta ajikin cabinet d'in kicin tana kuka.
Shikam bobo d'akinsa yanufa yana 'Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad'a wanka.
Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad'ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind'in tsaf.
Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d'akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k'arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa.......hummm ni shinema yau ko ruwan ba'a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta.
Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad'in my papa oyoyo.
Shima d'aukarta yayi yad'aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?.
Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi.
Oh 'yargatan momynta yafad'a yana sumbatar kumatun yarinyar.
Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha'awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad'agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad'an murgud'a baki.
Ya ce, "Niko?.
Nidaifa banceba ehe, itama tafad'a kamar badashi takeba.
Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani.
Da d'an gudu Rahma taje gaban firij tad'akko ruwa da cup takawo MASA.
Bobo yayi dariya tareda fad'in ashedai ana tsoron kishiya.
Gaba tayi tashige d'akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya.
Nawal ta CE, " papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya.
Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, "jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki.
d'akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud'e sannan yad'an lek'a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak'ura yajuya d'akin Rahma dansuyi jam'i.
Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid'ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi.
Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam'in magriba.
Bayan sun idar Rahma ta d'akko alkur'ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad'i, har lokacin sallar isha'i yayi suka mik'e domin gabatarwa.
Saida yamusu doguwar addu'a sannan kowa yamik'e suka fito falo.
Bobo yazube saman kujera yana fad'in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?.
A'a baby nagajine kawai....... ga abinci fa....Rahma takatse musu zancen tana kallonsu.
Fararen idanunsa yad'ago yana mata wani shu'umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki.
Nawal tamik'e shikuma ya ce, "nidai nagaji bazan iya hawan dining ba.
Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon.
Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, " kihad'amana a filet d'aya kawai, batace k'alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa.
Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, "guy d'innan komai yahad'a, cin abincinsama abin kallone.
Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali.
Tuni barci yad'auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d'auketa tamin barci ajiki.
Mik'ewa Rahma tayi domin d'aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik'e gam sannan yashiga k'ok'arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara.
Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d'alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, " wayyo bakina.
Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa.
Shinwai ni sa'ankine?.
Da sauri Rahma ta ce, "a'a dantaji zafin d'allar mata baki dayayi. Ya ce, " to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone.
Ayya my Angel sorry, namiki kamu?.
Kai tad'aga masa alamar eh.
Ahankali ya kwantar da ita acinyarsa, maimakon yamata kamunkai saitaji bakinsa akan nata, tabud'e baki zatayi magana yasamu damar zira harshensa......

๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€baya najuya musu karsuce nacika saka musu ido.
Saida aka d'auki tsawon lokaci sannan na juyo Dan inada tabbacin komai ya kammala.
Raham nagani tana cusa kanta acikin bobo suna dariya, da alama wani abun yafad'a mata taji kunya.
Ya ce, "kinga tashi muje mu kwanta, mik'ewa tayi cikin jin kunya, ta d'auki Nawal takai d'akinta, kayan barci ta canja mata itama ta canja, tana k'ok'arin hayewa gado saiga Bobo yashigo sanye cikin kayan barci shima.
Kallo d'aya tamasa ta kauda kai, shima baibi ta kantaba yamatsa kusada Nawal yamata kiss akumatu sannan yaja bargon yarufeta yana fad'in saida safe d'iyar albarka.
Itadai Rahma batace komaiba Dan harta kwanta agefen Nawal, jitayi anyi sama da ita, tafara wutsil wutsil da k'afafu wayyo ya Abdulmaleek kabarni barci nakeji, nidai yau bazanbar Nawal ita kad'aiba, pls kabarmu mu kwanta.
Bai sauraretaba har yakaita d'akinsa yadire agadon, tana k'ok'arin tashi yasa k'afa ya danneta, wayoyinsa yad'auka ya kashe sannan shima yahaye gadon yakwanta tareda jawota jikinsa.
Itakam tuni tafara kuka zuciyarta cike fal da tsoro, jin yafara mata abinda hankalinta bazai d'aukaba tafara kuka tana zame zame.
K'ara matseta yayi ajikinsa yana k'ara rud'a jikinta da sakwanni wad'anda sukeyin tasiri ajikinta da zuciyarta, amma

26 / 37